Subul Da Baka Book 2 Complete Hausa Novel
Book chapters
Choose a chapter and continue reading.
daku zuwa sanda za'a sallameku zasu dinga siyo muku abnci da duk abnda kuke bukata, ta dora bandiran kudi akan gadon inna ga wann ko zaku bukaci wani abu, Allah ya bada lfy Har ta fito bai motsa ba Inna ta kalleshi tace tashi ka bita Allah ya bada sa'a. Saura kadan kwalla ta zubo masa ya kalleta yace inna banida lfy zuciyata na min zafi ga humaira tana fushi dani bata kaunar kallona tun jiya bata min maggana. Ya kara langwabar da kai inna laifi na ne? Cikin tausayawa tare da mmkin soyayyarr da yake min tace ba laifinka bane humaira kuma kada ka damu wann halinta ne nima tana min irin wann. Yace inna in bata waya? Tace a'a bazan taba amincewa ka bata waya ba kayi hkri kamr yanda nasha fada maka to yau ma kalmae ce. Ya sauka kasa ya durkusa. DonAllah inna ki taimakeni kinga gobe nisa zanyi daku. Tace kayi hkri wann sharadin mahaifinta ne idan ka aureta saika bata. Jin wann batun yasa ya mike kamr me koyon tfy haka yabar dakin. Wani dunkulallen abu ya tokare min wuyana shi bai wuce ba shi ba fito ba na runtse ido a cikin raina ina fadin Innalillahi wa'innalihirraji'uan. Motsin su Aisha yasa na bude idona na dauka ko shine ya dawo da sauri na maidasu na rufe ruf a yau na tabbatar yayi min nisa. Anya zai dawo gareni? Na dafe kaina cikin ikon Allah sai kwalla suka zuraromin makar famfo inna ta kauda kanta. na fara rokon Allah ya cire min tunanin yarima kuma Alhmdllh na fara ragewa sosai. Da marece bayan mun gama awara ina zaune inna taje gidan kawu auwalu su Aisha sunje islamiyya kamr daga sama naji sallamar amira da gudu na tarota muka rike juna cike da murna na kalleta a lokacn data zauna Inna bata fada miki inata zuwa ban iskeki ba? Ta dan bata fuska wllh humaira inajin sakonki matsalar bana zama kullum nayi dariya sannu agogo. Ta kai min duka na kauce ta mike dama lbr nazo na baki sannan nayi miki albishir kiyi min murnar abnd ya sameni safiyar nan kuma muyi bankwana amma tunda....... Haba kawata yi hkr, da kinjawa kanki yarnya ta kara gyara zama humaira yanayi miki wani irin so wanda bazan iya fassara shi ba domin abnd ya faru lokcn da za'a tafi da gimbiya motar mu daban amma ni ya hanani nabi cikinsi ya sanyani a motarsu. Nida shi ne a baya tunda muka tafi kansa yake a duke har muka bar garin nan zuwa can ya dago ido jajur don saida na tsorata. Inason kawarki amma son bayada amfani gareni. Na sunkuyar da kaina kawai ina wasa da yatsuna wanda ke tukin motar ya juyo kaidai akwai dan iska yaushe muna kan layin raka matarka gida amma kana zancen wata? Shiru yayi kamr bada shi yake ba kinsna miskilancin mutumin naki. Yaja guntun tsaki daga nan bai kara mgn ba har muka isa. Humaira naje karshen mulki a sarauta naga inda ake takama da sarauta ashe su gimbiya basu iya komai ba? Motarmu na tsayawa wasu gardawan sarki suka zo wani ya kwanta saman shi ya sauka biyun kuma sukayi sama dashi bisa wani dan gaka suka daukeshi sukayi ciki dashi daga nan ban kara ganinshi ba sai washe gari. Kwana akayi shagali washe gari da misalin 12 akazo nemana na gane hakan ta yadda akayi kwatancen wacce suka shigo mota 1 da yarima cikina ya dinga kadawa sbd tsoro kada ace ko cigiya sukeyi. Munyi tafiya sosai kafin muje inda suke ya nuna wata kofa ki shiga ba tare da bata tym ba na shiga mazane shakare a falon duk gimansa sun cikashi na duba amma nakasa gane kowa a cikinsu da alama basu damu da shigowata ba. Keni sai tsoro ya kamani nayi saurin juyawa kamar daga sama naji ya kira sunana ashe yana kishingide cikin kujera yana kallona Hmmm miskilanci da kasaitarsa yana ba mutane tsoro, a tsorace na karasa inda yake ko kallona bayyi ba ya miko min wata rantsattsiyar wayarsa, ungo kisamin lamabr da kike gani zan iya magana da kawarki nakasa karba sbd kinga banida lamabar kowa a kaina wllh kota sadan gidanmu ban rike ba. Murya na rawa nace wllh banida lambar kowa akaina Allah ya taimakeka. Kallon da yayi min na rantse saida guntun fitsari ya zubo min idanunsa sukayi wani irin ja har wani ruwa ruwa ya kwanta. Tunda ya dauke kao bai sake kallon inda nake ba saida na kusan 1hr a haka nagaji iyakar gajiya har kafafuna sukayi sanyi, dogarawan dake tsaye suna masa firfita sai kallona suke na raina kaina a wurin ranar naji na tsani abotarmu dake. Da Allah ya taimakeni saiga wani abokinsa ya kalleni yace wann fa? Naga bakuwar fuska, ya kalleni da wann yatsinar tasa yace ki tafi mana. Simi-simi nabar gun kamar na bude kasa na shige don kunya. Bansan wace amsa ya bashi ba. An gama shagulgula amarya ta tare a gidanta wann sashe daya kirani gida yasha kayan kwalliya dukiya tasha kuka. Abnd ya bani mmk har yanzu basu bar al'adar nuna kwanan amarya ba. Sbd washe gari gida ya rude da gimbiya bata cika budurwa ba Abun kunyar gimbiya ya nemi komawa fitina da tashin hnkl. Ga yarima an nemeshi an rasa tun safe gimbiya ko sai kuka take sharbawa kamr ranta zai fita tana rantsuwa tana sharbewa wai bai kwanta aure da ita ba. Magana har gaban sarki gida ya sake rudewa duk inda ake zatonsa an aika amma ba'a tadda shi ba, hnkln gimbiya ya kara tashi mai martaba ya kara fusata ita kuwa mahaifiyarsa ko gezau saima fada data kamayi ita bata ga amfanin auren dole ba shin tunda yace bayaso bayaso a kyaleshi ya auri wacce yakeso mana. Aiko magana ta komawa sarki, ta kalleni Humaira munga tashin hnkl bana fatan sake ganin fushin babba idan haka yake. Maganar na zuwa wajen sarki kuma sai aka sami wayar sarki yace duk inda yake wllh ya bashi 3mins ya gurfana agabansa sannan ya aika aka kira sauran matan gidan cikin yan dakikai falon me martaba ya cika da ahalin gidan gimbiya na tsakiya har lokacn bata daina kuka ba zuwansa kawai ake jira. Shigowarsa ke da wuya ga mmkin kowa sai mai martaba ya mike ya dinga kwada masa mari har sau uku hancinsa kuwa ya balle da jini amma wllh ko gezau baiyi ba. Ni zaka kawowa raini? Ni zaka tozarta ka kunyata a idon dunia? Ka kwanta da matarka ko kuwa? Jinin dake zuba a hancinsa har ya fara bata gaban rigarsa fara, ya sunkuyar da kai a'a ban kwanta da ita ba. Ya fusata kayi hakane don ka nuna ban isa dakai ba? Ya kalli jakadiya saikije ki fada mutane yarinya bata kwanta aure ba Allah kuma zai saka mata bacin sunan dakayi mata. idan kuma nina haifeka wllh babu kai ba talaka komai ya dawo kunnena yau kuma na tabbtr da daurin gindin daka samu daga uwarka. Duk ranar da naji baka rabu da ita ba to wllh na yafeka dunia da lahira shashasha sakarai! Wann furucin na sarki ya haifar da zazzafar tsana da kiyayya tsakanin gimbiya da mahaifiyar yarima shima cin zarafin da akayi masa gaban jamaa ya kara sashi jin tsanarta fiye da baya. Sarki yayi musu kaca-kaca shida mahaifiyar sbd ina zargin ita ke goya masa baya. Sann yace da gimbiya dataga wani abu wanda baiyi daidai da tsarinta ba ta sanar dashi zaiyi maganin abun cikin gaggawa. Ana barin fada yaje ya zuba kankana akan habon jinin ya tsaya muna harabar gidan mukaji karar gimbiya sau daya. Muka razana kar dai ace shaketa yayi muka nemi shiga amma ya kulle kofar Ganin ya kullo kofar tsoro ya kamamu don munga shigarsa cikin tsananin fushi, karima ta kalleni gsky amira guduwa zanyi bana iya wan bala'in da gimbiya...uhm uhm wllh duk abnd yayi mata ita taja auren nan hadin iyayene, tun farko ya nuna mata bayaso shin idan ita mai wayo ce basaita lallabashi ba? Ga rashin so ga izgilanci da tsageranci mekike tunanin zai haifar? Kinga kuwa abnd tayiwa mahaifiyar humaira da ita kanta humairan? Wllh na tabbt gimbiya zata iyakisan kai, amma ke bakiga yanda ya shiga da fushi ba? Shin koma menene aiya riga ya faru ko kina iya balle kofar ki shiga? Ko dukansa yake kofa bude kina iya karbar gimbiya hannunsa ne? (Wannan rawar kan sai SIYYA) to wai humaira na sonsa da gaske? Kwarai saidai tsoro ya rinjayi son shiyasa ba kowa ke ganewa ba amma wllh humaira na sonsa matuka. Nayi saurin kai mata duka ni nace miki ina son sa? Kai-kai-kai ni kika doka? Baki sonsa kenan? To bari na tafi gida dama na dauka kina sonsa shiyasa na tsaya bata tym dina ina baki lbrnsa. Na marairaice yi hkri kawata dan karasa min wasa nake miki sorry, kina sonsa? Sosai ni kuwa ke sonsa zauna ki karsa min dukanta yayi? Wace irin fitina ce ya kara janyowa kansa? Na fakaiceta na mata gwalo, ta zauna idanunta sunyi ja kwalla ta taro mata taci gaba d acewa muna cikin wann magana humaira sai gashi ya fito ya sha kananan kaya yana ta uban kamshi hhar tym din acikin fushi yake. Dogarai suka rufa masa baya yayi hanyar shakatawa. Yana bacewa mukayi hanyar daki dake kallon nasa muna jiyo gunjin kukanta. A hamzarce muka nufeshi kwallan da take kokarin maidawa suka zubo gabana ya fadi na kosa naji abnd yayi mata ta kalleni kwallar na zuba wllh humaira duk irin isgilancinta saida ta bani tausayi, kwance take bisa gado yarima yayi mata kaca- kaca jini duk ya bata zanin gadon (wayyo Allah yarima ashe dai mugu ne kai?) Kukanta kawai kakeji har muryarta ta dashe amma bata iya ko motsawa hannu karima ta dora aka ta kurma ihu ni kuma na hau kyarma kukan yaki zuwa min hnklina ya bala'in tashi don ko a lbri wllh ban taba jin irin haka ba da gudu na fita zuwa sashen mama na sanar da ita abnd yake faruwa. Cikin halin ko in kula tace aje a sanar da jakadiya. Zuciata ta tsaya cak guri guda naji ya fita a raina sam, na sunkuyar
More Hausa novels
Rayuwarmu Book One Complete Hausa Novel
By Saadatu
Kururuwar Shaidan Book 1 Complete Hausa Novel
By M Shakur
Kwarton Manya Book 3 Complete Hausa Novel
By Ubeera
A Garin Mu Part One Complete Hausa Novel
By Billyn Abdul
A Rubuce Take Part One Complete Hausa Novel
By Billyn Abdul
Hariji Book 3 Complete Hausa Novel
By M Shakur
Search across the available chapters.