Soyayyanovels
Subul Da Baka Book 2 Complete Hausa Novel
Subul Da Baka Book 2 Complete Hausa Novel
By Sajida Niger
Login to keep your reading position saved.
Book Page Chapters
Subul Da Baka Book 2 Complete Hausa Novel

Subul Da Baka Book 2 Complete Hausa Novel

Author: Sajida Niger
Chapter 8 of 11
About 8 min read
Chapter progress: 0%
Listen Mode
Listen to this chapter using your device voice.
Ready to listen from this chapter.

Book chapters

Choose a chapter and continue reading.

Start chapters

ya hanaka qarasawa gdan? Yayi murmushi hakanan. Na miqa masa wayata turamata lambata nima ka sakaman tata. Yace to humaira manya wannan irin babbar waya? Nayi murmushi 'Ni don Allah gobema idan kanada lokaci zan zo gdan kadan gwagwada mani yadda take kasan sabon shiga, kuma ka turamani qur'ani da adu'o'i. Yayi dariya yayi ustaziya karfe nawa zaki shgo? Lokacin da kake nan, ni gobe ba inda zan je. Nace to zan shgo wajan goma zuwa sha daya. Muna bin hanya zamu koma gda wayar ta hau kuka nayi saurin latsawa na dauka a tunanina amira ce dan ko suna ban duba ba Assalamu Alaikun kinga lambar ta shigo? Yayi murmushi wacece har an fara rabawa qawaye lamba? Nayi jim, to me tafiya ne ya bugo yace maki gashi a cikin jirgi, nace au walhi ban duba bane kayi hakuri, Allah ya saukeku lafia. Amin ya Allah humaira zan kiraki idan na sauka. Na bawa qanena lambarki duk sati zaya dinga sako maki kati kinji? Ban san lokacin da nace haba harda wahala kuma? Yayi murmushi 'a wurinki yake wahala' hmmm to na gode. Zan kashe wayata sena kiraki idan mun sauka. Nace to masha Allah. Dai dai lokacin da muka isa dak, 'keda wa kuma ko kin turamata lambar ne? Nace a'a ibrahm ne tayi murmushi yayi kyau, nayi yar daria 'kai inna na lura kina cikin gwamnatin mutumin nan. Ai dole humaira yaron daya so naka ba don wani abu ba sbd Allah kuma dangi da yan'uwansa basu nuna kyama ba dole a soshi Kema harda yarinta ke damunki bazaki abnd nake nufi ba sai nan gaba. Bakina yayi SUBUL DA BAKA nace ina fa? Inna gurin shi daban yake a zuciata wanda yayi sanadiyar rabuwata da ciwona ai alhairnsa bazai gushe ba a zuciyata. Cikin raina nace kema kenan inna ni kuma nace me? Wanda ya cusa min soyayyarsa da karfin tsiya ba tare dana farga ba. Wayyo Allah wayyo sarki ya samu cikin damuwa. Na maida kwallar data zubo min. ** N9,035 muka kirga cinikinmu na awara na yau inna ta kalleni tana yar dariyar jin dadi. Kai Alhmdllh humaira mungode Allah ya taimaki yarima ya rufa masa asiri shine silar wannan rufin asirin da muke samu. Nayi murmushi inna kullum sai kin min fadan na manta dashi gashi ke har yau kinsa mantawa dashi shin kin kasa mantawa dashi inna yaushe nima zai gushe a raina? Ni kuwa kinsan shawarar dana yanke mana? Nace a'a tare da smiling don na kula zancen nawa zata kawar. Kinga muna da yan kudinmu na sana'a da wadanda ke ajiye me zai hana musa a gina mana daki babba daga can gurin tukwanen ruwan can mu koma wann kuma ya koma kicin sbd damuna? Na buga tsalle kwarai inna kin kawo shawara amma a gina mana ciki da falo yafi sirri. Ai kudi na keji humai, inna In Shaa Allah zasu isa har ayi rara dayawa. To shikenan dama inaso mu fara siyan kayan aurenki d an gama kada muji kunya ISA inna bazamu taba jin kunya ba Allah daiya kara rufa mana asiri tace amin. Kullum adduarmu kenan kuma Alhmdllh muna ganin budi. Babansu amira inna taba kudin siminti da yashi washe gari aka fara aikin da misalin 1pm nakaiwa masu ginin abnc kenan mukaji sallama kallo daya nayi mata nagane ta jikina ya mutu murus wani yanayi ya dawo min sabo. Tunda ta shigo idonta yake kaina da sauri na nufi daki inna mun shiga 3 ga innar...... Tsaye tabarni tayi waje da gudu cikin rudu, mashaa Allah jiki yayi kyau, ta fada tana murmushi. Inna tayi ajiyr hrt ta karasa tana yar dariya tace maraba lale sannunku da zuwa. Na fito daga dakin bayan sun zauna narakasa na gaidasu kaina kasa. Humaira ya jikinku ya bayan kwana 2? Nace ya warware Alhmdllh ina sunkuye da kai kasa. Na mike ina kokarin kawo musu ruwa da abnc tace zauna humaira ina zakije? Kaina kasa naceabnc zan kawo muku da ruwa, tayi yardariya tace Allah sarki wllh a koshemuke mungode Allah ya bada ladarniyya. Kowa na dakin yace ameen, nakoma na zauna kamr yanda ta bukata.Hameed ya turoni yace inji lfy kia barkaratun? Banyi mmki ba sbd nasanamira ce ta fada masa, inna ta fahimcihalin da nake shirin shiga don hakatayi saurin gaya mata abnd ya farugaba 1. Tayi jim to Allah yasa haka yafialkhairi a gareki inna tace ameen, tamike mu zamu koma ta fiddo kudimasu yawa ta aje a kusa dani ga wannasai jambaki da hoda. Da kyar naceangode don kunya inna ce tayi musurakiya har kofar gida.Ko zama batayi ba tace kai jamaawadannan mutane suna kaunarmuhumaira. Shiru nayi kawai sbd zuwanya haddasa min abubuwa da dama.Koda inna ta lura saitayi saurin sauyazancen zuwa lbrn ban dariya. Aini datace kisai jambaki ba wacce ta fado minarai sai ummu Ahmad Rufai ta sokotowacce akafi sani da ummu labour ita fahar kamfanin jambaki sunsan da ita ita ke banilbr wai wani mutum yayi sabuwaramarya jawara ranar data tare ya fitasiyo musu kaza daya dawo saiya tararta tasa huluna guda 3 a gaba tanatakuka ya karasa hnkli tashe amarya yaakayi ne ranar farin cikinmu kina kuka? Yace kiyi mgn wadannan hulunan fa?Tace hulun nan da kake gani wannranar da aka daura mana aure ya rasuwann kuma ana shirin kawoni gidansaya rasu shi kuwa wann ranar da akakawoni gidansa ya rasu kaga kuwa dolenayi kuka ta sake rushewa da kuka.Da jin haka sai ya cire hularsa ya jefamata saiki kara kice wann kuma wandaya gudu ne har ya bar miki kaza dagidan shine gaba daya haba! Saiyakwasa a guje! Hahahahahahha bansansanda na kwashe da dariya ba. Innatace tsaya ma kiji wani lbrn wasu barayine su 2 suka sato lemuka basu tsayako ina ba makabarta suna cikin rabosaiga wani mutum yazo wucewa saiyaji ana cewa kai ga naka niga nawa!Haba saiya ruga da gudu ga liman daisarsa sai yace Allah ya gafarta yanzunnan da zan wuce ta makabrta najimala'iku suna rabon yan wuta da yanaljanna, liman da jin haka yace ai saimuje muji wann ilimi ne babbab mefadakarwa, suna zuwa sai sukaji ana toga sauran naka ga nawa sai dayan yaceka manta akwai saura yace wannekenan? Yace wadannan biyun dakewaje fa? Haba! Su liman sai aka dafekeya wann ya wuce wancan wancan yawuce wannan hahahaahhahahaah!Wayyo cikina inna ta sani dariya hardakifawa Inna na jin dadin dama ina kaunar labarukan ban dariya. Ta kara cewa, sai wasu abokai su uku su ka kai matansu haihuwa asbt sai ga nurse tace ina mai aiki a twintower? Yace gani tayi dry tace cngrts matarka ta haifa maka twins. Tana komawa ba da jimawa ba kadan tadawo ina wandake aikin 3 crown? Gani kasami yan 3. Dayan naji najin haka sai yafashe da kuka lfy? Ni ina aiki a 7up ne... Narike cikina wayyo duniya inna shi bazai hakura ma azo kanshi ba yana tsoronkada ace an haifa masa yara 7..nakara kyalkyalewa da dry, cikin dry nace nima tsaya kiji wani inna akwai wani mai arziki yanada matarsa daya da dansa junior da yar aikinsa budurwa kyakkywa merry da kuma yaron gida suna zaune cikin jin dadi komai a wadace wata rana maigida ya kawo giyarsa mai tsada ya ajiye a firij yafita da niyyar in yadawi ya sha.yaron gida yabude firij yanaso yasha ruwa sai yayi ido 4 da giya kawai yakwashi giyar yashanye tas sai yacika kwalbar da yogot.aka duba giya tazama yogot oga ya kwalaqaYaron gida kira bulus ya amsa......(dayake nasan duk kunsan labarannan bari Na tsallakesu ANaM Dorayi) ta kyalkyale dariya haka mukayi ta labarai maau ban dariya. Raina yayi fes namanta da duk wata damuwa. Zuciyar innaZuwar mahaifiyar yama gushe kwatakwata daga raina. Wayar amira ta katseni daga dariyar na kara wayar a kunne lokacin sauran yar dariyar. Turawa sa kwai nafada cikin zolaya tayi murmushi mai fidda sauti to ya son ranki? Bugowa nayi ince don Allag ki aikawa inna wayarki mu yi magana nanemi tata ban samu ba yaya kuma yace baya gida.. Nace bari nakai mata wayar da kaina zan kiraki idan na isa Na sahidawa inna sannan nasaka hijabina na tafi. Zaure na tarar dakofar dakinsa bude nayi mmk da farkoamma da nayi wani tunani sai nagawautata watakila lokacn ya shigo. Daisata ko zama banyi ba ta bugo saidasuka gama sannan muka gaisa ina yardariya nace naga yayan ma ya dawo.Ban rufe baki ba tace na ina? Shi fabaya ma gari bako yayi wllh ko dagamalufashi ne sun daiyi waya yace yanahanya. Wann furar ma shina siyowa.Nace Ayya ta mike bari na kai masanayi saurin karba haba inna kawo nakai masa meye amfanina dama nasanrashin dan aike zaisa kikai da kankitunda gani ai shikenan. Tayi murmushito humaira Allah yai albrk yas amugaaurenku lfy. Nidai nayi gaba kawai.Kishingide yake na kunna kai wanikamshin turare ya dokeni fuskarsa rufeda littafi nayi sallama da sauri ya dagokai mukayi ido 4 domin kuwa idona nakansa. Ya Salam! Naji ya fada a hnkl.Ina wuni ga fura inji inna.ganin bashida alamar motsawa yasa na ajiye masana juya. A hnkl yace donAllah dawo!Cak na tsaya tare da juyowa na kalleshiya daga kai. Karki gujeni ki dawo gareniwayyo ni ashe yaudarata ake baki mutuba HAFSAT!!! Gabana yayi muguwarfaduwa na zaro ido na dafe kirji Ni? Yamike zai nufoni cikin wani irin yanayiidanunsa har sun kwao kwalla sainakwasa a guje nayi wurin inna. Yadda ta ganni yasata firgici ke Humaira menene? Itama duk ta firgice.. Shigowarsa yasa inna yin shiru, nikuma nakara matsawa kusa da ita sosai..durkusawa yayi gwuiwa 2 kamar mai neman gafara, sai kawai yafashe da kuka.. Inna wacece wannan? Don Allah kar kice mini ba Hafsat dita bace, wayyo ni dafwan, Allah ka kaddareni da jin tabbacin Hafsat ditace domin nashiga shakkun wannan sbd ta nuna tsoro a gareni sai yakara fashewa da kuka dai dai kuma lokacin Yaya yai sallama.... Na rikice na rude hankalina ya dunguzuma sai kawai nima nafashe da kuka ganin cewar wani balain ne ka ke neman haye min. Subhanallah inna meke faruwa ne? Inna ta rausayar da kai tonima sun sakani cikin rudu wlh. Cikin kuka nace inna yadai sakamu ni wlh ban san shi ba Yaya, don Allah yimasa bayani fada masa cewar ko ni wacece.. Wani kallo yayi min kafin ya kawar da fuskarsa

End of Chapter 8Continue to the next chapter or choose another story below.

More Hausa novels

Browse all books →
Previous Login to Save Next