Soyayyanovels
Subul Da Baka Book 2 Complete Hausa Novel
Subul Da Baka Book 2 Complete Hausa Novel
By Sajida Niger
Login to keep your reading position saved.
Book Page Chapters
Subul Da Baka Book 2 Complete Hausa Novel

Subul Da Baka Book 2 Complete Hausa Novel

Author: Sajida Niger
Chapter 7 of 11
About 8 min read
Chapter progress: 0%
Listen Mode
Listen to this chapter using your device voice.
Ready to listen from this chapter.

Book chapters

Choose a chapter and continue reading.

Start chapters

Subul da baka 2 page 2 Posted by ANaM Dorayi on 07:12 AM, 21-May-15 Under: Subul da Baka kuma akace damu za a tafi wallahi yau yau dinnan na dawo wanka kawai nayi don na cika alkawarin dana daukarwa.. Da sauri na kalleta' se kuma na sunkuyar da kaina kasa. Ta fiddo doguwar takarda tace: "Gashi yace dan Allah kada kiyi kuka' kiyi masa wannan alkawarin" Murmushi kawai nayi idona ya ciko da kwallo' tayi saurin kawar da fuskarta'sannan ta kara mikomin takarda ambulan doguwa. Ta mike' zan tafi akwai labari' amma se zuwa jibi idan na dawo' gobe zanje Karkasara shi yasa. Nayi murmushi tare da mikewa na rakata' rakiya mai nisa har kusan lungun gidansu sannan na koma. inna nacan tana wanke waken awarar gobe' su Aisha na taya ta na shiga dakia kagare inji takardar abinda ta kunsa' haka kawai jikina ya ba ni maganace mai dauke da kwanciyar hankali domin na tabbatar yana sane da halin da na shiga. Tun kafin na fara karantawa na qurawa rubutun ido, yadda yayi shi wara wara yaddazan fahimta, nace "Bismillla" "Gimbiya Humaira" Na runtse ido ina sauraton yanayin furtakalmar acan baya da yayi' wanda ya kasancemasa tamkar" SUBUL DA BAKA" "ina roqonki da girman Allah ki daure ki cije kada kiyi ma rubutunnan kuka, kiyi mini wannan alfarmar please! Humaira ba se na fada miki ba na tabbata kin fahinci kaunar da nake miki, na da de ina mafarkin samun macen da nake muradi kafin Allah ya hadani dake, amma rashin sa'a se muka sami banbancin ra'ayi damahaifina. Nayi duk iya kokarina in tallabomatsalar amma abu ya faskaradomin yayimini FURUCIN dana tsorata da shi, furucin daya tsoratani kuma ya firgitani. Don haka ina rokonki kiyi hakuri mu dauki abin nan kaddara duk da na fahimci cewa ni ban kwanta maki arai ba humaira bana son farida bana kaunarta wannan cutar kadai xata galabaitar dani soyayyarki kuma takaini lahira mu yafewa juna domin gobe xamu bar kasar nan xuwa australia a can xamu xauna dindindin inji sarki harsai bayan ransa in dawo in karbi sarauta ga cheque dina nan na banki duk nayi signing ki rinka fidda kudi kuma ki koma makaranta idan xakiyi aure ayi miki kayan daki insha Allahu xan kawo maki xiyara anytime. Kuka y hananani karasawa nayi nayi kamar raina xai fita inna ta shigo da sauri tana salati dakyar na bayyana mata wani abun shiru tayi tare da ficewa waje amma a zihiri na ga ranta ya baci bata yi mini maganar ba sai da daddare ina zaune saman abin sallah na hade kaina da guiwa cikin wani yanayi idanuna ina jin su tamkar garwashin wuta kirjina kuwa kamar an dora man dutsen dala Humaira inna ta kira sunana Na amsa naam murya ta kasa kasa Yanzu kinfi son ganin tunon asirin rayuwan mu akan rufuwan sa Nayi shuru ban amsa ba Ashe ba zaki hkr ba? Kwalla suka zubo mani nace wlh inna ba wannan ne damuwa ta Na bata lbrn takardar da aka kawo mun da abunda amira tazo man dashi ta harzuka to ina abunda ya dame ki dasu bance ki manta ba kuma nima ba zan taba mantawa dashi ba amma wlh ki cire maganar soyayya Yafi karifin ki humaira ba mijinki bane kiyi nesa da soyayyar wahala idan kika kuskure sai gimbiya tafiki kwanciyar hankali nayi saurin kai kaina kasa ina sujjada "Ya Allah kana ji Allah ka yi mini maganin matsala ta Allah kai ka haifar soyayya a zukatan mu Allah kayi magana maganin ta bayan kwana 2 inna tace gaskiya nima na goyi bayan ki koma makaranta amma baxamu taba kudinsa ba Sbd haka saimu shirya gobe muje Govt college muji idan zasu mai daki. Hakan kuw akayi ga mmkina aka sakani SS3 kuma saura 3mnths suyi exams na dage da karatu wanda rabinsa tunani ne. Dr ibrhm kuwa tun ina shareshi harna fara sakin jiki dashi sbd fadan inna kada nayi saki na dafe a dinga nunani nayi kwantai har an fara min shaidar me kudi nakeso, Inna ta buga tsaki sannan kiyi kaffa kaffa da masu zuwa wurin ki domin iyayen ki sunyi mugun kudiri akan ki maganar karatu kuma sun ce basu amince ba matukar kika ci. Gaba da zuwa wlh komai suka yi miki don kanki Ko don ina cikin damuwa? Sai maganar bata wani dame ni ba idan Allah ya nufe ni da ilimin bokon nan na tabbatar da kudin da ya bamu zasu ishe mu har zuwa wani lokaci ko da bamu sanaa balle ma muna awara ga cek bayan sati 2 na dayaye dr ibrahim yaci gaba da zuwa kusan kullun kwatsam rannan yazo ya ce zai tafi karo karatu an tura shi singapore kuma shekaru 4 zai yi inna ta nisa ta ce to Allah ya tabbatar da alkhairi amin ya fidda sabuwan waya mai kyau da tsada ya bani yace inna ga wannan zamu rinka gaisawa kusan kullun don Allah tace to bata angode kawai raina ya baci watau ya tabbata inna bata son tunda kiri kiri ta hana ya bani waya ya miko mani dalleliyar blackberry sabuwa dal na amsa fuskata babu yabo ba fallasa, Inna ta hararoni nayi kmr ban gani ba yana fiata ta jefoni da murfin kwano zaki bishi kuyi bankwana ko kuwa? Na mike idanuna cike da kwalla na bishi yana tsaye jikin katanga ya hada kaida bango mostina kawai yaji da alama ni din yake bukatar gani yayi saurin dagowa idanunsa sun dan yi ja abnd ban taba gani ba nayi saurin kauda kaina sbd wani abu da naji yana bakuntar zuciata ya dubeni yace humaira zan tafi amma bakin cikina bansami wata kwakkwarar amsa daga wurinki ba. Jikina yayi sanyi zuciata tayi kunci haka kawai nakasa fahimtar abnd ke damuna. Ya kara kwantar da murya na kasance ma'abocin son zama da mace kwaya 1 a rayuwata amma burina ya rushe lokacin da nayi katari da matar da muka sami babbancin akida. Wllh humaira ba don ina kaunarki nake kushe matata ba na rantse miki banajin dadinta ko alama. Kadan daga cikin abnd tayi min kuma shine mafi karanci data mari mahaifiyata agabana...... Da sauri na kalleshi yayi murmushi irin na takaici yace kuma ta hanani na saketa, ki taimakeni ki sanar dani matsayina a wurinki wllh humaira bazan taba wulakantaki ba magnrki taje ko ina a danginmu mamana kullum sai tayi zancenki babana kuma ya rasu. Kuma nayi promise bazan hadaku gida 1 ko unguwa 1 ba believe me humaira pls. Tunani yazo min idan nayiwa ibrhm wulakanci koban amsa masa ba banyiwa kaina ba kuwa? Wa nake jira wa kuma nake dashi a hannu? Idan har abnd yake fada gsky ne ai nayi dace amma matsalr nayita jira har 4yrs? Kamr ya karanci zuciata naji yace kada kiji nace 4yrs ki dauka ko zaki ta zaman zuwana ne a'a ISA duk year zan dinga zuwa inaso ki tabbtr min da mgnta ne ni kuma a yau din nan zan gabatar da maganata zan bar komai in yaso da nazo hutu ayi biki idan da hali mu tafi tare if nt saina barwa broda na komai daga baya sai ki bini idan kuma kina ganin akwai matsala donAllah ki sanar dani. Nayi shiru ina nazari shin idan nace baiyi min ba wa zai min a dunia? Ko haka zan zauna ba wan ba kanin? Kirjina yayi min nauyi idanuna suka ciko da kwalla har yaushe zan manta da yarima a rayuwata? Ko in baki tym muyi magana a waya? Nayi saurin daga kai na alamar eh. Yayi murmushi to shikenn sai munyi magana. Na daure nace Allah ya kiyaye ya bada sa'a. Yanayinsa ya nuna min yaji dadi nagode humaira thank U so much for ur prayers, na yi murmushi na juya na shiga gida. Ko zama banyi ba inna ta hau fada wllh humaira banajin dadin halayenki da kika tsira har yaushe zaki daina tunanin yarima a rayuwarki? Wllh inna ni..... Zaki kaffara don kin isa yinta kibar rantsuawa. Wannan kunge-kungen da kikeyiwa wann bawan Allahn na menene? Kwata kwata kin daina sauraron kowa, wallahi kiyi nesa da kanki, iyayenki sun hanaki karatu saboda wata manufa tasu daban, shin auren kuma sai kihana kanki wanda shine mutumcin kowace ya mace? Humaira asirinmu kike son tonawa? Kin mance abinda mahaifinki ya fada akan soyayyarku? Gabana ya fadi saboda yanayin yadda naji inna tayi maganar kamar zatayi kuka. Kinyi dai dai, kuma Allah yabaki sa'ar kin sauraron ibrahim, yaron arziki bna ki tunanin Allah ne yakawo miki madadin....? Tunda shima gwargwado yanada kyawunsa? Ilimin nan yana dashi, sannan ga arzikinsa na rufin asiri? Anya ba maganar mutane bane Humaira kwadayi ke fizgarki ba? Haba inna..... Rufe mini baki mara kunya to me kike nufi in ba kwadayin SARAUTA ba? Ga babanki Auwalu can yadauki alwashin sai ya cusa mana bakin ciki ni da ke, bansan abinda yake nufi ba, yana korafin jin zafin yayansa na auren masu kudi, shiyasa kike wannan sakarcin, to yasan maganinmu. Ko dan wannan ma bakya yiwa kanki fada ba? Kiyi fatan Allah ya baki nagari mai kaunarki da danginki.. Ta kawar da fuska amma ba komai kije kiyi abinda kika ga dama.. Na sauko kasa, Inna kiyi hakuri, in sha Allah zan sanar da Ibrahim cewa na amince da shi... Da sauri ta kalleni to shikenan ya wuce Allah yamana jagora nace amin... Kwalla suka zubo min narasa na menene ni kuma haka Allah ya taaro mini rayuwa?? Baniga karaty baniga aure tunda shi Ibrahim......koda yake yace idan nayarda zai dawo a yi biki. Sallamar yaro muka ji inna tace ya shigo. Wai humaira ta zo anbugo mata waya daga kasar waje Ina jin haka na miqe zumbur na . gane ameera ce. Ya miqo man lokacin da muka isa nida aisha. Na koma gefen shagon kusada bedi na kanga a kunne 'Hello' amira kun isa lafia? Lafia qalau, baki lafia ne naji muranki kamar kinyi kuka? Na girgiza kaina kamar tana kallona, lafiata lau ina fama da mura ne. Nima kuwa nayi waya. Don Allah? Ta fada tana murna. Walhi kuwa zan sanya a turo maki lambar se mu dinga magana da tawa. Yauwa to yayi kyau nagode.nace nima nagode qawata se na kiraki. Haba yaya me

End of Chapter 7Continue to the next chapter or choose another story below.

More Hausa novels

Browse all books →
Previous Login to Save Next