Subul Da Baka Book 2 Complete Hausa Novel
Book chapters
Choose a chapter and continue reading.
miki, don hk kedai ki fauwalawa Allah komai. Bari ina ina zuwa ga Gimbiya can tana kirana". Ta kashe. Kmr abin jira, Kiran Ibrahim ya shigo, naja wani dogon tsaki, wnn waya tana neman jawomin matsala, sbd ko motsin tsintsiya ba a son ji wlh. Ina dauka bai jira mun gaisa ba yace, " INA yau zan baro kasar nan ki saurare ni zuwa gobe da yamma". Na bude baki, amma sai na ji ya kashe. Da sauri na tashi zaune daidai lkcn da inna ta shigo, na ce. " kin ji wai Ibrahim yana hanya". Ta zaro ido, " zuwa ina? " "Nan zai taho, wai na saurare shi zuwa gobe da yamma". " Innalillahi wa'inna Ilaihi raji'un, ni kam a gaskiya ni kaina mgnr Ibrahim ina fa tangarda da ita, sbd hatsabibiyar matarsa tnd har ta furta kisa ko na kasa..." Kiran Amira ne ya shigo, na dauka, ta cigaba da lallashina tana bani hkr, nace ba komai, muka yi sallama. Jin wnn mgn yasa na fada mata mgnr safwan, ta girgiza kai. " Haba Humaira, kawai daga ya zo sai a amince da shi mun san halinsa? " " Nima hk na gani inna. shi baba bai gaya miki wane dattijon ba? Tayi dry, " bai fada ba, wlh jiya hr gidan naje ki kyale wdnn mutanen, Allah ya fi su". Washegari ya kama sauran kwana 2 tnd safe safwan yazo, na fita. Ya kalle ni, " yau ma kukan ne? " " A'a.Na fada a gajarce. " To gani ina mgn ta kwana? " " Na fidda wani" " wane ne? " " wani ne na fada kaina a Kasa. "Bashi da suna? " " yana da shi". "To fada". Na yi masa shiru. " Haba Humaira, me yasa ki ke son koyon karya, km da alama kmr ba halin ki bane". "Ya za a yi na yi maka karya? " "wlh karya kike yi, sbd hk ni zan je na gabatar da kaina". Na yi saurin dago Kai. " A'a wlh kada kaje, ban turaka ba". Ya kyalkyale da dry. " kin kama kanki, ni zan tafi sai kin ji daga gareni, sbd na lura baki da tunanin kanki, baki da shawarar kanki, haka baki da zabi".Yana gama fadin haka yayi tfyrsa. kmr na kirashi ya dawo muci gaba da tattaunawa har ya fahimce ni, amma na kasa. Na koma gida rai jagule. Ina ckn damuwar abinci Ibrahim yayi sllm hr ckn raina gaba na ya fadi, ya bada kululu. Da inna suka yi mgn snn ta ba mu wuri. Ya kalle ni ckn tausayawa, " wayyo Humaira dk kin rame, sannu ko wane tsanani tafe yake da sauki. Inna ta yi min bayani, na kuma gamsu, km nima ta fahimce ni, sbd hk zan tafi gida jibin itace ranar karshe, zamu zo da iyayena a yi komai, yau kinga yaushe na zagaya dangi har aka yi mgn? Gobe kuwa sai na sanar jibi tunda safe mu taho". Na dai yi shiru kawai, rayuwata ta kara jagulewa. " zan wuce, ki ci gaba da addu'a, zan aiko Yaro da kayan ki, suna waje ckn mota".Ya ajiye min bandir din kudi ya mike. Inna ta karaso, " yaronan ya bani tausayi Humaira, ki yi hkr da shi dk ya Snr da ni komai, kuma na amince da shi". Shiru kawai nayi mata. Da magariba ina zaune ina lazimi, yaro ya shigo ana sallama da Humaira. saura kadan in kurma ihu. Na kalle shi, " kace ta daina fita, sbd an yi mata miji, mata aure ce ynz". Inna da ke sallah ta yi gyaran murya. Takaicina ya karu, wai inna me ke damuta? Na fita raina kmr garwashi, zcyta sai zafi take yi. kamshin da ba ni taba mantawa ya daki hancina, nayi saurin kallonsa. Tsaye yake ya harde hnny a kirji, ni yake kallo, na durkushe sai kuka. Ya sunkuyo, " ki yi hkr Humaira, nasan kin yi fushi dani, wlh Humaira ba laifi na bane. ki daina kuka don Allah, menene damuwarki zuwa nayi muyi maganinta tare, Amira ta sanar dani komai". kuka nake, me ya kawo ka a wnn lkcn, me yasa kazo ka famamin ciwon da yaki wankewa? " Innalillahi wa'inna Ilaihi raji'un, don Allah ki saurare ni..." Na mike, " Don Allah ka tafi, wlh bani son ganinka a rayuwata, ba don na tsanekaba, a'a sai don na tsira da mutuncina, kai kuma ka gama da iyayenka lfy..." " saurara..." Nayi gida da gudu. Abin mamaki na kasa sanar da inna ko waye, ita kuma bata tmby ba. Zaune na kwana, duk wnd ya sani a da ynz ya ganni sai na bashi tausayi, nayi muguwar rama ga baki. Tashin hnkl sai ranar da adadi ya cika da safe, misalin karfe 10.30 na safe sai ga baba Auwalu su uku da buhun goro. jikina ya dauki rawa da yake zaune muke ni da inna a bakin kofa. Ya kalle mu a wulakance, sannan ya nefo ni da 20k. " To barkanki, wlh da na ba tsoho ha goran daurin aure nan mun dauki 2, Kuyi amfani da wnn, Na daura miki aure da wnd kika turo yau da safe karfe 9.30. Don haka ki shirya gobe zaku wuce babu mgnr taro". Na kalli inna itama ta kalle ni. kash!!! Nima ku nake kallo masu kr2, da wane ne aka daura auren da shi? safwan ko Ibrahim? Me ya kawo? mu tara a ltf na 3
Zaharaddeen Shomar
Whatsapp 08168575100
More Hausa novels
Rayuwarmu Book One Complete Hausa Novel
By Saadatu
Kururuwar Shaidan Book 1 Complete Hausa Novel
By M Shakur
Kwarton Manya Book 3 Complete Hausa Novel
By Ubeera
A Garin Mu Part One Complete Hausa Novel
By Billyn Abdul
A Rubuce Take Part One Complete Hausa Novel
By Billyn Abdul
Hariji Book 3 Complete Hausa Novel
By M Shakur
Search across the available chapters.