Soyayyanovels
Rayuwarmu Book One Complete Hausa Novel
Rayuwarmu Book One Complete Hausa Novel
By Saadatu
Login to keep your reading position saved.
Book Page Chapters
Rayuwarmu Book One Complete Hausa Novel

Rayuwarmu Book One Complete Hausa Novel

Author: Saadatu
Chapter 7 of 40
About 8 min read
Chapter progress: 0%
Listen Mode
Listen to this chapter using your device voice.
Ready to listen from this chapter.

Book chapters

Choose a chapter and continue reading.

Start chapters

"Daman ke nake jira mu wuce"

" Aunty na ni ka ɗai barka da dare"

Amina ta yi dariya ta kalli Umar ta ce.

"Allah ya shirya mana kai"

Umar ya yi dariya.

Aliyu ya ce.

"Karki biye ma wannan sarkin surutun kinga dare ya yi ga Shukrah ma tayi barci zo mu wuce gida"

Mama ta fito daga bedroom hannunta riƙe da leda taba Amina.

Amina ta duƙa har ƙasa ta karɓa  ta na godiya Aliyu ya karɓi Shukrah Umar ya ɗau Darraini dake barci suka fita.

Sun fita suka ga Inna a bakin window ta na tsaye.

Dukan su sun ganta amman suka nu na kamar basu ganta ba domin idan da sabo sun saba da halinta

hatta Amina ta san halin Inna.

Bayan sun fita Aliyu ya kalli Umar ya ce.

"Ka gayawa Isma'eel ya same ni a gida gobe idan Allah ya kaimu"

Aliyu ya karɓi Shukrah Amina ta karɓi Darraini a hannun Umar suka tafi.

Sun isa gida Amina ta kwantar da Shukrah a ɗaya bedroom ɗin da suke kwana ita da ƙanwarta ta yi wanka tasa kayan bacci  ta tsaya tana ma Shukrah addu'a.

Aliyu kuma ya wuce da Darraini bedroom ɗin su ya kwantar da ita ya shiga toilet ya yi wanka yasa kayan bacci ya yi addu'a ya kwanta.

Amina ta shiga ɗakin bayan tayi sallama Aliyu har ya yi bacci Amina ta zuba mishi ido tana kallon shi.

Ta na nazarin maganar Baffa tabbas akwai abinda yake shirin faruwa da rayuwar su.

Ita da kanta ta san Aliyu yana da yawan ɗaukar maganar mutane koda kuwa ba gaskiya suka fada mishi ba sannan akwai shi da yarda da abinda yaran shi suka faɗa mishi koda ƙarya ne sai ya hau kai ya zauna ya yi ta faɗa kamar zai ari baki.

Amina ta daɗe a zaune tana tunanin maganar Baffa tabbas ta san akwai dalilin da yasa Baffa ya faɗa mata wannan maganar.

A ƙarshe dai ta yanke shawaran zata tsananta  addu'a koma mainene yazo musu da sauƙi.

Darraini ta farka daga bacci ta na kuka Amina ta ɗauke ta shiga da ita toilet ta yi fitsari tasa mata pampas ta haɗa mata tea ta bata bayan ta gama sha ta kai ta bedroom ɗin su ta sama ta kaya ma rasu nauyi ta kwantar da ita kusa da Shukrah.

Har ta fita ta dawo ta ɗau Shukrah ta shiga da ita toilet tayi fitsari ta sanja mata kaya ta kwantar da ita ta ƙara musu addu'o'i ta jamu su kofar ta fita.

Kitchen ta shiga ta haɗo lipton ta zauna a parlour tana sha ta na tunani parlourn ya na ɗauke da saitin kujeru pink da fari ga ƙaton carpet a tsakiya shima pink da fari.

Lokacin da zasu tare Aliyu ya sanja mata kayan ɗaki komai na parlourn pink da fari ne kayan kallo fridge ɗin su babba show glass masha allah komai ya ji a parlourn.

Gaba ɗaya jikin Amina  ya yi sanyi gashi Baffa ya ce ta ƙara riƙe sirrinta.

Babu wanda zata iya shawara dashi bata da ƙanwa ko ɗaya mahaifiyarta ta  rasu bayan haihuwar Shukrah bada jimawa ba.

Sunan Darraini sunan mahaifiyar ta ne suke kiranta da suna Darraini Saadatul Darraini.

Amina ta kai wajen ɗaya da wani abu a zaune, kafin ta shiga bedroom ta yi alwala ta shimfiɗa darduma ta fara sallah.

Bayan ta idar ta ɗauki Qur'ani ba ta tashi a gurin ba sai da aka kira assalatu.

Amina ta shiga kitchen ta na shiga suka kawo nepa ta jona kettle ta ɗau plas ɗin ruwan zafi ta fita.

Bedroom ɗin su ta shiga ta aje plas ɗin ta shiga toilet ta ɗauko bucket ta juye ruwan plas ɗin ta shiga wanka bata jima sosai ba ta fito ta zauna a gaban mirror ta na shafa lotion.

Simple make-up ta yi ta sa doguwar riga ta fesa turare tayi ɗaurin ɗankwali ta yi kyau sosai.

Ta je gaban gado ta na cewa.

"Abban Shukrah lokacin sallah ya yi"

Aliyu da ya jima da farkawa tun kafin ta shiga wanka ya ƙura mata ido ya kasa cewa komai Amina ta tashi zata fita.

Aliyu ya ce.

"Zo kiji wata magana"

Amina ta yi hanyar barin ɗakin tana cewa

"Zaka rasa jam'i"

Ta fita ɗakin ta leƙa bedroom ɗin su Shukrah suna ta barci ta ja musu ƙofar ta fita kitchen ta koma ta samu ruwan da ta jona ya na tausa.

Ta koma ɗaki  ta samu Aliyu har ya yi alwala zai fita massalaci ta ce.

"A dawo lafiya"

Ta ɗau flas ɗin ta koma kitchen ta  juye ruwan ta ƙara jona wani ruwan ta fita ta koma bedroom daman bata ɗauke darduman da ta yi sallah a kai ba tana shiga a ka tayar da sallah.

Daga masallacin zuwa gidan su babu nisa gida uku ya raba.

Amina ta idar da sallah ta yi addu'o'i ta yi azkar bayan ta idar ta fita ta koma kitchen ta na zuwa ta samu ruwan ya tausa.

Ta kashe jikin socket ɗin ta fita ta koma ɗaki ta shiga toilet ta ɗauko bucket ta shiga kitchen ta juye duka ruwan zafin a ciki ta ƙara jona wani ruwan ta ɗau bucket ɗin ta fita.

Bedroom ɗin yaran ta shiga ta tayar da Shukrah ta shiga da ita toilet ta wanke mata baki ta yi mata wanka tasa ta ta yi alwala bayan ta yi ta ɗaura mata ɗaya daga cikin towel ɗin dake ra taye a toilet.

Amina ta fito Shukrah na biye da ita a baya Shukrah ta zauna saman ƙaramin kujeran dake gaban mirror Amina ta buɗe man shafawa ta miƙa wa shukrah.

Ta ɗauki Darraini ta shiga da ita toilet ta cire mata pampas ta yi mata wanka ta wanke mata baki ta ɗauko ta suka fito.

Amina ta na fitowa ta samu Shukrah tasa uniform ɗin school ta na sallah da  hijjab ɗinta har ƙasa.

Ta aje Darraini ta fita ta koma kitchen ta samu ruwan ya tausa ya kashe kanshi ta koma toilet ta ɗauko bucket ta juye ruwan zafin ta fita dashi.

Bedroom ɗin yaran ta leƙa ta samu Shukrah na shafama Darraini cream daman ta saba shirya ƙanwar na ta ganin Shukrah ta rage mata aiki

Amina ta yi hanyar bedroom ɗin su hannuta ɗauke da ruwan zafi.

Ta samu Aliyu zaune a saman darduma yana karatu.

Amina ta shiga bayan ta yi sallama toilet ta shiga ta ƙara wankewa saboda lokacin da za ta yi wanka ta wanke shi ta ɗauko bucket ɗin da ruwan zafin yake ciki ta shiga dashi toilet ta aje ta janyo ƙofar ta fito.

Ta samu Aliyu zaune ya na kallon ƙofar toilet.

Amina ta je kusa dashi ta duƙa ta gaishe shi Aliyu yasa hannu ya jawota jikin shi ya ce.

"Sannu da ƙoƙari matar aljanna"

Amina ta ɓata fuska ta ce.

" Baka amsa gaisuwata ba"

"Na yi kewarki da yawa" cewar Aliyu.

Amina za ta yi magana ta ji sallamar Shukrah a bakin ƙofa Aliyu ya amsa sallamar.

Ta Batulu ce ✍️

Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/LSKW0PJdQ6Z2S2wltDG6oT💖💖 RAYUWAR MU 💖 💖

*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v

💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️

*(J.W.A)*

_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️

Written by ✍️

Jagaban Jajirtattu 🥰

   (Ta Batulu )

*Page 15-16

Amina ta tashi a jikin Aliyu sannan ya basu izinin shigowa.

Shukrah ta shigo Darraini na binta a baya da uniform ɗin school Aliyu ya kalli Amina ya ce.

"Madam kin manta yau monday baki bamu breakfast ba"

Amina ta ce.

" Ruwan wankan ya na jiranka a toilet"

Shukrah ta duƙa har ƙasa ta gaishe da Aliyu sannan ta gaida Amina

Darraini itama tayi kamar yanda ta ga Shukrah ta yi.

Amina ta ce.

" Shukrah zo muje kitchen"

Darraini ta zauna ta jira mu

Aliyu ya ce.

"A'a karki

ƙona mun yarinya"

Amina ta yi dariya ta riƙo Shukrah suka fita

Aliyu ya aje Darraini a saman gado ya shiga toilet.

Amina taba Shukrah kayan miya ta gyara mata.

Ita kuma ta haɗa tea a ƙaramin cup ta fita bedroom ta shiga ta ɗauki Darraini da ta fara bacci ta fara bata tea saboda ita bata da juriyan yunwa.

Bayan ta gama bata tea ta kwantar da ita ta fita ta koma kitchen ta samu Shukrah har ta niƙa mata kayan miyan a greater.

Amina ta kunna gas saboda sun kashe wuta ta kwaso kayan ƙamshi ta zuba a tukunya tasa sugar tasa ruwa ta ɗaura a wuta.

Shukrah ta fita daga kitchen ta yi sallama ta shiga ɗakin Amina.

Amina ta cigaba da aikin ta bayan  ta sauke ruwan shayin ta  ɗauko wani flas ɗin ta juye wannan ruwan zafin a ciki.

Ta ɗaura tukunya a wuta ta zuba mai ta soya kayan miya ta yi sanwa tasa spices ta rufe tukunyar.

Sannan ta koma parlour ta fara gyarawa ka san cewar babu datti sosai yasa ba a ɗau dogon lokaci ba ta gama gyarawa ta sa turare ta koma kitchen ta samu ruwan ya tausa.

Ta kwaso indomie ta zuba ta rufe tukunyar ta kwaso albasa tana yanka bayan ta gama yan kawa ta zuba a ciki ta rufe ta yi ƙasa da wutan ta fita.

Bedroom ɗin yaran ta shiga ta gyara tasa turare ta kwaso musu jakan makaranta ta ɗauko darduman da suke shimfiɗawa idan zasu ci abinci ta rufe ɗakin ta fito.

Parlour tazo ta aje kayan hannunta ta kira Shukrah tazo ta fara kwaso cups a kitchen.

Ita kuma ta shimfiɗa darduman ta shiga ɗaki ta samu Aliyu zaune Darraini tacna jikin shi yana mata wasa Amina ta ce.

"Abban Shukrah komai ya yi ready"

Aliyu ya ɗauko  Darraini ya fito Amina kuma ta ɗau flas ɗin data aje ta fita.

Amina kitchen ta shiga ta aje flas ɗin ta sauke girkin ta ɗauko plas ɗin Darraini na school ta zuba mata indomie sauran ta juye a plate guda biyu.

Shukrah ta shigo kitchen Amina ta bata kayan tea ta je ta aje a saman darduma.

  Amina ta fita da plates ɗin data zuba indomie.

End of Chapter 7Continue to the next chapter or choose another story below.

More Hausa novels

Browse all books →
Previous Login to Save Next