Ramadan Promo!All users that send a manual request for premium upgrade on sallah day will be granted for 1 month free.
Soyayyanovels
A Duniyata Part One Complete Hausa Novel
A Duniyata Part One Complete Hausa Novel
By Billyn Abdul
Login to keep your reading position saved.
Book Page Chapters
A Duniyata Part One Complete Hausa Novel

A Duniyata Part One Complete Hausa Novel

Author: Billyn Abdul
Chapter 7 of 84
About 8 min read
Chapter progress: 0%
Listen Mode
Listen to this chapter using your device voice.
Ready to listen from this chapter.
Free access is active. You can keep reading and download during this access window.

Book chapters

Choose a chapter and continue reading.

Start chapters
Chapter 1 1,700 words Chapter 2 1,700 words Chapter 3 1,700 words Chapter 4 1,700 words Chapter 5 1,700 words Chapter 6 1,700 words Chapter 7 Reading now Chapter 8 1,700 words Chapter 9 1,700 words Chapter 10 809 words Chapter 11 1,700 words Chapter 12 1,700 words Chapter 13 1,700 words Chapter 14 1,700 words Chapter 15 1,700 words Chapter 16 1,700 words Chapter 17 1,700 words Chapter 18 1,700 words Chapter 19 1,700 words Chapter 20 1,700 words Chapter 21 1,700 words Chapter 22 1,700 words Chapter 23 1,700 words Chapter 24 671 words Chapter 25 1,700 words Chapter 26 1,700 words Chapter 27 1,700 words Chapter 28 1,425 words Chapter 29 1,700 words Chapter 30 1,700 words Chapter 31 1,700 words Chapter 32 400 words Chapter 33 1,700 words Chapter 34 1,700 words Chapter 35 1,700 words Chapter 36 1,148 words Chapter 37 1,700 words Chapter 38 1,700 words Chapter 39 1,700 words Chapter 40 1,700 words Chapter 41 1,700 words Chapter 42 1,700 words Chapter 43 956 words Chapter 44 1,700 words Chapter 45 1,700 words Chapter 46 1,700 words Chapter 47 1,700 words Chapter 48 1,700 words Chapter 49 1,700 words Chapter 50 1,700 words Chapter 51 30 words Chapter 52 1,700 words Chapter 53 1,700 words Chapter 54 1,484 words Chapter 55 1,700 words Chapter 56 1,700 words Chapter 57 1,700 words Chapter 58 1,700 words Chapter 59 1,700 words Chapter 60 1,700 words Chapter 61 1,373 words Chapter 62 358 words Chapter 63 1,700 words Chapter 64 1,700 words Chapter 65 1,700 words Chapter 66 1,700 words Chapter 67 1,700 words Chapter 68 1,700 words Chapter 69 1,700 words Chapter 70 1,700 words Chapter 71 1,700 words Chapter 72 1,700 words Chapter 73 1,700 words Chapter 74 1,700 words Chapter 75 1,700 words Chapter 76 1,700 words Chapter 77 1,700 words Chapter 78 1,700 words Chapter 79 1,700 words Chapter 80 1,700 words Chapter 81 1,700 words Chapter 82 1,700 words Chapter 83 1,700 words Chapter 84 642 words

yana qaunarta yana qaunarta har baisan iya adadi ba. Abu na biyu indai saddiq dinsa yana lafiya to komai me sauqi ne. A haka suka debi wata guda cur babu abinda ya sauya. Yadda kowacce safiya da ubangiji zai bullo da ranarsa haka zata fidda wani sabuwar muguntar don quntatawa cuzgunawa a garesu. Duk fushi zafin zuciya da rashin daukar raini irin nashi bai taba daga kai ya kalleta bare ya tanka mata ba,yana duba cewa ta girme masa,gaba take dashi,a qalla ta ninka shekarunsa sau biyu. Duka duka shekarunsa sha shida basu kai adadin shekarun da zai tsaya yana jayayya da babba ba. A hakane ALHAJI HAMZA KIBIYA ya waiwayo gida cikin iyalansa. Yaran suna ranshi matuqa,babu kuma ranar duniya da zata bullo ta bace bai tambayeta su ba idan suna waya,amsar kuma daya ce suna lafiya lau. Koda ya buqaci magana dasu tana gabatar masa ne da wani uzurin a kansu. Wanda ya rigaka kwana zai rigaka tashi. Sanda ya sanar da dawowarsa kaf ta hadasu ta musu mummunar jankunne data tsoratasu ainun. Saidai ko kadan shi bai tsorata ba,don ba komai yake bashi tsoron ba,bare a yanzun da zuciyarsa ke qarasa bushewa da qeqashewa akan komai na rayuwa. Yadda aka saba haka ta sakar musu,sukaci gaba da zuwa makaranta abba yana kaisu da kanshi kamar yadda yakeyi idan har yana gari. Ya tsumu sosai,zuciyarsa kuma ta cika da takaici da bacin rai me yawan gaske sanda ya isa class dinsu yaga yadda aka tsere masa a karatu. Kusan ranar duka ya qarar da ita wajen bibiyar dame dame akayi da baya nan?,ya karbi note books na classmate dinsa da dama ya taho dasu gida . Da yake abba yana nan akwai isashen lokaci 'yanci da kuma hutu,babu tarin aikace aikacen nan marasa dalili marasa kuma tushe ballantana makama,sai ya zauna ya qarar da dukka wuninsa a daki wajen ganin ya daidaita karatunsa dana 'yan uwansa. Bashi da matsala da saddiq,don ajinsu daya da musaddiq,kuma duk sanda suka dawo gida Faruqee yana hadasu su sake maimaicin karatu tare ta yadda zai zamana ba'a wuce saddiq din ba. Yana da wata irin baiwar basira ta gasken gasken,sharp brain dake da saurin koyo da kuma riqe abu tun yana dan mitsitsinsa ballantana a yanzun da yake shirin fara shiga shingen samartaka,danyan jini yana zagayawa da gudu a jikinsa. Wannan ya taimaka cikin sati gudan da abba ya musu hutu ya gama kammala komai,ya kuma tarar dasu tamkar dama dashi ake karatun. Sai a sannan ya samu sukuni ya soma dawowa daidai. Saidai kuma a satinne qarshen satin,a yammacin juma'a abban ya tattara ya koma lagos,abu guda daya dake alamta musu zasu koma RAYUWAR GIDAN JIYA kenan cikin gidan. ********* *_MONDAY_* Tushen aiki,bai sare ba ya shirya tsaf kamar yadda su Faruqee ke shiryawar,yana shirin Faruqee na rantse rantse da cewar ba abinda zai hanasu fita a makaranta yau din. Ya lallaba kitchen ya hada musu tea kaman yadda ya saba ya dawo ya bawa kowa,saidai ya tsallake me babban suna don yasan bazai sha ba,don kuwa tun daga wancan ranar data zagi abban bai sake ci ko shan wani abu da Faruqee zai dauko musu ba,ya tsani zagin iyaye matuqa,mutum ne kuma me fushi da gudun zuciya,wannan ya sanya yake takatsantsan,akan komai bai fiya zura jikinsa ba. Fitowa sukayi kamar wancan karon,saidai a yauma sun sameta hakimce a falon. Idonsa yadan lumshe yana addua daga qasan zuciyarsa. Ya tabbatar wannan zaman ta yishi ne saboda su,son a lokutan da abba yake gari kwata kwata nasa ganin qyallinta sai kusan shada zuwa sha biyu na rana. "Eh......wato akuyar daure an samu sake,to kuzo nan" Faruqee ne na farko daya fara cakewa guri daya,amma ya kama hannunsa ya jashi suka qarasa wajen. "Me zakuyimin ku?,tunda kuna da uba ya daure muku gindi?,ku tashi kuban waje,ku kuma ku koma ta inda kuka fito a cire uniform azo a kama aiki ko?" Cikin tsananin bacin rai Faruqee ya miqe yana nufar hanyar fita yana kuma qananun maganganu qasa qasa "Zagina kekeyi farouqu?,ka kuskura ka zageni ubanka zanci wallahi la'ada waje" Ta furta da hargagi tana nunashi da yatsa sanda suke kusa da ficewa daga falon. Abinda ya sanya me babban suna miqewa yana jin nauyi da kuma zafin zaginnan. Ko meye zatayi me ya gamo da iyayensu?,me su sukayi mata idan su din masu laifi ne a gareta?. "Don Allah mama ki barmu muje muma,idan mun dawo zamuyi miki duk aikin da kikeso" "Kai.....wasa nakeyi dakai?,zaka tashi ka bani waje ko sai na zagi uwarka mara daraja da ubanka dake qarqashin qasa?" Kamar saukar mashi haka kalamanta suka soki zuciyarsa,har sai daya kasa jurewa ya waiwayo yana dubanta. "Don Allah mama ko meye,ko meye mukayi miki ki mana hukunci ba tare da zagin iyaye ba......" "Ubanka da uwarka,shegen yaro me tsaurin ido,kaci ubanka" Ta fada har tana zullo tare da watsa masa daquwa. Ta jima da tsanar dama wannan kamewar tasa,ta jima da tsanar yadda yake da dauke kai da rashin hayaniya akan komai da zatayi masa,duk yadda takai ga tama masa wajen bashi baqin kashi da baqar wahala don ya magantu dukka ya shanye sai a yau din. Cikin qasa da minti guda launukan idanunsa suka sauya,baice qala ba amma kunnuwansa suna suna iya jin zafafan muggan kalaman da take jifanshi dasu. Ya tako a nutse ya iso gaban saddiq dake durqushe a gabanta ya sanya hannu ya damqi hannunsa ya tasheshi tsaye,abun sai ya masa kamanceceniya da sanda saddiq din ke tsananin roqon mahaifiyarsu akan kada ta tafi ta barsu. Bai waiwayeta ba,bai kuma dakata ba ya durfafi qofar fita daga falon kanshi tsaye,ba tsoro ba shakka ba kuma shayi "Ina zakaje,bance ba zakuje makaranta ba?" Ta furta da qaqqarfan sauti. Bai dakata ba bai kuma waiwayo ba ko ya nuna yasan tanayi har ya fice daga falon. A yau ta rushe dukkan wani ragowar kara da dagin qafa da yakeyi mata. Baya wasa da kalmar UBA sam a rayuwarsa,IYAYEN MA guda biyu,abba da Abbey. https://www.arewabooks.com/book?id=675041625c3130f457519997 ________________________ _QIRJIN ME HANKALI Miss xoxo_ _K'ALBIM Mamuhghee_ _AJIYA A DUHU Billynabdul_ _DUNIYATA Huguma_ _Dukka qunshin litattafan daga farko har qarshensu_ *hudu 2k* *uku 1500* *Biyu 1k* *Daya 500* _YADDA ZAKU BIYA IDAN KATI NE:_ *09032345899 KATIN MTN, IDAN AN TURA SHEDAR MA NUMBER ZAA TURAWA* *IDAN BANKI NE A TURA SHEDA ZUWA GA* *09033181070* *BANK NAME/SUNAN BANKI: ACCESS BANK* *ACCOUNT NUMBER/LAMBAR ASUSUN BANKI: 0022419171* *ACOUNT NAME/SUNAN DA KE ASUSUN BANKI:MARYAM SANI GUMMI* *AL'UMMAR MAQWAFCIYAR QASATA NIJER KUWA* 89825722 Nousaiba lawali maradi 1000cf *_Madalla da masoyan ZAFAFA BIYAR_* *_MADALLA DA KASANCEWARKU TARE DASU_* *D U N I Y A T A* *_H U G U M A_* *Arewabooks:Huguma* https://www.arewabooks.com/book?id=675041625c3130f457519997 PAGE 09 Ko Faruqee baisan da zuwansa makarantar ba sakamakon banbancin abinda kowannensu yake karanta,har sai sanda aka fito break. Har a sannan ranshi a jagule yake,bacin rai kowanne second yana sake motsa zuciyarsa. Faruqee ya sameshi daga bayan makarantar zaune qasan bishiya saman rairayin dake wajen,hannunsa riqe da busashen siririn reshen bishiyar yana tona qasa dashi,ya kafe qasar da idanu kamar me nazarin samar da wani abun amfani daga gareta. Ta gefansa ya zauna,yayi masa tambayar duniya akan ya akayi ya taho makarantar amma ya gaza cewa komai. Na Faruqee ba,tunda ya shiga class din baiyi manana da kowa ba,don bayajin koda ya bude bakinsa akwai wasu kalmomi da zasu iya fita daga cikinsa. Dole Faruqee ya haqura ya kuma tayashi zaman shurun,don dukkansu dama babu me 'yanci ko damar yin break,to inama kudin?,dukka dana transport din da komai ta hada ta kalmashe. Sai a hanyar komawa yaji komai daga bakin saddiq. Qwafa yaja yana girgiza kai "Duk yadda kake tunanin matar nan ta wuce nan,duk kuwa yadda zan fasalta maka,ta samu sassauci ne daga garemu shi yasa take abinda taga dama,ace mutum ya shiga shekara ta sha biyar,kana girma amma baka da 'yanci?" Shikam baima iya cewa komai ba har zuwa sanda qafafunsu suka maidasu gida. Sai da suka gilma ta gaban gidansu kafin su cimma gidan RIQOnsu a yanzu,idanunsa zube bisa fuskar gidan dake garqame da kwado. Take yaji wata matsananciyar kewar gidan da kewar Abbie da jadda suka saukar masa. Duk da suna rayuwa ne cikin matsakaicin matsayi na rayuwa,amma rayuwarsu rayuwa ce me 'yanci da kuma dadi. Duk da suna rayuwa da maama cikin wani baqon hali da murdaddiyar dabi'a.......hakan yafi musu sauqi a kan rayuwarsu ta yanzun cikin gidan RUQO. Ya janye idanunsa sanda ya dubu daidai wajen da mahaifinsa ya dogaro da qyar ya biyo bayan maaman yana cike da fatan zata dakata daga aiwatar da qudurinta nayin nesa da rayuwarsu,wani zafin akan na dazu ya sake yunqurowa ya mamaye zuciyarsa. Daga saman balcony din da zata sadaka da ainihin falon suka sameta a zaune ta hakimce. Faruqee ne a gaba,musaddiq yana biye dashi,sai me babban suna da ko qaunar hada idanu da ita bayayi. Zuciyarsa yadda take a zafafen nan tana ayyana masa abubuwa masu dama a kanta. "Idan ka kuskura ka qaraso na saina sanya an maka dukan tsiya......baka isa ka shigamin gida ba tunda kai din tantiri ne mara kunya.....nan gaba kadan shaye shaye zaka farayi da daba,kaga kenan ka samu hanyar da zaka hallakani a banza" Ta fada tana miqewa tsaye. Dukka su hudun sukayi carko carko suna dubanta da jin kuma wani sabon bala'in daya tunkarosu kuma bayan na dazu da safe. "Kai har ka isa na fadi magana ka sabamin bare ka maidamin?,don an zagi uwarka da ubanka,su su waye da ba za'a zagesu ba?,wato gaka kai me zuciya ko,to an zagesu din na kuma zagi banza da wofi". Da qarfi ya damqi hannun saddiq ya kuma soma ja da baya yana janye jikinsa daga wajen " Yauwa gwara daka fahimta,don wallahi kabar gidan nan kenan,tun yanzu kana tsayarmin ina ga nan gaba idan ka gama zama balagagge?". Da sassarfa Faruqee da har ya isa bakin qofar falon ya soma saukowa yana takowa zuwa garesa ganin suna nufar gate din fita daga gidan yana qwala masa kira da niyyar tsaidashi "Aisai ka bishi kaima don ubanku,na fiku iskanci qananun balagaggu" Ta furta tana komawa saman kujerar ta zauna "Bar nan gurin" Ta kwatsawa musaddiq daya mace a wajen saboda tsoro da mamaki tsawa,baiyi wata wata ba ya juya shima yabi bayan 'yan uwansa. Bai

End of Chapter 7Continue to the next chapter or choose another story below.

More Hausa novels

Browse all books →
Previous Login to Save Next