Ramadan Promo!All users that send a manual request for premium upgrade on sallah day will be granted for 1 month free.
Soyayyanovels
A Duniyata Part One Complete Hausa Novel
A Duniyata Part One Complete Hausa Novel
By Billyn Abdul
Login to keep your reading position saved.
Book Page Chapters
A Duniyata Part One Complete Hausa Novel

A Duniyata Part One Complete Hausa Novel

Author: Billyn Abdul
Chapter 37 of 84
About 8 min read
Chapter progress: 0%
Listen Mode
Listen to this chapter using your device voice.
Ready to listen from this chapter.
Free access is active. You can keep reading and download during this access window.

Book chapters

Choose a chapter and continue reading.

Start chapters
Chapter 1 1,700 words Chapter 2 1,700 words Chapter 3 1,700 words Chapter 4 1,700 words Chapter 5 1,700 words Chapter 6 1,700 words Chapter 7 1,700 words Chapter 8 1,700 words Chapter 9 1,700 words Chapter 10 809 words Chapter 11 1,700 words Chapter 12 1,700 words Chapter 13 1,700 words Chapter 14 1,700 words Chapter 15 1,700 words Chapter 16 1,700 words Chapter 17 1,700 words Chapter 18 1,700 words Chapter 19 1,700 words Chapter 20 1,700 words Chapter 21 1,700 words Chapter 22 1,700 words Chapter 23 1,700 words Chapter 24 671 words Chapter 25 1,700 words Chapter 26 1,700 words Chapter 27 1,700 words Chapter 28 1,425 words Chapter 29 1,700 words Chapter 30 1,700 words Chapter 31 1,700 words Chapter 32 400 words Chapter 33 1,700 words Chapter 34 1,700 words Chapter 35 1,700 words Chapter 36 1,148 words Chapter 37 Reading now Chapter 38 1,700 words Chapter 39 1,700 words Chapter 40 1,700 words Chapter 41 1,700 words Chapter 42 1,700 words Chapter 43 956 words Chapter 44 1,700 words Chapter 45 1,700 words Chapter 46 1,700 words Chapter 47 1,700 words Chapter 48 1,700 words Chapter 49 1,700 words Chapter 50 1,700 words Chapter 51 30 words Chapter 52 1,700 words Chapter 53 1,700 words Chapter 54 1,484 words Chapter 55 1,700 words Chapter 56 1,700 words Chapter 57 1,700 words Chapter 58 1,700 words Chapter 59 1,700 words Chapter 60 1,700 words Chapter 61 1,373 words Chapter 62 358 words Chapter 63 1,700 words Chapter 64 1,700 words Chapter 65 1,700 words Chapter 66 1,700 words Chapter 67 1,700 words Chapter 68 1,700 words Chapter 69 1,700 words Chapter 70 1,700 words Chapter 71 1,700 words Chapter 72 1,700 words Chapter 73 1,700 words Chapter 74 1,700 words Chapter 75 1,700 words Chapter 76 1,700 words Chapter 77 1,700 words Chapter 78 1,700 words Chapter 79 1,700 words Chapter 80 1,700 words Chapter 81 1,700 words Chapter 82 1,700 words Chapter 83 1,700 words Chapter 84 642 words

Sai daya feshe jikinsa da sassanyan turarensan nan na din din din sannna ya kalli lafiyayyen agogon fatar dake kwance luf saman fatarsa. Lokaci ya cika daidai kamar kullum da zaici wani abu,ya taka a nutse yana isa inda dan kyakkyawan silver tray din ke ajiye wanda komai ke ajiye samanshi bisa tsarin da akasan wanda zai mu'amala da tray din yake dashi. Har ya miqa hannu zai dauki glass mug din dake da murfi sai ya dakata saboda q arar wayarshi dake side pockets na suit nasa. Hannu ya zura ya zarota yana duba me kiran. Sunan nan dai na dazu ya sake bayyana "Amna....amna" Ya fadi sau biyu a hankali yana motsa jajayen labbansa da sukayi wani fresh suka sake fidda red color nasu kamar me amfani da wani kebantaccen abun shafawa labba Sai daya koma a nutse ya zauna saman sofa sannan ya daga kiran "Hamma......" "Amna......i will be busy today fa" "I know fa yaaya......anni ce kawai tace na gaya maka ka kirata" "Lafiya dai ko?" Ya tambaya yana dan motsa fuskarshi "Hamma......waye yasan tsakaninka da anni kuma?" Wani qaramin qasaitaccen murmushi ne ya subuce saman labbansa,wanda ya fidda kyawun fuskarsa sosai "Jealous girl" Ya furta a hankali. Siririyar dariya ta kufcewa amna din,ya latse wayar yana laluban number annin. Tunda ya tashi da sassafe kafin ya fita yayi kiran layin nata har sau biyu saidai ba'a daga ba,sai ya bada uzurin banbancin tazarar lokuta dake tsakanin nigeria da South Korea din wala'alla tana nata baccin ko don yanayin jikin nata ma. Tana gaban mirror tana fama da tazar doguwar sumarta. Wani abu guda daya da taqi jini shine duk abinda zai taba mata kai. Tun tana qarama daya daga cikin dabi'unta bata qaunar kitso kwata kwata,wannan ya sanya har sai da ummunta ta taba aske gashinta,saidai kowanne bawa da irin halittar gashinsa,don babu jimawa wata sumar ta fara taruwa ta kuma sake cika kan da yalwarta da santsinta har taso tafi ta baya da aka aske. Sake runtse idanunta tayi sanda ta sanya comb din a tsakanin gashinta,daidai sanda ta sake jin daddadan sautin nan irin na dazu. Ta wurga fararen idanunta saman purse din dake ajjiye saman madubin. Idanu ta zuba mata,kaman zata dauka sai kuma ta share taci gaba da abinda takeyi,wannan ya bawa wayar daman ci gaba da kadawa har ta gaji ta tsinke. Wayar ya sauke daga kunnensa yana duban fuskar wayar. Sai ya sake gwada kira yana mamaki kadan cikin ransa,don tunda yake da annin bai taba kiran wayarta sau biyu ba ba tare data daga ko ta biyo kiran ba,sai gashi yau kira na biyar kenan zaiyi mata,duk da annin da kanta tace ya kiratan zasuyi magana. Kodai akwai laifin da yayi mata?,ya tambayi kansa duk kuwa da yasan ba haka bane. Abune mawuyaci ka batawa annin rai,musamman su din sanyin idaniyarta guda hudu. Sake leqa fuskar wayar tayi a karo na uku kenan da ake kiran wayar. Suna daya ne dai MUHAMMADU. Siririn tsaki taja tana jawo wayar gabanta,cikin tarin abubuwan data tsana harda maimaita kiranta a waya koda kuwa kiran me muhimmanci ne. Ba wayarta bace amma ranta taji ya baci data duba taga miscal shida kenan harda na dazu,don haka dab da wayar zata katse ta daga adan zafafe ta karata a kunne. Karamar ajiyar zuciya ya saki Lokacin daya fuskanci an daga wayar,a hankali ya maida hankalinsa ga daukan kiran da akayi,cikin jikinsa sai ya dinga ji kaman ba anni bace. Koda cikin bacci anni ta daga kiransa zaya fahimta ballantana idanushi biyu. Kamfanin wayar ya fara irga sakannin da akayi ana riqe da duka layukan biyu,mamaki yaji yadan fara kamashi,yayin da a nata bangaren kuma ranta ya ninka baci akan na dazu. Ansan ba'a da abun fada aka addabi mutane da kira ba qaqqautawa?,an daga kuma zaa bar mutane da riqon waya a hannu?. "Idan ba wani abun fadin zaa ajjiye wayar" Ta fada tana cije lips dinta na qasa saboda haushin da takeji cikin ranta. Daga wayar yayi daga kunnensa yana duba number still duk da yasan number anni ce ba kuskure a ciki. Amma baquwar muryar me kama da muryar babies itace ta daure masa kai. Sai ya dakata daga takun da yakeyi don dauko mug dinsa,ya soke hannunsa a aljihun trouser na suit dinsa tamkar me jin sanyi "Who are you?" Yayi tambayar kai tsaye "Ina me wayar?" Ya sake jifanta da tambayar "Bansan me wayar ba.....koma wace me wayar wayan baya hannunta......ka jira idan ya koma hannunta ka sake kira" Ta amsa masa a taqaice tana gintse kiran. Sautin Din din din na yankewar kiran ya sakashi janye wayar a kunnensa mamaki yana kashesa "Who's she?" Ya furta a fili yana trying na sake kiran layin,saidai ya taras da na'ura tana gaya masa wayar a kashe take. Sosai ransa yayi qololuwar baci,wacce irin yarinya ce haka mara kunya wadda bata iya magana dana gaba da ita ba?. Maida akalar kiran nasa yayi ga musaddiq zuciyarsa na masa wani irin zafi. Bayan magana da take fadi kanta tsaye harda katse masa kira?,wayan nata ne?,ko itace tayi kiransa da zata katse masa waya?. Daidai sanda yake zaune a falon tun bayan wucewar maama da zuwaira kiran muhammad fu'ad ya shigo masa. A kasalance ya zaro wayar daga aljihun gaban rigarsa,yana tsammanin driver manu ne ya gaji da jiran fitowarsa yayi kiransa. Sunan da ya gani a rubuce jikin wayar ya sanyashi sauke ajiyar zuciya gami da daidaita zamansa. Ya jingina bayansa da kujerar yana kara wayar a kunnensa. A ladabce yayi masa sallama "Wa'alaikumussalam.....wace mara kunyar kuka bari wayar anni taje hannunta.....har tana katsema mutane kira?" "Turqashi!.....anzo wajen" Musaddiq ya fada qasan zuciyarsa. Ya sani kowanne bayani zaiyi masa ma ba lallai ya fahimta ba. Ya tsani ya kiraka ka katse masa waya har sai idan shi ya buqaci hakan. Bashi da abun ce masa don haka muryarsa a raunane wadda tayi laushi saboda tarin tunane tunanen dake kanshi yace "Kuskure aka samu hamma......kayi haquri....bari na hadaka da annin" Ya fadi yana miqewa tsaye. Dogon tsaki yaja kamar zai tsinke harshensa,ya koma saman sofa bed din ya zauna yana jawo mug din yana duban dafaffiyar tumeric fresh milk din ciki kamar yau ya saba ganinta. Da sassarfa ya soma kowawa ciki,dab da zai isa stairs din yaja ya tsaya saboda annin dake saukowa a nutse zuwa qasa *D U N I Y A T A* *_H U G U M A_* *Arewabooks@:Huguma* Page 36 "Dama baka tafi ba?" Anni ta jefa masa tambayar a nutse tana jifansa da kallon tuhuma. Kalar tausayi ya koma yana karya wuya "Bazan iya tafiya bane anni na barki" "Saboda kana tsoron kada ta cinye nama na?" Ta sake tambayarshi cikin salo na gatse. Ya gama fahimtar gatsen take masa amma sai ya basar yana binta da wayar lokacin data wuceshi tana zarcewa saman kajurun falon ta zabi daya ta zauna "Anni......hamma ne yakeson magana dake" Ya furta yana rusunawa a gabanta "Kiraminshi......wataqila yayita kiran layina bai sameni ba" Ta fada tana daukan remote hadi da sauya tashar dake aiki cikin tvn. Sipping yakeyi na madarar yana irga yadda agogon dake facing dinsa yake bugawa. Ranshi a bace yake amma yana qoqarin danne hakan. Qarar wayar ya sanyashi waiwayawa inda ya gangarar da wayar yana kallon kiran musaddiq. Yasan ba kiran qashin kansa bane.....na anni ne,don haka bai barta tana burari ba ya jawota ya daga yana sakata a kunne. Da wannan calmness din nashi yayi sallamawa anni. Itama ta amsa masa har cikin zuciyarta tana jin wani farinciki yana saukar mata da jin tasa muryar dake bayyanar mata lafiya qalau yake. "Barka da warhaka anni" Ya fada yana dan rusunar da kanshi tamkar yana a gabanta. Yana jin wannan respect din har cikin zuciyarsa "Barkanka me babban suna....." "Kin tashi lafiya?,ya jikin naki anni?.....ina fatan ba wani matsala ko damuwa?" Ya tambaya cikin kulawa. Ajiyar zuciya ta sauke hade da furzar da numfashi "Ba ciwo,sai damuwa da kukeson sakani kai da musaddiq". Maganar ta dukesu duka su biyun,har musaddiq dake zaune a gefe ta sanyashi daga kai cikin hanzari yana dubanta. " Subhanallah......subhanallah anni kiyi haquri.....me mukayi?" Ya furta yana jin damuwa sosai cikin ranshi tare da tuhumar kansa akan sanya damuwa ga ruhin da kullun burinsa ya kyautata musu?. "Fuad.....yau ka gaida maama daga safen nan zuwa yanzu?" Ta jefa masa tambayar data sanyashi dauke wuta,sannan a hankali ya hade labbansa guri daya ya kuma amsa mata a hankali da "A'ah". "Me yasa?" "Ba komai" Ya amsa mata kai tsaye,saboda shi din mutum ne da bai iya qarya ba sam komai girman laifinsa kuwa "Me ya hanaka daga wayarta sanda ta kiraka?" "Anni......fargaba kiranta yake sanyamin,anni banason ganinta tana kirana.....anni bana buqatar mu'amala da ita......nafiso taci gaba da nisantarmu anni kaman yadda tayi a baya......bama buqatarta......duk sanda zan ganta anni sai naji wani abu a kanta.....inama zaku fahimci laifi mafi girma data aikata mana wanda yafi tafiya ta barmu girma muni ciwo da kuma girman zunubi?" Wadannan sune abinda so samu ya kamata ya cewa annin,amma kuma bakinsa ya gaza furta hakan,sai shi kadai daketa jujjuya maganganun cikin zuciyarsa. Ya rasa waye zai zayyanawa su,ANNI dince,to amma bayaso yabar mata wani abu da zaya yi mata tsaye a zuciyarta ko kuma a rayuwarta. Damuwa itace abu na qarshe da yayi alqawarin tarewa anni shigarta,kamar yadda ta sanya duk wani qarfin iko na jiki dana aljihunta ta tare ma rayuwarsu kasancewa da wanzuwa cikin damuwa har kawo bigiren da suke kai haka a yanzu. Wannan tunanin ya sanya ya zabi bawa anni amsa ta hanyar cewa "Ba komai". " Ban tsammaci haka daga gareka ba Muhammadu,kanaso abbanku yaji ba dadi a ransa shima kamar yadda naji?" Ta fadi cikin tausa murya tamkar tana magana da qaramin yaro. "Ko kadan anni.....kema da muka sanya kikaji ba dadin yanzu haka kiyi haquri ki yafe mana......za'aci gaba da kokawa da zuciya,kuma zaa gyara in sha Allah". Murmushi ta saki tausayinsu yana narka mata zuciya. Lallai duk dan da baiyi sa'a da dacen uwa ba abun tausayi ne shi. "Bakuyimin laifi ba muhammad.....illa dai lahirarku da kuma fagen rayuwarku da nakeson na sake share muku ita tas". Idonsa ya lumshe yana jin zuciyarsa ta karaya......inama ana canjen uwa?.......inama ace anni

End of Chapter 37Continue to the next chapter or choose another story below.

More Hausa novels

Browse all books →
Previous Login to Save Next