Soyayyanovels
A Duniyata Part One Complete Hausa Novel
A Duniyata Part One Complete Hausa Novel
By Billyn Abdul
Login to keep your reading position saved.
Book Page Chapters
A Duniyata Part One Complete Hausa Novel

A Duniyata Part One Complete Hausa Novel

Author: Billyn Abdul
Chapter 78 of 84
About 8 min read
Chapter progress: 0%
Listen Mode
Listen to this chapter using your device voice.
Ready to listen from this chapter.
Free access is active. You can keep reading and download during this access window.

Book chapters

Choose a chapter and continue reading.

Start chapters
Chapter 1 1,700 words Chapter 2 1,700 words Chapter 3 1,700 words Chapter 4 1,700 words Chapter 5 1,700 words Chapter 6 1,700 words Chapter 7 1,700 words Chapter 8 1,700 words Chapter 9 1,700 words Chapter 10 809 words Chapter 11 1,700 words Chapter 12 1,700 words Chapter 13 1,700 words Chapter 14 1,700 words Chapter 15 1,700 words Chapter 16 1,700 words Chapter 17 1,700 words Chapter 18 1,700 words Chapter 19 1,700 words Chapter 20 1,700 words Chapter 21 1,700 words Chapter 22 1,700 words Chapter 23 1,700 words Chapter 24 671 words Chapter 25 1,700 words Chapter 26 1,700 words Chapter 27 1,700 words Chapter 28 1,425 words Chapter 29 1,700 words Chapter 30 1,700 words Chapter 31 1,700 words Chapter 32 400 words Chapter 33 1,700 words Chapter 34 1,700 words Chapter 35 1,700 words Chapter 36 1,148 words Chapter 37 1,700 words Chapter 38 1,700 words Chapter 39 1,700 words Chapter 40 1,700 words Chapter 41 1,700 words Chapter 42 1,700 words Chapter 43 956 words Chapter 44 1,700 words Chapter 45 1,700 words Chapter 46 1,700 words Chapter 47 1,700 words Chapter 48 1,700 words Chapter 49 1,700 words Chapter 50 1,700 words Chapter 51 30 words Chapter 52 1,700 words Chapter 53 1,700 words Chapter 54 1,484 words Chapter 55 1,700 words Chapter 56 1,700 words Chapter 57 1,700 words Chapter 58 1,700 words Chapter 59 1,700 words Chapter 60 1,700 words Chapter 61 1,373 words Chapter 62 358 words Chapter 63 1,700 words Chapter 64 1,700 words Chapter 65 1,700 words Chapter 66 1,700 words Chapter 67 1,700 words Chapter 68 1,700 words Chapter 69 1,700 words Chapter 70 1,700 words Chapter 71 1,700 words Chapter 72 1,700 words Chapter 73 1,700 words Chapter 74 1,700 words Chapter 75 1,700 words Chapter 76 1,700 words Chapter 77 1,700 words Chapter 78 Reading now Chapter 79 1,700 words Chapter 80 1,700 words Chapter 81 1,700 words Chapter 82 1,700 words Chapter 83 1,700 words Chapter 84 642 words

motsi tsakanin anni da maamah sai yaga tarin banbance babance. Da fari anni lafiyarsu kawai takeso taji kafin komai......amma ita nata uzurin su shigo suci abinci shi ta fara gabatarwa,abincin da ta tabbatar koda basuci a wajenta ba zasuci ako ina nema,amma kuma lafiya fa?. "Ayyukane suka tsaremu yau dukkaninmu,yanzu haka ma wani guri zan qarasa......amma in sha Allah i will do my best". Shuru ta danyi wuta tana dauke mata,yanzun qarfe tara harda rabi na dare,yaushe yaje wani waje,yabaro gurin kuma yazo wajenta?. " Okay,ina jira" Abinda ta fada kenan tana jin kamar ta bude masa abinda ke ranta. Bala'i da masifa takeson lullubeshi dashi,to amma ko dazun suna waya da hajja harira sai data gaya mata "Me garaje ba kasafai ya fiya cin nasara ba a dukka lamuransa,saikin saka haquri juriya da kauda kai kaman bakiga komai ba". Wayar ta cillar gefe,ta hada tafukan hannayenta cikin fuskarta. Wata irin tsanar anni da alhaji hamza tana mata masauki a zuciya tana kuma qara samun hauhawa cikin ranta. Inama ace yau zata budi idanu taga babu su cikin rayuwarsu?,da kowacce dama tazo mata yadda takeso. Iya tafiyar da sukayi cikin motar bawai zaman shuru kadai yayi ba,zuciyarsa ta gama nisa akan matsalar iya balla shingen asusun ajiyarsu har kuma a debi wani abun?. Ba shakka koma waye ya aikata hakan yana da alaqa me qarfi da kamfaninsu,yana kuma da alaqa ta kusa kusa da mika'il. Dole ya zamana yana da alaqa da mikail.....ko shi kansa mikail din ma gaba daya. Dalili......dukan abinda zai basu daman yin kutse kai tsaye da samun nasara haka a sauqaqe yana tare da mikail din. Dazu dazu ya danqa masa komai,cikin qasa da awa biyu kacal kuma ace komai ya faru?. "Muje gida" Ya bawa driver din umarni,wanda ba wanda ya binciki dalili tsakaninsu ukun suka sauya akalar tafiyar tasu. A tsaitsaye ya leqa anni sannan ya wuce zuwa sassanshi. Ya samu sassan nasa neat kamar ko yaushe kaman kuma yadda yake buqata. Ba duhu ba kuma haske me yawa sai matsakaicin hasken da bai fiya takurawa idanuwa ba. Ko ina qamshi yake fiddawa da wani irin moderate yanayi. Takalmanshi ya sabule daga bakin qofa yana sauya wasu lausasan flip flops,daya daga cikin hadimansa ya sunkuya ya daukesu yana adanasu cikin wani qawataccen ma'ajiyar takalma me daukan hankali. "Ku ajiye komai ku tafi,na sallami kowa.....sai da safe" Ya fadi musu yana takawa zuwa hanyar da zata sadashi da wani dan corridor da zai bashi daman isa bangaren dakunan baccinsa. Daga zuciyarsa har gangar jikinsa basu da wani karsashi ko qwari,to amma kasancewar zuciyar jaruma ce ya sanya bata gaza ba,sai daya tabbatar yayi wanka yayi sallah ya sauya kayan jikinsa sannan Kai tsaye ya dawo falon da babu kowa a cikinsa,saidai ya tabbatar security tako ina suna kai kawo cikin gidan dama wajen gidan. A nutse yake ratsa falon hannunsa zube a aljihun boxers din daya sanya tamkar wanda ya boyeshi saboda jin sanyi ko baya buqatar aga hannun nasa. Light blue kalan kayan sun masa wani irin kyau,saidai kuma fuskarsa tadan fada kadan wanda baya rasa nasaba da stress din yau daya tsinci kansa a ciki. Dining ya wuce kai tsaye,komai yana shirye cikin tsafta. Bayajin a duniya bayan anni akwai wanda yakai ameh sanin tsarinsa akan abinci. Yasan duk abinda ya bude cimarsa ce,kuma abinda yakeso ne,saidai kuma bayajin akwai wani sauran space da cikinsa zan dauki abinci,wannan ya sanya ya bude royal glass bowl din da tun bai bude ba yana iya ganin abinda yake ciki. Lafiyayyen fruit salad ne da aka samar dashi daga dukkan nau'in kayan marmari na nan qasar dama wanda bamu dasu a nan din. Baya rabo da fruit sam,don haka masu shirya masa store da fridge dinsa sunsan duk inda zasu samar masa da nauin fruit da cimar da yakeso din. Yadan diba da yawa,sai ya sauka a hankali ya duba ma'ajiyar shayinsa. Bayashan coffee sai idan dole ta kama,amma yasan sirrin shan black tea da ake masa hadi na musamman da abubuwa masu amfani ga lafiya irinsu cinnamon cardamom scent leaves da sauransu. Da kansa ya shirya komai saman tray ya nufi wata yar kyakkyawar books shelves ta ainihin gogaggen katako dake bangon gabas na parlor din. Hannu daya ya sanya ya murza wani abu da ba lallai ka iya lura da zamansa jikinta ba,sai ya sakeshi yasa hannu ya juyashi take qofa ta bayyana daga baya abinda ba zaka taba tunanin samuwarsa a wajen ba,ya taka ya shiga a hankali yana maida qofar yadda take. *D U N I Y A T A* *_H U G U M A_* PAGE 76 Daki ne da yakan jima bai shiga cikinsa ba sai muhimmin aiki irin haka ya taso. Saidai duk da haka komai a tsaftace yake. Wani irin table ne na musamman ya jawoshi gaban main table dake dauke da nau'ikan na'urorin computer iri daban daban,ya aza tray din hannunsa a kai,ya taka a hankali ya kunna kowanne lantarki dake dakin,ya bada haske sosai. Komai na dakin bisa tsari yake,da nau'o'in kalolin green masu qarawa idanu qwarin gani. Idanunsa saman systems din daya kunna guda biyu yana jiran su gama saituwa. Kadan kadan kuma yana kurbar black tea din da qamshinsa ke qara masa nutsuwa,kafin ya ajiye ya soma shan fruit salad din,daidai sanda komai na system din ya daidai ta,sai ya sake jawo kujerarsa gaba yana bata dukkanin hankalinsa. Cikin tsananin nutsuwa da qwarewa yake bin komai. Ya kusa kashe a qalla awa biyu cikakku kafin ya dakata,ya tura kujerarsa baya yana zubawa allon computer idanu yana duba abinda ya samu a tsahon zaman da awannin da ya kashe. Iska kawai yake furzarwa daga bakinsa,mamaki yana sake cikashi da samun bayanan duk da bai qarasa samun ragowar baya nan ba,amma ko iya wadannan bayanan da zaman da zaiyi da mikail sun isheshi samun kan komai. Ya dinga murza tafin hannunsa cikin na juna tamka ma jin sanyi,kanshi yana sake cakewa. "Jibril usman" Ya maimaita sunan idanunshi nakan sunan da bai samu damar samun ainihin fuskar me sunan ba. Tabbas ko wayeshi din mayen computer ne,kuma qwarrare a sanin fanninta,saidai duk da haka qwarewar tasa akwai saura,don akwao gurare da abubuwa daya gani wanda shi Jabril din da ya samu rufesu to ba shakka shi kansa yanzun bazaikai ga isa ga bayanan ba. Qaramin masanin computer zai iya saluting jibril,amma shi da mutane ire irensa zasuyi murmushi ne kawai,a karon farko kuma su fahimci saura taqi kadan yakai inda ya dace yakai din. Gefe daya ranshi ya sake ninka baci,duk wanda yaga aka zare kudin zaiyi tsammamin manyan hackers gagarumai wanda suka gagari duniya system dinsu ta hadu dashi......wannan kadai ya isa ya sake zaburar dashi lallai lallai yana buqatar yin garambawul wa security team dinsa,amma kafin sannan mikail shine mutum na farko daya dace ya dauki mummunan mataki a kansa,saboda shi da kansa ya yiwa tsaron company dinsu aiki,ya saka abubuwan da duk qwarewarka idan ba samun wani information mutum yayi ba zai wahala ya samu isa ga inda suka samu isa din. "Ina yaje?,waye ya bawa sirrinmu?" Wadannan sune tambayoyi guda biyu da yake buqatar ji daga bakin mikail din. Kodai yaci amanar company......ko an nemi rayuwarsa an masa barazana....kota dalilin sakacinsa bayanan sun fita. Washegari kaman kullum,yabi tsarin jawadalinsa na kullum tun daga gida har zuwa office. Qarfe shida da rabi yake kammala motsa jikinsa ya wuce wanka,idan ya fito yakan dan bar bathrobe jikinsa ya karbi newspaper da magazines ya duba,yadan duba saqonnin email da WhatsApp dinsa ya hada da shan ruwan duminsa ko dafaffiyar madarar shanunsa me tumeric. Sai bayan kammala dukka wadannan hidindimun sannan yake shiryawa,yayi breakfast ya wuce office. Kamar ko yaushe yau dinma bakwai da rabi ya fito daga toilet daure da bathrobe dinsa. Yanaso yau ya fita da wuri ne fiye da yadda ya saba fitan. Don ko da safe daya tashi ya sami missed calls din maama din kusan guda goma,wanda ya tabbatar tun na daren jiya ne. Yawan kiran nata kadai da takeyi yana sake bashi tabbaci ne a kanta. Ya jawo wayar ya turawa musaddiq text akan zuwa takwas ya shirya zai aikeshi wani guri,sai ya cire toilet slippers din ya sanya wasu tausasan rufaffun takalma ya soma takawa yana fita don riskar parlor ya duba newspapers din yau. Ba kowa parlor din sai ameh daketa zirga zirgar shiryawa ogan nasa dining,sai me sunan malam dake zaune saman lallausan turkey carpet din da aka qawata tsakanin kujerun. Me sunan malam din na daya daga cikin amintattunsa da basu da shamaki wajen samun daman isowa parlor dinsa. "Good morning sir" Ya fadi yana rusunar dakai "Morning me sunan malam.....mun tashi lpy" Ya amsa masa yana zama saman wata sofa guda daya data banbanta da sauran duka kujerun parlor din yana kai hannunsa saman dan qaramin table din da aka zube masa sabbin newspaper din bayan an kwashe na jiya. "Lafiya alhamdulillah sir" "Ma sha Allah" Ya furta yana bude page din farko na jaridar ba tare daya tsaya karanta bangonta dake dauke da title na labaran ciki ba. Labarin farko suka wafci idanunsa. Ya sake dawowa da baya bayan ya karanta layin farko da akayi da manya manyan zane. Bai tsaya bata lokaci ba ya koma bangon don sake duba title din da ya tsallakeshi a dazu. Tabbas duka abu guda suke nunawa cikin harshen turanci *_GAGARUMAR SATA.....AN WAWASHE KOMAI DAGA ASUSUN JADDA DIAMONDCHORE RESOURCES/AKWAI YIWUWAR DURQUSHEWAR COMPANY DIN NAN DA WANI DAN LOKACI_*. Jaridar ya juya tamkar ma ya manta wanne gidan jarida ne suka kafe labarin. Sai ya maidata ya ajiye yana dauko newspaper ta gaba. Ita dinma kaman wancan,bangon farko abinda yake rubuce kenan a jiki,ya sake juyawa shima ya duba gidan jaridar sai ya maidata itama din ya ajiye,ya sake daukan ta uku. To ita dinma babu wani canji,duka dai labari guda daya ne,abinda ya bashi tabbaci da yaqinin wannan shine labari na farko da zaiyi trending kenan yau a duniya kasuwanci. Idanu kawai yaci gaba da zubawa rubutun kamar wanda kwanyarsa ta kasa gano komai,ya daga idanunsa a nutse da suka fara sauya launi ya kalli ameh daketa goge dining din da kyau don kawar da qura datti ko maiqo komai qanqantarsa daga muhallin cin abincin boss din nasa da

End of Chapter 78Continue to the next chapter or choose another story below.

More Hausa novels

Browse all books →
Previous Login to Save Next