Ramadan Promo!All users that send a manual request for premium upgrade on sallah day will be granted for 1 month free.
Soyayyanovels
A Duniyata Part One Complete Hausa Novel
A Duniyata Part One Complete Hausa Novel
By Billyn Abdul
Login to keep your reading position saved.
Book Page Chapters
A Duniyata Part One Complete Hausa Novel

A Duniyata Part One Complete Hausa Novel

Author: Billyn Abdul
Chapter 3 of 84
About 8 min read
Chapter progress: 0%
Listen Mode
Listen to this chapter using your device voice.
Ready to listen from this chapter.
Free access is active. You can keep reading and download during this access window.

Book chapters

Choose a chapter and continue reading.

Start chapters
Chapter 1 1,700 words Chapter 2 1,700 words Chapter 3 Reading now Chapter 4 1,700 words Chapter 5 1,700 words Chapter 6 1,700 words Chapter 7 1,700 words Chapter 8 1,700 words Chapter 9 1,700 words Chapter 10 809 words Chapter 11 1,700 words Chapter 12 1,700 words Chapter 13 1,700 words Chapter 14 1,700 words Chapter 15 1,700 words Chapter 16 1,700 words Chapter 17 1,700 words Chapter 18 1,700 words Chapter 19 1,700 words Chapter 20 1,700 words Chapter 21 1,700 words Chapter 22 1,700 words Chapter 23 1,700 words Chapter 24 671 words Chapter 25 1,700 words Chapter 26 1,700 words Chapter 27 1,700 words Chapter 28 1,425 words Chapter 29 1,700 words Chapter 30 1,700 words Chapter 31 1,700 words Chapter 32 400 words Chapter 33 1,700 words Chapter 34 1,700 words Chapter 35 1,700 words Chapter 36 1,148 words Chapter 37 1,700 words Chapter 38 1,700 words Chapter 39 1,700 words Chapter 40 1,700 words Chapter 41 1,700 words Chapter 42 1,700 words Chapter 43 956 words Chapter 44 1,700 words Chapter 45 1,700 words Chapter 46 1,700 words Chapter 47 1,700 words Chapter 48 1,700 words Chapter 49 1,700 words Chapter 50 1,700 words Chapter 51 30 words Chapter 52 1,700 words Chapter 53 1,700 words Chapter 54 1,484 words Chapter 55 1,700 words Chapter 56 1,700 words Chapter 57 1,700 words Chapter 58 1,700 words Chapter 59 1,700 words Chapter 60 1,700 words Chapter 61 1,373 words Chapter 62 358 words Chapter 63 1,700 words Chapter 64 1,700 words Chapter 65 1,700 words Chapter 66 1,700 words Chapter 67 1,700 words Chapter 68 1,700 words Chapter 69 1,700 words Chapter 70 1,700 words Chapter 71 1,700 words Chapter 72 1,700 words Chapter 73 1,700 words Chapter 74 1,700 words Chapter 75 1,700 words Chapter 76 1,700 words Chapter 77 1,700 words Chapter 78 1,700 words Chapter 79 1,700 words Chapter 80 1,700 words Chapter 81 1,700 words Chapter 82 1,700 words Chapter 83 1,700 words Chapter 84 642 words

kansu tana jan qaramar qwafa qasan zuciyarta,ita daidai take dasu,babu wanda ta shirya bari ya takura rayuwarta ko ya quntata ta. Duk wani motsi nata yana karance da ita,har zuwa sanda ya daidaita zamansa saman kujerar sannan ya dubeta yana kiran sunanta "Asama'u" Kallonsa kawai tayi ba tare da tace komai ba "Ga yara nan na kawosu,yara ne kuma da kin sansu bawai baqi bane a wajenki,kin kuma san basu da wata matsala ko aibu ko wani abun fada cikin unguwar nan......alqawari ne da na yiwa kaina tsakanina da ubangijina,na kuma cika alhamdulillah,ina fatan zaki tayani riqesu bisa amana ko don maraicinsu". Wani kallo takeyi masa ranta cike fal da mamaki,ta karkace tana dubanss tare da tattara abinda zata ce masa "Yanzu bayan naka yaran har yaran maqota kakeyimin kalensu?" Ta aje maganar tana jin zafi cikin ranta da zuciyarta. Tana jin ta quna bata tsoron qauri,ta soma gajiya ta kuma soma qosawa tare da debe haso hadi da tsammani na samun shimfidaddiyar rayuwar data jima tana mafarki gami da shimfidawa cewa zata samu cikin gidan..... *SU SAKE DAWO MUKU DA WASU SABBIN LABARAI* *_BAYAN WASAN DA AKA BUGA GA WANI SABON WASAN_* *_MIQAQQIYAR TAFIYAR NISHADI_* *_KAFATAWA DA ZAFAFAN MUHAWARA_* *_LABARAI MASU DAURE KAI DA SANYA NISHADI A CIKIN ZUKATAN MASU KARATU_* *ZAFAFA BIYAR* *_MASUBURBUDAR LABARAI MASU CIKE DA HIKIMA DA DEBE KEWA DA WASA TUNANI TARE DA TSUMA ME KARATU DA TSUMAMMIYA KUMA TSAFTATACCIYAR SOYAYYA_* *Hanzarta shiga ayarin ZAFAFA FAMILY(WATO IYALAN ZAFAFA DA BASA GAJIYA DA KASANCEWA DA SU* _TA HANYAR SHIGA RUKUNIN MASU SIYAN LITATTAFANSU KAMAR HAKA_ _QIRJIN ME HANKALI Miss xoxo_ _K'ALBIM Mamuhghee_ _AJIYA A DUHU Billynabdul_ _DUNIYATA Huguma_ _Dukka qunshin litattafan daga farko har qarshensu_ *hudu 2k* *uku 1500* *Biyu 1k* *Daya 500* _YADDA ZAKU BIYA IDAN KATI NE:_ *09032345899 KATIN MTN, IDAN AN TURA SHEDAR MA NUMBER ZAA TURAWA* *IDAN BANKI NE A TURA SHEDA ZUWA GA* *09033181070* *BANK NAME/SUNAN BANKI: ACCESS BANK* *ACCOUNT NUMBER/LAMBAR ASUSUN BANKI: 0022419171* *ACOUNT NAME/SUNAN DA KE ASUSUN BANKI:MARYAM SANI GUMMI* *AL'UMMAR MAQWAFCIYAR QASATA NIJER KUWA* 89825722 Nousaiba lawali maradi 1000cf *_Madalla da masoyan ZAFAFA BIYAR_* *_MADALLA DA KASANCEWARKU TARE DASU_* *D U N I Y A T A* *_H U G U M A_* *Arewabooks:Huguma* *PAGE 04* A nutse ya daga kai ya watsa mata wani irin kallo. Yau ta fara fadin hakan,amma kuma ya dade yana karantar hakan daga dukka ayyukanta da motsinta. "Nayi tunanin akwai dattako fahimta da kuma qaunar juna a tsakaninmu da har yarana sukafi qarfin kice riqonsu kikeyi,na zaci cewa kina ji a jikinki da zuciyarki kina rainkn 'ya'yan da kika haifa ne a cikinki?" Wani abu ne yazo yayi mata tsaye a wuya,ta juya kanta gefe guda tana tattaunawa da zuciyarta kan "Har abada 'ya'yan riqo ba 'ya'ya na bane,'ya'yan wasu ba zasu taba zama 'ya'yana ba.....banda qaddara me zai hadani da riqon 'ya'yan wasu?" . Idanunsa a zube fes a kanta,ya gyara zamansa sosai yana sake ci gaba da kallonta "Inaso ki cire a ranki riqo kikeyi.....ba 'ya'yana na cikina bama.......hatta yaran dana kawo yanzu,inaso ki ji a ranki Tamkar suna rayuwa ne cikin gidan mahaifinsu a gaban uwa da kuma ubansu". Dukka haqurinta ya qare,ya tuqeta ta kuma kai bango,tana jin ba zata iya ci gaba da zama tana sauraronsa ba,don haka ta miqe tsam,ta kuma gegara ta gabansa tana barin falon. Da ido ya bita har zuwa sanda take shirin bacewa ganinsa. Ya jima yana ganin alamun da suke alamta masa akwai matsaloli masu yawa cikin rayuwar su farouq,amma yayita qaryata hakan gudun kawo damuwa da matsala cikin zaman uwar wani da d'an wani wanda keda wuyar sha'ani,sai gashi a qanqanin lokaci komai yana bayyana kansa daki daki. Numfashi ya zuqa ya fesar yana rufe idanunsa,qoqari yake ya saita kansa yana tunanin hanyar da zai daidaita komai. Tray din da faruqee ya ajjiye yabi da kallo,a dawowarsa daga lagos wannan karon ya fahimci kamar ma suke yiwa kansu girki harma su hada da ita idan ta kama,babu sakewa babu walwala sam tattare dasu. Ya lura da raguwar kuzarinsu kyara da kuma hantara daga gareta,saidai dukka ya kauda kai don bai kamaci a karon farko ya fidda soyayyar yaransa kai tsaye daga zuciyarsa har haka ba,bayaso yabar wani tabo ko targaden da zai kasa gyaruwa tunda wurwuri haka. Da idanu kawai yake bin dakin da kallo sanda Faruqee yaketa masa bayani zuciya da fuskarsa cike da zumudi da farinciki. "Kayi shuru?,ka tsaya a bakin qofa,ko dakin baiyi bane na gayawa abba a qaro wasu abun?" Faruqee ya fada jikinsa yana sanyaya da yadda yaga fuskarshi. Don a yadda ya zata zayaga farinciki sosai a fuskarsa kaman kwatankwacin nasa farincikin na dawowarsa cikin gidansu,farincikin samun aboki me hankali irinsa,farincikin samun aboki da yayi daidai da shekru da hankalinsa,ba aboli irin qaninsa ba da sam.baya gane wsu abubuwan saboda sabanin mizanin hankali da fahimta dake tsakaninsu. Karon farko yayi qoqarin sake fuskarsa da kyau yana kallon faruqee. Dakin gata kuma dakin yaran gata irin wannan da shi din bai taba samun kwatankwacinsa ba ta yaya zaice baiyi masa ba?. Dukka alatu da yayi saura a dakin bashi yake daukarsa ba.......duk da qarancin shekarun daka iya dakusar da tunanin yaro a sannan......amma shi sun bawa qwaqwalwarsa damar budewa da yin tunani me nisan zango akan "Wacce irin rayuwa zasu fuskanta a matsayinsu na agola bayan su kansu tsatson gidan basu tsira ba?,mene ne makomarsu?,meye farko da kuma qarshensu?" Tarin tambayoyin da baisan ta ina zaa fara sauke masa su ba "Nayi murna farouq" Ya furta a sanyaye,sunan da shi daya yake furtashi daidai yadda yake,don har yau bai taba kiransa da faruqee ba. Yadda qanin nashi ya zuba masa idanu ya sanyashi qoqarin sakewa,ya qaraso ainihin cikin dakin kamar yadda sauran suka kai ga shigowar. Qoqarin kauda komai ya dinga yi daga zuciyarsa,yana zaune daga falon yana iya jiyo muryoyinsu sama sama,saidai har yanzun baiji tashi muryar ba. Baiyi mamaki ba,don ya sani,yadda komai nasa ya fita daban daga cikinsu,haka dabi''arsa da halayyarsa ma ta zama daban. Abincin yaja ya soma ci bawai don cin abincin yana masa dadi ko yana burgeshi ba. Tunaninsa yayi zurfin da har ba komai dake wakana cikin falon yake ganewa ba,bai taba zata ba,bai kuma taba kawowa rabuwa da rabi'atu zai iya zame masa qalubale ba sai yanzun da dukkan alamu suka fara bayyana kansu. A karon farko har yaji ya fara tuhumar kansa da kansa,tare da nacin son gano meye ainihin laifin rabi'atu ne har ta cancanci a saketa?. Baici da yawa ba ya ture,ya miqe yana irgen lokaci,sai ya juya ya fara takawa zuwa dakin yaran. Dukkansu sunyi shirin bacci amma bandashi,yana zaune gefe daya na gadon farouq,ya goye hannayensa a qirjinsa tamkar wani babba da yayi nisa cikin nazarin wani abu. Motsin abban ya sanyashi waiwayowa,da sauri ya sauke hannayensa yayi qasa da kansa yana niyyar zamowa daga saman gadon "Yi zamanka me babban suna......tunanin me ka zauna kana yi?,duk 'yan uwanka sunyi shirin kwanciya banda kai?" Farouq dake zaune tsakiyar gadon yayi hanzarin karbar maganar dama tana damunsa tun dazu "Abba yaqi ya canza kaya,na bashi kayan bacci yaqi ya saka tun dazu" Hannu kawai abban ya miqawa farouq din,sai ya saka masa kayan baccin dake gefansa. Kayan abban yabi da kallo yana jujjyasu a hannunsa,sannan ya maida dubansa zuwa jikinsu dukka su ukun dake sanye da wasu kalolin kayan. "Amma faruqee ban gaya muku a bada kayan nan ba dukansu?,ina kayan dana kawo muku wancan tafiyar da nayi?" Ya qarasa tambayar yana maida idanunsa kan saddiq qaninsa. Har wani juyawa saida cikin saddiq din yayi,saboda tunawa da yayi da kakkaifan warning din da suka samu daga wajen matar gidan akan batun. "Abba,dukka mama ta karbesu,ta kuma gargademu kada mu sake mu sanar dakai,idan ba haka ba saita tsoma kawunanmu a ruwan zafi" Ba abba kawai ba,hatta me babban sunan saida maganar ta ratsashi duk da qananun shekarunsa,amma zuwa yanzu ya dade da yiwa kansa karatun qalubalen da suke shirin fuskanta "Ruwan zafi?" Abba ya furta cikin tsananin kaduwa da mamaki,sai faruqee ya gyadawa abban kai. Maganar ta ladabtar d abba ta sanyashi samun waje ya zauna. Yana tsoron ci gaba da wannan tafiyar tasu......yana tsoron garin neman lada ya rufta ya buge d wucewa jahannama,ya debo marayun Allah da nufin basu rayuwa me inganci,muddin Mariya bata goya masa baya ba meye makomar yaran?,ya gobensu zata kasance?. Tambayoyin da suka dinga karafkiya kenan a kansa. Indai haka ne ya zama dole yayi jan ido,ya zama dole yayi wuta wuta akan gidansa da iyalinsa. Ya sauke dukka nauye nauye haqqunan da suka zama wajibi dama wadanda basu zama wajibi bs,ya zama dole to itama ta bishi yadda ya kamata. "Ba komai,tashi me babban suna ka shirya,idan kun kammala ku kashe kayan wuta gaba daya kuyi addua ku kwanta" Yayi maganar ne yana sake nazartar dakin tare da kallon guraben da ga siya ma yaran abubuwa da dama ya ajjiye saboda jin dadin Rayuwarsu a yanzu ba komai a wajen sai gurbinsu. Sai daya kammala komai daga ainihin dakinsa sannan ya zarce dakin mariya. Ta gama shirin kwanciya tsaf tayi rub da ciki tsakiyar gado tana latse latsen waya. Fuska a hade ta daga kai ta kalleshi sau daya saita dauke kan nata ta maida ga wayarta tana sake tsuke fuska. "Tashi zamuyi magana" Ya fada cikin yanayin dake tabbatar mata da gaske yake,da kuma zafinsa ya shigo. Sai da tayi kamar ba zata tashi ba sannan ta miqe ta zauna sosai tana gyara wuyan rigar baccinta tare da tsuke fuska da kyau. *SU SAKE DAWO MUKU DA WASU SABBIN LABARAI* *_BAYAN WASAN DA AKA BUGA GA WANI SABON WASAN_* *_MIQAQQIYAR TAFIYAR NISHADI_* *_KAFATAWA DA ZAFAFAN MUHAWARA_* *_LABARAI MASU DAURE KAI DA SANYA NISHADI A CIKIN ZUKATAN MASU KARATU_* *ZAFAFA BIYAR* *_MASUBURBUDAR LABARAI MASU CIKE DA HIKIMA DA DEBE KEWA DA WASA TUNANI TARE DA TSUMA ME KARATU DA TSUMAMMIYA KUMA TSAFTATACCIYAR SOYAYYA_* *Hanzarta shiga ayarin ZAFAFA FAMILY(WATO IYALAN ZAFAFA DA BASA GAJIYA DA KASANCEWA DA SU* _TA HANYAR SHIGA RUKUNIN MASU SIYAN LITATTAFANSU KAMAR HAKA_ _QIRJIN ME HANKALI Miss xoxo_ _K'ALBIM Mamuhghee_ _AJIYA A DUHU Billynabdul_ _DUNIYATA Huguma_ _Dukka qunshin litattafan daga farko har qarshensu_ *hudu 2k* *uku 1500* *Biyu 1k* *Daya 500* _YADDA ZAKU BIYA IDAN KATI NE:_ *09032345899 KATIN MTN, IDAN AN TURA

End of Chapter 3Continue to the next chapter or choose another story below.

More Hausa novels

Browse all books →
Previous Login to Save Next