Ramadan Promo!All users that send a manual request for premium upgrade on sallah day will be granted for 1 month free.
Soyayyanovels
Zaytoonah Part One Complete Hausa Novel
Zaytoonah Part One Complete Hausa Novel
By Azizat
Login to keep your reading position saved.
Book Page Chapters
Zaytoonah Part One Complete Hausa Novel

Zaytoonah Part One Complete Hausa Novel

Author: Azizat
Chapter 116 of 161
About 8 min read
Chapter progress: 0%
Listen Mode
Listen to this chapter using your device voice.
Ready to listen from this chapter.
Free access is active. You can keep reading and download during this access window.

Book chapters

Choose a chapter and continue reading.

Start chapters
Chapter 1 1,689 words Chapter 2 1,523 words Chapter 3 1,583 words Chapter 4 1,696 words Chapter 5 1,682 words Chapter 6 1,693 words Chapter 7 1,594 words Chapter 8 1,673 words Chapter 9 1,663 words Chapter 10 1,668 words Chapter 11 1,678 words Chapter 12 1,698 words Chapter 13 1,687 words Chapter 14 1,699 words Chapter 15 1,656 words Chapter 16 1,634 words Chapter 17 1,681 words Chapter 18 1,675 words Chapter 19 1,655 words Chapter 20 1,613 words Chapter 21 1,669 words Chapter 22 1,655 words Chapter 23 1,671 words Chapter 24 1,650 words Chapter 25 1,677 words Chapter 26 1,696 words Chapter 27 1,598 words Chapter 28 1,699 words Chapter 29 1,694 words Chapter 30 1,659 words Chapter 31 1,683 words Chapter 32 1,309 words Chapter 33 1,691 words Chapter 34 1,697 words Chapter 35 1,553 words Chapter 36 1,588 words Chapter 37 1,682 words Chapter 38 1,680 words Chapter 39 1,677 words Chapter 40 1,649 words Chapter 41 1,700 words Chapter 42 1,698 words Chapter 43 1,676 words Chapter 44 1,625 words Chapter 45 1,633 words Chapter 46 1,675 words Chapter 47 1,693 words Chapter 48 1,668 words Chapter 49 1,688 words Chapter 50 1,647 words Chapter 51 1,653 words Chapter 52 1,568 words Chapter 53 1,689 words Chapter 54 1,699 words Chapter 55 1,669 words Chapter 56 1,578 words Chapter 57 1,564 words Chapter 58 1,660 words Chapter 59 1,694 words Chapter 60 1,415 words Chapter 61 1,653 words Chapter 62 1,690 words Chapter 63 1,685 words Chapter 64 1,618 words Chapter 65 1,652 words Chapter 66 1,674 words Chapter 67 1,687 words Chapter 68 1,699 words Chapter 69 1,644 words Chapter 70 1,698 words Chapter 71 1,691 words Chapter 72 1,671 words Chapter 73 1,689 words Chapter 74 1,679 words Chapter 75 1,677 words Chapter 76 1,678 words Chapter 77 1,655 words Chapter 78 1,683 words Chapter 79 1,696 words Chapter 80 1,700 words Chapter 81 1,694 words Chapter 82 1,697 words Chapter 83 1,692 words Chapter 84 1,668 words Chapter 85 1,554 words Chapter 86 1,666 words Chapter 87 1,677 words Chapter 88 1,694 words Chapter 89 1,667 words Chapter 90 1,700 words Chapter 91 1,670 words Chapter 92 1,670 words Chapter 93 1,655 words Chapter 94 1,640 words Chapter 95 1,607 words Chapter 96 1,668 words Chapter 97 1,659 words Chapter 98 1,689 words Chapter 99 1,675 words Chapter 100 1,614 words Chapter 101 1,610 words Chapter 102 1,700 words Chapter 103 1,683 words Chapter 104 1,657 words Chapter 105 1,698 words Chapter 106 1,700 words Chapter 107 1,695 words Chapter 108 1,656 words Chapter 109 1,683 words Chapter 110 1,699 words Chapter 111 1,699 words Chapter 112 1,641 words Chapter 113 1,696 words Chapter 114 1,626 words Chapter 115 1,695 words Chapter 116 Reading now Chapter 117 1,698 words Chapter 118 1,645 words Chapter 119 1,673 words Chapter 120 1,691 words Chapter 121 1,635 words Chapter 122 1,694 words Chapter 123 1,689 words Chapter 124 1,688 words Chapter 125 1,673 words Chapter 126 1,692 words Chapter 127 1,686 words Chapter 128 1,697 words Chapter 129 1,660 words Chapter 130 1,691 words Chapter 131 1,674 words Chapter 132 1,670 words Chapter 133 1,693 words Chapter 134 1,691 words Chapter 135 1,687 words Chapter 136 1,672 words Chapter 137 1,691 words Chapter 138 1,657 words Chapter 139 1,687 words Chapter 140 1,650 words Chapter 141 1,695 words Chapter 142 1,607 words Chapter 143 1,699 words Chapter 144 1,676 words Chapter 145 1,698 words Chapter 146 1,684 words Chapter 147 1,664 words Chapter 148 1,696 words Chapter 149 1,674 words Chapter 150 1,680 words Chapter 151 1,697 words Chapter 152 1,628 words Chapter 153 1,618 words Chapter 154 1,688 words Chapter 155 1,664 words Chapter 156 1,692 words Chapter 157 1,584 words Chapter 158 1,644 words Chapter 159 1,646 words Chapter 160 1,618 words Chapter 161 1,797 words

Hashir da Hadid su ka wani tafa suna dariya tareda juya keken su suka shige gidan.

Ƙwaƙwƙwaran numfashi mai kyau ta kasa yi. Yau da ace wani ne ya gaya ma ta abinda 'yan biyu su ka ce da ba za ta taɓa yarda ba amma sai gashi da kunnen ta ta ji komai. Wato da ƙarfi da yaji dai Justice ne Daddyn su.

Ya lura da yadda ta kaɗu da jin maganar yaran dan haka ya kauda hankalinta ta hanyar cewa "shekaru bakwai da su ka wuce na haɗu da wata yarinya mai karambani a wajen wani biki. Yarinyar da ƙarfi ta ke son shiga wajen da ake dinner bayan kuma ba ta da card ɗin shiga. Ta maƙalewa wani mutumi da ta kira Uncle Muhammad su ka barta ta shiga.

"Da ikon Allah wannan Uncle Muhammad ɗin ya sake ganinta a cikin jirgi bayan watanni kaɗan. Ba tareda ta ganeshi ba ta ma sa tayin plantain chips da ta ke ci. Da jirgi zai tashi ta fara karanto addu'o'i kala-kala har ta riƙe hannun sa ba tareda ta sani ba..."

"Ya Allah! Daddyn Raziya kai ne dama?"

Murmushi yai ya ce "na ƙara tsufa sosai ko?"

"Oh my goodness, shiyasa ranan da mu ka je gidan ka na ke tunanin kaman na taɓa sanin ka a wani waje, ashe kai ne"
Ta dafa kan ta tana É—an girgizawa cike da tunanin wannan coincidence É—in.

" Kalmar Allah ya isa tana da nauyi Zaytoon. Idan har zaman da za mu yi tana ƙarƙashin wannan kalmar ne, zan iya haƙura da zaman ko da kuwa abu ne da zai min ciwo"

Ya kwantar da kan sa jikin kujera yana kallon sama kaman mai tuno wani abu.

"Immediately da na gama Law School ina da dogon buri a rai na. Kwata-kwata ba ni da niyyar yin aiki ƙarƙashin gwamnati. Case na farko da na karɓa na wani Baffana na ne ƙanin Mai Martaba. Wani babban fili ne ake jayayya a kai. I was young, buri na kawai shine na ci first case ɗina ta ko wani hali. Aka shiga ƙara kotu mu ka fafata da lawyan gwamnati da ke kare Tsoho mai filin da kuma ni da na ke kare Baffana. In the end aka ba wa Baffana gaskiya aka ƙwace fili daga hannun Baba Sama'ila.

"Bayan mun fito daga kotu ina murna na ci case ɗin sai na ji an taɓani ta baya, juyawan da zan yi sai na ga wannan tsohon ne da akayi shari'ar da shi. Akwai tsantsan ɓacin rai da damuwa tattare da fiskar sa, ya ce min ("Na san kun fi ƙarfina, amma zan bar ku da Sarkin da baya zalunci. Allah ya isa fili na").

"Zaytoon ban iya bacci ba ranan ba. Kalmar Allah ya isan nan ya tsaya min a zuciya, ya hanani sukuni. Washegari na tafi ƙauyen Tsohon nan only to find out ana zaman makokin sa. Ashe bayan ya koma gida da ya shiga ya kwanta bai sake tashi ba. Ɓacin rai ya zama ajalin sa. Hankalina ya tashi matuƙa, i blamed myself for his death. Na koma na waiwayi case ɗin nan, na bi proper ways na yi bincike na gane cewa Baba Sama'ila bai sayarda filinsa wa Baffana ba. Yes Baffana ya ma sa tayin sayar da filin amma ya ƙi, shine aka yi fake documents da kuma sa hannun ƙarya aciki. Wasu marasa imani cikin ƙauyen su ka ba da shaidar zur akan cewa lallai Baba Sama'ila ya saida filin sa. Bayan na gama haɗa komai i met my uncle akan ya maidawa 'ya'yan Baba filin su ko kuma dai na sake buɗe sabon ƙara akan sa. Abu dai ta kai mu har gaban Mai Martaba still bai yarda ba. Ni na jagoranci yaran Baba Sama'ila aka ɗaukaka ƙaran nan har ta kai an ƙwace fili daga hannun Baffana an maidashi wajen Magadan Baba Sama'ila.

"Dalilin wannan har yau ba ma shiri da Baffa na. Saboda wannan shari'ar ya sa na fasa zama lawyer mai zaman kan sa na koma ɓangaren gwamnati na fara aiki har na kawo matsayin da na ke yanzu.

"Zaytoon, har kafin a bawa 'ya'yan Baba filin nan, ban taɓa yin bacci na kwanciyar hankali ba. Duk lokacin da na kwanta kalmar Allah ya isa da Baba yai shi ke hanani bacci..."

Kukan da ya ci ƙarfin sa ne ya hanashi ci gaba da maganar. Itama Zaytoonah hawaye fall ne a idonta.

Justice ya fito da handkerchief ya fara goge hawayen da ke fita a idon sa, sai dai yana gogewa wasu na fitowa.

"Daddyn Raziya ka yi haƙuri" Zaytoonah ta faɗa tana ɗaura hannunta akan cinyar sa.

Kusan minti biyu kafin ya iya tsaida kukan na sa ya juyo yana kallon Zaytoonah ya ce

"Ina son ki Zaytoon, amma ba zan iya zaman Allah ya isa da ke ba. Zan ba ki kwana uku ki yi tunani, in har kin yadda ni mugu ne marar adalci, wanda ba za ki iya zama da shi ba. Zan sawwaƙa mi ki. Da na zauna da ke ina zaluntar ki gara na danne zuciyata na rabu da ke na miki fatan alkhairi a rayuwar ki"

Jikinta ne yai sanyi, ta ma rasa mi za ta faÉ—a ma sa a wannan lokaci.

Ya sa hannu a baya ya jawo wata leda ya É—aura a cinyarta ya ce " ga tsarabar 'ya'yana. Ki gaishe min da su"...

***

Maganganun Justice ta ke ta juyawa a ranta wanda ya hanata bacci. Idan har za ta kira Justice mugu to ita ce babbar muguwar. Bayan matsalar Ghazala mi ya ma ta da har za ta kira shi da mugu. Ghazala ce fa Munafuka.

Ƙarfe tara na dare sai ga kiran Hajia Abu a wayarta. Ta tashi zaune ta ɗauka wayan tareda sallama.

"Ke wacce irin daƙiƙiyar yarinya ce, Iye?. Idan ma kin yi yaji ne dan kina tunanin Galadima zai zo ya yo bikon ki to kin yi kaɗan. Idan za ki tattara ki koma gida ki koma, idan kuma takardar ki kike buƙata sai ki yi magana a kawo miki har gida. Ba dan ma ƙaddara ba mi zai haɗa auren ki da Galadima"

Sarai ta san Ghazala ce da wannan aikin, wato har ta beza cewa ta yi yaji daga kwana uku da ta bar gidan.

"Hajiya waya ce Yaji na yi?. Mommy na ne fa ba ta da lafiya shine na zo duba ta"

Hajiya Abu ta ji gwiwarta ya sace, dama barazana ce kawai. Ko kaɗan ba ta son abinda zai ɓatawa Galadima record domin tanada ɓoyayyen buri akan sa na son ya gaji Mai Martaba idan rai ya halin sa.

"Ghazala ta ce da dukkan akwatunan ki kika tafi, ana zuwa gaisuwa da duka kaya ne?"

"Lah! Kayan da ke Abujan ne naga sun kwana biyu shine na dawo da su nan saboda zan É—auko wasu a nan É—in na tafi da su chan"

"To Allah ya ba ta lafiya"

Ba ta jira Zaytoonah ta ce Amin ba ma ta kashe wayar.

"Mommy ki ji wai har Ghazala ta fara yaÉ—awa wai na yi yaji"

Mommy da ke duba assignment É—in yara ta ce "to ba yajin ki ka yi ba?"

"To shine harta fara bezawa a gari"

"Mi za ta jira kuma tunda gidan mai gaba É—aya za ki bar ma ta"

"Allah ya sawwaƙa na bar ma ta gidan"

Sai da ta yi maganar kuma sai ta riƙe baki tana jin kunya. Mommy ta yi murmushi ta cigaba da abinda ta ke yi.
2/11/21, 10:04 PM - ****: 58

Bismillahir Rahmanir Rahim

*I'm back*

Washe gari Zaytoonah ta je salon aka wanke ma ta kai aka ma ta ƙananun ƙitso, aka ma ta gyaran farce kafin aka ma ta jan Lalle. Ba ta dawo gidan ba ma sai bayan Azahar.
Ta kira Baaba Nafy ta ce ma ta Justice yana nan bai tafi ba sai washegari zai tafi saboda ya je representing Mai Martaba zuwa ta'aziyya wani ƙauye.

Ƙarfe shida saura ta isa gidan Justice. Sai da su ka gaisa da Baaba Nafy kafin ta wuce ɗakin ta bayan ta ƙarfi kwandon abinci da ta zo da shi. Tunda ta cewa Baaba Nafy za ta zo ta sa aka gyara ma ta ɗakin ta dan haka bayan ta ajiye jakarta ɗakin Justice ta wuce, falon sa na nan tsaf-tsaf sai ƙanshi ya ke. Ɗakin ma a tsaftacce ya ke duk da ma Justice baya bari ma su aiki su shiga ma sa ɗaki shi ya ke gyara kayan sa. Ko a chan Abuja ma shi ya ke gyarawa ko ya saka Raziya, yanzu kuma da ya ke da Mata har biyu kowacce ranan kwananta sai shiga ta gyara ma sa.

Da ta gama É—an gyara abinda ba za a rasa ba komawa É—akinta ta yi ta É—auko sabon bedsheet ta zo ta shimfiÉ—a ma sa. Sabon rayuwa sabon bedsheet.
Da ta ga komai ya ma ta yadda ta ke so sai ta koma na ta É—akin. Alwala ta yi ta zo ta zauna a sallaya tana azkar kafin a kira sallar Magariba.

Gaba ɗaya a gajiye ya dawo. Ƙauyen da su ka je hanyar kwata-kwata babu kyau, sun ji jiki a tafiyar da su ka yi.
Da ke sai da ya tsaya yai sallar Isha ma kafin ya shigo gidan saboda da ya ci abinci kwantawa zai yi ya huta gajiya tunda gobe ma sabon hanya zai É—auka.

Bayan yayi wanka ya fito ya saka silk pyjamas ɗin sa baƙaƙe sannan ya fito falon ƙasa inda aka jera ma sa abinci.
Da ke ya ga dare ya yi bai yi niyyar cin abincin sosai ba. Tea da aka haɗa ya fara zubawa kafin ya buɗe warmers ɗin ya fara serving kan sa abinci. Lomar farko da ya ci ya tabbatar ba girkin Baaba Nafy ba ne, kamar dai girkin Zaytoonah amma kuma ta ina Zaytoonah za ta ma sa girki bayan tana chan gidan su. Har ya ɗaga waya zai kira Baaba Nafy ya tambayi wa yai girkin yau sai kuma ya fasa ya cigaba da cin abincin, ya sawa ransa ƙila kewanta da ya ke yi ya sa shi jin abincin kamar irin girkinta.

End of Chapter 116Continue to the next chapter or choose another story below.

More Hausa novels

Browse all books →
Previous Login to Save Next