Ramadan Promo!All users that send a manual request for premium upgrade on sallah day will be granted for 1 month free.
Soyayyanovels
A Jini Take Izzata Part Two Complete Hausa Novel
A Jini Take Izzata Part Two Complete Hausa Novel
By Billyn Abdul
Login to keep your reading position saved.
Book Page Chapters
A Jini Take Izzata Part Two Complete Hausa Novel

A Jini Take Izzata Part Two Complete Hausa Novel

Author: Billyn Abdul
Chapter 113 of 122
About 8 min read
Chapter progress: 0%
Listen Mode
Listen to this chapter using your device voice.
Ready to listen from this chapter.
Free access is active. You can keep reading and download during this access window.

Book chapters

Choose a chapter and continue reading.

Start chapters
Chapter 1 1,645 words Chapter 2 1,690 words Chapter 3 1,680 words Chapter 4 1,637 words Chapter 5 1,676 words Chapter 6 1,594 words Chapter 7 1,597 words Chapter 8 1,655 words Chapter 9 1,192 words Chapter 10 1,647 words Chapter 11 1,678 words Chapter 12 1,698 words Chapter 13 1,656 words Chapter 14 1,617 words Chapter 15 1,693 words Chapter 16 1,658 words Chapter 17 1,692 words Chapter 18 1,521 words Chapter 19 1,684 words Chapter 20 1,600 words Chapter 21 1,688 words Chapter 22 1,589 words Chapter 23 1,692 words Chapter 24 1,344 words Chapter 25 1,685 words Chapter 26 1,699 words Chapter 27 1,685 words Chapter 28 1,660 words Chapter 29 1,664 words Chapter 30 1,468 words Chapter 31 1,665 words Chapter 32 1,699 words Chapter 33 1,682 words Chapter 34 1,587 words Chapter 35 1,689 words Chapter 36 1,687 words Chapter 37 1,610 words Chapter 38 1,677 words Chapter 39 1,679 words Chapter 40 1,632 words Chapter 41 1,698 words Chapter 42 1,661 words Chapter 43 1,690 words Chapter 44 1,277 words Chapter 45 1,514 words Chapter 46 1,679 words Chapter 47 1,689 words Chapter 48 1,694 words Chapter 49 1,623 words Chapter 50 1,616 words Chapter 51 1,618 words Chapter 52 1,499 words Chapter 53 1,697 words Chapter 54 1,686 words Chapter 55 1,630 words Chapter 56 1,694 words Chapter 57 1,548 words Chapter 58 1,682 words Chapter 59 1,389 words Chapter 60 1,613 words Chapter 61 1,497 words Chapter 62 1,686 words Chapter 63 1,669 words Chapter 64 1,675 words Chapter 65 1,613 words Chapter 66 1,697 words Chapter 67 1,627 words Chapter 68 1,670 words Chapter 69 1,638 words Chapter 70 1,682 words Chapter 71 1,543 words Chapter 72 1,563 words Chapter 73 1,611 words Chapter 74 1,680 words Chapter 75 1,616 words Chapter 76 1,629 words Chapter 77 1,662 words Chapter 78 1,575 words Chapter 79 1,507 words Chapter 80 1,608 words Chapter 81 1,674 words Chapter 82 1,651 words Chapter 83 1,516 words Chapter 84 1,631 words Chapter 85 1,699 words Chapter 86 1,652 words Chapter 87 1,633 words Chapter 88 1,651 words Chapter 89 1,674 words Chapter 90 1,606 words Chapter 91 1,688 words Chapter 92 1,593 words Chapter 93 1,654 words Chapter 94 1,396 words Chapter 95 1,655 words Chapter 96 1,599 words Chapter 97 1,693 words Chapter 98 1,665 words Chapter 99 1,653 words Chapter 100 1,658 words Chapter 101 1,700 words Chapter 102 1,639 words Chapter 103 1,651 words Chapter 104 1,671 words Chapter 105 1,547 words Chapter 106 1,695 words Chapter 107 1,585 words Chapter 108 1,675 words Chapter 109 1,641 words Chapter 110 1,674 words Chapter 111 1,509 words Chapter 112 1,615 words Chapter 113 Reading now Chapter 114 1,691 words Chapter 115 1,694 words Chapter 116 1,688 words Chapter 117 1,681 words Chapter 118 1,656 words Chapter 119 1,670 words Chapter 120 1,698 words Chapter 121 1,689 words Chapter 122 1,691 words

"Didi.. Lulu.. Didi.. Lulu." Shi ne abin da yake ta faɗa cikin tsananin farin cikin ganinsu. Rungume shi suka yi a tare cike da kewarsa. Ita kanta Ammi murmushi ya ƙi barin fuskarta. Kallan 'ya'yan nata kawai take yi. Allah ne kaɗai ya san irin farin cikin da ta ji na ganinsu da ta yi. Sanda suka ƙaraso inda Ammi take, basu ɓata lokaci ba suka rungumeta. Tuni ƙwalla har ta cika idanun Ammi. Ta dai saurin maidata dan kar su ma ta karya musu zuciya.

"Ammi mun yi kewarki sosai." Didi ta faɗa. Lulu ta jinjina kai fuska a narke.

"Ni kaina yarana. Kun zo lafiya?" Ta tambaya cikin kulawa. Gaisawa sosai suka yi, shi dai Little ya yi shiru daga ya je jikin wannan, se ya koma jikin waccan. Ji yake kamar mafarki yake yau ma en uwansa ya sake ganinsu. Ga shi ma har sun dawo gida. Sosai yau ɗin ta kasance rana ta musamman a wajensu. Sun yi hira da Ammi sosai. Ta basu shawara, ta musu faɗa, ta kuma fahimci abubuwa da dama. Ciki kuwa har da cikin da Lulu ke ɗauke da shi. Ba su suka buɗi baki suka sanar da ita ba, amma duk wata alama ta me ciki ta gama bayyana a tattare da Lulun. Ga shi kuma ba ta iya cin dambun da Ammin da kanta ta tashi ta shirya musu ba, se da aka dafa mata wani abincin daban kafin ta iya ci. Ammi ta lumshe idanunta har cikin ranta tana jin farin ciki, musamman da ta ga alamar komai ya daidaitu tsakanin 'ya'yan nata da mazajensu. Se dai fatan Allah Ya ƙara musu zaman lafiya, ƙaunar juna da kwanciyar hankali me ɗorewa. Se da yamma sannan Lulu ta je gidansu Fatima Kabeer (Masoyiya). Kamar sa haɗiye juna saboda farin cikin ganin junansu. Haka suka zauna suna ta hira ta yaushe gamo. Se magribh sannan Masoyiyar ta rakota har gida kafin ta koma gida jiki duk ba daɗi. Ita kanta Lulu ji ta yi kamar kar su rabu, dan babu ƙarya sun yi kewar junansu.

Kasancewar Gwani ba ya nan, tun safe yana asibitin da Abeey yake, ya sa Bad Man ne ya wuce ɗauko su Didin. A harabar gidan ya tsaya yana jiran fitowarsu bayan ya shiga sun gaisa da Ammin. Ko a jikinsa, ganin Lulu da ya yi sun fito tare da Didi hakan be hana shi ƙarasawa inda take ba, ya yi azamar jawota jikinsa yana rungumewa.

"Sweetheart.." Ya faɗa yana lumshe idanunsa. Ita kam ji ta yi kamar ƙasa ta tsage ta shige dan kunya. Wanzuwar Lulu a wajen ita ce ta sanyata ji kamar ta fasa ihu. Shi kam da alama ko a jikinsa. Dan kuwa tana jikin nasa ya kalli Lulu da ke ƙoƙarin wuce su kamar ba ta gansu ba.

"Tweenienmu.." Ya yi maganar da ɗan murmushi a kan fuskarsa da yanzun lokuta da dama da wuya ka ganta a yanda ka san shi a da, musamman idan yana tare da Didi. Se a lokacin ta dakata ta ɗan yi murmushi cikin basarwa tace

"Barka da wannan lokaci Ya Areef."

"Barka dai.." Ya yi maganar yana sakin Didi.

"Thank God! Wannan mutumin!" Lulu ta faɗa a kan laɓɓanta, kafin ta fesar da iska daga cikin bakinta. Tura baki Didi ta yi dan ita kam ya gama bata kunya a gaban Lulu. Sarai ya lura da yanayinta, se dai ya basar kawai. Ya lura har yanzu ba ta gane yanda yake jinta a can ƙasan zuciyarsa ba ne. Kwata kwata ba ya ji ze iya ɓoye ƙaunarta da yake, musamman ma kuma da ya kasance a gaban er uwarta ne ba gaban wani can daban ba.

"Uncle.!" Ya jiyo muryar Little da ke tahowa wajen. Yana ƙarasowa ya rungume shi yana dariya. Hannu Bad Man ya saka ya ɗaga shi yana faɗin

"Areef!" Ya ƙare yana murmushi dan ba ƙarya ya yi kewar yaron shi kansa.

"Uncle kai ma ka dawo gidan nan?" Ya tambaya cike da farin ciki, dan shi a tunaninsa har su Didin ma sun dawo ne. Girgiza kai Bad Man ya yi kana yace

"A'ah na zo ne in ganka.. Amma zan dawo."

"Su Didi fa?" Ya tambaya yana buɗa baki kamar wani babba me wayo

"Su ma za su dawo."

"Kai!!" Ya faɗa yanayin fuskarsa na sauyawa. Se ma ya soma taɓe baki kamar ze yi kuka. Da sauri Bad Man yace

"Kar ka damu.. Za su dawo Uhmm?" Ya ƙare yana kallansa. Se ya jinjina kai a sanyaye. Bad Man ya ja kumatunsa yana faɗin

"That's my boy.. Oh yah, give me five!" Ya faɗa yana miƙa masa hannunsa. Se ya ba shi hannunsa suka tafa yana dariya. Se a lokacin sannan ya sauke shi yana faɗin

"Maza shiga gida.." Se da ya juya ya kalli Lulu da Didi da suke kallansa kamar za su yi kuka kafin ya tafi da gudu zuwa cikin gidan. Ajiyar zuciya ya sauke yana tashi tsaye sosai. Ya so ya samu ya gaisa da Abba, se dai har yanzun Abban be dawo ba. Dalili kenan da ya sanya ya haƙura kawai, da niyyar wani lokacin ya zo takanas ya gaishe da Abban.

Ita kam Lulu tamkar er kallo ta zama, dan ba ta taɓa tunanin Bad Man ɗin haka yake ba. Domin kuwa yanzun ma hannu ya saka ya buɗewa Didi ƙofar gidan gaba, ta juya da niyyar kallansa, ya marairaice fuska yana kauda kai ba tare da ya bari sun haɗa ido ba. Se ta juya da niyyar kallan Lulu, ita ma ta yi saurin janye idanunta tana basarwa. Bad Man da ke lura da duk abin da take ya yi murmushi har fararen haƙoransa na bayyana. Kawai se ta shiga ciki, ya kulle ƙofar kafin ya zagaya. Se a lokacin ya juya ya kalli Lulu yace

"Matar ɗan uwa mu wuce koh?" Se ta jinjina kai tana ƙarasowa ta shiga cikin motar. Babu ɓata lokaci ya ja motar suka fice daga cikin gidan. Ko a cikin motar ma duk da driving yake, hakan be hana shi kamo hannun Didi cikin nasa ba. Duk da yanda take ɗan ta babbasarwa saboda wanzuwar Lulu a wajen amma shi ko a jikinsa. Da dai ta ga babu sarki se Allah kawai se ta yi shiru, ta saki hannun nata, ya kuwa riƙe gam idanunsa na kan titi. Sosai Lulu ta ji daɗin hakan, ko babu komai ta san Didin tata ta samu mijin da ke ƙaunarta. Ba ma ita kaɗai ba dukkansu sun samu masu ƙaunarsu. Kawai se ta ji tana kewar nata mijin, ta lumshe idanunta tana jin wani murmushi na ƙwace mata. Yana ida parking na motarsa driver ma na parking motar da ya ɗauki Gwani ciki. Don haka kusan a tare suka sauka. Idanun Gwani na kan inda ze hango tauraruwar tasa. Cikin ƙanƙanin lokaci kuwa ya hangota ta yi kyau, tamkar wadda ta gama shiri yanzun. Ya saki murmushi yana jin wani sanyi na ratsa shi. Yau ɗin da ya wuni be ganta ba duk se yake jinsa tamkar mara lafiya, yanzun kam da ya ganta se yake jinsa zam-zam.

"Ina fata dai ba ka wujijjiga min mata da ɗa ba da wannan driving ɗin naka." Gwani ya faɗa lokacin da ya ƙaraso inda suke idanunsa a kan Bad Man. Buɗe ido ya yi kafin yace

"Umm lallai ka ga me mata da ɗa.. Toh tambayeta mana." Ya ƙare yana rungume hannunsa a ƙirji yana maida dubansa kan Lulu. Jinjina kai Gwani ya yi kafin ya shiga takawa zuwa inda Lulu take. Se ta soma ɗaga kai tana kallan Bad Man da Didi da ke kallansu. Fatanta da addu'arta kawai Allah Ya sa kar yace ze riƙota ko wani abun. Cikin ikon Allah kuwa addu'arta ta karɓu, dan kuwa ƙarasowa ya yi se dai dab da ita. Ya zuba mata idanunsa, ita ma kuma shi take kalla. A hankali kamar me raɗa yace

"Ina fata dai be wahalar min da ku ba?" Har ta buɗe baki cike da mamaki da niyyar tambayar ita da wa? Se kuma murmushi ya ƙwace a kan fuskarta. Ta jinjina kai a hankali tana faɗin

"Ehh.." Juyawa Gwani ya yi yana murmushi, idanunsa a kan Bad Man yace

"Allah Ya taimake ka." Dariya Bad Man har ma da Didi suka yi, dan babu ƙarya abun ya burgesu. Musamman irin kallan da suke bin junansu da shi ɗazun, wanda kallan farko za ka karanto irin soyayyar da kowannensu ke wa ɗan uwansa.

.. Ba a ɗauki lokaci me tsayi ba, shirye-shiryen tafiyarsu Saudiyya komai ya kankama. Dan haka suka sake yin sallama da dangi na kusa kafin suka kama hanya se ƙasa me tsarki. Kowa na yi musu fatan alkhairi, da fatan a yi ibada lafiya, a kuma samu nasara a rashin lafiyar Abeey. A ranar da suka sauka kai tsaye asibitin suka fara wucewa. A kusa da asibitin kuma akwai hotel, a nan suka kama ɗakuna biyu da za su zauna. Kama ɗakin kawai suka yi, suka bar Didi da Lulu. Ya yin da su kuma suka koma asibitin dan ƙarasa duk wasu abubuwa da suka kamata saboda kasancewar yau ɗin shi ne zuwansu na farko. A can asibitin da ma suka bar Ummeey. Dan haka inda suka barta a nan suka zo suka sameta.

"Ina kuka bar 'ya'yan nawa?" Ummeey ta tambaya tana kallansu su duka.

"Yanzu haka suna cikin ɗakin hotel ɗin da ke kusa da asibitin nan Ummeey.. Idan ki na buƙatar wani abu se mu je a raka ki." Bad Man ne ya ba wa Ummeey wannan amsar. Ta yi murmushi kafin ta amsa da

"Toh madallah.." Suna nan zaune suna jiran shigowar wanda Daddy ya haɗa su da shi Abeey da ke kishingiɗe a kan gadon ɗakin ya kalli Gwani yace

"Kun dai dage se na samu lafiya." Ya ƙare yana kallan Gwani da ya san ya fi kowa shiga damuwa idan ba shi da lafiya.

"Abeey bayan lafiyar ma kuma, ai ka ga babban abun da ya kawo mu shi ne ziyartar ɗakin Allah." Murmushi Abeey ya yi kafin ya amsa da

End of Chapter 113Continue to the next chapter or choose another story below.

More Hausa novels

Browse all books →
Previous Login to Save Next