Ramadan Promo!All users that send a manual request for premium upgrade on sallah day will be granted for 1 month free.
Soyayyanovels
Zaytoonah Part One Complete Hausa Novel
Zaytoonah Part One Complete Hausa Novel
By Azizat
Login to keep your reading position saved.
Book Page Chapters
Zaytoonah Part One Complete Hausa Novel

Zaytoonah Part One Complete Hausa Novel

Author: Azizat
Chapter 121 of 161
About 8 min read
Chapter progress: 0%
Listen Mode
Listen to this chapter using your device voice.
Ready to listen from this chapter.
Free access is active. You can keep reading and download during this access window.

Book chapters

Choose a chapter and continue reading.

Start chapters
Chapter 1 1,689 words Chapter 2 1,523 words Chapter 3 1,583 words Chapter 4 1,696 words Chapter 5 1,682 words Chapter 6 1,693 words Chapter 7 1,594 words Chapter 8 1,673 words Chapter 9 1,663 words Chapter 10 1,668 words Chapter 11 1,678 words Chapter 12 1,698 words Chapter 13 1,687 words Chapter 14 1,699 words Chapter 15 1,656 words Chapter 16 1,634 words Chapter 17 1,681 words Chapter 18 1,675 words Chapter 19 1,655 words Chapter 20 1,613 words Chapter 21 1,669 words Chapter 22 1,655 words Chapter 23 1,671 words Chapter 24 1,650 words Chapter 25 1,677 words Chapter 26 1,696 words Chapter 27 1,598 words Chapter 28 1,699 words Chapter 29 1,694 words Chapter 30 1,659 words Chapter 31 1,683 words Chapter 32 1,309 words Chapter 33 1,691 words Chapter 34 1,697 words Chapter 35 1,553 words Chapter 36 1,588 words Chapter 37 1,682 words Chapter 38 1,680 words Chapter 39 1,677 words Chapter 40 1,649 words Chapter 41 1,700 words Chapter 42 1,698 words Chapter 43 1,676 words Chapter 44 1,625 words Chapter 45 1,633 words Chapter 46 1,675 words Chapter 47 1,693 words Chapter 48 1,668 words Chapter 49 1,688 words Chapter 50 1,647 words Chapter 51 1,653 words Chapter 52 1,568 words Chapter 53 1,689 words Chapter 54 1,699 words Chapter 55 1,669 words Chapter 56 1,578 words Chapter 57 1,564 words Chapter 58 1,660 words Chapter 59 1,694 words Chapter 60 1,415 words Chapter 61 1,653 words Chapter 62 1,690 words Chapter 63 1,685 words Chapter 64 1,618 words Chapter 65 1,652 words Chapter 66 1,674 words Chapter 67 1,687 words Chapter 68 1,699 words Chapter 69 1,644 words Chapter 70 1,698 words Chapter 71 1,691 words Chapter 72 1,671 words Chapter 73 1,689 words Chapter 74 1,679 words Chapter 75 1,677 words Chapter 76 1,678 words Chapter 77 1,655 words Chapter 78 1,683 words Chapter 79 1,696 words Chapter 80 1,700 words Chapter 81 1,694 words Chapter 82 1,697 words Chapter 83 1,692 words Chapter 84 1,668 words Chapter 85 1,554 words Chapter 86 1,666 words Chapter 87 1,677 words Chapter 88 1,694 words Chapter 89 1,667 words Chapter 90 1,700 words Chapter 91 1,670 words Chapter 92 1,670 words Chapter 93 1,655 words Chapter 94 1,640 words Chapter 95 1,607 words Chapter 96 1,668 words Chapter 97 1,659 words Chapter 98 1,689 words Chapter 99 1,675 words Chapter 100 1,614 words Chapter 101 1,610 words Chapter 102 1,700 words Chapter 103 1,683 words Chapter 104 1,657 words Chapter 105 1,698 words Chapter 106 1,700 words Chapter 107 1,695 words Chapter 108 1,656 words Chapter 109 1,683 words Chapter 110 1,699 words Chapter 111 1,699 words Chapter 112 1,641 words Chapter 113 1,696 words Chapter 114 1,626 words Chapter 115 1,695 words Chapter 116 1,691 words Chapter 117 1,698 words Chapter 118 1,645 words Chapter 119 1,673 words Chapter 120 1,691 words Chapter 121 Reading now Chapter 122 1,694 words Chapter 123 1,689 words Chapter 124 1,688 words Chapter 125 1,673 words Chapter 126 1,692 words Chapter 127 1,686 words Chapter 128 1,697 words Chapter 129 1,660 words Chapter 130 1,691 words Chapter 131 1,674 words Chapter 132 1,670 words Chapter 133 1,693 words Chapter 134 1,691 words Chapter 135 1,687 words Chapter 136 1,672 words Chapter 137 1,691 words Chapter 138 1,657 words Chapter 139 1,687 words Chapter 140 1,650 words Chapter 141 1,695 words Chapter 142 1,607 words Chapter 143 1,699 words Chapter 144 1,676 words Chapter 145 1,698 words Chapter 146 1,684 words Chapter 147 1,664 words Chapter 148 1,696 words Chapter 149 1,674 words Chapter 150 1,680 words Chapter 151 1,697 words Chapter 152 1,628 words Chapter 153 1,618 words Chapter 154 1,688 words Chapter 155 1,664 words Chapter 156 1,692 words Chapter 157 1,584 words Chapter 158 1,644 words Chapter 159 1,646 words Chapter 160 1,618 words Chapter 161 1,797 words

"Raziya wannan hutun zan coaching É—in ki akan basic Mathematics. With that ba za ki samu matsala ba Insha Allah. Kwana huÉ—u a sati ya mi ki?"

Raziya ta watsawa Zaytoonah harara ganin hankalin Justice yana kan waya.

"Kwana É—aya ya isa" ta faÉ—a fiskarta a haÉ—e

"5 days Raziya, and ban da rashin kunya"

"Daddy"

"Je ki adana result É—in a file É—in ki"

"Yes Dad" ta faɗa tareda karɓan result ɗin a hannun Zaytoonah.

Sai da ta fita Justice ya kamo hannun Zaytoonah ya ma ta kiss ya ce "Na gode" Zaytoonah ta yi murmushi ta ce "My prince kar ka damu Insha Allah zan yi ƙoƙarina a kan ta"...

***

"Hello" ta faɗa lokacin da ta amsa kiran baƙuwar number mai code ɗin ƙasar America

"Zaytoonah"

"Ya Allah! Muhsinah ya ki ke. Ya su Daddy"

"Mu na nan lafiya. Ina 'ya'ya na?"

"Sun tafi Islamiyya"

"Kwana biyu 'yar uwa, ya ki ke? hope kuna zune lafiya da kishiyar ki"

"To gamu nan dai, kin san mi ta yi kwanan nan. Wani sharri ta zo da shi wai tanada infection kuma daga wajena aka samu"

"Haba!"

"Wallahi. That crazy woman actually thinks i'm stupid fa"

"To ai ke ki ka ba ta dama"

"A da kenan yanzu na yi hankali"

Muhsinah ta kwashe da dariya. Sai da ta gama ba ta labarin yadda su ka wanye da Ghazala kafin ta sako ma ta tambayar da ta sa Muhsinar É—auke wuta.

"Maman Habib ki koma dan Allah. I know its not easy but forgive him please"

Sai da ta yi kusan 30 seconds kafin ta sauke numfashi ta ce "i cant Zaytoonah. Ba zan iya ba, its over"

"Kin zaɓi ki rabu da shi har abada kenan. What about your kids?"

"Ba zan iya ba" ta furta tareda kashe wayar.

Sosai Zaytoonah ta ke tausayawa Muhsinah. Rabuwa da Miji ba abu ne mai sauƙi ba especially idan kana son shi. Despite the fact AbdulHameed ya ƙi ya saketa, Muhsinah ta rantse ba za ta koma ba, bayan ta warke tattarewa ta yi ta koma America wajen Baban ta. Yaran kuma na nan wajen Kakannin su.

Shigowar Justice É—akin ne ya katse ma ta tunani.

"Ba dai fita za ka yi ba?"

"Za ki yi missing É—ina ko"

"Na ga ba ka jima da dawowa ba ne"

"Jiya ya kamata na je na yi yankan farce amma na manta, yau ma sai da na shigo na tuna"
Ta sa hannu a kafaÉ—un sa tana faÉ—in "wannan Tsoho ba dai mantuwa ba, anya idan ka fi haka ba da sanda za mu haÉ—a ka ba"

Ya ɗaura hannun sa a ƙugunta ya jawota jikinsa ya ce "idan ke ce 'yar jagorar i dont mind"

Dariya ta yi tana faÉ—in ba zai ma kai haka ba.

"Na iya yankan farce fa. If you dont mind i could do it for you"

"Ofcourse Sweetheart"

Ta kamo hannun sa ta zaunar da shi kan kujera sannan ta ɗauko kayan aiki tareda ƙaramar towel. Ta zauna ƙasa ta ɗaura ƙafarsa akan ƙafarta ta fara yanke ma sa farcen.

"Ka san a ina na koyi aikin nan?"
Ta tambaya lokacin da ta gama ƙafa ɗaya ta fara ɗaya ƙafar.

A zaton sa sunan mijin ta za ta kira sai ya ji ta ce
"A ƙafar Daddy na" ta yi murmushi ta ce "Mommy ce ke ma sa, sai ranan su ka yi faɗa, dan ya ƙula ta sai ya kirani ya ce na ma sa. The truth is ya sha yanka a wajena ranan. But still bai haƙura ba, ya ce dole sai ni zan ƙarisa ma sa.

"Daga nan kuma ya maida shi permanent ni ke ma sa yankan farce, tun ban iya ba har na ƙware"

Hawaye ne ya fara zubo ma ta ta yi saurin gogewa amma ina tana gogewa wani na bin wani.

"I miss him" ta faÉ—a lokacin da ya jawota jikin sa.

Sun jima a haka kafin ta janye jikin ta ta ce bari ta ƙarisa ma sa yankan.

***

Wannan karan dukkan su suka je weekend Zaria. Tun ranan Alhamis su ka tafi, ranan Jummu'a akwai Public holiday da aka bayar na Maulidi shiyasa dukkan su su ka taho tunda ba aiki sai ran Talata.

Ranan Jummu'ah ya kama ranan kwanan Ghazala, da ke Galadima ya ba da umurnin ayi abincin sadaka gaba ɗaya aka haɗa hannu ake yi. Suna cikin aiki, sauran ma su aiki aka fara taɗi ana habaici ƙasa-ƙasa. Da farko Zaytoonah ba ta gane da ita ake ba sai da ta ji Baaba Nafy ta ce "ku ji tsoron Allah. A wajen mu matsayi ɗaya su ke da shi tunda dukkan su ƙarƙashin inuwar Yallaɓai su ke"

Baaba Nafy ba sa'ar su ba ce dan ko Ghazalar za ta ba ta kusan shekaru shatakwas zuwa ishirin.

Zaytoonah ta É—ago ido ta kalli Ghazala da ke yanka cabbage sai wani murmushi ta ke yi.

Kamar za ta yi magana sai kuma ta yi shiru dan biye mu su ma ɓata lokaci ne, dan ba girmanta ba ne.

"Ai ba mu san Yallaɓai ya yi aure ba sai da haske ta shigo gidan nan, tauraruwar Galadima Allah ya ja zamanin ki"

Wata mata ta faÉ—a wanda ko sunan ta Zaytoonah ba ta sani ba.

"Allah ya kawo Magajin gida nan da wata tara Amin"

Murmushin fiskar Ghazala ya É—auke É—if kamar É—aukewar wutan NEPA.

Zaytoonah ta kauda kan ta kamar ba ta ji abinda aka faÉ—a ba.

Abubuwa da dama su ka dinga yawo a kwanyar Ghazala. Maganar Magaji ya taɓa ta sosai, ba wai ta wuce shekarun haihuwa ba ne amma kuma propability ɗin samun ciki is very low compared to Zaytoonah wacce yanzu ne ma ta cika shekara ashirin da huɗu a duniya. Idan ba ta manta ba haihuwar ta na biyu ta yi allurar tazarar haihuwa saboda lokacin ba ta son cigaba da haihuwa da Alhaji Bashir. Shekara ɗaya da yin hakan ma ta rabu da shi.

Suma ma su yiwa Ghazala kirarin da su ka ga ta haÉ—e rai sai su ka yi shiru...

Yau tun safe ba su da wuta, kamar wutan anguwar ta su ne ta samu matsala. Tun ƙarfe biyar na yamma aka tada generator ya ke ta aiki.

Ƙarfe takwas na dare Zaytoonah ta shiga wanka. Yau kwanan ta ne, zuwa ƙarfe tara ta san Galadima zai dawo daga Fada.
Ta fito daga wanka tana shafa mai Generator ya mutu.
Da sauri ta fara laluben wayan ta dan ta haska ɗakin kawai wayar ta faɗi ƙasa, ta tsugunna ta lalubo wayar tana ƙoƙarin kunna shi kawai ta ji kamar an taɓa ma ta baya nan da nan ta ƙwalla ƙara, jikinta ya fara ƙyarma.

"Ben dont kill me, please dont kill me"
Ta faɗa tana yin baya-baya saboda Ben kawai ta ke gani a idonta yana riƙe da bindiga.

Raziya da Hajiya Ghazala ne su ka shigo É—akin da gudu.

"Zaytoonah" Ghazala ta kira tana haskata da wayarta.

"Zuhayr help me, save me D, save me" abinda ta ke faɗi kenan har lokacin jikinta na ɓari.

"Anty Zaytoonah" Raziya ta faÉ—a tana matsawa kusa da ita.

"Raziya ki matsa ƙila Aljanu gareta. Je ki kira Baba Maigadi a zo ma ta ruƙiyya"

Ta faÉ—a tana janye Raziya daga wajen. Dukkan su fita su ka yi daga É—akin su ka bar Zaytoonah a wajen tana cigaba da sunbatu.

Raziya ta yi ƙasa da gudu yayinda Ghazala ta shiga kiran numbar Justice.

ÆŠaya daga cikin dogarai ma su tsaron gidan Raziya ta samu ta gaya ma sa ya zo inji Ghazala, Aljanun Zaytoonah sun tashi.

Da farko ya so ƙin shiga dan iyakar sa tsakar gidan sai kuma falon Justice da ke ƙasa idan ya buƙaci ganin su. Sai dai yadda Raziyan ta ke magiya ya sa shi bin bayanta da sauri.

Yana shiga ya tadda Ghazala a falon ƙasa tana waya.

"Wallahi hauka tuburan ta ke yi Hajiya. Yanzu dai na sa an kira dogari zai ma ta ruƙiyya"

Daga ɓangaren Hajiya Abu ta ce "Kul, banda wannan ganganci. Kar namijin da ya shiga wajen ta. Ku dai bar ta a ɗakin zuwa Galadima ya iso"

Ghazala ta amsa da toh.

Cewa dogarin ta yi ya tsaya a wajen zuwa Galadima ya iso saboda kar Zaytoonah ta fito ta mu su wani abin.

"Hajiya su Falaq na É—aki"

"Na tura Baaba Nafy wajen su"

Ai ba ta tsaya jin maganar ba ta haura saman.

Ganin É—akin Zaytoonah a buÉ—e kuma tana jin muryan su Hadid ya sa ta wuce wajen.

"Mom its me Hadid"

"Mom please ba kowa a nan mu ne kawai. Ni da Hadid ne"

Zuwa lokacin É—akin ya É—au haske saboda torchlight da kuma wayar da Baaba Nafy ta kunna. Tana haurowa sama ta samu 'yan biyu da Falaq a É—akin.

A hankali Zaytoonah ta fara sauke numfashi ganin da gaske dai 'ya'yanta ne a gaban ta...

Da sauri-sauri Galadima ya shigo gidan har lokacin Ghazala na zaune a falon ƙasa.

"Ina ta ke?" Ya faɗa da ƙarfi.

ÆŠakin ta.

Yana wucewa itama ta bi bayan shi da sauri.
Lokacin Zaytoonah ta samu nitsuwa, tana zaune a kan gado sun sata a tsakiya.

Shigowar sa É—akin ya sa Baaba Nafy ta ja hannun Falaq da Raziya su ka bar É—akin.

"Are you Ok"

"I'm sorry" ta furta a hankali.

"Sannu ya jikin?Baaba Nafy ne ta miki ruƙiyya?"

Irin kallon da Justice ya watsa ma ta ne ya sa ta yi shiru. Ta juya ta fice daga É—akin...

Bayan ya lallaɓa Zaytoonah ta yi bacci tukunna ya fito ya hau ma su aiki da masifa kan ta ya za a bari generator ya mutu, duk da zuwa lokacin an gyara amma a hakan sai da yai ta faɗa. Su kan su sun yi mamakin wannan faɗan dan ba halin Galadima ba ne.

***

End of Chapter 121Continue to the next chapter or choose another story below.

More Hausa novels

Browse all books →
Previous Login to Save Next