Ramadan Promo!All users that send a manual request for premium upgrade on sallah day will be granted for 1 month free.
Soyayyanovels
A Duniyata Part One Complete Hausa Novel
A Duniyata Part One Complete Hausa Novel
By Billyn Abdul
Login to keep your reading position saved.
Book Page Chapters
A Duniyata Part One Complete Hausa Novel

A Duniyata Part One Complete Hausa Novel

Author: Billyn Abdul
Chapter 24 of 84
About 4 min read
Chapter progress: 0%
Listen Mode
Listen to this chapter using your device voice.
Ready to listen from this chapter.
Free access is active. You can keep reading and download during this access window.

Book chapters

Choose a chapter and continue reading.

Start chapters
Chapter 1 1,700 words Chapter 2 1,700 words Chapter 3 1,700 words Chapter 4 1,700 words Chapter 5 1,700 words Chapter 6 1,700 words Chapter 7 1,700 words Chapter 8 1,700 words Chapter 9 1,700 words Chapter 10 809 words Chapter 11 1,700 words Chapter 12 1,700 words Chapter 13 1,700 words Chapter 14 1,700 words Chapter 15 1,700 words Chapter 16 1,700 words Chapter 17 1,700 words Chapter 18 1,700 words Chapter 19 1,700 words Chapter 20 1,700 words Chapter 21 1,700 words Chapter 22 1,700 words Chapter 23 1,700 words Chapter 24 Reading now Chapter 25 1,700 words Chapter 26 1,700 words Chapter 27 1,700 words Chapter 28 1,425 words Chapter 29 1,700 words Chapter 30 1,700 words Chapter 31 1,700 words Chapter 32 400 words Chapter 33 1,700 words Chapter 34 1,700 words Chapter 35 1,700 words Chapter 36 1,148 words Chapter 37 1,700 words Chapter 38 1,700 words Chapter 39 1,700 words Chapter 40 1,700 words Chapter 41 1,700 words Chapter 42 1,700 words Chapter 43 956 words Chapter 44 1,700 words Chapter 45 1,700 words Chapter 46 1,700 words Chapter 47 1,700 words Chapter 48 1,700 words Chapter 49 1,700 words Chapter 50 1,700 words Chapter 51 30 words Chapter 52 1,700 words Chapter 53 1,700 words Chapter 54 1,484 words Chapter 55 1,700 words Chapter 56 1,700 words Chapter 57 1,700 words Chapter 58 1,700 words Chapter 59 1,700 words Chapter 60 1,700 words Chapter 61 1,373 words Chapter 62 358 words Chapter 63 1,700 words Chapter 64 1,700 words Chapter 65 1,700 words Chapter 66 1,700 words Chapter 67 1,700 words Chapter 68 1,700 words Chapter 69 1,700 words Chapter 70 1,700 words Chapter 71 1,700 words Chapter 72 1,700 words Chapter 73 1,700 words Chapter 74 1,700 words Chapter 75 1,700 words Chapter 76 1,700 words Chapter 77 1,700 words Chapter 78 1,700 words Chapter 79 1,700 words Chapter 80 1,700 words Chapter 81 1,700 words Chapter 82 1,700 words Chapter 83 1,700 words Chapter 84 642 words

Tsai tayi da idanunta tana kallon notifications din har suka gama jerin gwanon shigowarsu suka qare. Kaman ta sharesu ta isa kai tsaye ga abinda zai sadata da mashkur sai kuma ta sauya tunani. Ma'ajiyar saqonnin ta shiga,ta fara bin sunayen mutanen da suka aje mata saqon daya bayan daya don bata jin tana da isashen lokacin da zata tsaya budewa da karantawa. Kamar yadda ta zata,ta samu saqonnin mashkur da yawa fiye dana kowa,saita wuce kowanne saqo ta tafi saqon daya tura mata na qarshe kwanaki biyu da suka wuce. Sallamarsa kadai ta amsa,ta tura masa ta maida wayar ta aje saman locker tana bin fuskar wayar da kallo,zuciyarta na shirya mata yadda komai zai tafi. Ta jima da ajjiye mashkur saboda yadda zalamarsa ta fito a fili. Ta jima da ganin ta barshi a gefe saboda yadda halinsa yasha banban dana kowa cikin mutanen da ta taba tarayya dasu cikin rayuwarta. To amma yanzu silar matsalar aisha tana ganin wannan shine right time da zata koya masa darasi shima yabi sahun sauran mazan da suka shude cikin rayuwarta. Agogon dake manne saman kanta ta kalla tana qoqarin dawo da nutsuwarta waje guda. Zuciyarta ke wani irin rawa tamkar dai ta soma gajiya da al'amuran da suke tunkarota cikin rayuwa. Wasu su shude,wasu kuma suna ci gaba da fuskantarta da babbar BARAZANA. kamar mintuna goma sha biyar sun qaru akan lokacin dawowarsu daga islamiyya na ainihi. Aje dubanta tayi saman hijabinta na sallah,saita miqa hannu ta dauka tana miqewa da zummar duba inda suka maqale. Bata wasa da duk wani abu da ya shafesu musamman fita da dawowarsu gida. Duk da su din kwata kwata basu san ko ina ba idan ka dauke hayoyi da layukan dakan sadasu da makarantarsu. Kaman jira akeyi tayi taku uku daidai wayar ta dauki ringing. Duk da ta jima bataji ringing din wayar ba amma babu abinda ta manta daga sautinta. Taku ukun ta sakeyi ta dawo tana duban wayar bayan zuciyarta ta gama ayyana mata waye din me kira "Mashkur" Kaman yadda ta aje number dinsa. Siririn murmushin da bata shirya ba ya subucewa labbanta. Tana tsaye tana ci gaba da duban wayar har ta qaraci burarinta ta yanke. Bata da niyyar daga kiran kwata kwata a yanzun,don ba tsarinta bane samun komai daga wajenta cikin sauqi ba. Ta yardarma kanta tana da tsada,tsadar data sanya kowanne namiji da zai ratsa ta cikin DUNIYARTA yarda da hakan,ya kuma bita da tsarinta a yadda ya sameta. Kaman yadda ta zata bazai kira sau daya ya bari ba haka taji wayar ta sakeyin qara,salin alin ta koma ta maidata silent,sannan ta jawo Locker ta wurgata ta rufe ta kuma soma takawa hanyar falonsu tana zura hijabin saman wuyanta. Shimfidadden kwarjinin dake boye bayan fuskarta ya sake bayyana sosai tamkar ta sanya hijabin ne don ado ba domin biyan buqatarta ba. Slippers dinta masu taushi ruwan hoda dake daga bakin qofar da zura ma fararen qafafunta,ta murda handle din qofar ta bude ta tura ta fito. Fayau tsakar gidan nasu yake da wadataccen filin nan da baya rabo da tsafta duk da iyalin da gidan ke qunshe dashi. Kamar kowanne lokaci kamar kuma yadda suka maidata ABUN KALLO. Kowanne motsinta yana saman idanun mafi yawa daga cikinsu,bawai don su bata kulawar data dace ba....bawai don suyi mata gyara idan tayi kuskure ba......badon kulawa ta qauna ba.......saidai don wani radin kansu da biyan buqatar qashin kansu. Tana da wani irin kaifin nazarin fahimtar meke kai kawo a kewayenta. A zaune take ko tafiya take?. Wani yanayi da a baya baya cikin dabi'unta,kuma bata dashi,amma yanayi da salon rayuwa ya tilastata kasancewa hakan. Dab da rijiyar gidan wadda daga ita sai hanyar da zata sadaka da ainihin farfajiyar gidan ta ganta. Tsaye gaban rijiyar dauke da cup da alama ruwa ta gama sha. Sanye take da atamfa classic da aka yiwa dinkin zamani riga da skirt daya zauna daidai jikinta. Kanta ba dankwali wannan zai baka damar hango baqar sumarta me sulbi da suka gada ainihi daga mahaifinsu.

End of Chapter 24Continue to the next chapter or choose another story below.

More Hausa novels

Browse all books →
Previous Login to Save Next