Ramadan Promo!All users that send a manual request for premium upgrade on sallah day will be granted for 1 month free.
Soyayyanovels
A Duniyata Part One Complete Hausa Novel
A Duniyata Part One Complete Hausa Novel
By Billyn Abdul
Login to keep your reading position saved.
Book Page Chapters
A Duniyata Part One Complete Hausa Novel

A Duniyata Part One Complete Hausa Novel

Author: Billyn Abdul
Chapter 36 of 84
About 6 min read
Chapter progress: 0%
Listen Mode
Listen to this chapter using your device voice.
Ready to listen from this chapter.
Free access is active. You can keep reading and download during this access window.

Book chapters

Choose a chapter and continue reading.

Start chapters
Chapter 1 1,700 words Chapter 2 1,700 words Chapter 3 1,700 words Chapter 4 1,700 words Chapter 5 1,700 words Chapter 6 1,700 words Chapter 7 1,700 words Chapter 8 1,700 words Chapter 9 1,700 words Chapter 10 809 words Chapter 11 1,700 words Chapter 12 1,700 words Chapter 13 1,700 words Chapter 14 1,700 words Chapter 15 1,700 words Chapter 16 1,700 words Chapter 17 1,700 words Chapter 18 1,700 words Chapter 19 1,700 words Chapter 20 1,700 words Chapter 21 1,700 words Chapter 22 1,700 words Chapter 23 1,700 words Chapter 24 671 words Chapter 25 1,700 words Chapter 26 1,700 words Chapter 27 1,700 words Chapter 28 1,425 words Chapter 29 1,700 words Chapter 30 1,700 words Chapter 31 1,700 words Chapter 32 400 words Chapter 33 1,700 words Chapter 34 1,700 words Chapter 35 1,700 words Chapter 36 Reading now Chapter 37 1,700 words Chapter 38 1,700 words Chapter 39 1,700 words Chapter 40 1,700 words Chapter 41 1,700 words Chapter 42 1,700 words Chapter 43 956 words Chapter 44 1,700 words Chapter 45 1,700 words Chapter 46 1,700 words Chapter 47 1,700 words Chapter 48 1,700 words Chapter 49 1,700 words Chapter 50 1,700 words Chapter 51 30 words Chapter 52 1,700 words Chapter 53 1,700 words Chapter 54 1,484 words Chapter 55 1,700 words Chapter 56 1,700 words Chapter 57 1,700 words Chapter 58 1,700 words Chapter 59 1,700 words Chapter 60 1,700 words Chapter 61 1,373 words Chapter 62 358 words Chapter 63 1,700 words Chapter 64 1,700 words Chapter 65 1,700 words Chapter 66 1,700 words Chapter 67 1,700 words Chapter 68 1,700 words Chapter 69 1,700 words Chapter 70 1,700 words Chapter 71 1,700 words Chapter 72 1,700 words Chapter 73 1,700 words Chapter 74 1,700 words Chapter 75 1,700 words Chapter 76 1,700 words Chapter 77 1,700 words Chapter 78 1,700 words Chapter 79 1,700 words Chapter 80 1,700 words Chapter 81 1,700 words Chapter 82 1,700 words Chapter 83 1,700 words Chapter 84 642 words

anni din. Bata da wani buri a rayuwa daya wuce dukka wannan daula dukiya da kuma mulki su dawo qarqashin kulawarta,su dawo qarqashin mulkinta,su dawo qarqashin umarninta. Tunda ya sauko ya kasa wucewa yabar gidan kamar yadda anni ta umarceshi,kawai sai ya samu kansa da samun waje ya zauna saman tsadaddu kuma lafiyayyun sofas din da suka zamo ado wa falon. Kujeru ne na musamman kaman yadda kowanne falo na gidan ke qawace da nashi kalar kujerun. Ba komai yakeyi ba,kawai yana zaune ne hakanan,saidai kuma zuciyarsa tayi nisa da gangar jikinsa. Tun yana da shekaru biyu a duniya yasan wacece ita,yasan abune me matuqar wahala ta iya zama da anni ta sauko lafiya qalau ba tare data gasa mata maganganu masu ciwo ba. Damuwar anni damuwarsu ce,sukan gwammace ciwo bacin rai damuwa ko jarrabawa ta samesu amma tabar musu anninsu ta zauna lafiya. Motsi da alamun takun mutum da yaji yaja hankalinsa,ya waiwaya da sauri daidai sanda ta kammala sauka daga stairs din take doso ainihin falon ta yadda zata cimma qofar fita waje. Da idanu ta kafeshi har zuwa sanda ta cimmasa a inda yake tsaye goye da hannayensa. "Ka gaza tafiya ko saboda kada kabar wajen na bata ran qanwa ko yayar ubanka!" Ta furta a zafafe. Kadan zuwaira ta matsa hannuwanta "Da ruwan sanyi ma saika dafa dutse......kiyi a hankali" Ta furta mata qasa qasa. Kalamanta sun samu gurbi a zuciyarta saidai basu samu damar sauketa daga fushinta ba gaba daya,don haka taci gaba da kallonsa a sanda yake tsaye a gabanta ba tare da yace komai ba. Kimanin mintuna biyu kafin ta furxar da iska daga bakinta sannan ta juya tana barin falon zuwairan na biye da ita. Sanda suke ratsa farfajiyar farko ta gidan zuwa na biyu.....duk da maganganu da zuwaira keyi wanda duka akan abinda ya faru cikin gidanne amma hakan bai dauke hankalinta daga tarin zalla zalla kuma galla gallan motocin dake ajiye qarqashin sashen ajiyar motoci na gidan ba. *SU SAKE DAWO MUKU DA WASU SABBIN LABARAI* *_BAYAN WASAN DA AKA BUGA GA WANI SABON WASAN_* *_MIQAQQIYAR TAFIYAR NISHADI_* *_KAFATAWA DA ZAFAFAN MUHAWARA_* *_LABARAI MASU DAURE KAI DA SANYA NISHADI A CIKIN ZUKATAN MASU KARATU_* *ZAFAFA BIYAR* *_MASUBURBUDAR LABARAI MASU CIKE DA HIKIMA DA DEBE KEWA DA WASA TUNANI TARE DA TSUMA ME KARATU DA TSUMAMMIYA KUMA TSAFTATACCIYAR SOYAYYA_* *Hanzarta shiga ayarin ZAFAFA FAMILY(WATO IYALAN ZAFAFA DA BASA GAJIYA DA KASANCEWA DA SU* _TA HANYAR SHIGA RUKUNIN MASU SIYAN LITATTAFANSU KAMAR HAKA_ _QIRJIN ME HANKALI Miss xoxo_ _K'ALBIM Mamuhghee_ _AJIYA A DUHU Billynabdul_ _DUNIYATA Huguma_ _Dukka qunshin litattafan daga farko har qarshensu_ *hudu 2k* *uku 1500* *Biyu 1k* *Daya 500* _YADDA ZAKU BIYA IDAN KATI NE:_ *09032345899 KATIN MTN, IDAN AN TURA SHEDAR MA NUMBER ZAA TURAWA* *IDAN BANKI NE A TURA SHEDA ZUWA GA* *09033181070* *BANK NAME/SUNAN BANKI: ACCESS BANK* *ACCOUNT NUMBER/LAMBAR ASUSUN BANKI: 0022419171* *ACOUNT NAME/SUNAN DA KE ASUSUN BANKI:MARYAM SANI GUMMI* *AL'UMMAR MAQWAFCIYAR QASATA NIJER KUWA* 89825722 Nousaiba lawali maradi 1000cf *_Madalla da masoyan ZAFAFA BIYAR_* *_MADALLA DA KASANCEWARKU TARE DASU_* *D U N I Y A T A* *_H U G U M A_* PAGE 35 Ta sauke wata qatuwar ajiyar zuciya me nauyin gaske "Bugatti,rolls Royce,Lamborghini Aventado,Brabus G_wagon,Mercedes Benz,BMW......zuwaira?" Ta qarashe lissafin jerin motocin da idanunta suka gani din tana waiwaya ga zuwairan "Na'am?" "Kinsan adadin lissafi da qiyasin kudaden wadannan motocin kuwa?,kinsan waye da waye matsayi da matakin rayuwa suke cillashi zuwa ga mallakarsu?,kinsan wanne me tsananin sa'ar ne cikin duniya yake da rabon samun wadannan motocin?.....zuwaira ace d'ana keda su amma ya rasa a gidan da zaya barni sai a wannan wulaqantaccen gidan?" Ta fadi da mugun zafi tana nuna gidan da suke tsaye a gabansa da yatsa. Kamar yau ne zuwairan ta saba ganin gidan,kamar ba cikinsa take kwana take tashi ba,ta daga kai tana duban gidan da maama din ke kira da wulaqantacce. Kyakkyawan gini ne da aka yishi madaidaici me dauke da madaidaiciyar harabar dake dauke da mota qirar range Rover guda biyu duka don biyan buqatar matar gidan. Wadatacciyar haraba dake dauke da dogayen katangu da kuma yalwataccen gate dake qarqashin kulawar mutum daya wato malam saidu. Akwai qaton kitchen da aka zuba masa dukka kayan tasarrufin girki kamar kitchen din 'yar bana bakwai,kitchen din dake maqale da store dake danqare da kayan abincin da yafi qarfin cikin mutum ashirin da zasu shekara kullum suna ci kuma ana kyauta dasu. Babban falo me dauke da dining area......bedrooms guda hudu da kowanne aka qawatashi da kayan gado 'yan turkey masu asalin kyau da tsada,kaman yadda aka qawata falon da kayan turkey din hatta da curtains da carpet kuwa. Wuta 24hrs,engine wanki dana guga,Ac hade da fanka,me aiki guda daya a cikin gida,da kuma me kula da farfajiyar gidan namiji baya ga me gadi malam saidu. Albashin naira dubu dari duk wata ga mamallakiyar gidan. Nisan buri......zurfafa da kuma zarmewa a son zuciya.....take laifuka,dannesu da manta abinda baya ta haifar ya lullube idanunsu su dukka biyun "Indai zaa yi qiyasi bisa irin nau'in arziqin fu'ad.....idan dai zaa yi duba da gidan daya sanya wadancan mutanen wanda idan aka sanya gidanki cikin nasu baifi matsayin boys quarters na gidan ba......tabbas ya wulaqanta haqqin haihuwa......hakanan ire iren wadannan gidajen kinfi qarfin zama a cikinsa saidai kiyi kyautarsa ga irinmu" "Zuwaira" Ta kira sunanta cikin jaddadawa "Na'am" "Ki rubuta ki ajiye.....muddin ban raba tsakaninsa da aminatu ba tabbas ban haifu 'yar halak ba...." Maganarta ta qarshe kenan da tayi ta kutsa kanta cikin gidan tana jin gaba daya gidan tafi qarfin wanzuwa a ciki. "Subhanallah......innalillahi wa'inna ilaihi rajiun" Malam saidu ya furta yana dire qaramar radio din dake hannunsa yanata kokawar kunnata. Sake maimaita salatin yayi,kansa yana sake daurewa sosai. To amma meye ya kawo wannan cin ALWASHIN?. Me ya kawo wannan CIN BURIN. Saita rabashi da anni?,rabuwa ta har abada?,sai ta mallakeshi?,MALLAKA kamar wani miji?. Shin me ya kaita alwashi akan DAN DA BA NATA BA?,wanne rashin imani ne zata tasamma shiga tsakanin UWA da D'A?,shin mene ne alaqarsu?,wacece ita a tsakaninsu?. Kasa kunna radio din yayi,yayi shuru tamkar yana nazarin wani abu dake shirin tunkarowa. Ya gaza fahimtar tsakanin ita da ANNI WACE MAHAIFIYAR?,WACE KUMA UWAR?. Cikin nutsatstsen takunsa ya miqe daga zaman da yayi saman sofa bed yana sanya rufaffun takalmansa na fata berluti brand da suka dace da suit da lafiyayyen suit dinsa *hugo Boss* brand da sukayi fice wajen fidda luxury suit daga zare da yaduka gami da auduga mafi daraja a duniya. Tsaye yayi gaban mirror yana cirar madaidaicin comb da yake amfani dashi wajen taje kwantacciyar sumar dake fuskarsa qasan habarsa da kuma kansa. Sumar da ko yaushe cikin sheqi take da asalin santsinta da wani irin darkness da gashin yake dashi nuturally. Sosai fuskarsa ta sake fresh,cikakkiyar eyebrows dinsa da eyelashes dinsa masu baqin gashi sun sake fidda ainihin kyawun fuskarsa,sun kuma sake taimakawa kyakkyawar qasumbarshi wajen sake qawata fuskarsa da wani irin ajiyayyen kwarjini.

End of Chapter 36Continue to the next chapter or choose another story below.

More Hausa novels

Browse all books →
Previous Login to Save Next