Ramadan Promo!All users that send a manual request for premium upgrade on sallah day will be granted for 1 month free.
Soyayyanovels
A Duniyata Part One Complete Hausa Novel
A Duniyata Part One Complete Hausa Novel
By Billyn Abdul
Login to keep your reading position saved.
Book Page Chapters
A Duniyata Part One Complete Hausa Novel

A Duniyata Part One Complete Hausa Novel

Author: Billyn Abdul
Chapter 63 of 84
About 8 min read
Chapter progress: 0%
Listen Mode
Listen to this chapter using your device voice.
Ready to listen from this chapter.
Free access is active. You can keep reading and download during this access window.

Book chapters

Choose a chapter and continue reading.

Start chapters
Chapter 1 1,700 words Chapter 2 1,700 words Chapter 3 1,700 words Chapter 4 1,700 words Chapter 5 1,700 words Chapter 6 1,700 words Chapter 7 1,700 words Chapter 8 1,700 words Chapter 9 1,700 words Chapter 10 809 words Chapter 11 1,700 words Chapter 12 1,700 words Chapter 13 1,700 words Chapter 14 1,700 words Chapter 15 1,700 words Chapter 16 1,700 words Chapter 17 1,700 words Chapter 18 1,700 words Chapter 19 1,700 words Chapter 20 1,700 words Chapter 21 1,700 words Chapter 22 1,700 words Chapter 23 1,700 words Chapter 24 671 words Chapter 25 1,700 words Chapter 26 1,700 words Chapter 27 1,700 words Chapter 28 1,425 words Chapter 29 1,700 words Chapter 30 1,700 words Chapter 31 1,700 words Chapter 32 400 words Chapter 33 1,700 words Chapter 34 1,700 words Chapter 35 1,700 words Chapter 36 1,148 words Chapter 37 1,700 words Chapter 38 1,700 words Chapter 39 1,700 words Chapter 40 1,700 words Chapter 41 1,700 words Chapter 42 1,700 words Chapter 43 956 words Chapter 44 1,700 words Chapter 45 1,700 words Chapter 46 1,700 words Chapter 47 1,700 words Chapter 48 1,700 words Chapter 49 1,700 words Chapter 50 1,700 words Chapter 51 30 words Chapter 52 1,700 words Chapter 53 1,700 words Chapter 54 1,484 words Chapter 55 1,700 words Chapter 56 1,700 words Chapter 57 1,700 words Chapter 58 1,700 words Chapter 59 1,700 words Chapter 60 1,700 words Chapter 61 1,373 words Chapter 62 358 words Chapter 63 Reading now Chapter 64 1,700 words Chapter 65 1,700 words Chapter 66 1,700 words Chapter 67 1,700 words Chapter 68 1,700 words Chapter 69 1,700 words Chapter 70 1,700 words Chapter 71 1,700 words Chapter 72 1,700 words Chapter 73 1,700 words Chapter 74 1,700 words Chapter 75 1,700 words Chapter 76 1,700 words Chapter 77 1,700 words Chapter 78 1,700 words Chapter 79 1,700 words Chapter 80 1,700 words Chapter 81 1,700 words Chapter 82 1,700 words Chapter 83 1,700 words Chapter 84 642 words

"Lallai na sake yarda da maganar bokan can.....lallai akwai aiki qwarai akan yaronkin nan" Hajja ta fada duk da nata yaron da matarsa data shanya a waje kowanne cikin motarshi yana jiran fitowarta. Labba maamah ta cije kadan sannan ta saki sanda take maida riga maras nauyi a jikinta "Ni kuma cewa nayi miki zan qyale wannan aikin ya cimmani?,na zuba idanu naga iya gudun ruwansa na yau kawai......amma duk abinda yakai gobe zakiji kirana......a gobe nakeso mu koma a fara aikinnan" "Ai da zafi zafi akan bugi qarfe....." Hajjan ta fadi zuciyarta na saqa mata abubuwa masu yawa. Har bakin gate din farko ta tako tana yiwa qawartata godiya da ban gajiya. A nan suka gaisa da yahaya da matarsa. Yadda ta samesu a jere kowanne da mota yana jiran dakon fitowar hajjan ba tare daya isa yabar wajen ba ba bisa umarninta ba ya sake ninka kwadayinta itama na kaiwa wannan bigiren,sai taji kamar ta jawo wadannan kwanakin da tayi imanin suna dab da zuwa......ranar ea zata nunawa aminatu da hamza cewa ruwa ba sa'an kwando bane.....hakanan koda giwa ta fadi tafi qarfin wawa. Haka siddan?,daga maqotaka?,ba sidi ba sadada a kama mata yara a musu muguwar mallaka?,bayan ko sanda ta tafinma suna da wayon da zasu iya kula da kansu?. Da wannan qananun mitocin ta isa cikin gida. Ya kusa minti ashirin yana fuskantar gate din gidan,harde da hannayensa kawai yana duban qofar kwanyarsa tana digesting maganganun da sukayi da malam saidu daga hanyar masallaci zuwa dawowarsu. Baisan a wanne matsayi zai ajjiye maamah din ba.....karo na uku da wani abu ya sanya yake tunanin ANYA ITA DINCE TA HAIFESU?,anya ita din UWACE?,akwai zuciya irin ta uwaye a qirjinta kuwa?. Me yasa kullum DUNIYA itace a gabanta sama da komai?,yayi tunanin shi da kowa ma zata canza ko kuma ta canza din.....amma sai kuma akasin tunaninsu ya biyo baya.....akasin tunanin da shi kadai gani na zuciya da lura da bin takunta sannu a hankali suke karanta masa komai a kanta....karatun da idanuwa kadai sunyi kadan su iya fahimta ko ganeshi. Hannayensa ya sauke jikinsa a mugun mace,baya jin zai iya komawa cikin gidan nan,idanma yace zai koma din abinda zai wanzu tsakaninshi da ita bame dadi bane. Ko haduwarsu na 'yan mintuna kadai ya sake wani karatun. Ya dawo lafiya?,wacce nasara ko qalubale ya riska?,duka ba damuwarta bane......damuwarta shine KUDI.....me yasa bai turo ba?. Abu guda daya da bai taba faruwa tsakaninshi da anni ko abba ba......basu taba neman anini taro ko sisi daga hannunshi ba.....a hakan take neman kudin da zata rabashi da Alhaji hamza da aminatu?,mutanen da su suka bashi RUHI na rayuwa da yake yawo a jikinsa a yanzu?. Kansa ne yaji ya sara,sai ya sake qara azamar barin qofar gidan ya juya zuwa nasu gidan. Gidan da a baya shine gidan maqota a wajensu amma a yanzun basu da gidan daya kaishi. Tun a gate ya sallami kowa,ya gaya musu da wuri zai kwanta don gobe zasu fita da wuri,duk da baida yaqinin goben a yadda zai tashi saboda wani nannauyan ciwon kai daya saukar masa yanzu yanzu. Tun bai qarasa sassansa ba ya kashe duka wayoyinsa,yabi ta qofar baya don bayason kowa yasan ya shigo din ya wuce sassansa. Bai kunna kowanne fitila na sassansa da zai bada alamar yana ciki ba,sai ya wuce a hankali kamar kazar da qwai ya fashewa a ciki zuwa study room dinsa,ya tura qofar ya shiga ya maida ya rufe. Zaune kawai yayi saman sofa idanunshi a kulle,yayi nisan nazarin da shi kansa baisan wane zare a tunanikansa zai kama ba. Abu daya ne da yafi daure masa kai da dagula masa lissafi,qoqarin da takeyi da gaske na sai ta raba tsakaninsu,indai haka ne wannan fitar tasu tana da alaqa da qudurinta.....indai haka ne kudin da take nema lallai yana da alaqa da qudurinta......indai kuma haka ne tabbas wannan BAQUWAR FUSKAR akwai tata rawar cikin mission din......duk da yasan wannan din tsohon quduri ne dake ranta.....amma dukkan alamu sun nuna ta samu MAKAMASHI. *D U N I Y A T A* *_H U G U M A_* PAGE 59 Shuru ne ya biyo baya tsakaninsu,babu wanda yace da dan uwansa komai tsakanin ita da anni din. Daga yanayin tsaiwarta da yadda take bin komai da wani irin kallo ta tabbatar ba alkhairi bane ya kawota,don haka taci gaba da abinda takeyi din ba tare data ce komai da ita ba. Baifi minti biyu ba kacal sai ga amna ta dawo "Yace gashi nan...." Ta bata amsa tana sake binta da kallo tamkar a tsorace,sannan ta qarasa ta dauki plate dinta ta koma kusa da annin ta naniqe ta zauna tana ci gaba da satar kallon maamah din. Da sallama ya shigo falon cike da kamalar nan tasa dake shimfide saman fuskarsa,sanye yake da jallabiyya ruwan qasa,kansa sanye da qaramar hula tashi ka fiya naci. Amna da anni ne suka amsa sallamar tashi,yayin da maamah ta dubeshi kadan kafin ta dauke kanta "Mariya ce?,....bismillah......zauna mana" Ya fada yana zama kujerar dake daura data anni. Kamar tace ba zata zauna ba,to amma kuma zaman yafi kamata tayin,don tanason daga qarshe ta gasa masa maganganun da indai ya haifu zai fara janye jikinsa daga dukkan wata mu'amala ta fu'ad dama rayuwarsa gaba daya,yabar mata 'ya'yanta kamar yadda kowacce uwa keda iko da nata yaran. "Muna lafiya.....ina fata kuma lafiyar ko?" Gyara zamanta tayi sosai tana dora qafarta daya kan daya,sannan ta saka idanunta sosai cikin nasa "Wajenka nazo hamza" Ta fadi kanta tsaye,abinda yaja hankalin anni kenan tadan daga kai ta dubeta,sai kuma ta saukar tana son kwashe hankalinta sam sam daga kansu. "To ai gani.....Allah yasa lafiya" Fuska ta qanqance tana dubansa idanunta a ciki. "Al'amarinku yana bani mamaki hamza yana kuma dauremin kai.........duk duniya ban taba ganin inda ake irin haka ba sai a kanku,hankaka mai da dan wani naka?......amma mu ajjiye wannan batun......tunda kun zab lallai sai na zama maqasqanciya a gabanku akan 'ya'yana?......ba laifi don komai da ka gani a rayuwa lokaci ne.....kuma iyaka gareshi......" Ta furta qasan ranta tana hangen iya adadin lokacin da ya rage musu wanda alaqar uwa da uba zata wanzu a tsakaninsu.....da tazarar lokacin da alaqar zata juye zuwa alaqar gagarumin abokin adawar da duk duniya fuad din zai wayi gari bashi da abokin adawa irinsa. Burinta shine ta bude idanu taba tsabtsar gaba da adawa mai qarfin gaske ta qullu tsakaninsu......irin adawar da zata bawa kowa mamaki ta kuma shiga sahun tarihi......tabbas saita fanshe dukkan wani baqinciki da suma cusa mata......hakanan ba zata qyale ba sai sunyi aman duk wani da sukaci daga cikin arziqin fuad......koda kuwa wannan gidan da suke ciki yana cikin jerin sahun mallakar fu'ad din. "Wai nikam hamza.......ban sani ba ko cikin duhu ne a sannan?......hadaka da kuma gamayya kukayi da ubansu fu'ad yayin samuwar cikinsu?,ma'ana tare kukamin cikinsu ko kuwa?" Ba alhaji hamza kibiya kadai ba,hatta anni dake zaune daga gefe ba tare da shiga shirginsu ba sai data cira kanta da sauri maganar tana dukanta "Subhanallahi.......innalillahi wa inna ilaihi raji'un" Alhj hamza ya fada zallan mamaki yana saukar masa,idanunsa akan fuskar amna wadda ta yunqura tana miqewa ba tare data tsaya daukan plate din abincin ba saboda yadda maganar ta girmimi kunnuwanta. "Mamaki kukayi?,to ai ba abun mamaki bane duba da yadda kuka qanqame min rayuwar 'ya'ya hamza" Ta kuma fadi cikin izza ba shakka ko d'ar a cikin idanunta. "Mariya cikin hankalinki kike kuwa?" Anni ta gaza jurewa ta fada tana kafeta da idanunta. Wurga kallonta tayi zuwa ga annin "Kinga ina iface iface ne ko yage yage da zakiyimin wannan tambayar?" "Shin mene marabar dambe da fada mariya?,ai hauka nau'i nau'i ne.....nakin ina kyautata zaton ta wannan fuskar yazo" "Kamar yadda cutarwarku tazo da sigar yaudara da damfara ba.......na rantse da Allah a yau inda fu'ad yana a faqirinsa bashi da komai da tuni kun watsashi shi da dan uwansa........." "Kaman yadda zamantowarsu halittar da zaki iya mora ta sanya kika dawo cikin rayuwarsu ba?....bayan kin watsar dasu a sannan kina zaton su din ba masu amfani bane,nauyi ne kawai a wuyanki?". Anni ta maida mata amsa ta hanyar katse numfashinta bacin rai yana fara nuna alamun tasiri cikin muryarta "Ya isa aminatu......ban yarda ki sake cewa wani abu ba" Alhaji hamza ya fada yana daga mata hannu. Ya gama karantar akwai abubuwa masu tarin yawa a bunne cikin zuciyar maamah din,biye matan da annin zatayi shi xai bata damar furzar da maganganun da idan suka qyaleta basu tanka mata ba har ta mutu saidai ta mutu dasu a cikinta. Dole ta ninke dubban maganganun da suke tsinkulinta a rai kawai don ta bawa abban girmansa,amma bawai don abinda take da shirin furtawa itama ya qare ba,ta kauda kai tana hadiye fushinta ba tare data sake jefa baki a maganarsu ba "Ka gaya masa ya bini.....domin kuwa duk duniya ba wanda akace aljannarsa tana qarqashin qafarta face ni.....komin lalacewata......ka taimaka ka sakar masa mara ya rabu dani lafiya kaman yadda na tabbatar ka rabu da naka lafiya......ka shaida masa yazo ya bani kudin dana buqata a hannunsa.......bawai alfarma nake nema ba......ka gaya masa dole ne yayimin...." Tana kaiwa nan ta miqe tsam,idanunta akan anni da tayi kaman batasan da wanzuwarta a wajen ba. Taso ace annin taci gaba da ja,don tana da tarin maganganun da takeso ta amayar mata "Wallahi duk d'an da ya hana uwarsa bacci.......shima bazai huta ba" Ta furta tana juya hankali kwance tana barin falon. Shuru ne ya biyo baya,duk kuwa da cewa ta gama ta kuma fita daga gidan ma gaba daya "Hasbunallahu wani'imal wakil" Alhaji hamza ya furta gauraye da wata ajiyar numfashi me nauyi idanunsa na kallon waje daya. Baisan wanne irin abune yake dawainiya da mariya ba......baisan kuma wanne girman laifi sukayiwa rayuwarta haka da take musu kallon wasu manya manyan abokan adawarta ba. Anni batace komai ba kaman yadda shima bai buqaci tace ba,tanata qoqarin sarrafa bacin ranta da ganin ta hadiyeshi ba tare data barshi ya mata tasiri ba "Ina muhammadu?" Alhaji hamza yayi tambayar yana duban annin "Bansan ina yayi ba.....mun rabu dashi a dazu kan zai shiga wajenta" Ta amsa masa a taqaice. Karkacewa yayi ya ciro wayarsa daga aljihun jallabiyyarsa ya soma trying number din fuad din. Sosai

End of Chapter 63Continue to the next chapter or choose another story below.

More Hausa novels

Browse all books →
Previous Login to Save Next