Ramadan Promo!All users that send a manual request for premium upgrade on sallah day will be granted for 1 month free.
Soyayyanovels
A Duniyata Part One Complete Hausa Novel
A Duniyata Part One Complete Hausa Novel
By Billyn Abdul
Login to keep your reading position saved.
Book Page Chapters
A Duniyata Part One Complete Hausa Novel

A Duniyata Part One Complete Hausa Novel

Author: Billyn Abdul
Chapter 13 of 84
About 8 min read
Chapter progress: 0%
Listen Mode
Listen to this chapter using your device voice.
Ready to listen from this chapter.
Free access is active. You can keep reading and download during this access window.

Book chapters

Choose a chapter and continue reading.

Start chapters
Chapter 1 1,700 words Chapter 2 1,700 words Chapter 3 1,700 words Chapter 4 1,700 words Chapter 5 1,700 words Chapter 6 1,700 words Chapter 7 1,700 words Chapter 8 1,700 words Chapter 9 1,700 words Chapter 10 809 words Chapter 11 1,700 words Chapter 12 1,700 words Chapter 13 Reading now Chapter 14 1,700 words Chapter 15 1,700 words Chapter 16 1,700 words Chapter 17 1,700 words Chapter 18 1,700 words Chapter 19 1,700 words Chapter 20 1,700 words Chapter 21 1,700 words Chapter 22 1,700 words Chapter 23 1,700 words Chapter 24 671 words Chapter 25 1,700 words Chapter 26 1,700 words Chapter 27 1,700 words Chapter 28 1,425 words Chapter 29 1,700 words Chapter 30 1,700 words Chapter 31 1,700 words Chapter 32 400 words Chapter 33 1,700 words Chapter 34 1,700 words Chapter 35 1,700 words Chapter 36 1,148 words Chapter 37 1,700 words Chapter 38 1,700 words Chapter 39 1,700 words Chapter 40 1,700 words Chapter 41 1,700 words Chapter 42 1,700 words Chapter 43 956 words Chapter 44 1,700 words Chapter 45 1,700 words Chapter 46 1,700 words Chapter 47 1,700 words Chapter 48 1,700 words Chapter 49 1,700 words Chapter 50 1,700 words Chapter 51 30 words Chapter 52 1,700 words Chapter 53 1,700 words Chapter 54 1,484 words Chapter 55 1,700 words Chapter 56 1,700 words Chapter 57 1,700 words Chapter 58 1,700 words Chapter 59 1,700 words Chapter 60 1,700 words Chapter 61 1,373 words Chapter 62 358 words Chapter 63 1,700 words Chapter 64 1,700 words Chapter 65 1,700 words Chapter 66 1,700 words Chapter 67 1,700 words Chapter 68 1,700 words Chapter 69 1,700 words Chapter 70 1,700 words Chapter 71 1,700 words Chapter 72 1,700 words Chapter 73 1,700 words Chapter 74 1,700 words Chapter 75 1,700 words Chapter 76 1,700 words Chapter 77 1,700 words Chapter 78 1,700 words Chapter 79 1,700 words Chapter 80 1,700 words Chapter 81 1,700 words Chapter 82 1,700 words Chapter 83 1,700 words Chapter 84 642 words

kulashi ba anji muryarta a matsayinsa na qanin mahaifi a gareta. Sakaya qofar kawai tayi ta sake zuge labulen sosai sannan ta wuce uwar dakin ta yadda ba zata tsaya bata lokacin jin meke faruwa a tsakiyar gidan nasu ba,domin ita din tana cikin jerin sahun irin mutanen nan ne dai basa shiga abinda bai shafesu ba,wanda ya shafesun ma sai tura takai bango,bata da magana sam sam bare hayaniya. Wannan hali nata da siffarta ta sanyi da sauqin hali da kuma yauqinta ya sanya da yawa suke mamakin WANNAN DABI'A TATA......Dabi'ar da har yanzu su kansu basu da cikakken yaqinin a kanta,duk da cewa suna kallon gamsassun hujjoji ai sun gama bayyana a fili a game da ita. Babban bedroom ne qwarai wanda iya dauke gado da wardrobe guda bibbiyu,sai dressing mirror guda daya. Duk da cewa wai daga bacci aka tashi amma dakin neat yake,komansa akan tsari,ga kuma wani sassanyan qamshi da yake fita kaman dai yadda falon yake. Daya gadon da yake shine qarami ta nufa,wanda ke lullube da lallausar shimfida da tattausan blanket peach color. Tun batakai ga zama ba rurin da wayarta keyi ya cika mata kunnuwa,sai ta haye saman gadon ta lalubo wayar ta cirota daga gefan pillow dinta. Iphone 15 ce dake dauke da wata irin cover me kyau data dace da wayar da kuma me wayar gaba daya,ta zubawa sunan dake yawo saman screen din idanu *_ibraheem_* ya nuna mata. Wani gajeran murmushin gefan baki ta saki dake cakude da wani emotion. Siririn tsaki taja saman harshenta,ta fara qoqarin rejecting kiran "Done and dusted.......an gama da shafinka tun a jiya" Ta fada qasan ranta tana tuna yadda al'amura suka tafi mata successful kaman yadda aka saba. Sai data tabbatar tayo blocking ta kuma shafe duk wani abu daya shafeshi cikin wayar,bata bar hujja ko qarama ba da zata nuna tsohuwa ko sabuwar alaqa ko kuma mu'amala tsakaninta dashi ba. Ta sake bin wayar ta tabbatar komai ya koma kaman da,sannan ta duba wata ma'ajiya ta daban ta lalubi wata number ta kira ta kara wayar a kunnenta. Bugu biyu aka daga ana sallama cikin zaquwa da zumudi "Ina fatan saqon ya riskeki?" Tayi tambaya zuwa ga daya sashen "Ya riskeni qwarai kuwa tun a daren jiya.......ina godiya......na gode sosai,ina me baki haquri kuma akan sabanin Fahintar da nayi miki a farko.....gashi kuma ko sunanki ma ban sani ba" "Ba buqatar hakan......infact ma daga yau ba zaki sake samu na ko jin muryata ba......abinda na baki kiyi qoqarin tattalashi,ki kuma boyeshi daga sanin mijinki.......abu na qarshe saiki tayashi jiyya.....kinsan yadda zaki sanya masa tawakkali cikin zuciyarsa,don nayi imani ya zuwa yanzu zaiyi wahala bai zauce ba,na barki lafiya" Ta yanke kiran ba tare data barta tace komai ba,duk da tarin abubuwan fada masu yawa da take dasu take kuma son gaya matan. Itama goge number dinta tayi ta kuma sakata a sahun sauran tarin lambobin dake akwatin katangewa dake cikin wayarta. Layinta layi ne dake da wani irin tsaro na musamman,wanda ba kowacce number da bata yarjewa bace take iya samunta. Tana da ire irensa sunfi guda ashirin,duk kuma sanda take da muradi ra'ayi ko kuma buqatar hakan ya taso tana iya sauke wanda taga dama ta dora wani. Tana shirin shigewa duvet ta kwanta wani kiran ya sake shigo mata. Batason takura sam,sai taja tsaki tana kallon fuskar wayar. Shine din dai,batasan me yasa ya matsa da yawa ba,bataso a yanzun akwak enough kudi a hannunta,tanaso taje hutu koda na taqaitaccen lokaci ne kafin ta fada zuwa wani agenda din. "Tsautsayi da alama keta kiranka" Ta furta qasa qasa ta jawo wayar tana rejecting kiran shima sannan ta kashe kiran gaba daya ta jefar da wayar. Kanta ta mayar ta qudundune sosai cikin blanket din,saidai ko minti biyar bata yi ba cikakke ta miqe zumbur kamar wadda aka tsikara,ta sauko daga saman gadon tana qoqarin daure gashinta me santsi dake rufe gefan fuskarta. Kyakkyawar drawer dinta ta bude banqaran hijabs,ta fidda wani qaramin farin hijab cikin jerin hijban da take amfani dasu a lokaci irin haka idan zata shiga wanka. Sama kanta ta zurashi,wanda wannan ya fidda kyakkyawar fuskarta tsakanin hijab din,ya kuma fidda wata sihirtacciyar kama akan fuskar tata. Towels dinta ta nufa ta zari guda daya,sannan ta matsa gefan daya drawer dinta ta jawo ta can qarshe ta fidda set na kayan wankanta dake cikin wani dan kyakkyawan kwando kaman kwandon kaba,ta rataye toweldon saman kafadarta ta fara takawa a hankali tana fita a dakin tare da sake gauke fuskarta da kyau wanda kusan haka dabi'arta take duk sanda zata fita zuwa ainihin tsakar gidan nasu,duk da dama ita din ba matum bace data cika fara'a. Duka duka mutanen dake sabgarsu a safiyar ranar cikin sararin tsakar gidan ba zasu wuce mutum biyar ba. Dukkaninsu kuma mata ne da a shekaru suke qasa da nata shekarun idan ka dauke mutum daya dake ta bakin kitchen dinsu,zaune saman kujera 'yar tsuguno tana ta kokawa da wutar ice da take qoqarin kunnawa hayaqinta yana dawo mata cikin idanu yana sake tunzurata da hasalata. Duk wanda suka hada ido dashi sai ya janye dubanshi daga kanta kamar yadda itama kusan haka take musu,duk kuwa da cewa wasunsu suna son tankawa a gareta kaman yadda a wasu lokutan yake kasancewa,saidai wanzuwar ta bakin kitchen din ya sanya ba wanda yayi gigin aikata hakan a cikinsu. Bata dakata ba har ta isa bakin makewayensu da ko yaushe yake cike da tsafta da kulawa,ta xare towel din wuyanta ta azashi saman qofar bandakin idanunta nakan shaheed,yaron da aka kawoshi yaye daga gidan mahaifansa zuwa gidan kakanninsa. Yaron yayarta ne,yayarta ta kusan biyar,d'iya a wajen gwaggo mace ta biyu a wajen mahaifinsu. Ido suka hada da yaron,sai ya sakar mata murmushi,a hankali itama ta motsa bakinta tana maida masa martani. Tana da wani boyayyen soyayya ta yara a zuciyarta,saidai zuwan yaron sai ya zame mata kamar wani mabudi ko kuma wanzuwar sabon abu da bata saba gani ba cikin gidan wato murmushi kowacce safiya a tsakar gidan mahaifinta wanda ya jima da shudewa tun bayan gushewar mahaifiyarta. Tanason yiwa yaron magana,amma tayi imani rayuka zasu iya baci daga qarshe,dole ta kauda kai,ta sirka ruwan zafin data fito dashi ta fada wankan. Kafin ta kammala taji masu buqatar shiga bandakin da yawa,masu qananun mitoci da qorafi duka sunayi,wasu su juya wasu su zauna suna dakonta gami da ci gaba da yasar da maganganun da tayi imanin da biyu suke yinsu kamar yadda suka saba. Zuwa yanzu ta fara tunanin yadda zata maida qaramin dakin dake kusa da dakinsu toilet. Daya daga cikin dabi'a daya ta gidansu data tsana kenan,sharing toilet. Gini ne irin na da wanda duk yawan jama'ar gida suna hadaka ne a bandaki qwaya daya tal!. Zata iya cewa da sauqi nasu tunda akwai wadatar tsafta. Ko data fito babu wanda tabi takai,sai data kammala uzurinta na daura alwala a nan bakin famfo sannan ta tattaro kayanta tana barin wajen. Sai a sannan ta kallo mata biyun dake zaune daga bakin bishiyar. Daya ta girmi daya a shekaru,saidai dayar ta dara dayan jiki. Sun kalleta sun kuma dauke idanu kamar basu ganta din ba. Ba abinda ya dameta da hakan "Ina kwananku?" Ta furta da muryarta me laushin nan tana yin gaba ba tare da tayi koda yunqurin tsaiwa ba da salon gaisuwar da duk safiyar duniya bata daukewa kowacce cikin su ukun ba muddin zasu hadu a farfajiyar gidan. Amsa mata sukayi kaman yadda suka saba din,can qasa suna kuma binta da wannan kallon dake dauke da tarin ma'anoni can qasan ransu,wasu. sun furta su sun kuma bayyana,wasunsu kuwa an barwa zuciya AKWATIN SIRRI. *SU SAKE DAW O MUKU DA WASU SABBIN LABARAI* *_BAYAN WASAN DA AKA BUGA GA WANI SABON WASAN_* *_MIQAQQIYAR TAFIYAR NISHADI_* *_KAFATAWA DA ZAFAFAN MUHAWARA_* *_LABARAI MASU DAURE KAI DA SANYA NISHADI A CIKIN ZUKATAN MASU KARATU_* *ZAFAFA BIYAR* *_MASUBURBUDAR LABARAI MASU CIKE DA HIKIMA DA DEBE KEWA DA WASA TUNANI TARE DA TSUMA ME KARATU DA TSUMAMMIYA KUMA TSAFTATACCIYAR SOYAYYA_* *Hanzarta shiga ayarin ZAFAFA FAMILY(WATO IYALAN ZAFAFA DA BASA GAJIYA DA KASANCEWA DA SU* _TA HANYAR SHIGA RUKUNIN MASU SIYAN LITATTAFANSU KAMAR HAKA_ _QIRJIN ME HANKALI Miss xoxo_ _K'ALBIM Mamuhghee_ _AJIYA A DUHU Billynabdul_ _DUNIYATA Huguma_ _Dukka qunshin litattafan daga farko har qarshensu_ *hudu 2k* *uku 1500* *Biyu 1k* *Daya 500* _YADDA ZAKU BIYA IDAN KATI NE:_ *09032345899 KATIN MTN, IDAN AN TURA SHEDAR MA NUMBER ZAA TURAWA* *IDAN BANKI NE A TURA SHEDA ZUWA GA* *09033181070* *BANK NAME/SUNAN BANKI: ACCESS BANK* *ACCOUNT NUMBER/LAMBAR ASUSUN BANKI: 0022419171* *ACOUNT NAME/SUNAN DA KE ASUSUN BANKI:MARYAM SANI GUMMI* *AL'UMMAR MAQWAFCIYAR QASATA NIJER KUWA* 89825722 Nousaiba lawali maradi 1000cf *_Madalla da masoyan ZAFAFA BIYAR_* *_MADALLA DA KASANCEWARKU TARE DASU_* *D U N I Y A T A* *_H U G U M A_* *Arewabooks:Huguma* PAGE 15 A nutse take ratsa falon harta cimma uwar dakin nasu. Duk takunta guda daya sauke qafarta da dauketa zuciyarta cike take da kewa. Wata qatuwar kewa data zamewa kowanne motsi na rayuwarta lazim. Kewa ce da zaiyi wuya ita iya barin gangar jiki. Kewar mahadin rayuwa jigon rayuwa mahadin numfashi wato MAHAIFIYA. Duk yadda lokaci yakai ga wulwula gudu,duk yadda zamani yakai ga fara yin tsaho da nesanta bawa daga dukkan tunani radadi da damuwoyin abubuwan da suka shude amma ya gaza yin nasara a kanta ta wannan fannin. Mahaifiya daban take cikin rayuwar 'ya'yanta,babu ma ya mahaifiya irin tata......jajirtacciyar uwa data zamewa maraicinsu sutura,ta zame musu bango abun dafawa,ta hana musu kuka akan rashin mahaifinsu.....sai gashi a yanzun suna kuka.....irin kukan da kunnuwa ba zasu iya ji ba,idanuwa ba zasu iya gani ba.......ta saka dukkan wani qarfi da iyawarta ta tare wannan shingen maraicin......tozarta da wulaqantar rayuwa dake shirin danne musu numfashi har ya zuwa lahirar duniyarsu.......tallafewar data sabbaba mata tarin ciwuka.......nauyi me yawa a qirjinta da rayuwarta......ya kuma bude mata qofofi masu fadin gaske cikin rayuwarta......ya maida JARUMA a mafi yawan lokuta.....wani lokacin kuma MAFARAUCIYA dake bude dukkan qarfin qwanji dana zuciyarta don cimma burikanta. Ya dasa mata abubuwa masu yawa cikin ZUCIYARTA ya kuma sanya dolen dolen ta sauya akalar rayuwarta ta fanni da dama. Ta koma tamkar tarwada me wahalar kamawa cikin ruwan da take ninqaya. Ta kuma koma tamkar hawainiya dake canza kala

End of Chapter 13Continue to the next chapter or choose another story below.

More Hausa novels

Browse all books →
Previous Login to Save Next