Ramadan Promo!All users that send a manual request for premium upgrade on sallah day will be granted for 1 month free.
Soyayyanovels
A Jini Take Izzata Part Two Complete Hausa Novel
A Jini Take Izzata Part Two Complete Hausa Novel
By Billyn Abdul
Login to keep your reading position saved.
Book Page Chapters
A Jini Take Izzata Part Two Complete Hausa Novel

A Jini Take Izzata Part Two Complete Hausa Novel

Author: Billyn Abdul
Chapter 25 of 122
About 8 min read
Chapter progress: 0%
Listen Mode
Listen to this chapter using your device voice.
Ready to listen from this chapter.
Free access is active. You can keep reading and download during this access window.

Book chapters

Choose a chapter and continue reading.

Start chapters
Chapter 1 1,645 words Chapter 2 1,690 words Chapter 3 1,680 words Chapter 4 1,637 words Chapter 5 1,676 words Chapter 6 1,594 words Chapter 7 1,597 words Chapter 8 1,655 words Chapter 9 1,192 words Chapter 10 1,647 words Chapter 11 1,678 words Chapter 12 1,698 words Chapter 13 1,656 words Chapter 14 1,617 words Chapter 15 1,693 words Chapter 16 1,658 words Chapter 17 1,692 words Chapter 18 1,521 words Chapter 19 1,684 words Chapter 20 1,600 words Chapter 21 1,688 words Chapter 22 1,589 words Chapter 23 1,692 words Chapter 24 1,344 words Chapter 25 Reading now Chapter 26 1,699 words Chapter 27 1,685 words Chapter 28 1,660 words Chapter 29 1,664 words Chapter 30 1,468 words Chapter 31 1,665 words Chapter 32 1,699 words Chapter 33 1,682 words Chapter 34 1,587 words Chapter 35 1,689 words Chapter 36 1,687 words Chapter 37 1,610 words Chapter 38 1,677 words Chapter 39 1,679 words Chapter 40 1,632 words Chapter 41 1,698 words Chapter 42 1,661 words Chapter 43 1,690 words Chapter 44 1,277 words Chapter 45 1,514 words Chapter 46 1,679 words Chapter 47 1,689 words Chapter 48 1,694 words Chapter 49 1,623 words Chapter 50 1,616 words Chapter 51 1,618 words Chapter 52 1,499 words Chapter 53 1,697 words Chapter 54 1,686 words Chapter 55 1,630 words Chapter 56 1,694 words Chapter 57 1,548 words Chapter 58 1,682 words Chapter 59 1,389 words Chapter 60 1,613 words Chapter 61 1,497 words Chapter 62 1,686 words Chapter 63 1,669 words Chapter 64 1,675 words Chapter 65 1,613 words Chapter 66 1,697 words Chapter 67 1,627 words Chapter 68 1,670 words Chapter 69 1,638 words Chapter 70 1,682 words Chapter 71 1,543 words Chapter 72 1,563 words Chapter 73 1,611 words Chapter 74 1,680 words Chapter 75 1,616 words Chapter 76 1,629 words Chapter 77 1,662 words Chapter 78 1,575 words Chapter 79 1,507 words Chapter 80 1,608 words Chapter 81 1,674 words Chapter 82 1,651 words Chapter 83 1,516 words Chapter 84 1,631 words Chapter 85 1,699 words Chapter 86 1,652 words Chapter 87 1,633 words Chapter 88 1,651 words Chapter 89 1,674 words Chapter 90 1,606 words Chapter 91 1,688 words Chapter 92 1,593 words Chapter 93 1,654 words Chapter 94 1,396 words Chapter 95 1,655 words Chapter 96 1,599 words Chapter 97 1,693 words Chapter 98 1,665 words Chapter 99 1,653 words Chapter 100 1,658 words Chapter 101 1,700 words Chapter 102 1,639 words Chapter 103 1,651 words Chapter 104 1,671 words Chapter 105 1,547 words Chapter 106 1,695 words Chapter 107 1,585 words Chapter 108 1,675 words Chapter 109 1,641 words Chapter 110 1,674 words Chapter 111 1,509 words Chapter 112 1,615 words Chapter 113 1,674 words Chapter 114 1,691 words Chapter 115 1,694 words Chapter 116 1,688 words Chapter 117 1,681 words Chapter 118 1,656 words Chapter 119 1,670 words Chapter 120 1,698 words Chapter 121 1,689 words Chapter 122 1,691 words

"Toh Allah ya kawo mafita.." Daga haka ya soma tafiya dan barin ƙofar gidan. Cike da fatan ƙin samun kowa a tsakar gidan ya shiga, cikin sa'a kuwa babu kowa. Kai tsaye ɗakin nasa ya wuce. Cikin sa'a Lulun na can ɗakin Ummeey. Neman waje ya yi ya zauna a kan gadon yana saka hannu ya ware abin da ke kansa ya ajje shi gefe. Ya ɗauki hannayensa duka biyun ya ɗora a kan baƙar sumar kansa idanunsa a lumshe. Farar fuskarsa har wani ja ta yi, haka zalika idanunsa. Sake runtse idanunsa ya yi saboda yanda idanunsa babu abin da suke hangowa se wannan hoton. Ya yi iya bakin ƙoƙarinsa wajen cire hoton daga ƙwaƙwalwarsa amma ya kasa. Dama haka take? Ya tambayi kansa. Tambayar da ita kaɗai ke yawo a cikin ƙwaƙwalwarsa. Girgiza kai ya shiga yi kamar wanda aka ba shi amsar tambayar da ya yiwa kansa. Se ya cigaba da zama cikin ɗakin na tsawon mintuna 5 sannan ya miƙe tsaye, ya shiga zagaye inda yake ɗin gaba ɗaya ransa a cunkushe kamar yanda fuskarsa take. Iska ya ɗan fesar da ita daga cikin bakinsa, yana so hakan ya fice masa a rai, ya kuma dena damuwar sosai. Be san me ya sa ya ji ransa ya mugun ɓaci ba, wanda ko da shi ya zaɓeta a matsayin mata iya abin da ze yi kenan. Se dai ya rasa dalilin da ya sa ya ji sam ya kasa amincewa da abin da Abbatin ya faɗa. Ga dai sheda nan duka ya kawo masa, har da hoto kuwa, amma duk da haka neman wata hanya yake yi da ze sa ya yi fatali da hakan, hanyar da za ta danne duk wata sheda da aka nunawa Abbatin. Babban abin da ya sa ya sanya wa duk abin da Abbatin ya faɗa masa ayar tambaya, yanda har aka tare shi aka faɗa masa abin da matar Abokinsa ta yi. Idan dai har da gasken ba sa so a yaudare shi me ya sa kai tsaye ba a zo an same shi shi da kansa ba?. Lumshe idanunsa ya ɗan ƙara yi, daidai lokacin da hoton ya sake dawo masa. Se ya yi saurin buɗe idanun nasa yana fesar da wata zazzafar iska daga bakinsa.

"Idan kuma haka ɗin ne fa? Idan da gaske duk abin da aka faɗa tana aikatawa fa?" Zuciyarsa ta raya masa hakan. A fili ya furta

"Hasbunahallahu wa ni'imal wakeel.." ya faɗa yana neman waje ya zauna. Cikin kuma ƙanƙanin lokaci ɓacin ransa ya daɗu, se ya ji kamar ana masa bita ne a kan abubuwan da Abbati ya faɗa masa.

"Me ya sa na amince da auranta?" Ya tuhumi kansa yana tunanin idan har wannan al'amari ya je kunnen wasu mutanen me ze faru? Se dai kuma har abada ba ze taɓa yin hukunci ba tare da bincike ba, dan haka abu mafi muhimmanci shi ne sanin gaskiyar lamarin.

... Ya yi mamakin ganin kiran Mami ɗin cikin wayarsa, se dai kawai ya ɗaga da sallama a bakinsa. Se da suka gaisa sannan Mami tace

"Na kira ne na yi maka jaje a kan abin da ya faru.." Se ta ɗan dakata a nan sannan ta ɗora da

"Na kuma sake baka haƙuri a kan wannan rashin da ka yi. Allah ya zaɓa maka wadda ta fita zama alkhairi.." Sosai ya ji daɗin addu'ar Mamin dan haka ya yi murmushi sannan yace

"Godiya nake sosai Madam. Allah ya bar zumunci.."

"Ameen Kaseem. Ai babu komai.." Mami ta faɗa tana murmushi sosai.

"Amma wani hanzari ba gudu ba.. ka na ji na?"

"Ehh.." cewar Kaseem. Se da Mami ta nemi waje ta zauna tana tunanin ta inda za ta fara wannan zancen, se dai kawai ta maaze tace

"Me ze hana tunda ka rasa Afrah ka yi tawakkali ka nemi wata? Da ba a yi wa Afaaf aure ba ni da kaina zan haɗaku. Se dai kowaccensu yanzu haka tana ɗakin mijinta, dan haka ni na yanke shawarar yi maka tayin er wajena Jadwa. Idan dai har ka amince zan san yanda zan yi na shawo kanta ta amince maka.." ta ƙare tana dariyar yaƙe, cike da fatan abin fa ze fito daga bakinsa ya zama amincewa ne da tayin da ta masa. Se dai addu'ar tata ba ta karɓu ba, dan kuwa buɗar bakinsa se cewa ya yi.

"Allah sarki.. Na gode sosai.. Allah ya saka da alkhairi, na kuma ji daɗin wannan tayin da kika mini, ko babu komai hakan ya nuna kin aminta da ni ne. Se dai kuma tare da dukkan wata girmamawa nake ce miki ki yi haƙuri.. amma na gode da wannan tayin. Ina nufin ba na buƙatar haɗin, ba kuma dan komai ba se dan yanzun babu batun soyayya a tare da ni, ba na buƙatarta sam. Ko da zan yi ma ba yanzu ba.."

"Ai babu matsala, in dai Jadwa ce za ta iya jiranka. Kai na san ma da kanta za ta chanjaka, ta cire maka wannan ƙudurin a ranka.." Murmushi ya yi kawai sannan yace

"Ki yi haƙuri Madam.. Yanda na faɗa ɗin dai shi ne.. Na gode sosai.." Cikin ɓacin rai Mami ta katse kiran tana jin wani irin takaici na mamayeta. Haushin Kaseem ɗin na kamata, ta zubar da mutuncinta ta tallata masa ɗiyarta amma ya watsa mata ƙasa a ido? Ta yi wata ƙwafa a fili tana furta

"Shashasha.."

"Mami.." Jadwa ta faɗa tana turo baki.

"Me ya faru?" Mami ta faɗa tana kallanta a fusace.

"Yanzu ya zamu yi kenan?"

"Ya kuwa za mu yi, banda mu sauya zani.." Mami ta faɗa tana miƙewa.

"Kawai ki ba ni numbersa, zan san yanda zan yi na shawo kansa Mami.." Jadwa ta faɗa tana kallan Mamin.

"Aou wai ba ki ji haushi ba?" Mami ta faɗa cike da mamaki tana kallan Jadwan saboda ta riga ta san halin zuciya irin ta Jadwan. Se dai kuma ta ga kamar ba ta ji haushi ba bayan ita a wajenta kamar cin mutunci ne Kaseem ɗin ya musu.

"Ban ji ba.." ta faɗa tana ɗauke kai gami da yamutse fuska. Da dai ta fuskanci da gasken Jadwa take se ta haƙura ta ɗauki wayarta dan ba ta number Kaseem ɗin. Ba ta kai ga gama karanto mata number ba, wani kiran ya shigo cikin wayarta. Da sauri ta ɗaga wayar tana neman waje ta zauna.

"Hello Hajiya komai ya kammalu.." Daga can ɓangaren aka faɗa. Murmushi Mami ta yi tace

"Babu wata matsala kenan?"

"Ƙwarai kuwa. Se jiran sakamako kuma.."

"Na gode ƙwarai da gaske.. Ka sake tura min account ɗinka za ka ji ni.."

"Dena godiya Hajiya.. Aiki ne na yi a kan aiki, so duk ƙaruwarmu ce wannan ɗin.." daga can ɓangaren aka faɗa.

... A yatsine take bin ko ina na gidan da kallo fuskarta kamar tana kallan kashi ko wani abun makamancinsa. Da ƙyar ta buɗe baki tace

"Babu kowa a gidan ne?" Ta tambaya sanda ta baro soron gidan. Fitowar Ummeey kenan daga cikin ɗaki hannunta ɗauke da dadduma za ta gogewa Abeey kayansa ta ji maganar Mamin. Se ta juya ta kalleta, ta ɗauka za ta ji sallama daga bakinta se dai ba ta sake cewa komai ba se kallan Ummeeyn da take yi.

"Maraba.. shigo.." Ummeey ta faɗa fuskarta babu yabo ba fallasa.

"A'ah babu buƙata. Na zo wajen 'yata ne." Se a lokacin Ummeey ta fahimci wajen wadda ta zo ɗin, dan haka tace

"Tana ciki.." Daga haka ta yi gaba zuwa wajen da ta ajje dutsen guga dan ɗauka ta soma gugar. Tsaki Mami ta ja wani irin takaici na sake kamata. Wai a ce Lulu ke zaune cikin gidan nan a matsayin gidan aurenta. Ba ta taɓa tunani ba, ba kuma ta taɓa zato ba. Ita da Didi ce ma se ta haƙura tace dama haka ƙaddararta take, amma Lulu fa? Se kuma kawai ta yi murmushi tana tunanin ai kuma duk wata matsala ta zo ƙarshe tunda ta gama samun mafita. Tura ƙofar ɗakin Gwanin ta yi tana wurga idanunta dan ganin inda za ta hango Lulun tata. Se dai ba ta hangota ba, se da ta ida shiga ɗakin sannan ta hangeta a zaune kan gadon, Little na kan cinyarta yana bacci. Da sauri Mami ta ƙarasa tana faɗin

"Lulu.." Kamar a mafarki ta jiyo muryar Mamin, se dai ta san yaudarar kanta ne kawai take yi, amma duk da haka se ta ɗaga kanta dan tabbatarwa kanta da muryar da kunnuwanta suka jiye mata. Cikin sakannin da basu wuce 3 ba idanunta suka sauka a kan Mami. Ba ta san lokacin da ta yi wani uban tsalle ba, ta diro daga kan gadon, har ba ta san yanda aka yi Little ya sauka daga kan cinyarta ba. Rungume Mamin ta yi lokaci ɗaya tana fashewa da kuka. Ita ma Mamin rungumeta ta yi tana shafa bayanta a hankali ba tare da tace komai ba. Sun shafe wajen minti 1 a hakan sannan Mami tace

"Yi haƙuri.. mu je mu zauna.." ta yi maganar tana janta suka ƙarasa wajen gadon. Se da ta bi gadon da kallo tana wani yamutse fuska sannan ta zaunar da Lulu kana ta zauna ita ma. Se a lokacin ta kalli Lulun cike da tsoro tace

"Na shiga 3 ni Sadiya.. Lulu ke ce kika dawo haka? Kin ga yanda kika lalace a cikin kwanakin nan? Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un.." ta faɗa tana sake riƙo hannunta. Ita dai Lulu ta kasa cewa komai se sheshsheƙa da take yi.

"Ki yi shiru ki dena kukan kin ji? Matsalar mu ta zo ƙarshe.. Kamar yanda na alƙawarta miki zan fitar dake daga gidan nan, toh hakan ce za ta faru.."

"Amma Mami shi ne kika ƙi zuwa se yanzu?" Ta tambaya idanunta cike tafff da ƙwalla.

"Ki yi haƙuri daughter.. Ai dai ga ni na zo koh? Toh ki kwantar da hankalinki, dan kuwa ban tashi zuwa ba se da na gama samar mana da mafita.." Cikin matuƙar farin ciki Lulu tace

"Da gaske Mami? In tashi mu tafi yanzu?" Ta yi maganar tana ƙoƙarin miƙewa. Maidata zaunen Mami ta yi tana faɗin

End of Chapter 25Continue to the next chapter or choose another story below.

More Hausa novels

Browse all books →
Previous Login to Save Next