Ramadan Promo!All users that send a manual request for premium upgrade on sallah day will be granted for 1 month free.
Soyayyanovels
A Duniyata Part One Complete Hausa Novel
A Duniyata Part One Complete Hausa Novel
By Billyn Abdul
Login to keep your reading position saved.
Book Page Chapters
A Duniyata Part One Complete Hausa Novel

A Duniyata Part One Complete Hausa Novel

Author: Billyn Abdul
Chapter 81 of 84
About 8 min read
Chapter progress: 0%
Listen Mode
Listen to this chapter using your device voice.
Ready to listen from this chapter.
Free access is active. You can keep reading and download during this access window.

Book chapters

Choose a chapter and continue reading.

Start chapters
Chapter 1 1,700 words Chapter 2 1,700 words Chapter 3 1,700 words Chapter 4 1,700 words Chapter 5 1,700 words Chapter 6 1,700 words Chapter 7 1,700 words Chapter 8 1,700 words Chapter 9 1,700 words Chapter 10 809 words Chapter 11 1,700 words Chapter 12 1,700 words Chapter 13 1,700 words Chapter 14 1,700 words Chapter 15 1,700 words Chapter 16 1,700 words Chapter 17 1,700 words Chapter 18 1,700 words Chapter 19 1,700 words Chapter 20 1,700 words Chapter 21 1,700 words Chapter 22 1,700 words Chapter 23 1,700 words Chapter 24 671 words Chapter 25 1,700 words Chapter 26 1,700 words Chapter 27 1,700 words Chapter 28 1,425 words Chapter 29 1,700 words Chapter 30 1,700 words Chapter 31 1,700 words Chapter 32 400 words Chapter 33 1,700 words Chapter 34 1,700 words Chapter 35 1,700 words Chapter 36 1,148 words Chapter 37 1,700 words Chapter 38 1,700 words Chapter 39 1,700 words Chapter 40 1,700 words Chapter 41 1,700 words Chapter 42 1,700 words Chapter 43 956 words Chapter 44 1,700 words Chapter 45 1,700 words Chapter 46 1,700 words Chapter 47 1,700 words Chapter 48 1,700 words Chapter 49 1,700 words Chapter 50 1,700 words Chapter 51 30 words Chapter 52 1,700 words Chapter 53 1,700 words Chapter 54 1,484 words Chapter 55 1,700 words Chapter 56 1,700 words Chapter 57 1,700 words Chapter 58 1,700 words Chapter 59 1,700 words Chapter 60 1,700 words Chapter 61 1,373 words Chapter 62 358 words Chapter 63 1,700 words Chapter 64 1,700 words Chapter 65 1,700 words Chapter 66 1,700 words Chapter 67 1,700 words Chapter 68 1,700 words Chapter 69 1,700 words Chapter 70 1,700 words Chapter 71 1,700 words Chapter 72 1,700 words Chapter 73 1,700 words Chapter 74 1,700 words Chapter 75 1,700 words Chapter 76 1,700 words Chapter 77 1,700 words Chapter 78 1,700 words Chapter 79 1,700 words Chapter 80 1,700 words Chapter 81 Reading now Chapter 82 1,700 words Chapter 83 1,700 words Chapter 84 642 words

wucewar nadra da haneefa makaranta,tana daga parlor huda na cikin uwar dakin qudundune a bargo da sunan bata da lafiya ba zata samu daman zuwa makaranta. Ta shirya hakanne don tana sanya ran sabreen din zata fita ta barta a dakin kamar jiya,tasha hirar soyayya da hameed dinta,wanda a yanzu duk duniya bata jin akwai sauti ko muryar da takai tasa dadi da daraja. Amma ga sabanin mamakinta yadda taga sabreen din kwance yana gaya matane ba lallai bane ta fita ba yau din. Tayi tsaki cikin bargon yafi a qirga,tayi juyi daga hagu zuwa dama sau ba adadi. Tana iya ganin yadda wayarta dake qasan filo keta haske alamun kiran hameed wato naseer ne yake shigowa amma tsoro ya hanata dagawa. A hankali a hankali ta dinga jin duk wata juriya tata tana qarewa,muradinta da burinta kawai shine yadda zata samu taji muryar hameed dinta. Sannu a hankali ta dinga jin hirarsu ta jiya tana dawowa _akan sonki bana tsoron kowa,zan kuma iya komai a gaban kowa saboda ke....zan iya sadaukar da komai a kanki,zan kuma iya rabuwa da kowa,kefa?,zaki iya?,ki gwadamin wataran_. Kalaman Hameed kenan ko yaushe a kanta. Muddin zai sadaukar har haka ita me zaya hanata ta sadaukar?. Tambayar data yiwa kanta kenan,abinda kuma ya cire sauran dan tsoron dake ranta ta jawo wayar ta daga ta kara a kunnenta. Wata wawiyar ajiyar zuciya ya sakar mata kamar qaramin yaro "Har na fidda rai.....huda kina azabtar dani,kullum kafin na samu jinki sai nasha baqar wuya?,sai na shafe awanni ina lalubenki?,bayan ni ko agaban waye bana iya wofantar dake huda?,koda waye a wajen zan ambaceki zan kuma yi waya dake.....me yasa huda ni bazakimin wannan sadaukarwar ba?". Yadda yayi maganar sai ya bata tausayi sosai,harma taji tana zargin kanta daqin daga wayar tasa tun dazu "Allah huda idan aka wayi gari na mutu sonki ne ya kasheni" Duk wata tsiga ta jikinta sai data zuba......son da yake mata wai da gaske ne har yakai haka?. "Kina mamaki kuma kina musu ko?,kinason tabbatarwa?" Cike da quruciya da rashin sanin kan rayuwa ta furta masa "Eh" "Nan da kwana uku xan dawo ya kama ranar Monday,zaki yarda na shigo makaranta na daukeki?.....zan kaiki inda zan nuna miki zallar soyayyata a gareki ki ganta quru quru.....kin yarda kinaso ki gani tawan?". Sai ta narke wuya zuciyarta na karkata gason ta gani din. Can qasan ranta kuma fal mamaki,tadai kusa ganin wannan soyayyar da yaketa faman zuguiguita mata ita......ta kusa ganin soyayyar nan dai da takeji anata magana a kanta. "Zan miki tanadi na musamman,zaki gani da idanunki.....daga ranar nasan ba zaki sake musu shakka ko kokwanto ba". Janta yayi zuwa cikin hirar sosai duk da sama sama take amsa masa a darare amma hakan bai dameshi ba,sake jan ra'ayinta kawai yakeyi,yana kuma sake dulmiyata cikin kogin qaunarsa. Kadan kadan takejin motsi daga dakin,to amma sai kunnuwanta sukafi tafiya zuwa tsakar gidan gidan nasu. Don ta tabbatar huda bacci takeyi ko sanda ta fito,ta share wannan maganar tana dauko wayarta ta lalubi number jib. *D U N I Y A T A* *_H U G U M A_* PAGE 79 "Allah dai yaja kwana hajjaju......our young hajiya" Jib din ya fadi cikin fara'a. Karamin tsaki taja tana kauda zancan,haka kawai ita batajin komai akan kudin,bata kuma jin wata walwala. Duk wani tsari da jib din yakeyi mata tana jinsa ne kawai,don nata lissafin duka ba'a wannan bangaren yake ba. Uwa uba shi Kansa jib din bataji ya tsarawa kansa komai ba,ita kuma yanzu su dinne a gabanta da sauran yara marayun nan da take kwana dasu ta kuma tashi dasu cikin ranta. "Ka sameni gidan marayun nan,zamu qaraso nida busari" Ta bashi saqon a taqaice "Okay to ba damuwa.....amma ke me kika warewa kanki?" "JIB....ajiye maganarnan haka a gefe,kada kabarmu mu jiraka please" "In sha Allah" Ya fada mamakin halayenta suna sake ninkuwa a ranshi. Kafin ta ajiye wayar tahau ta daya sim din data saba neman busari,ta tura masa saqo sannan ta ajiye wayar tana dan furzar da iska daga bakinta gami da zubawa labulen qofar falon idanu kamar me nazari akan yadda aka sarrafashi. Kadan kadan ta dinga jin kamar dai motsinne daga dakin da kaman sautin murya a can qasa. Tun tana basarwa har ta miqe,ta taka a hankali ta soma nufar dakin. "Eh" Kalmar da aka fadi qasa qasa ta shiga kunnenta sanda ta yaye labulen dakin. Hasken daya ratso falon zuwa uwar dakin ya ratsa blanket din da take ciki ya kuma alamta mata wanzuwar wani a dakin,sai tayi wata mutuwar kwance zuciyarta tana tsananta bugawa ta latse wayar tana turata tsakanin katifar da bagon gadon. Daqyar take iya hadiyar yawu saboda tsoro,tun yaushe nema aka shigo bata sani ba,kada dai ace ta jima a tsaye tana jinta?,wannan tunanin kadai ya sanya jikinta jiqewa da gumi kamar an watsa mata ruwa. Hannu ta sanya ta yaye bargon,sai ta runtse idanunta "Keda waye kike magana?" Sabreen ta jefa mata tambayar tana zube mata idanun nan nata masu kaifi. "Magana kikaji yaa sabreen?" Shuru tayi dajin tambayar datai matan,sai ta girgiza kai alamun aah bayan ta gama qare mata kallo "Wannan gumin fa?,ko zazzabi kikayi ya sauka?" Ta sake jefa mata tambayar amma wannan karon da salon son kamo abun farauta "Eh.....eh nima haka naji" Idanunta ta maida ta lumshesu sannan ta bude. Ta gama bata hint,ta kuma gama hada dukkan wasu abu da takeso,ta sanyata a ajujuwa kuwa tun daga sauyawarta zuwa yau,kuma ta fadi a kowanne aji......tana jin sunzo matakin qarshe ita da ita,sai ta sake mata blanket din,ta juya tana takawa a nutse zuwa inda take adana kayan wankanta ta diba tana fita a dakin. Da wani malalacin kallon ta bita har ta gama ficewa,haka kawai taji kaman akwai wani abu ba daidai ba "Idan ma akwai.....idanma kuma ta gane aiba wan sabon Allahn kikayi ba" Wannan tunanin ya bata qwarin gwiwa ta tabe baki,ta maida kanta filo tana jin yadda zuciyarta ke bugawa sosai,daga bisani kuma ta koma tunanin hirarrakinsu da hameed kaman yadda ta saba. Cikin qanqanin lokaci suka isa babban gidan kula da marayu,wanda yana cikin gidajen da suke karban kaso mafi tsoka daga dukkan abinda ta samu. A yau din kabakin arziqin data kai musu ya faranta ran kowa. Hakanan list da tayi na abubuwan da zata aiwatar musun ya sanya kowa kokwanton anya da gaske take?. A duka shekarunta ina taga adadin wadannan kudaden?. Ayyuka ne da zasu canza fasalin gidan gaba daya ya canza cimarsu harma karatun yaran gidan. Tsari ne kuma data dauki sunayen 'yammatan ciki da suka isa aure suke da buqatar tallafin kayan daki da kayan kitchen harma da suturar fitar biki. A ranar gaba daya gidan a yamutse yake da tsananin mamakin ayyukan da tace zatayi din. Saidai daga bisani shigaban gidan ya basu nutsuwa ta hanyar fadin "Ta iya yiwuwa 'yar wani hamshaqin attajirin ce mu bamu sani ba ta bad da sawu,ko daga suturar jikinta da fatarta zakasan cewa kaman hakan zai yuwu,kudai godewa Allah daya turo me dauke mana damuwarmu koda yaushe,gashi a wannan karon bayan tallafin data saba bayarwa zata mana aikin da mutanen dake da ikon yi masu yawan gaske suka gaza yi mana......zata mana aikin dana tabbata muddin ya tabbata matsalolinmu masu yawa zasu kauce". Ta yita share qwalla me yawa a hanyar komawa gida,yaran suna mata gizo cikin idanuwanta. Wato maraya a wannan zamanin daidai yake da wani abu maras alfanu cikin al'umma muddin ba dukiya aka mutu aka bar masa ba?,hankula da idanuwan al'umma duka sun toshe?,me arziqi shine mutum?,me arziqi shike da amfani?,idan yau kana da abun hannu kowa qoqarin rabarka yakeyi?,kowa so yake ya hada dangantaka dakai komai qanqantarta?,kowa so yake ace kuna da alaqa kunsan juna?. Anya mutane a yau kuwa sunsan iya adadin bala'i da masifar zubar ruwan hawaye a idanun maraya qwalli daya tak a garesu?,anya suna tunawa da girman haqqinsa da ma'aiki yayi gargadi da jan kunne akai?. Bibo ta fado mata a rai,saita dinga juya kai kawai,matar tana daya daga cikin mutanen da zasu azabtar dasu tsananin azaba inda Allah ya qaddari mutuwa ta dauke ummeensu a sanda suke dukkaninsu qananu......arrahmanu arraheem ubangiji da baya hadawa bawa abu biyu......sai ya dauke musu sanyin idaniyarsu a sanda ita nata hankalin da qarfin ya fara kawowa. Ya sanya mata qarfin zuciya da kuma qarfin halin iya tare musu tashin hankali da masifa komai girmanta,ya sanya rainonsu da kulawa dasu a hannunta tun bata wuce itama a raineta ba. (YAKE BAIWAR ALLAH!....tabbas riqo yana da wahala.....riqo yana da daci yana da nauyi,amma kisani......DA KI RIQE YARO KI AZABTAR DASHI GWARA KI TUN FARKO KICE BA ZAKI KARBA RIQON BA yafi miki sauqi da mafita har a wajen Allah muddin kikasan zuciyarki ba zata iya jure da kiyaye wannan amanar ba.....AMMA WALLAHI WALLAHI WALLAHI kikayi kuskure kika karbi riqo don ki burge ko kada a zargeki,to wallahi idan nace KINA CIKIN MASIFA ma kadan ne.....ba zaki san girman bala'i da kike ciki ba sai ranar gobe qiyama......hatta ubangiji bayason kuka maraya shi da yayi kowa yayi komai ya kuma qaddara hukuncin maraici a kansa IDAN KINSAN akwai maraya yanzu haka da kike banbanta riqonsa dana 'ya'yanki.....to ki gaggauta yiwa kanki hisabi tun kafin ranar zuwan hisabin na gaske.......idan har kinsan akwai maraya yanzu haka a hannunki.....to ki gaggauta gyarawa kafin ki barwa 'ya'yanki masifa da bala'in da zaiyita bibiyar rayuwarsu,kiyi qoqari kifi qarfin wannan tsokar dake qirjinki wadda ake kira da ZUCIYA.....kiyi qoqari kifin qarfin wannan maqiyin naki wato SHAIDAN.....Allah ya bamu ikon fin qarfin wadannan ababe guda biyu ameen summa ameen). "Kaini gidan malam" Ta fadiwa busari a nutse,wanda bai musa ko ya tambayi ba'asi ba ya karkata akalar motar. Zuciyarsa shima cike take da farinciki,don yana cikin alherin tashi daga dan adadaita sahu,zuwa mamallakin shago sukutum da guda a babbar kasuwar kantin kwari nan da sati uku kacal. Kusan duk wanda ya kwana ya tashi a kamfanin yasan da faruwar komai. Yayin da sake fitar labarin boyayyar badaqalar data afku qasa da wasu awanni ya sake sanya mutane da yawa na kamfanin mamaki musamman wadanda basu san komai ba,basusan kuma abinda ake ciki ba. Kowa da kansa da kansa ya yiwa hisabi,don shigowar boss Muhammad kamfanin ya sake sanya kowa shiga taitayinsa.

End of Chapter 81Continue to the next chapter or choose another story below.

More Hausa novels

Browse all books →
Previous Login to Save Next