Ramadan Promo!All users that send a manual request for premium upgrade on sallah day will be granted for 1 month free.
Soyayyanovels
A Duniyata Part One Complete Hausa Novel
A Duniyata Part One Complete Hausa Novel
By Billyn Abdul
Login to keep your reading position saved.
Book Page Chapters
A Duniyata Part One Complete Hausa Novel

A Duniyata Part One Complete Hausa Novel

Author: Billyn Abdul
Chapter 55 of 84
About 8 min read
Chapter progress: 0%
Listen Mode
Listen to this chapter using your device voice.
Ready to listen from this chapter.
Free access is active. You can keep reading and download during this access window.

Book chapters

Choose a chapter and continue reading.

Start chapters
Chapter 1 1,700 words Chapter 2 1,700 words Chapter 3 1,700 words Chapter 4 1,700 words Chapter 5 1,700 words Chapter 6 1,700 words Chapter 7 1,700 words Chapter 8 1,700 words Chapter 9 1,700 words Chapter 10 809 words Chapter 11 1,700 words Chapter 12 1,700 words Chapter 13 1,700 words Chapter 14 1,700 words Chapter 15 1,700 words Chapter 16 1,700 words Chapter 17 1,700 words Chapter 18 1,700 words Chapter 19 1,700 words Chapter 20 1,700 words Chapter 21 1,700 words Chapter 22 1,700 words Chapter 23 1,700 words Chapter 24 671 words Chapter 25 1,700 words Chapter 26 1,700 words Chapter 27 1,700 words Chapter 28 1,425 words Chapter 29 1,700 words Chapter 30 1,700 words Chapter 31 1,700 words Chapter 32 400 words Chapter 33 1,700 words Chapter 34 1,700 words Chapter 35 1,700 words Chapter 36 1,148 words Chapter 37 1,700 words Chapter 38 1,700 words Chapter 39 1,700 words Chapter 40 1,700 words Chapter 41 1,700 words Chapter 42 1,700 words Chapter 43 956 words Chapter 44 1,700 words Chapter 45 1,700 words Chapter 46 1,700 words Chapter 47 1,700 words Chapter 48 1,700 words Chapter 49 1,700 words Chapter 50 1,700 words Chapter 51 30 words Chapter 52 1,700 words Chapter 53 1,700 words Chapter 54 1,484 words Chapter 55 Reading now Chapter 56 1,700 words Chapter 57 1,700 words Chapter 58 1,700 words Chapter 59 1,700 words Chapter 60 1,700 words Chapter 61 1,373 words Chapter 62 358 words Chapter 63 1,700 words Chapter 64 1,700 words Chapter 65 1,700 words Chapter 66 1,700 words Chapter 67 1,700 words Chapter 68 1,700 words Chapter 69 1,700 words Chapter 70 1,700 words Chapter 71 1,700 words Chapter 72 1,700 words Chapter 73 1,700 words Chapter 74 1,700 words Chapter 75 1,700 words Chapter 76 1,700 words Chapter 77 1,700 words Chapter 78 1,700 words Chapter 79 1,700 words Chapter 80 1,700 words Chapter 81 1,700 words Chapter 82 1,700 words Chapter 83 1,700 words Chapter 84 642 words

**"Anni an gama komai" Ta furta sanda take saukowa daga saman tsararren dining area din daya dauki kyakkyawan family dining table na wani mulmulallen tangaran kai kace an samar dashi ne daga burbushin diamond ko gold da kamfanin jadda ke wankewa su fiddashi. Fara ce tas,mai matsakaicin tsaho,saidai bata da qiba ko qanqani. Yanayin sumar gaban kanta kawai zai fada maka akwai suma me yawa a saman kanta wadda bata da duhu ta danyi brown kadan bame yawa ba. Yanayin yadda ta datsi daurin dankwalinta daga tsakiyar kanta shi zai baka daman ganin hakan sosai. Straight gown ce a jikinta ta atamfa me igiyoyi hagu da dama wadda ta daureta daga gefen qungunta guda daya. "Ma sha Allah.....sannunku da qoqari....sun wuce ne?" Anni data daga kanta daga tab din hannunta da take duba wasu addu'o'i ta fada. Fuska tadan yamutsa kadan tana zama kujerar gefan annin gami da ajiye qaramin towel din hannunta a side table sannan ta dauki wayarta dake ajiye akai tana qoqarin budeta "Kowa ya wuce......yanxun abba da hamma kawai muke jira" Ta qarasa maganar murmurshi yana subuce mata. "Umhummm......wato shi saddiq shine marainin wayonki da baki ta tasa ko?" Anni ta fada tana maida idanunta ga addu'o'inta . Fuska ta yamutsa,duk da bata kalli annin ba amma ta amsa "Bar wannan anni,wa yake ta tasa,ba abinda ya iya sai takurawa mutum ba dalili......hamma takurawarsa me dalili ne idan bakayi abinda yace ba ko baka kiyaye dokarsa ba......amma yaa saddiq.....hmmmm....ko wayar nan yanzun ya shigo yana ina dannawa sai yayi challenging dina" Ta qarasa maganar tana zamewa ta kashingida saman kujerar tana maida hannunta kan shafinta na X. Ita da annin kowa ci gaba yayi da uzurin gabansa,wannan ya bawa falon daman daukan shuru na wani lokaci kafin ta daga kanta. Haka kawai ta qarewa anni kallo sai ta saki dariya "Anni.....kinsan tsadar kayannan?" Ta fada tana kallon kwantaccen lace din jikin annin dake wani yauqi da santsi duk kuwa da cotton ne. Peach color da ratsin green,bashi da nauyi ko kadan "Saikin fada 'yar kasuwa......" Ta amsa mata ba tare data dubeta ba "Anni Allah hamma yana shagwabaki......ki zauna da kaya me tsada haka a gida duk dogayen rigunanki?....amma dai....to,hala abba aka yiwa kwalliya?" Ta fada qasa qasa tana qunshe bakinta da hannu. Kadan ta dubeta ta harareta "Akwai kayan da sukayi tsadar da zan kasa yiwa abban kwalliya dasu?" Kai ta girgiza tana qoqarin maida kanta ga wayarta tana qoqarin boye dariyarta "Babu anni.....anni ta abbanmu". "Amna.... Qoqarin maidani kakarki kike ko?" "Aah anni wallahi" Ta fada da sauri tana duban anni still tana son shanye dariyarta "Kici gaba.....inajin zan dauki shawarar farouqu ne,zaki komawa nanna ne kiyi zamanki a can". Kyabe fuska tayi da kyau tana aje wayarta gefe kaman zata saki kuka "Dama haka yaa farouq din yace?,duk haqurin zama cikin mazan da nakeyi ban da sister?....." "Oho koma.meye gwara ki koma can,tunda kinga can dinma akwai mata 'yan uwanki sai kinfi jin dadi". Sosai ta sake kwabe fuska tana duban anni "Da gaske anni zaki iya bayar dani?" Daga kai tayi ta dubeta "Ba mace bace ke?,wataran ba aure zakiyi ba?" Ta tambayeta,ai kuwa saira soma matsa hawaye tana juyawa annin baya "Ai dama na sani......gidan nan babu wanda yake sona sai hamma da abba na......shi dama yaa farouq kaman ya bayar dani kyauta yakeji.....ni bazanyi aure ba.....dake zan yita zama". Yadda tayi maganar zata yita zaman da ita sai ya bawa anni dariya amma ta dake "Sai kiyi kuma" Tace tana ci gaba da scrolling sama tana duba adduo'inta. "Kinga.....ki daina biyewa ta BB farouq.......indai ina nan ba wanda zai matsa miki.......i swear" Muryar musaddiq ta biyo bayan sallamarshi. Tuni ta miqe ta zauna sosai tana qoqarin goge hawayenta. "Kaima kana biye musu yaa musaddiq wani lokacin.....amma dai ka fisu" Ta fada tana daidaita zamanta saman kujerar. Qaramar dariya ta qwacewa anni tana qoqarin ajiye tab dinta a gefe "Uhumnnn..... Ai dama ba kasafai akewa amna abun arziqi ba.....wanda ke mata abun arziqi kai tsaye a gidannan Muhammadu ne......har kun dawo?" Ta tambayeshi tana duban musaddiq dake dariya qasa qasa. "Eh anni.....su abban basu iso ba?" "Sun sauka amma basu qaraso gidan nan ba.....amma na tabbata suna dab da isowa don tun dazu suka tafi daukosu". Ta amsa masa tana miqa hannu ta karbi purse din nata da yake miqa mata. Tana yunqurin budewa su kuma suna magana tsakaninsu shi da amna. Ta zuge jakar cikin rashin tabbas da yaqini,ta bude ne kawai don taga meye yayi saura a cik,me ta samu?,amma ga mamakinta sai ta samu komai a muhallinsa ba tare da an canzawa komai waje ba bare a cire wani abu,sai wayarta data nuna low battery da alama ba'abi ta kanta bama bare a sakata a charge. "Ikon Allah" Ta fada,abinda yaja hankalin amna da musaddiq kanta "Ba abinda aka rasa a ciki musaddiq.....ba abinda ta taba kota dauka" Ta fada da mamaki idanunta cikin jakar "Nima dana bude nayi mamaki,amma nace bari na kawo miki ki duba komai bansan ko akwai wani abun daban ba" "Aiko yadda na zuba kudin a jere ba'a canza tsarinsu ba" Ta fada tana sake fiddosu "Amma dai ka yiwa yarinyar godiya ka karbamin number wayarta ko?,ko mamarta na sake yiwa godiya?" "She's not natural fa anni" Ya fada a taqaice "Kamar yaya?" Ta tambaya cikin rashin fahimta. "To nidai anni ko qyallinta ban gani ba,a bakin wani waje wani ya tareni ya bani,baicemin komai ba ya juya,nima haka na juya da kan motata na dawo gida" "Ikon Allah......gashi bata bari ko sau daya na mata godiyar alkhairin data yimin ba.....na kasa manta damuwa da kulawar data nunamin" Annin ta fadi tana juya abun a ranta. Bai samu ce mata komai ba saboda qarar bude gate da shigowar motocin da suke da tabbacin baqinsu sun iso "Alhamdulillah" Anni ta fada tana murmurshi gami da ajiye wayar da jakar a gefe. *D U N I Y A T A* *_H U G U M A_* PAGE 53 Dukkansu da sallaman a bakunnasu suka shigo. Suka amsa musu suna miqewa tsaye tare da dakon qarasowarsu cikin falon,saidai amna ta kasa jurewa. Da sauri ta taka zuwa bakin qofa ta riqe abbannata da kyau tana dariya idanunta saman fuskar fu'ad "Abba sannu da zuwa....hamma....hamma sannu da zuwa" Ta furta matsanancin murmushi yana subuce mata "Sannu 'yar abba qanwar hamma.....hamman dai aka matso a tarba aka fake da abba". Abban ya fada yana lakuce mata kumatu. Dariya suka saki fu'ad yana tayasu da murmushinsa "Amnee......barkammu" Ya amsa mata cikin kulawa. Sakin abba tayi ta matsa dab da fu'ad din tana karbar briefcase dinsa "Su amna an iya munahirci" Muryar sadiq ta shiga kunnenta,sadiq din dake tsaye ta bayansu abban. Gotasu tayi kadan tana leqensa,sai ta bata fuska "Duk abinka bazanyi welcoming naka ba.....abba me yasa baku samu wata bolar South Korea kun yar dashi kun gudo ba?" Ta qarasa tambayar tana kallon abba a shagwabe. Ba wanda maganar bata bawa dariya ba a cikinsu "Idan muka yar dashi ke zaki fara qorafin muje mu dauko miki shi ai" "Allah bazan nemi wannan ba....." "......me qarya?" Saddiq ya datsi numfashinta yana fadi idanunsa a waje "Dan aljanna" Ta fadi tana juya idanunta abinda zai sake tabbatar maka da sauran quruciya a tare da ita,hakanan kuma tana fama da sakalcin auta da gasken gaske. Kasa jiran isowar abban tayi,sai ta taka ta ruskeshi a tsakiyar falon. Ta rusuna tana masa sannu da zuwa gami da gaidashi duka tare da qoqarin amsar qananun tarkacen dake hannunsa. Cikin nashi tsananin kulawar da kallon kewa yake amsa mata,fuskarsa ta wadatu sosai da fara'a yana tambayar lafiyarta dama ta jama'ar gidan gaba daya. Hankalinsa yana kansu,qauna da kulawar dake tsakanin anni da abba sune abu guda daya tak da suka rage wadanda suke bashi hope din wataran qila zai iya aure. Soyayyar da sukema juna wani irin dasashen abu ne da har yanzu yake tasiri a tsakaninsu,babu alamun gushewa sam sam. Yanayin rayuwarsun yana burgeshi,wata irin mu'amala annin kewa abba,irin mu'amalar da bai taba ganinta ba tsakanin MAAMAHnsa da ABBEY dinsa ba. Mu'amalar da bai taba zaton akwaita tsakanin miji da mata ba sai a wajen annin. Gabanta ya qarasa shima kaman ko yaushe,cike da ban girman nan da yake jinsa har cikin ruhinsa ya tsugunna yana gaidata. Bata iya tsaiwa saman kanshi ba saboda girman shima da take bashi sakamakon sunan MUHAMMADU da yake dashi......da wata ajiyayyar kima da martaba da take ganinsa dashi saboda dattakon halinsa data sani tun bai cika shekara sha takwas bama a duniya.......uwa uba yadda yake tattalin farincikinta kadai ya sanya kowanne lokaci takejin tamkar jikinta ya tsaga ya fito. "Lafiya alhamdulillah me babban suna.....jiki na warware tun tuni......dama ta jima bata tashi ba,akasi kawai aka samu a ranar,nafi tunanin kuma matar da mukayi salla tare ne turarenta yayimin qarfi da yawa". Dan qwarya qwaryar zama sukayi cikin falon na duba lafiyar juna,qananun zolaya tsakanin amna farouq da musaddiq abban yana shiga yana raba gardama kafin daga bisani anni tayi umarni "Abinci ya zama ready.....zaku shiga ku watsa ruwa tukunna ko?" Ta fada tana duban abba me gayya me aiki "Hakan yana da kyau ko me babban suna?" Ya maida tambayar ga fu'ad. Murmushi kadan ya saki,suna girmama ra'ayinsa qwarai,sunan da yake dauke dashi ya bashi wannan girman a iyalin da suka san girma da martabar sunan. Wani abu da sam sam bai gani ba ga maamah,tana iya kiransa a lokacin quruciya da sunan ta kuma zabga masa zagi fada da sauransu "To abba" Ya amsawa Alhaji hamza yana miqewa. Farouq ne ya miqe ya dauki luggage din fu'ad din yana nufar qofa "Muje na taka maka badon halinka ba......don wallahi ka shiga uku duk sanda mukayi aure muka barka kai kadai a gidan nan". Yayi maganar qasa qasa yadda su abba ba zasuji ba. Harara fu'ad ya zabga masa yana jan qaramin tsaki "Sannu tattabara sarkin aure?,yanzun ma idan kaga dama ka koma mana ka gani?......ni gwara fa ku qara gaba ku barni daga ni sai anni ko mayi kumari". Dariya ya fashe da ita harda buga qafa kadan "Kayi asara wallahi.....kai ta qara qiba ma kake,kaci gaba da gandamewa a gaban annin?,idan bakayi wasa ba gaba gaba sadakarka za'a bayar Allah......" "Munyi asara dai ni

End of Chapter 55Continue to the next chapter or choose another story below.

More Hausa novels

Browse all books →
Previous Login to Save Next