Ramadan Promo!All users that send a manual request for premium upgrade on sallah day will be granted for 1 month free.
Soyayyanovels
A Duniyata Part One Complete Hausa Novel
A Duniyata Part One Complete Hausa Novel
By Billyn Abdul
Login to keep your reading position saved.
Book Page Chapters
A Duniyata Part One Complete Hausa Novel

A Duniyata Part One Complete Hausa Novel

Author: Billyn Abdul
Chapter 54 of 84
About 7 min read
Chapter progress: 0%
Listen Mode
Listen to this chapter using your device voice.
Ready to listen from this chapter.
Free access is active. You can keep reading and download during this access window.

Book chapters

Choose a chapter and continue reading.

Start chapters
Chapter 1 1,700 words Chapter 2 1,700 words Chapter 3 1,700 words Chapter 4 1,700 words Chapter 5 1,700 words Chapter 6 1,700 words Chapter 7 1,700 words Chapter 8 1,700 words Chapter 9 1,700 words Chapter 10 809 words Chapter 11 1,700 words Chapter 12 1,700 words Chapter 13 1,700 words Chapter 14 1,700 words Chapter 15 1,700 words Chapter 16 1,700 words Chapter 17 1,700 words Chapter 18 1,700 words Chapter 19 1,700 words Chapter 20 1,700 words Chapter 21 1,700 words Chapter 22 1,700 words Chapter 23 1,700 words Chapter 24 671 words Chapter 25 1,700 words Chapter 26 1,700 words Chapter 27 1,700 words Chapter 28 1,425 words Chapter 29 1,700 words Chapter 30 1,700 words Chapter 31 1,700 words Chapter 32 400 words Chapter 33 1,700 words Chapter 34 1,700 words Chapter 35 1,700 words Chapter 36 1,148 words Chapter 37 1,700 words Chapter 38 1,700 words Chapter 39 1,700 words Chapter 40 1,700 words Chapter 41 1,700 words Chapter 42 1,700 words Chapter 43 956 words Chapter 44 1,700 words Chapter 45 1,700 words Chapter 46 1,700 words Chapter 47 1,700 words Chapter 48 1,700 words Chapter 49 1,700 words Chapter 50 1,700 words Chapter 51 30 words Chapter 52 1,700 words Chapter 53 1,700 words Chapter 54 Reading now Chapter 55 1,700 words Chapter 56 1,700 words Chapter 57 1,700 words Chapter 58 1,700 words Chapter 59 1,700 words Chapter 60 1,700 words Chapter 61 1,373 words Chapter 62 358 words Chapter 63 1,700 words Chapter 64 1,700 words Chapter 65 1,700 words Chapter 66 1,700 words Chapter 67 1,700 words Chapter 68 1,700 words Chapter 69 1,700 words Chapter 70 1,700 words Chapter 71 1,700 words Chapter 72 1,700 words Chapter 73 1,700 words Chapter 74 1,700 words Chapter 75 1,700 words Chapter 76 1,700 words Chapter 77 1,700 words Chapter 78 1,700 words Chapter 79 1,700 words Chapter 80 1,700 words Chapter 81 1,700 words Chapter 82 1,700 words Chapter 83 1,700 words Chapter 84 642 words

ya nuna saman fuska to akwai wani labarin a qasan zuciya. Sakin fridge din tayi bayan ta rufeshi tana takowa tsakiyar dakin "Wacce irin tafiya kukayi ne yau ke dasu nadra?,kinsan dai banason kuna raba tafiya ko?" Ta fadi tana zama idanunta still akan fuskar huda din. Fuska ta bata ba kaman dazu ba tana duban sabreen "Wallahi dama nace zamu hadu dasu.....kawai adda ina fitowa na samu wai sun wuce gida?,yau bansan me yasa aka rarraba mana lokacin tashi ba" Ta qarasa maganar fuskarta a bace da gaske. Idanunta tadan dauke daga kanta tana sauke numfashi "Banason irin wannan tafiyar,kome raba lokacin su dinga jiranki" Cikin ranta tana jin abun kwata kwata baiyi mata ba. Qaramar dariya ya sakarwa kansa bayan ta shige gidan. Fara takawa yayi hankali kwance yana barin layin. Tabbas shima zai buga nasa wasan yadda ya dace,zaiyi wasa da rayuwarta da kuma hankalinta yadda ya kamata......zai gigita mata rayuwa ya dagula dukkan wani lissafi nata......zai guntule dukkan wani farinciki nata kaman yadda ta gurgunta ta kuma dagula rayuwa da nutsuwarsa. Yanaji a ransa abun zai bashi nishadi qwarai,zai kuma qarasa goge baqinciki qunci da takaicin data qunsa masa. ********Cikin nutsuwar nan tasa yake saukowa daga matakalar jirgin riqe da kyawawan briefcase guda biyu. Tasa data Alhaji hamza kibiya. Biye yake da dattijon,yana aje tasa qafar a duk muhallin da ya cire. Kamilallen dattijon da adadin furfurar dake baibaye a fuskarsa da kuma gashin kansa suka sake tabbatar da dacewar sunan dashi. Cikin kamala yake komai nashi,sanye da shadda dinkin babbar riga da maroon hula dara sak ainihin shigar marigayi malam aminu kano. Muhammad fu'ad jadda,mamallakin kamfanin jadda diamond chores resources wanda ke biye dashi a baya. Sanye cikin dinkin kaftan da yayi matuqar qara masa kwarjini da wani irin haiba me cika idanun me kallonsa. Idan ka kallesu shida Alhaji hamza kibiya din zakayi tsammanin shine ainihin mahaifi gareshi saboda yadda tsahonsu yake kusan daya da kuma murjewar jikin. Bayansa kuma sadiq ne janye da luggage dinsu. Shikam t.shirt ne jikinsa da trouser,ya lullube qafafunsa da lafiyayyen boots ba kaman fu'ad ba dake sanye da wani lafiyayyen halfcover ba dan qa sar itali da aka samar dashi da dinkin hannu(sau da dama mu a nigeri muna raina takalman hannu,amma a qasashen qetare babu takalma masu daraja da tsada irin handmade shoes,wani ma kana ce masa handmade ne ka bata show din ,nija my nation Tare suka jero kafada da kafada shi da Alhaji hamza din zuwa muhallin da farouq yafi tsaiwa a duk sanda yazo daukosu daga tafiya irin wannan. Ko a yanzun da suke nufar mota don isa gida ma duk hirar akan kasuwanci ce. Abun yana bawa Alhaji hamza mamaki. Duk qwarewarsa da qaunarsa da kasuwanci fu'ad din ya shallakeshi. Kowacce rana kowacce safiya,kowanne dare da wuni plan din rayuwarsa da komai nasa yana kan kasuwanci. Me za'a bunqasa?,me za'a qirqira?,me kuma za'a gyara?,ina ne nasara take a bunqasata?,ta ina faduwa take ayi hanzarin bawa gurin kulawa da kariya?. *D U N I Y A T A* *_H U G U M A_* PAGE 52 Yana jingine da motar yana kallonsu,idanunsa fes a kansu. Yana masa dadi yana kuma sanyawa ya manta cewa fu'ad ba dan uwansa bane na jini a duk sanda ya ganshi kamar haka da Alhaji hamza din. Yana alfahari yana kuma qara ninka alfaharinsa akan muhammad fu'ad din. Shi kansa ya sallama......jajirtaccen mutum ne da jajircewa take a cikin jinin jikinsa. Ya maida idanu a hankali akan yanayin takunsa. Tafiya ce me cike da ginshira gami da cikakken kuzari da karsashin da zai bayyana maka adadin cikakkiyar lafiyar da yake da ita. Daga abban har fu'ad din hankalinsu baya wajen,yana duba wani qaramin takardu da suke dauke da bayani da taswirar burinsa na gaba wato ginin katafaren kamfanin samar da kayan ado na sarqoqin mata da zai dinga amfani da wani sashe na ma'adanan da yake haqowa. Tun daga fitowarsu gaba daya security guards dinsa da ya bari a gida kowanne ya koma kan aikinsa. Dukan inda ya ajiye qafarsa nan suke maida tasu. Murmushi ya subucewa farouq,ya dawo kenan,kuma yanzun za'a fara. Bayaso abba ne ya tilastashi daukan guardsmen duba da yanayin qarancin tsaron da ake fama dashi. Uwa uba ma zaiyi wahala a nasibin rayuwa daya samu......da irin mu'amalarsa ace ya zauna haka gayansa yana yawo babu masu tsaron lafiya tattare dashi. Wani lokacin idan yaso yana kubce musu ne yayi fitarsa shi kadai a mota yasha iska ya dawo. Ba kasafai ya fiya son fita qasashen waje sai idan harka haka ta taso takai kayan da sunyi yawan yayi wakilci......amma yanzun ya koyi fita din lokaci bayan lokaci haka siddan ma don ya samu ya sarara yayi rayuwarsa shi kadai. Mutum ne da bayason matsi,bayason takura,zai iya rayuwa me dogon zango shi kadai a wani muhalli na daban,shi yasa ko a yanzun a sassansu gini ne me zaman kansa dake dauke da bedroom and parlor da toilets kowa shi kadai. Saddiq da musaddiq sun hade dakunansu saboda kowa nashi apartment din ya masa girma. Amma oga fu'ad shi daya ne a nashi,hakama farouq,sai shi farouq din da lokaci bayan lokaci yakan dawo sassan fu'ad din yayi kwanaki yana kwana a nan sannan ya koma wajensa. Kullum ya hangi fu'ad din daga nesa ba abinda yake tunawa sai wannan matashin dan bautar qasar,mara tsoro kuma mara shakka,cikakken jarumin daya shiga yankin daba nasa ba,yayi abinda koda haifaffen yankinne ya aikata bazai sha ba.....ya kubuta da tarin nasara. Farouq yadan sake murmusawa yana tuna yadda yaci wahala bayan uban gudun da sukayi,ya tuna yadda fu'ad din yayi jinyarsa tamkar ba dashi akayi gudun ba "Ba abinda nakeji man.....ni dakai ba daya bane,sau nawa ana gaya maka ka dinga gym saboda yuwuwar samuwar irin wadannan lokutan na qwatar kai?,sai kuyita zama kaman mata,baku da wani banbanci dasu?" Ya tambayi farouq din a wancan lokaci yana dage masa dukka girarsa bayan ya bashi maganin ciwon jiki yasha. "Yanzu wannan pain killer din da kake fana dashi......da warm water da fenugreek kake sha da yafi maka amfani". Harara ya balla ma fu'ad din yana dubansa "Ba zaka qarasa kasheni ba da wadannan home remedies din naka ba" Sai ya juya ma fu'ad din baya yana sauke numfashin wahala yabar fu'ad din da sakin siririn murmushin nan nasa me tsada. Miqewa yayi yana dauke cup din "Idan home remedies bai kasheka ba......son jiki da rashin exercise....aci a kwanta duka ya kasheka......naga wanda zai aureka da qaton tumbi" Ya qarasa maganar yana jefa kwalin lemo a dutsbin. Duk da farouq na cikin yanayi a sannan saida murmushi ya qwace masa.....fu'ad mahadin rayuwarsa ne kuma mahadin zuciyarsa ne kaman yadda ya tabbatar a wajen fu'ad dinma haka yake. Kafadarsa y Ta dama yaji an daka "Murmushin me kake kai kuma?" Sassanyar muryar nan tasa sake cakude da wani deepness ta shiga kunnen farouq. Kallonsa ya dora saman fuskar fu'ad din yana jin yawan kewarsa da yayi "Ina nan ina kallon gujajjen dan bautar qasar nan da bai kammala service dinsa ba sai a garin kano". Murmurshin nan da shi daya ke iya fidda masa shi daga kan fuska ya saki kadan yana sake kaiwa kafadarsa duka. Dariya kadan ya saki shima farouq din "Ina hasaso yadda zasu cinye namanka danye duk sanda suka fahimci daga ma'adanin qasarsu ne aka samar da attajirin nan mamallakin jadda diamondchore company........" Murmurshin ya sake sanyashi saki,sai ya saka tafin hannunsa saman wuyansa yana dan karyar da wuyan kadan "Naman muhammad jikan jadda yafi qarfin cinsu umaru...." Ya bashi amsa da anihin sunansa,abinda ya sanya farouq din sakin dariya sosai. Kafadar fu'ad din yadan bubbuga "Na sani.....nafi kowa sanin wannan dan uwan nawa wanne iri ne......tun daga ranar da mukayi temple run dinnan na sake yadda da hakan..." "A nan zaku gama hirar ne?,idan ku baku gaji ba ku tallafa ku kaini naga aminatu na" Muryar abba ta sauka kunnuwansu. Fu'ad ne ya waiwaya don farouq yana fuskantar abban ne. Dan murmusawa kadan fu'ad yayi ya matsa yana yunqurin budewa abban qofa,amma farouq ya rigashi "Dukkanku kai da abban yau qarqashin hidimata kuke....baqinmu ne ku daga South Korea". "Sannu sarkin noma.....godiya muke" Shima abban ya fada cikin barkwanci bayan ya shiga motar. Dashi da farouq din baya suka shiga bayan ya bawa shugaban security dinsa umarnin su bisu a baya. Kusan duka a hanya ma dai tattaunawar ta kasuwanci ce. Farouq din yana bawa abban labarin yadda abubuwa suka kasance bayan tafiyarsu "Amma tabbas sai ka sake sanya idanu akan mika'il.....ina suspecting wani abu tattare dashi,duk da bana ce gashi ba,amma nasan kai din zaka fini fahimtar komai" Farouq din ya furta. Idonsa fu'ad ya dauke daga kan wayar hannunsa,wanda saqon mika'il dinne ya shigo,mutum na farko daya fara masa saqon barka da dawowa kafin kowa. Bai cewa farouq komai ba,amma kuma maganar tasa ta samu gurbi sosai a zuciyarsa ta zauna,sai ya gyada kansa a hankali yana sake maida dubansa ga wayar.

End of Chapter 54Continue to the next chapter or choose another story below.

More Hausa novels

Browse all books →
Previous Login to Save Next