Soyayyanovels
A Duniyata Part One Complete Hausa Novel
A Duniyata Part One Complete Hausa Novel
By Billyn Abdul
Login to keep your reading position saved.
Book Page Chapters
A Duniyata Part One Complete Hausa Novel

A Duniyata Part One Complete Hausa Novel

Author: Billyn Abdul
Chapter 84 of 84
About 3 min read
Chapter progress: 0%
Listen Mode
Listen to this chapter using your device voice.
Ready to listen from this chapter.
Free access is active. You can keep reading and download during this access window.

Book chapters

Choose a chapter and continue reading.

Start chapters
Chapter 1 1,700 words Chapter 2 1,700 words Chapter 3 1,700 words Chapter 4 1,700 words Chapter 5 1,700 words Chapter 6 1,700 words Chapter 7 1,700 words Chapter 8 1,700 words Chapter 9 1,700 words Chapter 10 809 words Chapter 11 1,700 words Chapter 12 1,700 words Chapter 13 1,700 words Chapter 14 1,700 words Chapter 15 1,700 words Chapter 16 1,700 words Chapter 17 1,700 words Chapter 18 1,700 words Chapter 19 1,700 words Chapter 20 1,700 words Chapter 21 1,700 words Chapter 22 1,700 words Chapter 23 1,700 words Chapter 24 671 words Chapter 25 1,700 words Chapter 26 1,700 words Chapter 27 1,700 words Chapter 28 1,425 words Chapter 29 1,700 words Chapter 30 1,700 words Chapter 31 1,700 words Chapter 32 400 words Chapter 33 1,700 words Chapter 34 1,700 words Chapter 35 1,700 words Chapter 36 1,148 words Chapter 37 1,700 words Chapter 38 1,700 words Chapter 39 1,700 words Chapter 40 1,700 words Chapter 41 1,700 words Chapter 42 1,700 words Chapter 43 956 words Chapter 44 1,700 words Chapter 45 1,700 words Chapter 46 1,700 words Chapter 47 1,700 words Chapter 48 1,700 words Chapter 49 1,700 words Chapter 50 1,700 words Chapter 51 30 words Chapter 52 1,700 words Chapter 53 1,700 words Chapter 54 1,484 words Chapter 55 1,700 words Chapter 56 1,700 words Chapter 57 1,700 words Chapter 58 1,700 words Chapter 59 1,700 words Chapter 60 1,700 words Chapter 61 1,373 words Chapter 62 358 words Chapter 63 1,700 words Chapter 64 1,700 words Chapter 65 1,700 words Chapter 66 1,700 words Chapter 67 1,700 words Chapter 68 1,700 words Chapter 69 1,700 words Chapter 70 1,700 words Chapter 71 1,700 words Chapter 72 1,700 words Chapter 73 1,700 words Chapter 74 1,700 words Chapter 75 1,700 words Chapter 76 1,700 words Chapter 77 1,700 words Chapter 78 1,700 words Chapter 79 1,700 words Chapter 80 1,700 words Chapter 81 1,700 words Chapter 82 1,700 words Chapter 83 1,700 words Chapter 84 Reading now

abu ne ya cakewa kawu a rai,ya tsani zina,ya tsani harkar neman matan banza,kaman yadda ya tsani shaye shaye,barshi kawai da cacarsa data zame masa masifa wanda dama tana da shiga jiki. Kai tsaye yaji tsantsar cin fuska ce ya tanadeta zaiyi musu wannan ya sake aza wutar qaimi a zuciyarsa,ya karkace kaman yadda yakanyi a yanayi irin wannan,ya kalli Mikhail da kyau "Idan dai har ya zama mallakin naka kana da wannan damar" Ya bashi amsar da wani irin kakkaifan kallon dake gaya masa kai tsaye na SAI NA BAKA DAMAR CINYE GIDAN SANNAN ZAKA AIKATA HAKAN. Izza da jin cewa zai samu nasara akan kawun ya sanyashi ninka abinda kawun ya zuba shima ya zuba cikin cacar aka fara buga wasan. Tashin farko kawun ya maido takardun gidan yayi tafiyar ruwa da kudaden da mikail ya zuba,abinda ya jawo hautsinewar wajen,hankula dukka suka komo wajen,aka fara yo dafifi,wadanda aka cinye suke alhini dukansu karsahinsu ya dawo,sai aka fara zuba sabon wasa. Da daya da daya ya dinga zuba abinda ya ciyo kawu sama'ila yana kwashewa. Duk abinda ya zuba kawun ya cinye shaidan zuciya da kuma mato saisu gaya masa ya sake zuba wani,zai iya yuwuwa ya samu nasarar dawo da abinda aka cinye masa a baya. Tafi tafi cikin qasa da awa biyu sai gashi yana tashi daga Mikhail me manyan kudi yana komawa asalin mikail dinsa kaman yadda ya shigo wajen. Cikar awa biyu cif komai ya qare!.kawu sama'ila ya wawushe duk wata kadara daya cinyo daga wajen wasu ya zuba!,ya koma tsurar yadda ya shigo musu a wajen!. Sowa ihu murna da tafi ya cika wajen,ainihin sunan kawu sama'ila na teburin ya soma dawowa bakunansu wato DA BANBANCI!. Kowacce tsiga ta jikin mikail zubawa takeyi. Idanunsa sun kada sunyi jazur,jijiyoyin kansa sun fito rada rada. Sosai yakejin ya muzanta,ya toxarta. Ta yaya zai bari wani qaramin alhaki tsohon daya bashi shekaru masu tazara ya kafa tarihi a kansa?,tarihin da muddin ya bari ya tabbatu a haka.....to ko shakka babu ya xubar da kimarsa da kwarjininsa a idanun abokan cacarsa dake bashi wani irin girma. Karon farko a rayuwarsa da wani yayi nasara a kansa,shi kuwa ta yaya zai bari haka ta tabbata?. "Ga wasu kudaden na zuba.....azo a sake zama!!" Ya furta da qarfi,sautin daya sanya wajen yin dif aka zuba masa ido. Da sauri mato ya kalleshi,ya kuma ja hannunsa da qarfi yana dubansa qasa qasa "Wanne kudi kuma ya rage maka indai ba motar da mukazo a ciki ba zaka saka?" "Qyaleni mato.....bakajin habaicin da suke yada min?,dole na aje musu tarihi,dole sunan mikail suma yaci gaba da wanzuwa a kunnuwansu da bakunansu da wajen cacarsu". "Wanne kudi ya rage maka?!" "Ragowar abinda aka bari a asusun jadda" Ya fada yana jin zuciyarsa ta qeqashe,kuma tabbas wannan kudin xai dawo da sauran kudin da duka narke,duk kuwa da yasan mugun gangancin dake cikin aikata haka. "Kada kayi haka!" Mato ya fadi a gigice. "Anma yi" Ya amsa masa ba fargaba ko shayi saboda ya bawa kansa tabbacin shine keda nasara. Wayarsa ya fidda yabi dukkan process yayi transfer kudin da suka rage zuwa account din wanda zai ajiye kudin,idan nasara tasa ce ta dawo masa,idan ta kubce kuma dukka kudi sun tabbata mallakar KAWU!. Daidai lokacin da akayi alerting mutum biyu fitar kudin,sai fuad dake zaune yana bibiyar komai ya lumshe ido yana sauke siririyar ajiyar zuciya,daidai sannan kuma kira ya shigo masa. Ko daya duba sai yaga daga department din da aka kira ya daga yana cewa "Just keep an eye on it,naga komai" Sai ya kife wayar yana maida dubansa ga allon system din yana qoqarin tracking account na wanda aka sanya kudin. *_TURQASHI....QAQA QARA QAQA,BAZANCE KOMAI BA .....amma akwai ZAZZAFAR TURKA TURKA FA.....MUJE ZUWA_* *HUGUMANKU CE* * , . , . _GoBack SummaryInformation DocumentSummaryInformation WpsCustomData Infinix X6819 TECNO LD7 WPS Office 1a53450ff78f46c9a382e96366f95ab3

End of Chapter 84Continue to the next chapter or choose another story below.

More Hausa novels

Browse all books →
Previous Login to Save Book Page