Ramadan Promo!All users that send a manual request for premium upgrade on sallah day will be granted for 1 month free.
Soyayyanovels
A Duniyata Part One Complete Hausa Novel
A Duniyata Part One Complete Hausa Novel
By Billyn Abdul
Login to keep your reading position saved.
Book Page Chapters
A Duniyata Part One Complete Hausa Novel

A Duniyata Part One Complete Hausa Novel

Author: Billyn Abdul
Chapter 82 of 84
About 8 min read
Chapter progress: 0%
Listen Mode
Listen to this chapter using your device voice.
Ready to listen from this chapter.
Free access is active. You can keep reading and download during this access window.

Book chapters

Choose a chapter and continue reading.

Start chapters
Chapter 1 1,700 words Chapter 2 1,700 words Chapter 3 1,700 words Chapter 4 1,700 words Chapter 5 1,700 words Chapter 6 1,700 words Chapter 7 1,700 words Chapter 8 1,700 words Chapter 9 1,700 words Chapter 10 809 words Chapter 11 1,700 words Chapter 12 1,700 words Chapter 13 1,700 words Chapter 14 1,700 words Chapter 15 1,700 words Chapter 16 1,700 words Chapter 17 1,700 words Chapter 18 1,700 words Chapter 19 1,700 words Chapter 20 1,700 words Chapter 21 1,700 words Chapter 22 1,700 words Chapter 23 1,700 words Chapter 24 671 words Chapter 25 1,700 words Chapter 26 1,700 words Chapter 27 1,700 words Chapter 28 1,425 words Chapter 29 1,700 words Chapter 30 1,700 words Chapter 31 1,700 words Chapter 32 400 words Chapter 33 1,700 words Chapter 34 1,700 words Chapter 35 1,700 words Chapter 36 1,148 words Chapter 37 1,700 words Chapter 38 1,700 words Chapter 39 1,700 words Chapter 40 1,700 words Chapter 41 1,700 words Chapter 42 1,700 words Chapter 43 956 words Chapter 44 1,700 words Chapter 45 1,700 words Chapter 46 1,700 words Chapter 47 1,700 words Chapter 48 1,700 words Chapter 49 1,700 words Chapter 50 1,700 words Chapter 51 30 words Chapter 52 1,700 words Chapter 53 1,700 words Chapter 54 1,484 words Chapter 55 1,700 words Chapter 56 1,700 words Chapter 57 1,700 words Chapter 58 1,700 words Chapter 59 1,700 words Chapter 60 1,700 words Chapter 61 1,373 words Chapter 62 358 words Chapter 63 1,700 words Chapter 64 1,700 words Chapter 65 1,700 words Chapter 66 1,700 words Chapter 67 1,700 words Chapter 68 1,700 words Chapter 69 1,700 words Chapter 70 1,700 words Chapter 71 1,700 words Chapter 72 1,700 words Chapter 73 1,700 words Chapter 74 1,700 words Chapter 75 1,700 words Chapter 76 1,700 words Chapter 77 1,700 words Chapter 78 1,700 words Chapter 79 1,700 words Chapter 80 1,700 words Chapter 81 1,700 words Chapter 82 Reading now Chapter 83 1,700 words Chapter 84 642 words

Masu zuba kunnen abinda zai faru da kalar matakin da zai dauka suka ci gaba da sanyawa,yayin da a nasa bangaren ya nutsa cikin bincike tare da tattaunawa da taimakon dan uwansa kuma shaqiqinsa farouq. Ganawa ce takai tsaye kuma da mutum na farko bayan shigarsa kamfanin da sukayi da manager din banking da yake mu'amala dashi,wanda suka iso su uku da biyu cikin nasu ma'aikatan. Hankalinsu kusan yafi na fuad tashi,don sun sani ba qaramar nasara bace ace kamfani kamar wannan yana da asusu dasu,hakanan kuma....gagarumar asara da faduwa ce ace a yau ya rufe account dinsa dasu sanadiyyar wannan. "Baku da laifi sir......coz kusan sai aka shigar da komai da ake buqata da zai bawa mutum damar accessing da account din sannan kuka bada damar fitar kudin......inda kuskuren yake shine......amount din da aka fidda din ya cancanci ace anyi alerting namu kafin a bada daman fiddashin.....saboda akwai hanyoyin da mukebi wajen fidda kudade masu nauyi irin haka........kuma kun san da hakan......anyway...sakacin security team namu yafi na kowa.......sai kuma ma'ajij company da yake number one" Ya qarashe maganar yana komawa ya zauna sosai yana gyara wuyan suit nashi. Matsowa sadiq yayi dab dashi a nutse ya rada mishi "Hamma......mun gaza samun mikail har yanzu mu shaida masa zaman da za'a yi yau din". Kansa ya gyada "Kar damu dashi......idan inason ganinsa ko ina ya shiga zan sanya ne a kawomin shi.......but nafison ya kawo kansa da kansa in a legal way.....ka rabu da nemansa" "Okay" Ya fadi cikin gamsuwa. Ya yadda da hamman nasa,ya sani ba ordinary mutum bane tuntuntuni......bayajin a yanzu ko farouq zai gaya masa wayeshi saboda kaf gidan yafi kowa kasancewa dashi cikin awanni masu yawa. Fara aiki dashi ya sanya kullum kwanan duniya yake sake shiga ransa. Baisan haka hamman nasa yake da shiga rai ba sai yanzu......baisan haka kyakkyawar mu'amala take yawo a jininsa ba sai yanxu da aiki yake hadasu adadin awanni masu yawa. Hannu ya miqa ya karba file din da suka iso masa dashi na dukka bincike da nasu bibiyar da sukayi. Kusan wasu guraren abubuwan da suka bincika yazo daidai da nasa,wani gurin kuma sun kasa accessing information din jibril wanda shi a yanzu haka yana da komai. Abu daya ya kasa yarda dashi shine......jibril bashi kadai yayi wannan aikin ba.....dole akwai wani a tare dashi......wanin kuma yana qarfafa zargin muddin ba mikail bane da kanshi ya dauki duka information din ya miqa musu da zummar cin amana ba......to na jikin mikail ne wanda yake tare dashi. Hannu ya bawa manager din sukayi musabaha "Mr Joshua mamallakin bankin yana miqa jajensa......yanzu haka yana hanyar zuwa kowanne lokaci,da fatan zaa karbi baquncinsa". Wani abu me kama da murmushi kawai yayi yadan dage kafadarsa,sukayi sallama dashi ya fice. Iska me zafi ya fitar a bakinsa,ya miqe yana zare suit din jikinsa na saman ya ratayeta a muhallin da aka tanada don ratayewar. Ya duqa yana zare takalmin qafarsa hadi da magana da saddiq "Awa nawa ya rage mu shiga meeting?" "Thirty minutes hamma" "Good......yanzun security team kawai nakeson gani,kayi cancel sauran staffs......infact ma banason susan da zaman.......ina da buqatar binciken sirri a kansu don dole mu nemo me fidda mana information......ka gayawa me sunan malam immediately after meeting inason ganinsa" *D U N I Y A T A* *_H U G U M A_* PAGE 80 "Done" Ya fada kaman yadda ya saba. Daga kai farouq yayi ya kalli saddiq din "Kalleshi kaman mutumin kirki........ya addabemu cikin gida......sai yazo company sai ya zama wani me biyayya.....thank god da Allah ya hadaka da fu'ad......da nine da tuni ka kusa sakamin hawan ruwa" Ya qarashe maganar yana daukan gorar ruwan da fu'ad ya dauko musu saman table yana mamakin yadda qananun hidima na cikin office yake yi da kansa,duk da cewa yana da qarfin ikon da ko taka qasa yace bazaiyi ba akwai masu yi masa. "Bakasan mutane da yawa da suka fiya wasa ba suna da wani boyayyen talent?". "Talent a wajen wa wai?,wannan?,kawai dai Allah ya tattaro mana shi da taimakonka" Ya fadi yana bude murfin ruwan. Bai amsa ba fu'ad,yadai saki siririn murmushin da ba lallai ka iya fahimtarsa ba yayi bismillah can qasa ya soma zuqa a hankali. Kafin yakai ga dire cup din kira ya ratso wayarsa,saddiq yafi kusa da ita don haka yace "Hamma amna ce" "Kai dauki kace mata lokacin aiki ne yanzun" Kai fu'ad ya girgiza da sauri yana aje ruwan. Wayar ya miqa masa,ya sake duba kiran sannan ya daga "Good morning hamma" "Mornin lovy dovy". Qaramin murmushi ta saki "Hamma ka tashi lafiya?,yau ka fita early kuma anni tace baka tambayeni bama" Ta qarashe fada da shagwabar nan tata data zame mata jiki. Murmushi ya saki "Ban tambayeki ba amma kina raina amna.....wani muhimmin abune ya taso.....kiyimin addua,ki gayawa anni ma idan tazo sallan dhuha tayimin addu'a.....but karkice mata wani abu ne ya taso,just kice munyi waya nace tayimin addu'a during salat of dhuha". "In sha Allah hamma.....Allah ya kula ya tallafa" Ta fada cikin kulawa "Ameen autan anni" Murmushin jin dadin sunan ta saki "Hala rival dina baya kusa hamma......yaji da kunnensa sunan dai nawa ne" "Karki bari na dawo gida na iskeki....." Saddiq dake gefan fu'ad ya fadi da sauri. Kai ya daga fu'ad din ya jefa masa harara "A gaba na?" "Sorry sir" Ya fadi yana shafa kansa. Abun ya yiwa amna dadi,yana iya jiyo qaramar dariyarta har ya katse kiran. "Baka hasko komai game da mikail ba?" Farouq ya jefa masa tambayar sanda yake qoqarin duba wani saqo daya shigo system din nasa daga department na wanke dukka diamond din da aka haqo don tabbatar da kyansa da ingancinsa. Fararen idanunsa kewayayyu da hasken system din ya qara haskewa ya daga ya dubeshi na wasu sakanni sannan yace "Kai me ka hango?". "Guy din bashi d gaskiya kwata kwata.....and ina kyautata zaton yana da masaniya akan komai koda bada saninsa akayi ba". "Na fahimci haka......but akwai wani abu ko wani behind him....." "It's true.....ni tun tafiyarka South Korea na karanci abubuwa masu yawa game dashi,bamu samu zama bane yadda naso har wannan abun ya faru......amma bari mu fita a meeting dinnan" "Yayi" Ya amsa masa yana duba lokaci. Wata irin zazzafar tattaunawa ce ta wanzu tsakaninsa duk wani dake under security team. Jiki da zukata sunyi laqwas da wani irin tsoro da kuma firgici. Bacin ran da suka gani a fuskar boos din nasu ya sanyasu cikin tashin hankali,domin kuwa wani abune da basu taba ganinsa a tattare dashi ba. Dukka bayanan da suka bashi kusan yazo iri daya akan nasa da wanda baki suka bashi,saidai akwai wasu sauye sauye cikin nasu "Na baku 2days to find full details na dukka team din da sukayi wannan aikin......na tabbatar ba aikin mutum daya qwal bane......team work ne tabbas!" Ya fadi yana doka file din saman table din da yake kai. Zuciya da qwaqwalwarsa duka a zafafe ya dawo office,yayi nufin yin alwala don yayi salat dhuha kaman yadda ya saba sai yaga lokaci ma duka ya qwace,duk da haka bai fasa daura alwalar ba saboda ita kadai tana saka masa sanyi cikin zuciyarsa "I need rest please.....duk meson ganina ka gaya masa sai after one hour......kayi shutting komai saina nemeku" Yayi magana da mutanen dake tare dashi. Da daya da daya kowa ya fice har saddiq. Farouq ya miqe a hankali "Ina zaka kai kuma?" "Zan bar CEO ya huta haka nan......da gaske brain dinka yana buqatan shuru na wasu lokuta". "Ko zan huta da ganin kowa banda kai farouq" Ya amsa masa yana jingine bayansa jikin sofan da ya canza mata siffa daga kujera ta koma qaramin gadon hutawa cikin sakan talatin. Murmushi farouq ya saki,sai ya kalli agogonsa sannan yace "Na sani.....but now dai dole farouq yadan matsa kadan Shima.....zanje nayi waya da fanna......yau duka ban kira naji lafiyarta ba". Kiran sunan fanna kawai da yayi ya sanya ya daga masa hannu ba tare da yace masa komai ba,sai ya sake sakin qaramar dariya yana takawa "Anyi zancan SOYAYYA zaka birkice.....bari na qara matsawa da hanzari......hala daya cikin matan naka ne ma zasu kawo maka ziyara". Yayi zancan yana kaiwa qofa. Maganarsa ta sanya fu'ad sakin murmushin dole duk da bai shirya ba,sai ya bude idonsa a hankali yana bin bayan farouq da kallo har ya qarasa ficewa,ya maida idon ya rufe bayan ya saita security na qofan nasa da wani qaramin remote a gefansa ta yadda babu me iya damunsa,duk da ya bada warning ma reception nasa da kuma saddiq. Shi a wannan ire iren situation dinma idan har yace soyayyar zaiyi baisan ta yadda zai fuskanceta ba.....baisan ma ta inda zai kwasota ba. Yasha ji daga bakin farouq rashin bada kulawa da bada lokaci yana kawo macewar soyayya.....shi kam ya tabbatar wannan shine dalili na farko da zai saka tasa soyayyar mutuwa murus. Ya tuna 'yammata biyu da farouq ya takura ya hadasu.....abinda dukka ya rabasu dashi shine lack of caring. Sometimes ma mantawa yakeyi da babinsu,koda kuwa ta hanyar tura tex bare kira bare aje gayin tattaki zuwa gidajensu. Da kansu suka fahimta baida lokaci,suka kuma samawa kansu salama zancan ya mutu murus,shima suka shafa masa lafiya. A hankali kekenapep din ke gangarawa da ita layin gidan malam din,ya kuma tsaya daidai gidan. "Na gode......kana iya tafiya,gobe idan Allah ya kaimu zan nemeka saimu qarasa komai,ka gaida ummaah da kyau" "Zataji in sha Allah....tace zatayi tattaki da kanta don miki godiya". Murmushi kawai ta saki tana sauka daga napep din,idanunta kan muhallin da malam ke bada karatu. Ba jamaa wajen,ta kalli agogon hannunta,da sauran lokaci akan lokacin daya saba xama,sai ta taka a nutse tana wucewa cikin gidan. Kamar kullum ta taras da rumasa'u tana aikace aikacen gida,matar malam na daga rumfarta a zaune tana tsince busashen zogale. "Maraba da diyata" Ta fadi cikin fara'a da murmushi tana sauke farantin zogalen daga cinyarta gami da karkade zaninta da ya d'an baci da kadan. Har qasan zuciyarta kuma tana jin dadin dawowarta da wuri,ba kaman wancan karon ba data tafi ta jima bata waiwayosu ba. Itama tata fuskar da murmushi tare da jin dadin yadda aka samu wasu halittu da suka damu da rayuwarsu ta qarasa shiga cikin rumfar,bayan ta zame halfcover din qafarta "Aah.....ina sauran jikokin

End of Chapter 82Continue to the next chapter or choose another story below.

More Hausa novels

Browse all books →
Previous Login to Save Next