Soyayyanovels
A Duniyata Part One Complete Hausa Novel
A Duniyata Part One Complete Hausa Novel
By Billyn Abdul
Login to keep your reading position saved.
Book Page Chapters
A Duniyata Part One Complete Hausa Novel

A Duniyata Part One Complete Hausa Novel

Author: Billyn Abdul
Chapter 31 of 84
About 8 min read
Chapter progress: 0%
Listen Mode
Listen to this chapter using your device voice.
Ready to listen from this chapter.
Free access is active. You can keep reading and download during this access window.

Book chapters

Choose a chapter and continue reading.

Start chapters
Chapter 1 1,700 words Chapter 2 1,700 words Chapter 3 1,700 words Chapter 4 1,700 words Chapter 5 1,700 words Chapter 6 1,700 words Chapter 7 1,700 words Chapter 8 1,700 words Chapter 9 1,700 words Chapter 10 809 words Chapter 11 1,700 words Chapter 12 1,700 words Chapter 13 1,700 words Chapter 14 1,700 words Chapter 15 1,700 words Chapter 16 1,700 words Chapter 17 1,700 words Chapter 18 1,700 words Chapter 19 1,700 words Chapter 20 1,700 words Chapter 21 1,700 words Chapter 22 1,700 words Chapter 23 1,700 words Chapter 24 671 words Chapter 25 1,700 words Chapter 26 1,700 words Chapter 27 1,700 words Chapter 28 1,425 words Chapter 29 1,700 words Chapter 30 1,700 words Chapter 31 Reading now Chapter 32 400 words Chapter 33 1,700 words Chapter 34 1,700 words Chapter 35 1,700 words Chapter 36 1,148 words Chapter 37 1,700 words Chapter 38 1,700 words Chapter 39 1,700 words Chapter 40 1,700 words Chapter 41 1,700 words Chapter 42 1,700 words Chapter 43 956 words Chapter 44 1,700 words Chapter 45 1,700 words Chapter 46 1,700 words Chapter 47 1,700 words Chapter 48 1,700 words Chapter 49 1,700 words Chapter 50 1,700 words Chapter 51 30 words Chapter 52 1,700 words Chapter 53 1,700 words Chapter 54 1,484 words Chapter 55 1,700 words Chapter 56 1,700 words Chapter 57 1,700 words Chapter 58 1,700 words Chapter 59 1,700 words Chapter 60 1,700 words Chapter 61 1,373 words Chapter 62 358 words Chapter 63 1,700 words Chapter 64 1,700 words Chapter 65 1,700 words Chapter 66 1,700 words Chapter 67 1,700 words Chapter 68 1,700 words Chapter 69 1,700 words Chapter 70 1,700 words Chapter 71 1,700 words Chapter 72 1,700 words Chapter 73 1,700 words Chapter 74 1,700 words Chapter 75 1,700 words Chapter 76 1,700 words Chapter 77 1,700 words Chapter 78 1,700 words Chapter 79 1,700 words Chapter 80 1,700 words Chapter 81 1,700 words Chapter 82 1,700 words Chapter 83 1,700 words Chapter 84 642 words

girman ta'addanci irin nasu ba. *_ALBISHIR A GAREKU!!_* *_SHIN KUNSAN UMMUMAHNOOR LUXURIES TA TANADAR MUKU INGANTATTUN KAYAN ADO NA FITA KUNYA KUWA?_* *_KAMAR SU_* Atamfofi Laces Shadda Materials Takalma Jakunkuna Mayafai Trolley Sarka da dan kunne Oil perfumes *_karki tsaya sanya har ayi babu ke,maza garzaya ta nan_* Numbers 08034469681 08135142610 Handles Instagram @ummu_mahnoor_luxuries TikTok username @ummu_mahnoor_luxuries Facebook ummu_mahnoor_luxuries *_inganci da kwalliya shine muradinmu_* ________________________ *SU SAKE DAWO MUKU DA WASU SABBIN LABARAI* *_BAYAN WASAN DA AKA BUGA GA WANI SABON WASAN_* *_MIQAQQIYAR TAFIYAR NISHADI_* *_KAFATAWA DA ZAFAFAN MUHAWARA_* *_LABARAI MASU DAURE KAI DA SANYA NISHADI A CIKIN ZUKATAN MASU KARATU_* *ZAFAFA BIYAR* *_MASUBURBUDAR LABARAI MASU CIKE DA HIKIMA DA DEBE KEWA DA WASA TUNANI TARE DA TSUMA ME KARATU DA TSUMAMMIYA KUMA TSAFTATACCIYAR SOYAYYA_* *Hanzarta shiga ayarin ZAFAFA FAMILY(WATO IYALAN ZAFAFA DA BASA GAJIYA DA KASANCEWA DA SU* _TA HANYAR SHIGA RUKUNIN MASU SIYAN LITATTAFANSU KAMAR HAKA_ _QIRJIN ME HANKALI Miss xoxo_ _K'ALBIM Mamuhghee_ _AJIYA A DUHU Billynabdul_ _DUNIYATA Huguma_ _Dukka qunshin litattafan daga farko har qarshensu_ *hudu 2k* *uku 1500* *Biyu 1k* *Daya 500* _YADDA ZAKU BIYA IDAN KATI NE:_ *09032345899 KATIN MTN, IDAN AN TURA SHEDAR MA NUMBER ZAA TURAWA* *IDAN BANKI NE A TURA SHEDA ZUWA GA* *09033181070* *BANK NAME/SUNAN BANKI: ACCESS BANK* *ACCOUNT NUMBER/LAMBAR ASUSUN BANKI: 0022419171* *ACOUNT NAME/SUNAN DA KE ASUSUN BANKI:MARYAM SANI GUMMI* *AL'UMMAR MAQWAFCIYAR QASATA NIJER KUWA* 89825722 Nousaiba lawali maradi 1000cf *_Madalla da masoyan ZAFAFA BIYAR_* *_MADALLA DA KASANCEWARKU TARE DASU_* *D U N I Y A T A* *_H U G U M A_* *Arewabooks:@Huguma* https://www.arewabooks.com/book?id=675041625c3130f457519997 PAGE 31 ___________________________ Wani murmushi ya saki "Ai basu ba,ko jamaa da muke tare dasu sukasan abinda muke dauke dashi sunanmu matattu......maganar diamond da gold akeyi farouq.......kasan nauyi da girman ma'adanin dake jikinmu?......mutanen nan sun wuce duk sani da tunaninka.....ni kaina da na yarda mubi Samuel da shirina,na san kuma cikin su waye zan shiga,kaine nake zaton bakasan irin girman wajen da muka shiga ba.....banda saa tana tare damu bamu isa mu shiga wannan wajen bama bare akai ga samun abinda muka samu kuma har mu gudo lafiya lau dashi......daga yanzu har zuwa sanda zamu koma qasarmu rayuwarmu na cikin hadari......take care dude...." Ya fada yana bugun kafadar farouq da ya gama mutuwar zaune. Bin fu'ad kawai yakeyi da kallo yana mamaki. Yasan girman hatsarin fiye dashi amma yayi kaman bai sani ba?,ko a yanzun wannan uban wahalallen gudun ceton ran da sukasha shi kaman ma baiyi ba?. A yadda ya sanshi da I don't care manner da rashin shiga abubuwan rayuwa sosai bai taba zaton ya iya daukar risk da tarar aradu da ka ba sai a yanzu. Tun daga tashar da suka samu mafaka sukasan lallai an baza nemarsu,a daren suka haye motocin kaya dake lodin arewa suka wuto gida.......wanda sai daga bisani abba yasan komai. Yayi fada yayi fada kaman zai ari baki......ya kuma yi musu fadan da bai taba musu shi ba,musamman me babban suna da yake girmama sunansa yake kuma qaunar yaron har cikin ransa. ANNI ce ta sanya baki aka samu ya lafa sannan aka fara tunanin yadda zaa yi da abinda ya haqo din,tunda ya riga ya shigo hannu ba batun ace za'a maida musu. Bisa dukkan dokoki da tsare tsare kan tsaftatacciyar hanya aka tsara komai ya zama dukiyar da a yanzun suke juyata shida farouq dinsa. Abban kuma ya zame musu jagora madubi.....ma'adanin kuma ya zama shine kasuwancinsu.....babbar masana'antar karbar haqaqqun ma'adanai su tace su gyarashi su fiddashi xuwa manyan qasashe,irinsu china,south Korea japan UK da manyan qasashen dake hulda da cinikayyar ma'adanan qasa masu tsada da daraja. A nahiyar africa JADDA DIAMONDCHORE RESOURCES ya zama kamfani na daya da qasashen ke rububin karbar kaya a hannunsu bayan doke Coregeo mining company din da yayi. Kamfanin daya jima yana murza zarensa da kyau,sai gashi rana tsaka JADDA DIAMONDCHORE RESOURCES yazo yasha gabansa ta ba zata,al'amarin daya haifar da takun saqa me girma a zuciyar kamfanin. Duk da fu'ad yasan da wannan......amma ya dauka normal competition da kishi ne da kan iya faruwa tsakanin kowanne kasuwanci,saidai ga mamallakin kamfanin JOE abun ba haka bane. *_D A W O W A_* Dubansa abba yayi bayan ya aje mug din hannunsa "Kwanaki nawa ya rage mu tafi ne me babban suna?" Zama yayi sosai yana goge gumin fuskarsa da dan qaramin towel din da magaji(hadiminsa) ya miqo masa. "Ba zamu wuce sati daya ko kwana biyar ba abba,hankalina yana kan anni......jikintan nan ya fiya matsawa da yawa" Yayi maganar alamun abun yana tabashi ya bayyana har saman fuskarsa. Idanu abban yadan zuba masa,har a ransa yana cike da zallar mamaki na yadda me babban suna ke damuwa da anni da rayuwarta fiye da dukkansu su ukun. Annin da abban yake ganin ba itace halitta ta farko data cancanci samun wannan qauna da kulawa daga gareshi shi din ba......annin da yake ganin kulawar da yake bata baifi ya bata kaso hamsin cikin dari ba.......ita kanta wasu lokuta tana sanya damuwa a ranta game da inda yafi karkatar da kulawar tasa sama da daya bigiren da shine dolensa,.....kuma akafi buqatar hakan daga gareshi. "Yanzun haka ma nan da awa daya zan fita,zamu gana da ceo na Labrilliante company,zan miqa musu iya abinda zasu samu.....don abba wannan karon tunanina ya fara sauyawa" Maganar fu'ad cikin tatacciyar nutsuwar nan tasa da wani irin jan aji kamar mace ya dawo da Alhaji hamza daga tunaninsa "Wanne tunani ne fu'ad?" Zamansa ya gyara sosai yana bawa abba dukkan kallo da hankalinsa "Abba......a yadda mutanen nan daga kowacce qasa suke rububin siyan resources namu da muke fiddowa daga qarqashin qasar da Allah ya shimfida mana kadai ya isa ka fahimci suna amfani damu ne suna kuma amfani da damarsu......yanzu haka a daren jiya kafin na kwanta sai dana karba kira daga wani company dake japan bayan ainihin kamfanin da muke kaiwa kaya......suna taya kayanmu akan farashin da wancan kamfanin basa bamu......wannan shi yasa nayi wani nazari......abba ya kamata qasarmu ta amfana da wadannan ma'adanai masu tsada da daraja,wanda mu Allah ya mallakawa su.....abba inda a qasarsu wadannan ma'adanai suke,babu wani baqar fata daya isa ya sameshi.....it's hardly ka iya isa wajen......nayi tunanin bude babban company da zai dinga sarrafa wadannan ababen zuwa kayan qyale qyale na mata.....don dama company daya muke da na alhaji rayyan(dangantakar zuciya),shi kuma duwatsu masu daraja suke sarrafawa ba gold ko diamond ba". Shuru abba yayi yana girgiza kai. Tabbas fu'ad din yazo da tunani me kyau daya kamata ace tuntuni sun yishi "Na yarda da wannan tunanin naka.....to amma fu'ad qarqashin haka akwai tarin matsaloli da qalubale......" "Na sani abba......insecurity na qasarmu ma kawai qalubale ne......amma a hakan.....ya zama dole mu raya qasarmu da kowanne qaramin chance da muka samu a rayuwarmu......tsoro da tunanin asara ko faduwa shine abinda zaici gaba da kasheta kowacce rana......bayan tsoron dauko shi akayi aka dasa mana shi a zukatanmu......kuma ake da buri da fatan ganin ci gaba da wanzuwarsa har zuwa rayuwar na bayanmu" "Best son ever" Abban ya furta yana sakin wani irin murmushi tare da jin qarin alfahari da fu'ad din,gefe guda kuma yana taya ainihin mahaifinsa murnar samun nagartaccen yaro mara tsoro irin muhammad fu'ad din. Qas yayi da kansa cikin girmama abban "A tayamu da addu'a abba" "Kullum cikinta muke" "Allah yaja kwana,ya qara lafiya me amfani" Ya masa addu'ar da yake jinta har cikin zuciyarsa. Agogon dake manne a bango ya kalla,sai ya miqe a nutse yana cewa "Zan qarasa ciki abba na shirya kada na sabawa lokaci" "Hakan yayi kyau" Abba ya fada fu'ad din yana sake burgeshi saboda yadda ya dauki alqawari da matuqar muhimmanci kaman yadda yake girmama lokaci. A nutse ya tura qofar dakin da sallama a bakinsa,duk kuwa da yasan ba wanda zai taras a ciki. Dakine da duka duka basufi sati guda a cikinsa ba......amma har ya kama ya kuma rine da sassanyan qamshin nan nasa dake iya bawa zuciya nutsuwa da kwanciyar hankali koda cikin radadi da qunci take. Towel din hannunsa ya rataye,ya kuma matsa gaba kadan ya ajjiye takalmin motsa jikinsa wanda daga ranar da suka tasamma barin Korea sunansa shara. Baya yawo da kaya,kowacce qasa zaije,koda kwana nawa zaiyi single yake tafiya abinsa,saidai yana sauka a qasar komai da zai buqata na amfani zai sanya a tanadar masa,yana gama amfani dashi kuma a nan zai barshi ya qara gaba. Matsawa gaba kadan yayi gaban wata mini dispenser da tafi kama da tulun zamani wadda ke zaune saman wani kyakkyawan table kusa da mirror,ya dauki disposable cup ya matsi ruwan dake da madaidaicin yanayi ya fara sha a hankali bayan yayi tsaye gaban madubin idanunshi a kai kamar me karantar yadda yake zuqar ruwan zuwa cikinsa. Ya gama ya ajiye saman madubin yana fidda siririyar iska yana ci gaba da kallon fuskarsa a madubin. Kyakkyawar sumar kansa data wadatu da tsafta ya taba sannan ya gangaro zuwa madaidaiciyar qasumbarsa data hade da gemunsa wadda ta zamawa fuskarsa wani lafiyayyen ado daya qara fidda zahirin kyawun fuskarsa,ta kuma qara masa wani mahaukacin kwarjini. Gemun da qasumbar daya zama topic of discussion a wajen 'yammatan da suka marmace a kansa. Kusan kowacce tana gayawa kanta namiji babu gashi a fuska ai mace ne,bata taba ganin qasumba da gemu da yakai kyan nasa ba......tsabar macewa a soyayya ne.....ko kuma zallar tsagwaron gaskiya suka fadi?. Rigar jikinsa ya yaye zuwa sama sannan ya zareta ya ajjiyeta saman gadon,wannan ya bawa Ginannun muscles din jikinsa bayyana muraran. Muradden jikin da zai gaya maka adadin lokutan da aka bata ana bashi kulawa ta fannin lafiya da cin lafiyayyen abinci me gina jiki. Yayi taku daya don dauko bath set nashi zai wuce toilet sai ya fasa,ya dawo da baya ya dauki wata farar samsung dake ajjiye saman mirror din. Yaga miscal amma sai ya fara maida hankalinsa ga dalilin daukar wayar,ya latsa ya fara lalubar magaji. Umarni ya bashi na abincin da zai hada masa kafin ya fito,saiya maida wayar yana shirin ajeta kira ya shigo wayar. Cak ya tsaya yana kallon sunan dake tsalle saman wayar. MOM kaman yadda farouq ya dauka da hannunsa yayi masa saving. Kafe sunan yayi da idanuwa,wayar tana kadawa hade da zuciyarsa. Sunan yake tuna ma'anarsa da kyau cikin kwanyarsa.....wadda aka maqalawa sunan ta cancanci wannan sunan kuwa anya?......ta dace

End of Chapter 31Continue to the next chapter or choose another story below.

More Hausa novels

Browse all books →
Previous Login to Save Next