Ramadan Promo!All users that send a manual request for premium upgrade on sallah day will be granted for 1 month free.
Soyayyanovels
A Duniyata Part One Complete Hausa Novel
A Duniyata Part One Complete Hausa Novel
By Billyn Abdul
Login to keep your reading position saved.
Book Page Chapters
A Duniyata Part One Complete Hausa Novel

A Duniyata Part One Complete Hausa Novel

Author: Billyn Abdul
Chapter 73 of 84
About 8 min read
Chapter progress: 0%
Listen Mode
Listen to this chapter using your device voice.
Ready to listen from this chapter.
Free access is active. You can keep reading and download during this access window.

Book chapters

Choose a chapter and continue reading.

Start chapters
Chapter 1 1,700 words Chapter 2 1,700 words Chapter 3 1,700 words Chapter 4 1,700 words Chapter 5 1,700 words Chapter 6 1,700 words Chapter 7 1,700 words Chapter 8 1,700 words Chapter 9 1,700 words Chapter 10 809 words Chapter 11 1,700 words Chapter 12 1,700 words Chapter 13 1,700 words Chapter 14 1,700 words Chapter 15 1,700 words Chapter 16 1,700 words Chapter 17 1,700 words Chapter 18 1,700 words Chapter 19 1,700 words Chapter 20 1,700 words Chapter 21 1,700 words Chapter 22 1,700 words Chapter 23 1,700 words Chapter 24 671 words Chapter 25 1,700 words Chapter 26 1,700 words Chapter 27 1,700 words Chapter 28 1,425 words Chapter 29 1,700 words Chapter 30 1,700 words Chapter 31 1,700 words Chapter 32 400 words Chapter 33 1,700 words Chapter 34 1,700 words Chapter 35 1,700 words Chapter 36 1,148 words Chapter 37 1,700 words Chapter 38 1,700 words Chapter 39 1,700 words Chapter 40 1,700 words Chapter 41 1,700 words Chapter 42 1,700 words Chapter 43 956 words Chapter 44 1,700 words Chapter 45 1,700 words Chapter 46 1,700 words Chapter 47 1,700 words Chapter 48 1,700 words Chapter 49 1,700 words Chapter 50 1,700 words Chapter 51 30 words Chapter 52 1,700 words Chapter 53 1,700 words Chapter 54 1,484 words Chapter 55 1,700 words Chapter 56 1,700 words Chapter 57 1,700 words Chapter 58 1,700 words Chapter 59 1,700 words Chapter 60 1,700 words Chapter 61 1,373 words Chapter 62 358 words Chapter 63 1,700 words Chapter 64 1,700 words Chapter 65 1,700 words Chapter 66 1,700 words Chapter 67 1,700 words Chapter 68 1,700 words Chapter 69 1,700 words Chapter 70 1,700 words Chapter 71 1,700 words Chapter 72 1,700 words Chapter 73 Reading now Chapter 74 1,700 words Chapter 75 1,700 words Chapter 76 1,700 words Chapter 77 1,700 words Chapter 78 1,700 words Chapter 79 1,700 words Chapter 80 1,700 words Chapter 81 1,700 words Chapter 82 1,700 words Chapter 83 1,700 words Chapter 84 642 words

idanun yana cewa "Bismillah" Tare da maida idon nasa saman farar takardar gabansa da daya daga cikin ma'aikatan ya gabatar. Sai da yayi namijin qoqarin daidaita nutsuwarsa sannan ya fara gabatar masa da komai daki daki. Sai data buda qaramar handbag dinta ta tabbatar ta sanya komai a ciki sannan ta fiddo dubu biyu a ciki ta miqawa huda dake tsaye a gabanta "Masu kamfanin pure water zasu kawo ruwa....ki basu wannan idan sun kawo.....naso saikun wuce islamiyya kafin na fita.....amma it's urgent.....kiyi qoqari ku fita da wuri kada kuyi latti" "A dawo lafiya" Ta fadi bayan ta karbi kudin. Qasan ranta fal farinciki,a yau din zatayi hira da hameed yadda ranta keso,don zata saitawa su nadra hanya zuwa islamiyya ne ita kuma ta baje kolin soyayyarta yadda ranta yakeso. Gaban haneefa ta qarasa tana sakin murmushi,itama haneefa din murmushi ta saki,hannunta ta dora saman sumarta data cirewa dankwali. A kullum fuskar haneefa ba wanda take tuna mata dashi sai umminsu. Akwai shaquwa da sabo me tsanani tsakaninsu.......amma duk da haka saida mutuwa tayi aikinta ta raba tsakaninsu. "Ayimin addua auta....zan kawo miki abun dadi" "A dawo lafiya yaa sabreen........amma yau kam sabuwan teddy nakeso ki sayamin" "Ke kuwa ki rasa abinda zaki zaba sai Teddy?" Nadra ta fada tana qyalqyala dariya "To madam tsokana.....ba ruwanki" Sabreen tayi hanzarin katse nadra data wuce daki tana ci gaba da dariyar tsokana din hadi da yiwa sabreen a dawo lafiya. Tana takawa don fita daga layinsu ta isa bakin titi amma tunanin qannen nata ne a ranta. Batason ko kadan yadda kullum sai ta fita ta barsu,wani lokaci su fita tare saidai su rufe dakin,harma wasu lokutan su rigata dawowa. A yanzun huda tafi tsaye mata a rai,tunda har ta cika shekara sha biyar ta shiga ta sha shida tana da buqatar sanya idanunta a kanta,don mataki ne da komai daga nan yake farawa daga rayuwar yarinya. Duk da inda ace ita din me gata ce,ita dinma tana buqatar kulawa ne tare da qarasa rainon tarbiyyarta. Ko kusa ko alama bata lura dashi ba,don tayi nisa a tunaninta,sai muryarsa taji daga gefanta. "Um uhmmm......sai ina kuma haka?" A nutse ta waiwaya tare da sake rage yanayin tafiyar tata tana kallonshi. Tsaf yake kallonta,ya turo hula gaban goshinsa yana mata wani irin kallo. Idanunta ta dauke don bata buqatar yanayin kallon da yake binta dashi. Ta sani haushinta yakeji qwarai,tun waccar ranar data hanashi kudi. Wannan duka ba damuwarta bane,don idan da sabo ta saba,sai ta watsar da wannan batun kamar kullum tace dashi "Barka da warhaka kawu.....an yini lafiya?" "Ras na wuni.....ko kin dauka zan mutu ne saboda kin hanani kudinki?,to kisha kuruminki 'yar nan......cikin satinnan da yardar me duka arziqi zai fashemin......sunana zai fantsama a duniyar masu arziqi......daga sama'ila zan koma alhaji ismai'il sha maka Allahu". A mamakance take kallonsa,tadai sani bashi da wata sana'a data wuce caca,kuma muddin ka jishi yana lissafin maquden kudade irin wannan to wata caca za'a buga kuma yake sanya ran zai cinye. "Allah ya bada sa'a.....amma dai kawu.....caca" "Akul naji bakinki.....dani dake ai dan juma ne da dan jummai... Ke har gwara ni duk tsiya". Kanta ta dauke tana hadiye wani abu daya tsaya mata a wuya,bata sake tanka masa ba sai ta fara takawa tana barin wajen. Har tayi taku hudu qwarara ya qwala mata kira da ainihin sunanta "Aminatu" Dakatawa tayi don ba zata iya ci gaba da tafiya ba,ba'a canzawa tuwo suna,duk duniya kawu sama'ila ubanta ne. "Ke wato baki jin ko dar idan an miki gugar zana ko?,to miqomin wani abu nan,ki rubuta shi a lissafi duka cikin satin nan zan biyaki" Ya fada yana miqa mata hannu tamkar ya bata ajiya. Idanu ta xuba masa,sai kuma ta sanya hannu tana sauke jakarta daga kafada,ta zuge ta fidda dubu dubu guda hudu ta miqa masa. Karba yayi yana juyasu alamun a raine suke a wajensa,sai ya yatsina fuska "Ki rasa abinda zaki ban sai wannan?,kai Allah ka dawo mana da arziqinmu za'a sha kallo wallahi......" Daga haka ya juya yana cusasu a aljihu tare da barin gurin bai kuma sake bi takan inda zataje din ba. Kasa ci gaba da tafiya tayi har sai daya bacewa ganinta,ta kada kai ta na yin gaba kamar kullum zuciyar nan cike da nazarin rayuwa . Tun daga rasuwar mahaifinsu har ta mahaifiyarsu bai taba miqo komai yace musu gashi ba wai don su rayu.....amma ita ba zata iya qirga ko lissafa adadin sau nawa ya karba daga hannunta ba,kuma a raine,ba godi bare na gode. Ya riga ya bata shaidan da zata nuna na cewa shi take nema,wannan ya sanya bata samu matsalar shiga kamfanin ba tun daga gate din farko gate na biyu,ta zarce zuwa main entrance,ta ratsa reception da sauran guraben da kamfanin yake dashi kai tsaye kuma ta isa ga office din. Tayi amfani da code din ya kuma bude mata successful. Ta tura qofan a hankali kamar me tsoron shiga qaramin murmushi na sauka saman fuskarta "Quda a wajen kwadayi akan mutu" Ta furta qasa qasa tana sanya qafafunta cikin office din. Har ta fara takawa sai kuma ta tsaya cak tana wurga idanunta sassa sassa na qawataccen office din da aka narka kudi akayi masa wani irin lafiyayyen tsari me daukan hankali. Tabbas tasan babu yadda za'ayi guri irin wannan ya rasa CCTV camera,indai kuma hakanne ta yaya zata iya gudanar da komai ba tare data samu wata matsala ba?. Dan wani abu cikin kunnenta ta matsa,muryar JIB ta bayyana,sai ta danja da baya kadan ta raba qafa tsakanin office din da veranda din da jerin gwanon office din yake don bataso ta fito gaba daya ko ta shiga gaba daya don kada camera din ya samu damar nunata "Ni dakai duka bamuyi tunanin CCTV ba jib?". "Ya salam" Ya fadi yana aje wani numfashi "Haka ne......wasu lokuta dama kece ke mana hasshen irin wadannan abubuwan......ba matsala bane,manyan kamfanoni irin wadannan akwai irin cameras din da suke amfani dasu,katseshi ba zaiyi wahala ba nasan takan irinsu sosai......yanzu ki tsaya daga nan inda kike...kafin ki shiga ki gano mana daga wanne saiti camera din yake shikenan kawai" "Okay....." "....karki datse connection daga nan har mu gama aikin" "So kaji komai tsakaninmu kenan bayan sirri ne?" Ta fada cikin dan salon zolaya da wani lokaci takeyi masa. Dariya ya qyalqyale da ita kadan yana fadin "Tuba nake....Allah yabar soyayya". Sai kawai ta saki murmushi kadan tana tura qofar hadi da sake qarewa office din kallon tsaf. Cikin qasa da minti goma ta gano komai suka kuma katse sadarwa da tsaida aikin camera din. Da dan hanzari ta ajjiye hand bag dinta. Tanaso tayi komai ne ta gama kada damar ta subuce mata yazo ya shigo. Sai data tattara dukka hankalinta da nutsuwarta ta karanci inda komai yake ajiye a office din,gudun kada ta taba wani abu ta kasa maidashi daidai inda yake hakan ya nuna masa alamar tayi masa bincike. Hatta da biro dake ajiye qwaya daya tal saman teburin sai data karanci a yadda yake ajiye din,ta dauka ta kuma gwada maidawa ta tabbatar ya zauna kaman yadda aka ajiyeshi. Wayarta ta fidda,ta sake yiwa office din qaramin video komai da komai sannan ta maida wayar jakar,ta kuma shiga aikin bincika komai daki daki. Baya ga abinda suke nema taga abubuwa da yawa cikin office din,irinsu condom dake nuna mata lallai riqqaqqen dan bin mata ne,taaba irin masu tsadar nan da sauran abubuwan maye. Abinda ya sake darsa mata mugun tsanarsa kenan,wutar kuma ta tabashin ta hanyar kwakwashe masa komai tana sake ruruwa cikin ranta. Ya zama dole ta durqusar dashi,durqusarwar da bazai sake tashi ba. Maida komai tayi kaman ba wani abu daya faru a office din,ta tattare duk abubuwan da take nema din tayi musu ajiya ta musamman cikin jakarta. Hatta da wani qaramin ledar cake da akaci aka barshi sai data tabbatar ta maidashi yadda yake,ta gyara rolling dinta da kyau tana sauke numfashin samun nasarar kammala komai ba tare daya dawo ba. Maqoshinta taji ya bushe tana da buqatar ruwa,sai ta taka tana nufar kyakkyawan fridge din dake girke waje daya. *D U N I Y A T A* *_H U G U M A_* PAGE 70 Turus tayi tana kallon yadda aka maqare gidan farko na fridge din da wasu kalan kwalabe da bata saba ganin irinsu ba. A hankali take dubasu har ta fahimci kwalaben na meye?. Kwalaben giya ne tabbas,ta maida idanunta ta lumshe tana furta "Innalillahi" Can qasan harshenta. Sai kuma taja jikinta baya a hankali tana matsawa daga jikin fridge din don batajin zata iya shan wani abun sha daya fito daga fridge din komai halascinsa. Zuciyarta ke qara bugawa da tsanarsa haushi da kuma takaici. Shikam mikail dame zaiji?,abubuwan ai sunyi masa yawa,sun masa yawan da batasan wanne a ciki zai iya dauka ba. Kaman ana son bata amsar tambayarta sai qofar tayi qaramar qara alamun ana budeta ne,ba jimawa ya bayyana cikin office din yana dubanta da murmushi "Am so sorry dear......ina fata banyi keeping naki da yawa ba......boss ne idan ya tashi aikinsa tamkar engine.......baya gajiya,na samu na kubota da qyar". Idanunta ta dauke daga kan files din da yake rungume dasu,wanda ta tabbatar a cikinsa sauran bayanan da take nema suke. Ta kalato dukkan dauriyarta ta jefeshi da qaramin murmushi "You deserve it ai....." "Wow......serious?" Ya fada da wani irin zumudi da zakwadi yana qarasowa gabanta dab da ita ya zauna har yana neman hade gwiwoyinsu guri guda. A dabarance ta miqe da sauri,sai ya bita da kallo. Taji a jikinta yana kallonta ne don haka ba tare data juyo ba tace "Bari nayi fitsari kadan" "Oh....okay to dear" Ya fada yana dora files din saman table din cikin ransa yana qissima yadda a yau din zai gwangwaje,a yau din zai kashe duk wata qishirwa tasa dake damunshi a rai.....a yau zaiyi morewar da bayajin ko daren amarcinsa zaiyi wannan. Gaban madubij toilet din ta tsaya tana sauke numfashi idanunta akan fuskartata. Muryarta can qasa tace "Please jib.....muyi komai mu gama da sauri......banason ganin fuskarshi kwata kwata" "I know.....zanyi iya qoqarina......amma please kada kice zakiyi halin hawainiyar nan taki" Dan murmushi ta saki,yasan halinta sarai,koda nawa aikin zai basu idan ta motsa mata tana iya cancel dinsa

End of Chapter 73Continue to the next chapter or choose another story below.

More Hausa novels

Browse all books →
Previous Login to Save Next