Ramadan Promo!All users that send a manual request for premium upgrade on sallah day will be granted for 1 month free.
Soyayyanovels
A Jini Take Izzata Part Two Complete Hausa Novel
A Jini Take Izzata Part Two Complete Hausa Novel
By Billyn Abdul
Login to keep your reading position saved.
Book Page Chapters
A Jini Take Izzata Part Two Complete Hausa Novel

A Jini Take Izzata Part Two Complete Hausa Novel

Author: Billyn Abdul
Chapter 28 of 122
About 8 min read
Chapter progress: 0%
Listen Mode
Listen to this chapter using your device voice.
Ready to listen from this chapter.
Free access is active. You can keep reading and download during this access window.

Book chapters

Choose a chapter and continue reading.

Start chapters
Chapter 1 1,645 words Chapter 2 1,690 words Chapter 3 1,680 words Chapter 4 1,637 words Chapter 5 1,676 words Chapter 6 1,594 words Chapter 7 1,597 words Chapter 8 1,655 words Chapter 9 1,192 words Chapter 10 1,647 words Chapter 11 1,678 words Chapter 12 1,698 words Chapter 13 1,656 words Chapter 14 1,617 words Chapter 15 1,693 words Chapter 16 1,658 words Chapter 17 1,692 words Chapter 18 1,521 words Chapter 19 1,684 words Chapter 20 1,600 words Chapter 21 1,688 words Chapter 22 1,589 words Chapter 23 1,692 words Chapter 24 1,344 words Chapter 25 1,685 words Chapter 26 1,699 words Chapter 27 1,685 words Chapter 28 Reading now Chapter 29 1,664 words Chapter 30 1,468 words Chapter 31 1,665 words Chapter 32 1,699 words Chapter 33 1,682 words Chapter 34 1,587 words Chapter 35 1,689 words Chapter 36 1,687 words Chapter 37 1,610 words Chapter 38 1,677 words Chapter 39 1,679 words Chapter 40 1,632 words Chapter 41 1,698 words Chapter 42 1,661 words Chapter 43 1,690 words Chapter 44 1,277 words Chapter 45 1,514 words Chapter 46 1,679 words Chapter 47 1,689 words Chapter 48 1,694 words Chapter 49 1,623 words Chapter 50 1,616 words Chapter 51 1,618 words Chapter 52 1,499 words Chapter 53 1,697 words Chapter 54 1,686 words Chapter 55 1,630 words Chapter 56 1,694 words Chapter 57 1,548 words Chapter 58 1,682 words Chapter 59 1,389 words Chapter 60 1,613 words Chapter 61 1,497 words Chapter 62 1,686 words Chapter 63 1,669 words Chapter 64 1,675 words Chapter 65 1,613 words Chapter 66 1,697 words Chapter 67 1,627 words Chapter 68 1,670 words Chapter 69 1,638 words Chapter 70 1,682 words Chapter 71 1,543 words Chapter 72 1,563 words Chapter 73 1,611 words Chapter 74 1,680 words Chapter 75 1,616 words Chapter 76 1,629 words Chapter 77 1,662 words Chapter 78 1,575 words Chapter 79 1,507 words Chapter 80 1,608 words Chapter 81 1,674 words Chapter 82 1,651 words Chapter 83 1,516 words Chapter 84 1,631 words Chapter 85 1,699 words Chapter 86 1,652 words Chapter 87 1,633 words Chapter 88 1,651 words Chapter 89 1,674 words Chapter 90 1,606 words Chapter 91 1,688 words Chapter 92 1,593 words Chapter 93 1,654 words Chapter 94 1,396 words Chapter 95 1,655 words Chapter 96 1,599 words Chapter 97 1,693 words Chapter 98 1,665 words Chapter 99 1,653 words Chapter 100 1,658 words Chapter 101 1,700 words Chapter 102 1,639 words Chapter 103 1,651 words Chapter 104 1,671 words Chapter 105 1,547 words Chapter 106 1,695 words Chapter 107 1,585 words Chapter 108 1,675 words Chapter 109 1,641 words Chapter 110 1,674 words Chapter 111 1,509 words Chapter 112 1,615 words Chapter 113 1,674 words Chapter 114 1,691 words Chapter 115 1,694 words Chapter 116 1,688 words Chapter 117 1,681 words Chapter 118 1,656 words Chapter 119 1,670 words Chapter 120 1,698 words Chapter 121 1,689 words Chapter 122 1,691 words

__ A hankali ya ƙarasa inda take yana kallanta da fuskarsa ta masu bacci, se da ya je dab da ita sannan ya zauna yace kamar ze yi kuka

"Lulu me aka miki? Waye ya dake ki?" Ya tambaya yana saka hannunsa kamar ze iya ɗagota. Tun bayan fitar Mami se a lokacin ta iya ɗago kan nata, ta kalli Little da jajayen idanunta da suka taasa saboda kukan da ta yi. Se kawai ta rungume shi ta cigaba da kukan me cin rai. Da dai ya ga babu wata mafita kawai se shi ma ya biye mata suka dinga yin kukan tare. Se da ta ji har kukan Little ɗin na nema yafi nata ƙarfi sannan ta soma tsagaitawa ta shiga sauke ajiyar zuciya kamar za ta shiɗe. Cikin ƙarfin hali tace

"Ka yi shiru ka ji?" Se da ya ji ta yi shirun kuwa sannan shi ma ya yi shirun yana cigaba da kallanta kawai. Babu jimawa kuma ya koma baccin, se ta kwantar da shi a kan gadon ta koma ta cigaba da zama har lokacin ƙirjinta be dena bugawa da ƙarfi ba. Wani irin tsoro take ji duk da har yanzu ta kaasa fahimtar inda ainahin wasu daga cikin zancen Mamin suka dosa.

A nutse a kuma yanda jikinsa ke a sanyaye tun ɗazun, uwa uba kuma ɓacin ran dake ta taso masa ya saka hannu ya buɗe ƙofar ɗakin ya shiga. Ko sallama a iya kan laɓɓansa ya iya yinta. Tunda ya shigo yake jiyo sautin ajiyar zuciyar da take ta saukewa. Be yi tunanin komai ba tunda dai ya san babu ta yanda za a yi ta san da wannan hoton. Se ya ƙarasa cikin ɗakin a nutse ya yaye labulen. Tana zaunen dai kamar wadda aka dasa, ya ɗauke kansa yana mayar da shi kan gadon da Little ke kai. Kai tsaye nan ya ƙarasa, ya saka hannu ya ɗauke shi ya fice daga ɗakin zuwa ɗakin Ummeey. Wajen minti 5 se ga shi ya dawo cikin ɗakin. Sam ba ta san da shigowarsa ba, ba kuma ta san da ficewarsa ba saboda yadda ƙwaƙwalwarta ta yi nisa cikin tunani barkatai. Ya shafe tsawon minti 1 a tsaye ba tare da yace komai ba, ya ma rasa ta inda ze fara. Se ya ji yana so ya zargeta se ya ji ya kasa, haka kawai duk da komai a bayyane yake amma zuciyarsa ke son kawo masa zato me kyau a kanta. Ya ɗan lumshe idanunsa yana buɗe su sannan ya fiddo da madaidaiciyar wayarsa daga cikin aljihu, ya ɗan yi danne_danne na en sakanni kafin ya ɗauke kansa, ya maida dubansa kan Lulu yace muryarsa a ɗan shaƙe, wadda idan ka san Gwanin ka na jin muryar za ka ce yana cikin fushi ne, fushi ma na sosai kuwa.

"Tashi.." Har cikin kanta ta ji muryarsa, saboda yanda ba ta yi tsammanin jin muryar wani ba, ba ta kuma san da wanzuwar wata halitta ba bayan ita da Little tun bayan da ta tafi tunanin har yanzu da ta dawo. Don haka a zabure ta buɗe jajayen idanunta ta watsa su kan Gwanin dake tsaye shi ma yana kallanta. Yanayin yanda ta kalle shin ba tare da ta shirya ba ya sanya ƙwayar idanunsu sarƙewa cikin na juna a karon farko kenan. Cikin lokaci ƙanƙani zuciyoyi biyu suka harba, kowanne kuma da abin da yake saƙawa. Saurin ɗauke idanunsa Gwani ya yi yana sake gyara tsayuwarsa gami da riƙe wayarsa sosai. Karon farko a rayuwarta da ta ji ta kasa yiwa Gwanin musu ko da kuwa gwadawa ne, se ta ji gaba ɗaya wani irin tsoro ya zo ya bi ya mamayeta. Haka nan kawai ta ji ta kasa sukuni da zuwansa wajen, gani take kamar akwai abin da ya kawo shi. "Ko dai a kan abin da Mami ta faɗa mata ne?" Ta tambayi kanta tana tashi zaune gaba ɗayanta. Duk da yanda duk ta soma sire masa, mamaki da kuma tunanin idan da gaske ta aikata abin da ake zarginta da shi me ze biyo baya? Hakan be hana shi mamakin yanda ta tashi zaunen kamar yanda ya umarceta ba tare da gardama ko wani abin makamancinsa ba. Ƙirjinta wani irin bugawa yake yi, duk da bayan ta tashin tazarar dake tsakaninsu ta ragu, amma hakan be dameta ba sam, damuwarta ɗaya shi ne jin abin da ze fito daga bakinsa. Kamar kuwa ya san take tunani se ya soma faɗin

"Afaaf.." Ba ta san lokacin da ta sake kallansa da narkakkun idanunta ba waɗanda suke cike taff da ƙwalla kamar ba yanzu ta gama kuka ba. Tun zuwanta gidan be taɓa kiran sunanta ba, ko da a makaranta ne se da dalili yake kiran sunan. Dan haka shi kansa se da ya ji shi daban, yayin da ita Lulu duk da halin da take ciki, hakan be hanata ji kamar ba sunanta ya ambata ba, saboda yanda sunan ya fito daidai daga cikin bakinsa. Ba ta kai ga amsawa ba ta tsinto muryarsa yana faɗin

"Me ya sa kika zaɓi rayuwar nan? Me ya sa kika zaɓi zubarwa da kanki mutunci da na iyayenki? Me ya sa ba kya so ki zama 'ya ta gari wadda iyayenta za su yi alfahari da ita? Me ya sa kika so ɓata rayuwarki da ƙananun shekarunki? Shin ba kya tunanin sakayyar da zaki samu tun a nan gidan duniya ballantana kuma a can? Me ya sa kika zaɓi rayuwar da tafi kama da ta dabbobi? Me ya sa?" Ya yi maganar yana kallanta. Kallansa take yi sosai kamar me son gano wani abun daga cikin fuskarsa. Kenan dai da gaske Mami take abin da ta faɗa, shi kenan shi ma yana mata kallan er iska. Daidai lokacin da wasu hawaye masu ɗumi suka soma zubowa daga cikin idanunta, ta lumshe idanun nata tana jin yanda jikinta ya ɗauki rawa fiye da ɗazu.

"Ban sani ba.. ban san a kan me kake magana ba.. Wallahi ban sani ba.." ta faɗa cikin raunanniyar murya kamar ba Lulu ba. Ɗan rufe idanunsa ya yi lokaci ɗaya yana buɗe su a lokaci ɗaya. Gaba ɗaya ma shi zancen ba ya so, ba kuma ya so a ja da nisa. Musamman yanda yake jin kansa na cigaba da sarawa tun lokacin da abin ya faru har zuwa yanzu. Wayarsa ya juyo da ita zuwa kan fuskar Lulun ba tare da ya kalli wayar ba. Da ƙyar ya iya buɗe baki yace

"Wace ce wannan?" Ya yi tambayar yana tsareta da idanunsa masu mugun kwarjini. Kamar wadda ta soma ganin waya a yau haka ta bita da kallo, daidai lokacin da idanunta suka sauka a kan hoton ta ji kanta ya shiga juyawa kamar an ɗagata ana juyi da ita. Ba tare da ta sani ba ta miƙe tsaye har lokacin idanunta da suka tsaya ƙyam a kan wayar suna kai ba tare da ko ƙiftawa ne ta yi ba. Ta kai hannunta dake wani irin rawa ta karɓi wayar tana cigaba da kallan hoton. Idan ka ganta se ka ɗauka wadda ba ta taɓa ganin waya ba ce. Se dai tsananin mamaki da ruɗewa sune suka sanyata hakan, suka kuma sanya ta kasa furta komai, ta kuma kasa aiwatar da komai bayan kallan wayar da take. Tunda take kallan hoton yake cigaba da kallan fuskarta yana nazarin yanayinta. Wani irin jiri da ta ji ya kwasheta yana shirin watsar da ita ƙasa, shi ne ya sanyata saurin zubewa a ƙasa kawai wayar hannunta na suɓucewa idanunta a lumshe. Gaba ɗaya ganinta se da ya ɗauke na wucin gadi, ƙwaƙwalwarta ta dena aiki na wucin gadi. Har tsawon minti 1 ba ta furta komai ba. Se da ta yi ƙarfin hali wajen ganin ta buɗe baki ta soma magana, maganar tata ma da gaba ɗaya ta dusashe, haka zalika fuskarta ita kanta ta koma kalar tausayi, kai ba zaka taɓa cewa Lulu ba ce. Girgiza kai take yi a sa'ilin da ta soma magana cikin wani irin kuka me tsuma zuciyar me sauraro

"Ba haka nake ba wallahi.. Ba haka nake ba.. Wallahi ba haka nake ba.." Shi ne abin da take maimaitawa kawai tana cigana da girgiza kai. Ɗan lumshe idanunsa Gwani ya yi kamin yace

"Wace ce a jikin hoton nan?"

"Ni ce.. Amma ban san waye ya ɗauka ba.. Ban sani ba wallahi.." Haka kawai ya ji bugun zuciyarsa ya ƙaru, kenan tana nufin da gasken ita ce rungume da wani? Kenan hakan ta faru, hoton ne kaɗai ba ta san an ɗauka ba?. Se ya ji gaba ɗaya ya sare da lamarin, jikinsa ya yi wani mugun sanyi, kamar yanda ɓacin ransa ya ƙaru. Ko bi ta kan wayarsa be yi ba ya fice daga ɗakin. Wani sabon kukan ta fashe da shi a fili tana faɗin

"Na shiga 3.." ta faɗa kanta a tantagaryar ƙasa hawayen na zuba a ƙasan.

... A bakin ƙofar sashen suka haɗu da Atine. Cikin girmamawa ta gaida shi, ya amsa kamar ba ze ce komai ba se kuma yace

"Ina me coffee..?" Ya tambaya a yatsine. Har ga Allah ba ta gane abin da yake nufi ba, hakan ne ya sanyata faɗin

"Yallaɓai ban fahimta ba.." ta faɗa tana murmushi dan kar ta je ya gwaɓa mata magana. Yatsine fuska ya yi kamin yace

"Yarinyar da ke dafa Coffee tana ajje min.."

"Aiyo Afrah kenan.." Wayar hannunsa ya ɗan danna sannan yace

"Saƙo zan ba ki.." ya ɗan dakata a nan kafin ya ɗora da

"Ta cigaba da kawowa morning nd night.." Jin abin da ya faɗa ne ya sanya Atine jin wani irin daɗi, ko babu komai wannan ɗin matakin nasara ne. Wannan ɗin kuma nasara ce babba. Gyara tsayuwarta ta yi tace cike da fatan ya amince da abin da za ta faɗa ɗin

"A min aikin gafara Yallaɓai.. Ka da Hajiya Salma ta ɓata min idan ta ji na shiga harkar ka da yarinyar nan.." Kallan Atine ya yi kamar wata sa'arsa sannan yace

End of Chapter 28Continue to the next chapter or choose another story below.

More Hausa novels

Browse all books →
Previous Login to Save Next