Ramadan Promo!All users that send a manual request for premium upgrade on sallah day will be granted for 1 month free.
Soyayyanovels
A Jini Take Izzata Part Two Complete Hausa Novel
A Jini Take Izzata Part Two Complete Hausa Novel
By Billyn Abdul
Login to keep your reading position saved.
Book Page Chapters
A Jini Take Izzata Part Two Complete Hausa Novel

A Jini Take Izzata Part Two Complete Hausa Novel

Author: Billyn Abdul
Chapter 32 of 122
About 8 min read
Chapter progress: 0%
Listen Mode
Listen to this chapter using your device voice.
Ready to listen from this chapter.
Free access is active. You can keep reading and download during this access window.

Book chapters

Choose a chapter and continue reading.

Start chapters
Chapter 1 1,645 words Chapter 2 1,690 words Chapter 3 1,680 words Chapter 4 1,637 words Chapter 5 1,676 words Chapter 6 1,594 words Chapter 7 1,597 words Chapter 8 1,655 words Chapter 9 1,192 words Chapter 10 1,647 words Chapter 11 1,678 words Chapter 12 1,698 words Chapter 13 1,656 words Chapter 14 1,617 words Chapter 15 1,693 words Chapter 16 1,658 words Chapter 17 1,692 words Chapter 18 1,521 words Chapter 19 1,684 words Chapter 20 1,600 words Chapter 21 1,688 words Chapter 22 1,589 words Chapter 23 1,692 words Chapter 24 1,344 words Chapter 25 1,685 words Chapter 26 1,699 words Chapter 27 1,685 words Chapter 28 1,660 words Chapter 29 1,664 words Chapter 30 1,468 words Chapter 31 1,665 words Chapter 32 Reading now Chapter 33 1,682 words Chapter 34 1,587 words Chapter 35 1,689 words Chapter 36 1,687 words Chapter 37 1,610 words Chapter 38 1,677 words Chapter 39 1,679 words Chapter 40 1,632 words Chapter 41 1,698 words Chapter 42 1,661 words Chapter 43 1,690 words Chapter 44 1,277 words Chapter 45 1,514 words Chapter 46 1,679 words Chapter 47 1,689 words Chapter 48 1,694 words Chapter 49 1,623 words Chapter 50 1,616 words Chapter 51 1,618 words Chapter 52 1,499 words Chapter 53 1,697 words Chapter 54 1,686 words Chapter 55 1,630 words Chapter 56 1,694 words Chapter 57 1,548 words Chapter 58 1,682 words Chapter 59 1,389 words Chapter 60 1,613 words Chapter 61 1,497 words Chapter 62 1,686 words Chapter 63 1,669 words Chapter 64 1,675 words Chapter 65 1,613 words Chapter 66 1,697 words Chapter 67 1,627 words Chapter 68 1,670 words Chapter 69 1,638 words Chapter 70 1,682 words Chapter 71 1,543 words Chapter 72 1,563 words Chapter 73 1,611 words Chapter 74 1,680 words Chapter 75 1,616 words Chapter 76 1,629 words Chapter 77 1,662 words Chapter 78 1,575 words Chapter 79 1,507 words Chapter 80 1,608 words Chapter 81 1,674 words Chapter 82 1,651 words Chapter 83 1,516 words Chapter 84 1,631 words Chapter 85 1,699 words Chapter 86 1,652 words Chapter 87 1,633 words Chapter 88 1,651 words Chapter 89 1,674 words Chapter 90 1,606 words Chapter 91 1,688 words Chapter 92 1,593 words Chapter 93 1,654 words Chapter 94 1,396 words Chapter 95 1,655 words Chapter 96 1,599 words Chapter 97 1,693 words Chapter 98 1,665 words Chapter 99 1,653 words Chapter 100 1,658 words Chapter 101 1,700 words Chapter 102 1,639 words Chapter 103 1,651 words Chapter 104 1,671 words Chapter 105 1,547 words Chapter 106 1,695 words Chapter 107 1,585 words Chapter 108 1,675 words Chapter 109 1,641 words Chapter 110 1,674 words Chapter 111 1,509 words Chapter 112 1,615 words Chapter 113 1,674 words Chapter 114 1,691 words Chapter 115 1,694 words Chapter 116 1,688 words Chapter 117 1,681 words Chapter 118 1,656 words Chapter 119 1,670 words Chapter 120 1,698 words Chapter 121 1,689 words Chapter 122 1,691 words

.. "Yarinyar nan ba ta da lafiya Affan. Ka tabbatar ta ci abinci sannan ta sha magani.. Zazzaɓi ne ya kamata da sauri haka, idan akwai maganinsa cikin na jiyan da ka siyo se ka ba ta. Idan kuma babu zuwa safiya se a maidata asibitin.."

"Toh Ummeey." Ya faɗa yana soma takawa.

"Amm ba ka ji ba?" Ummeey ta faɗa tana kallansa. Se ya dawo yana faɗin

"Na'am.."

"Ya kamata idan ta samu sauƙi ka kaita ta leƙa ko da er uwarta ne, za ta ji daɗi."

"In Sha Allah.."

"Allah ya ba da lafiya.. Ameen." Daga haka ya wuce ɗakin nasa.

A nutse ya saka hannu ya yaye labulen idanunsa a kan gadon. Tana kwance tana baccin da be daɗe da ɗaukarta ba tun bayan da ta farka ta yi Sallah. Ya ƙarasa ya nemi gefen gadon ya zauna, kansa a ƙasa ya faɗa duniyar tunanin da yanzun ta zama abokiyarsa. Ya kai wajen minti 2 zaune a hakan kafin ya soma jin tarinta. Da sauri ya juya yana kallanta lokacin da take ƙoƙarin tashi hannunta a kanta da har lokacin yake juya mata. Miƙewa ya yi se dai be yi yunƙurin yin wani abu ba ganin da ya yi ta ma tashi zaunen da kanta. Yamutsa fuska take yi se dai ba za ka gane kuka take yi ba se ka kalli fuskarta ka ga hawayen da ke zuba a kan fuskarta. Kwata kwata baccin ya ƙi ɗaukarta yanzu, ta rasa yanda za ta yi. Gaba ɗaya ji take kamar an sauyata. Sam ba ta san da shigowarsa ba se lokacin da ta ji muryarsa yana faɗin

"Ya kike jin jikin naki?" Ya tambaya yana kallanta. Da sauri ta kalle shi ba tare da ta shirya ba. Se kuma ta yi saurin ɗauke kan nata tana faɗin

"Ba sauƙi.." Ta faɗa tana cigaba da yamutsa fuska. Murmushi ya suɓuce masa ba tare da ya shirya ba. Ya ɗan girgiza kansa yana faɗin

"Kukan fa?" Ba ta ba shi amsa ba se shirin komawa kwanciyar da ta yi. Ya yi saurin faɗin

"Kar ki kwanta.." ya yi maganar yana ƙarasawa inda ya ga ledar magangunanta ya ɗauko. Sannan ya ja abincin da Ummeey ta kawo ya matso da shi gabanta. Neman waje ya yi ya zauna a kan bedside drawer bayan ya matso da ita kusa da gadon. Ba tare da ya kalleta ba ya soma fito da maganin. Ita kam Lulu da ko ƙamshin maganin ta tsana har idanunta sun sake tara sabuwar ƙwalla. Ɗagowar da ze yi ya kalleta ya ga tana girgiza kai tana kallansa fuskar nan a narke kamar ba Lulu ba. Ɗaga mata kai ya yi alamar "Lafiya?" Da sauri kuwa ta buɗe baki tace

"Wallahi ba na son magani.. Ba na so wallahi.." Ta faɗa daidai lokacin da wasu hawaye suka zubo a kan fuskarta. Ɗan lumshe idanunsa ya yi yana miƙewa yace bayan ya sake matsar da abincin kusa da ita.

"Ni ma ba magani na ce ki sha ba. Maza ki ci abinci.." Ya yi maganar yana nuna mata abincin. Girgiza kai nan ma ta yi tace

"A ƙoshe nake.." ta faɗa da sauri. Shi ma girgiza kan ya yi sannan yace

"Ba ki ƙoshi ba. Ko ki ci abincin nan ko kuma ki sha maganin."

"Don Allah ka yi haƙuri wallahi duka ba na so. Bakina babu daɗi, kuma so nake na kwanta." Ta yi maganar tana lumshe idanunta da suka janye saboda ciwon kan.

"Maganin kike so kenan?" Ya tambaya yana kallanta, be jira amsarta ba yace

"Well.." Se ya yi maganar yana soma ɓallo maganin daga cikin gidansa. Kamar za ta saka ihu haka ta ji, ji take kamar ta ƙyale shi ta yi kwanciyarta, se dai ba ta jin za ta iya aikata hakan. Dan haka se janyo abincin kawai ta yi ta shiga kaiwa bakinta ba tare da tana bari ta tauna ba, ita dai kawai dan ya ga ta ci abincin ya ƙyaleta, ya dena mata zancen maganin da tun kafin ta kai shi bakinta take jin kamar ta yi amai. Babu laifi ta ci abincin duk da kawai turawa take yi dan ba za ta iya cewa ga ɗanɗanonsa ba. Se dai tun kafin ta kai ga shan ruwa ta ji gaba ɗaya abincin na neman dawo mata. Hakan ne ya sanyata ƙoƙarin miƙewa. Se dai tana yin ƙoƙarin miƙewar se kuwa ta yi luuu ta koma tana shirin zubewa, ya yi saurin saka hannunsa ya riƙota. Idanunta gaba ɗaya a rufe suke saboda yanda take jin gaba ɗaya garin na juya mata kamar ze faɗo mata a kai, ga kuma Jikinta dake rawa bayan wani mummunan zafi da ya ɗauka. Yanda ya riƙota ɗin ya sanya suka ɗan samu kusanci, wanda hakan ya janyo har hucin zazzafan numfashin da take fitarwa yana iya ji. Tunda ta yi ƙoƙarin faɗuwar nan se ta kasa miƙewa duk da yanda har lokacin take jin aman na taho mata amma ta kasa wani yunƙuri. Se cigaba da kakarin da ta yi, sam be fahimci abin da take ƙoƙarin yi ba, se ƙoƙarin ajjeta da ya fara yi a kan gadon, ba tare da ta shirya ba gaba ɗaya abincin da ta ci ya dawo, cikin rashin sa'a kuma rabinsa duka ya sauka ne a jikin Gwani.

"Ya ilahy.." ya furta a kan laɓɓansa yana kallan yanda ta ɓata shi da kuma ƙasan gadon. Se kuma ta koma sauke numfashi tana girgiza kai saboda yanda take jin jikinta kamar ana sassara mata shi. Se kuma ta ɗan buɗe idanunta da ƙyar ta kalle shi daidai lokacin da yace

"Tashi ki je ki gyara jikin ki.." ya faɗa ba tare da ya sake kallan jikinsa ba. Ya kuma faɗa ne kawae duk da a yanda take ya san ba za ta iya wani tashi ta je ta gyara jikin nata ba. Cigaba ta yi da kallansa ta yi tunanin ze rufeta da faɗa ne ko kuma wani abun makamancin hakan, se dai ga mamakinta se ta ji be damu da abin da ta masa ɗin ba face faɗa mata da yake yi ta je ta gyara jikinta.

"Ka yi haƙuri don Allah.." ta yi ƙarfin halin faɗar hakan. Idanunsa ya sanya cikin nata, sannan ya lumshe su lokaci ɗaya yana jinjina kansa. Gane abin da yake nufi ya sanyata sauke ajiyar zuciya. Se ta fara ƙoƙarin tashi idanunta a rufe saboda tsoro take ji, dan idan a buɗe idanun suke ba za ta iya ko da ƙoƙarin ba ne. Ganin yanda take tangaɗi kamar wata er maye ya sanya shi kawai saka hannunsa ya riƙota. Taimaka mata ya yi zuwa banɗakin duk da yanda take ta noƙewa da nufin ya barta za ta iya kai kanta. Amma sanin da ya yi ba iyawar za ta yi ba ya sanya shi ƙyaleta har se da ya kaita banɗakin. Yana shirin juyawa dan ficewa ya tuna shi ma fa jikinsa a ɓace yake. Duk da haka dai se ya fice ɗin kawai. A bakin ƙofar ya tsaya yana tsumayin fitowarta. Se dai kafin lokacin ya saka hannunsa ya cire rigar jikinsa da ta ɓaci ya musanyata da wata kafin ta fito. Se da ya shafe wajen minti 5 a tsaye amma har zuwa lokacin ba ta fito ba. Ya ɗan gyara tsayuwarsa yana cigaba da jiran fitowar tata. Se dai har zuwa bayan wasu mintuna ba ta fito ba. A hankali ya matsa bakin toilet ɗin se dai ga mamakinsa tana zaune hannunta dafe da kanta.

"Ya Allah!" Ya faɗa yana ɗan cije gefen lips ɗinsa na ƙasa. Kamar ba wani abun ze yi ba ya ɗan ƙara tsayawa na tsawon sakanni sannan ya ƙarasa cikin toilet ɗin. Sam ba ta san da shigowarsa ba har se da ta ji hannunsa ɗore a kan hijab ɗinta lokaci ɗaya kuma yana faɗin

"Daure ki tashi.." Ya yi maganar babu yabo babu fallasa kuma a hankali. Se ta ɗaga kai da sauri a kuma tsorace. Se dai yanda kanta ya sara ya sanyata saurin runtse idanunta. Da hakan ya yi amfani da hannunsa wajen soma ƙoƙarin yaye hijab ɗin jikinta da shi ne ya ɓaci. A tsorace duk da yanda take jin jikinta ta yi ƙarfin halin danne hijab ɗin da hannunta tana girgiza kai, jajayen idanunta cike da hawaye. Iska ya ɗan fesar daga bakinsa sannan ya ɗan girgiza mata kai shi ma fuskarsa babu yabo babu fallasa. Ganin da ya yi ba ta da niyyar barinsa ya yi abin da ya soma, kuma ya gaji da jiran nata ya sanya shi saka hannunsa ya ɗauke nata hannun da ta danne hijab ɗin. Babu ɓata lokaci kuma ya yaye hijab ɗin gaba ɗaya. Kawai se ta fashe da kuka tana yin ƙasa da kanta. Shi ko bi ta kanta ma be yi ba se jefa hijab ɗin da ya yi cikin wani bokiti sannan ya ɗauki ruwa a buta ya sake matsawa kusa da ita. Duk da yanda take kukan, tana kuma jin tsoron yi masa rashin kunya saboda kirkinsa gareta da kansa ya gyara mata jikin nata. Sannan ya haɗa da hijab ɗin nata da rigarsa ya wanke su tass ba tare da jin wani ƙyashi ba. Se da ya gama wanke duka sannan ya fitar da su ya shanya kana ya dawo cikin ɗakin. Zuwa lokacin har ta kwanta ta lulluɓe jikinta, dan ko tashi ta je ta ɗauki wani hijab ɗin kasawa ta yi. Tsayawa ya yi yana kallanta ta cikin abin lulluɓar, ganin yanda ta takure waje ɗaya kamar munafuka. A nutse ya ƙarasa ya kalli fuskarta da ta yi mugun fayau kamar wadda ta yi wata da watanni tana ciwo. Ya ɗan lumshe idanunsa yana jin ya zama dole gobe ya kaita asibiti ko da allura ne su mata se tafi mata sauƙi a kan maganin. A hankali ya kai hannunsa kan wuyanta ya ɗan taɓa, fiye da ɗazu ma yanzu jikin ya sake yin zau kamar garwashi. Ya sauke ajiyar zuciya yana ɗakko wayarsa daga aljihu ya kalla sannan ya maidata, se kuma ya soma takawa ya bar wajen. Bayan wajen minti 2 ya dawo hannunsa ɗauke da wani ƙaramin towel. Kai tsaye kan bedside drawer ɗin nan ya sake zama, a hankali yace

End of Chapter 32Continue to the next chapter or choose another story below.

More Hausa novels

Browse all books →
Previous Login to Save Next