Ramadan Promo!All users that send a manual request for premium upgrade on sallah day will be granted for 1 month free.
Soyayyanovels
A Jini Take Izzata Part Two Complete Hausa Novel
A Jini Take Izzata Part Two Complete Hausa Novel
By Billyn Abdul
Login to keep your reading position saved.
Book Page Chapters
A Jini Take Izzata Part Two Complete Hausa Novel

A Jini Take Izzata Part Two Complete Hausa Novel

Author: Billyn Abdul
Chapter 76 of 122
About 8 min read
Chapter progress: 0%
Listen Mode
Listen to this chapter using your device voice.
Ready to listen from this chapter.
Free access is active. You can keep reading and download during this access window.

Book chapters

Choose a chapter and continue reading.

Start chapters
Chapter 1 1,645 words Chapter 2 1,690 words Chapter 3 1,680 words Chapter 4 1,637 words Chapter 5 1,676 words Chapter 6 1,594 words Chapter 7 1,597 words Chapter 8 1,655 words Chapter 9 1,192 words Chapter 10 1,647 words Chapter 11 1,678 words Chapter 12 1,698 words Chapter 13 1,656 words Chapter 14 1,617 words Chapter 15 1,693 words Chapter 16 1,658 words Chapter 17 1,692 words Chapter 18 1,521 words Chapter 19 1,684 words Chapter 20 1,600 words Chapter 21 1,688 words Chapter 22 1,589 words Chapter 23 1,692 words Chapter 24 1,344 words Chapter 25 1,685 words Chapter 26 1,699 words Chapter 27 1,685 words Chapter 28 1,660 words Chapter 29 1,664 words Chapter 30 1,468 words Chapter 31 1,665 words Chapter 32 1,699 words Chapter 33 1,682 words Chapter 34 1,587 words Chapter 35 1,689 words Chapter 36 1,687 words Chapter 37 1,610 words Chapter 38 1,677 words Chapter 39 1,679 words Chapter 40 1,632 words Chapter 41 1,698 words Chapter 42 1,661 words Chapter 43 1,690 words Chapter 44 1,277 words Chapter 45 1,514 words Chapter 46 1,679 words Chapter 47 1,689 words Chapter 48 1,694 words Chapter 49 1,623 words Chapter 50 1,616 words Chapter 51 1,618 words Chapter 52 1,499 words Chapter 53 1,697 words Chapter 54 1,686 words Chapter 55 1,630 words Chapter 56 1,694 words Chapter 57 1,548 words Chapter 58 1,682 words Chapter 59 1,389 words Chapter 60 1,613 words Chapter 61 1,497 words Chapter 62 1,686 words Chapter 63 1,669 words Chapter 64 1,675 words Chapter 65 1,613 words Chapter 66 1,697 words Chapter 67 1,627 words Chapter 68 1,670 words Chapter 69 1,638 words Chapter 70 1,682 words Chapter 71 1,543 words Chapter 72 1,563 words Chapter 73 1,611 words Chapter 74 1,680 words Chapter 75 1,616 words Chapter 76 Reading now Chapter 77 1,662 words Chapter 78 1,575 words Chapter 79 1,507 words Chapter 80 1,608 words Chapter 81 1,674 words Chapter 82 1,651 words Chapter 83 1,516 words Chapter 84 1,631 words Chapter 85 1,699 words Chapter 86 1,652 words Chapter 87 1,633 words Chapter 88 1,651 words Chapter 89 1,674 words Chapter 90 1,606 words Chapter 91 1,688 words Chapter 92 1,593 words Chapter 93 1,654 words Chapter 94 1,396 words Chapter 95 1,655 words Chapter 96 1,599 words Chapter 97 1,693 words Chapter 98 1,665 words Chapter 99 1,653 words Chapter 100 1,658 words Chapter 101 1,700 words Chapter 102 1,639 words Chapter 103 1,651 words Chapter 104 1,671 words Chapter 105 1,547 words Chapter 106 1,695 words Chapter 107 1,585 words Chapter 108 1,675 words Chapter 109 1,641 words Chapter 110 1,674 words Chapter 111 1,509 words Chapter 112 1,615 words Chapter 113 1,674 words Chapter 114 1,691 words Chapter 115 1,694 words Chapter 116 1,688 words Chapter 117 1,681 words Chapter 118 1,656 words Chapter 119 1,670 words Chapter 120 1,698 words Chapter 121 1,689 words Chapter 122 1,691 words

"Wallahi babu abin da kika min Maimuna. Idan ma kin min na yafe miki. Ki yi haƙuri dai ki ɗauki kuɗin nan ki koma garinku, Zan neme ki zuwa nan gaba. Sannan ki tabbatar kin riƙe min sirri, kamar yanda muka bar shi a wajen ke ma ki bar shi a wajen. Hakan ne kaɗai kuma ze sa ki din ga ganin aikena duk sanda na ga dama ba se ƙarshen wata ba." Da dai Maimuna ta ga Mom ta dage, haka tana ji tana gani ta shirya kayanta ta bar gidan har da kuka. Dan babu ƙarya gidan ya mata, tana yanda ta ga dama a cikin gidan, ga wadata, ga uwa uba kuɗin da take samu duk ƙarshen wata. Se dai ta wani ɓangaren tana jin ɗan sanyi idan ta tuna da kuɗin da Mom ɗin ta bata kafin ta fito. Se a lokacin sannan hankalin Mom ya kwanta da ta buɗe idanunta ta ga babu Maimuna cikin gidan.

Haka rayuwa ta cigaba da garawa, Areef kullum girma da wayo yake ƙara yi. Har kuma lokacin madara yake sha. Dan kuwa tun ranar da aka haife shi Mom ta gwada shayar da shi amma sam yaron nan ya ƙi karɓa. Idan ma aka tilasta shi se ya fashe da kuka. Haka ya din ga musu kuka, ga yunwa yake ji, ga shi ita kuma babu ruwan mama ko kaɗan, ga shi ma yaron ya ƙi kamawa ko hakan ze sa ya zo. Da dai ta ga da gasken ba karɓa ze yi ba ga shi kuma yunwar yake ji, se ta sanarwa da Daddy aka siyar masa madara. Aikuwa sosai ya sha madarar, ya shanye wadda aka haɗa masa tass. Daga nan kuwa se ya hau bacci. Tun daga ranar se ya kasance madara ita ce abincinsa, dan kuwa har lokacin tana cigaba da gwada shayar da shi amma ba ya karɓa se madarar. Tun tana gwadawa har ta zo ta haƙura ta cigaba da ba shi madarar kawai. Zuwa lokacin da Areef ya soma tasawa se ya kasance yaron na da wani mugun farin jini, ga wani shahararren kyau da kullum ƙaruwa yake yi. Har wasu en uwan Mom kan mata gori wataran da faɗin

"Daɗin auren miji kyakkyawa kenan.. Yanzu dai kalli ɗanki Salma.." Ita kuma a lokuta da dama amsarta ba ta wuce.

"Kwa ci kanku.." Soyayya Mom ke nuna masa kamar za ta maida shi ciki, haka Daddy ma jinsa yake har ƙasan ransa, sosai yake ƙaunar yaron. Dan tun da ya same shi se ya zamana komai Areef ɗin, ba shi da wani zance idan ba na Areef ɗin ba. Hakan ba ƙaramin yi wa Mom daɗi yake ba, musamman idan a gaban Mommah ne, se ta ji kanta ya ƙara girma, ta yi ta buɗe hanci kenan tana jijjiga kai ita a lallai dole me ɗa. Se dai me?? Tun da Areef ɗin ya soma wayo se wata matsala kuma ta tunkaro mata, matsalar da ta so bata tsoro har ta ɗaga mata lissafi. Ƙalubale na farko da Mom ta soma fuskanta shi ne yanda wata irin soyayya da shaƙuwa ta ƙullu tsakanin Mommah da Areef. Kai se ka ce iyayensa biyu ne cikin gidan nan. Yanda yakewa Mommah abubuwa idan ba ka san uwarsa ba se ka ɗauka ita ta haife shi. Ai tuni Mom ta tashi tsaye a kansa, ta shiga hana shi abubuwan da yake yi. Daga ƙarshe ma se ta dena barinsa duk inda ta san ze haɗu da Mommah. Se dai ƙalubale na biyu da ya fi kowanne ɗaga mata hankali shi ne wayar gari da aka yi Areef na kiran Hajiya Sa'adah da suna Mommah. Lokacin kam har duka ta so yi masa amma ta kasa, ta kama kunnansa ta ja ranta a ɓace tace

"Kar na sake ji ka kira waccan matar da Mommah ka ji koh?" Shiru ya yi kawai yana kallan Mom ba tare da yace komai ba. Dan kuwa tun yana ƙarami yake da shegen taurin kai da wata iriyar zuciya. Wadda duk sangartawar da Mom ta masa ne ya janyo hakan. Wai a hakan ma dan Daddy na kwaɓarsa ne yana tsawatar masa. Da dai ta ga idan ta yi faɗa har ta gama ba lallai ya tanka mata ba, se ta janyo shi tana murmushi tace

"My boy.. Kar ka sake kiranta da Mommah ka ji? Ka ga ai ba ita ce Mom ɗinka ba?" Ta ƙare tana murmushi.

"Toh." Ya amsa da hakan kawai.

"Dats my boy.." Ta faɗa tana kama kumatunsa.

Ta ɗauka ba za ta sake ji ya kira Hajiya Sa'adah da Mommah ba, se dai kamar ma tura shi ta yi dan kuwa cigaba ya yi da kiranta da hakan yana kuma cigaba da zuwa wajenta, dan kuwa haka nan kawai yake son zuwa wajen matar kuma tun yarinta. Ita kanta Mommahn ba ta san dalilin da ya sa ta tashi da matsananciyar ƙaunar Areef ɗin ba. Idan a rana be zo sashenta ba kuma ba su haɗu a sashen Daddy ba, se ta ji kamar ta bi shi sashensu ta gan shi. Jinsa take kamar ɗanta da ya rasu. Daga nan se rayuwar gidan ta soma chanjawa. Dan kuwa a lokacin ne Mom ta shiga fito da sinƙi_sinƙin rashin mutunci. Da ta ga babu haza, Mommahn ta ƙi ƙyale mata ɗa se ta shiga yada habaici da maganganu marasa daɗi game da Mommah. Waɗanda ta san ko da a da ba su taɓata ba yanzun dole su taɓata. Da Mom za ta gane ƙaunarsu daga Allah ce da ta ƙyale su ta rabu da su. Se dai ina, ita sam ba ta so ta ga wani abu da ze kawo kusanci tsakanin Mommahn da Areef ɗin. Ita da a so samunta ne ma sun tashi da matsananciyar ƙiyayyar junansu, da se tafi kowa farin ciki. Amma tun da hakan ta faru se ta tsiro da tura shi makarantar kwana tun a primary. A nan ne Daddy ya nuna mata ba ta isa ba. Da dai ta ga da gasken Daddy ba ze amince a kai shi makarantar da take so ba se ta huce haushinta a kan Mommah da ke cikin ɗakin lokacin da suka sake yin maganar da Daddy. Areef na gefen Mom yana danna wayar Mommah da ya je ta buɗe masa yake game. Ta saka hannu ta fuzge wayar daga hannun Areef tace cikin ɗaga murya

"Dallah can ba ni wayar nan kafin na yi rashin kirki.." Ta ƙare tana ajje wayar a kan centre table ɗin gabanta. Sannan ta ɗora da

"A ƙyale min ɗa mana.. A ƙyale min ɗa haka nan.. Idan mutum ya haifa ya din ga shishshigewa al'amuransa.. Haba.." Ta kai ƙarshe tana sakin tsaki gami da miƙewa tsaye dan ficewa daga ɗakin.

"Salma.." Daddy ya faɗa a kausashe dan ya fahimci abin da take nufi. Se ta koma ta zauna ba tare da ta kalli Daddyn ba. Ya sauke ajiyar zuciya yana faɗin

"Kar ki ƙara maimaita wannan kuskuren.. Idan ba haka ba zan ɗauki mataki a kai. Ɗa kuma ke kika haife shi mun san wannan.. Amma kuma idan da kaara ai ɗan Sa'adah ne."

"A'ah wallahi ba nata ba ne tun da ba ita ta haifa min shi ba.."

"Ya isa haka.. Je ki." Daddy ya katseta da faɗin hakan. Se kuwa ta ja hannun Areef suka fice daga ɗakin fuuu kamar za ta tashi sama.

"Ki yi haƙuri.. Allah ze kawo miki masu albarka.. Rayayyu kuma lafiyayyu." Daddy ya faɗa a tausashe yana kallan Mommah. Se ta yi murmushin nan na yaƙe da ake cewa ya fi kuma ciwo sannan tace

"Babu komai Rankayadaɗe.. Allah Ya amsa addu'arka." Tun daga ranar Mommah ta yi ƙoƙarin fita daga sabgar Areef duk da yanda zuciyarta ba ta son hakan, amma dan son a samu zaman lafiya ya sanyata janye jikinta daga al'amuransa. Shi kam ko a jikinsa haka idan yana so ze zo sashenta ya yi wasansa, idan ya gaji ya tafi nasu sashen. A yanzu dai haka Mommah ta din ga janye jikinta daga gare shi, se dai idan ya zo se su yi ta abinsu da Baba Atine. Hakan ba ƙaramin daɗi ya yi wa Mom ba, duk da dai ita da a so samu ne ma su dena magana kwata kwata. Amma har zuwa lokacin ya ƙi dena ce mata Mommah, haka dai ta haƙura ta rabu da shi dan ta ga alama ba ze dena ba.

Haka rayuwa ta cigaba da tafiya, wasu abubuwan sun chanja ya yin da wasu ba su chanja ba, ciki kuwa hadda halayyar Mom. Arziƙin Alhaji Matawalle kuwa ban da haɓaka kullum babu abin da yake yi. A cikin tsukun ne kuma Hajiya mahaifiyar Alhaji Matawalle ta rasu bayan gajeriyar rashin lafiya. Ba ƙaramin taɓasu mutuwar ta yi ba musanman da babu wanda ya taɓa kawo mata mutuwar a irin wannan lokacin. Haka dai suka haƙura suka cigaba da yi mata addu'a. Cikin ikon Allah kuma har zuwa yanzun babu wadda ta sake samun ciki a cikinsu. Duk da haka Mommah ba ta gaji ba, wajen addu'a Allah Ya bata ko ta samu ta ga jininta a duniya, ta kuma huta da gorin da Mom ke mata, wanda ba ta gajiya da shi sam kamar ita ma wayonta ko dabararta ne ya bata Areef. A haka rayuwa ta cigaba da tafiya, har zuwa lokacin da Areef ya shiga University, bayan tataɓurzar da aka sha tsakanin Mom da Daddy a kan fitarsa ƙasar waje. Mom ta kai wajen sati tana bibiyar Daddy a kan fitar tasa, amma kullum amsa ɗaya take samu, ta je kawai. Yau ma kamar kullum ta shigo ɗakin ta nemi waje ta zauna.

"Yallaɓai magana na zo mu yi da kai." Se da ya ɗaga kai ya kalleta sannan yace

"Ina jin ki.."

End of Chapter 76Continue to the next chapter or choose another story below.

More Hausa novels

Browse all books →
Previous Login to Save Next