Subul Da Baka Book 2 Complete Hausa Novel
Book chapters
Choose a chapter and continue reading.
da kaina na kassara abnd ke zuciaya wanda ya bakunceni yanzun nan. Abin haushi wai jakadiya na zuwa saita rangada guda wllh nan da nan mata suka cika dakin a ka ciccibi gimbiya wasu sukayi toilet da ita tana uban ihun zafi wasu kuma suka yaye zanin gadon sukayi fada dashi. In takaice kiki har dinki akayi mata yaji mata ciwo sosai saida tayi jinyar sati w tun daga ranar ina kula ko kallon arziki bata samu daga gurinsa. Bayan 2wks yana zaune falo mun kawo masa b/ fast yana rike da waya a hannunsa kullum haka yakeyi a she pic dinki ne ajiki yake kallo kwatsam saiga gimbiya wllh humaira idan ni yayiwa wann wulakancin ko shine autan maza na hakura dashi. Amma don rashin zuciya irin na gimbiya daga fitowarta ko kunyar mu bata ji ta ta haye kan cinyarsa tana wani kissa aiko karaf idon ta ya kai akan wayar shi tayi sama da wayar tana surfa uwar ashar tana zazzaga bala'I wai me kake nufi dani ne ko an gaya maka abinci kawai nazo ci? Kin ji fa wato ita bata ji haushin abunda ya mata ba har wani neman shi take yi Wannan yar iskan kenan bata kyale ka ba har yanzu. To wlh ga mai marta ba zan kai ka kuma shi zan ba wayar ai bata karasa ba yayi kukan kura ya amshe wayar shi ta harziko sai kawai ta fara zagin sa banza dan talaka wanda bai gaji arziki ba wanda suka yiwa sarauta haye ai da bamu san asalin angulu ba duk abunda kayi babu mamaki tunda sarautar BORE ce kuma hakkina da kake tauye man Allah ya isa..... Bata karasa ba ya juyo ya kalle mu yace duk mu fita wlh a. Falo ya. Kara yi mata wani wulakancin ya barta nan kwance yayi tafiyan shi ranar nida karima muka taimaka mata ta gasa jikin ta kamarna bata shawarar ita ma ta kyale shi mana sai kuma nayyi shuru a tunani na a tunda an kara na 2 bata bari a kara na 3 ba Bayan kwana 2 ya kira ni yace na kawo mashi tea ba madara da dankali. Na ttafi zan kai masa na ga gimbiya tace na bata wannan na hada mai wani (kiji neman. Dalili da rashin zuciya) ina cikin hada masa kashi na 2 ya shigo kicin din ganin ina aikin yasa bai yi magana ba amma da ganin shi ranshi ya baci kinsan halin mutumen naki. Da KASAITA Har ya juya zai tafi na yi sauri na duka nace *llah ya taimaka kayi mini gafara na hada maka zan kawo gimbiya ta amsa tace na hada maka wani ya yatsina fuska kamar yadda ya saba kafin yayi magana Kina iya bari na fasa maza kije ki shirya zamu je garin ku ki raka ni wurin kawar ki watakila dalilim zuwa dake ta saurareni wlh wlj humaira daga ni har shi bamu san gimbiya ta fito ba ashe jakadiya ta aika aka kira mata ta tura ta gun sarki a shaida masa abinda yake shirin yi Tayi shigewarta daki na fiti a shirye yana zaune a falo yana shirin mikewa kenan aka turo kiransa a fada nazauna a saman kujera dogari ya kalle ni ya ce harda ke ma yar rakiyan yake kira gabana ya fadi ashe tunmi ya fahimci abunda ke faruwa Muna isa mai marta ba ya fara bala'I inda yake shiga bata nan yake fita ba duk yaddake sin kare kansa amma abu ya faskara ya dinga yi masa muna nan kalamai wadanda zasu bi shi matukar bai rabu da ke ba in takaice maki magana mafarin ya ce zasu bar kasar kenan da zama don ya manta dake shi da sarki ya mutu ya zo a bashi sarauta idan kuma ya saba ko da gigi yazo naija to babu shi har abada duk wanda yake son gani yayo waya zaa tura mashi shi ni kuma aka gargade ni akan duk randana sake biye masa muka aikata hakkan to zanyi zaman bursuna na shekara 20 a gidan sarauta kwalla suka zubo mata ina kallon ta ta ce humaira wlh muna fitowa fada wuri ya smau ya zauna kawai naga ya fashe da kuka nima sai na taya shi ya kalle ni bani da saa dunia ni kuma kaddarar da Allah ya nufe ni da ita kenan to shine fa aka bamu butu kafin cikin mu a zabi wacce zaa tafi da ita a matsayyin mai aiki ranar da zamu taho ya bani takardar nan ya ce na kawo maki amma dom Allah kada kiyi kuka sbd haka zai tafi ki kawo rply na kai masa kuma zamu rinka waya da yaya zan ce ya rinka kawo maki muna gaisawa nace to tayi juyin duniya nace wlh bani da wata amsa ta gaida shi dole ta kyale. Ni Lbrn da amira tazo man dashi shi ya sa komai ta koma mini sabo nayi kuka har kaina yafara ciwo
More Hausa novels
Rayuwarmu Book One Complete Hausa Novel
By Saadatu
Kururuwar Shaidan Book 1 Complete Hausa Novel
By M Shakur
Kwarton Manya Book 3 Complete Hausa Novel
By Ubeera
A Garin Mu Part One Complete Hausa Novel
By Billyn Abdul
A Rubuce Take Part One Complete Hausa Novel
By Billyn Abdul
Hariji Book 3 Complete Hausa Novel
By M Shakur
Search across the available chapters.