Ramadan Promo!All users that send a manual request for premium upgrade on sallah day will be granted for 1 month free.
Soyayyanovels
Zaytoonah Part One Complete Hausa Novel
Zaytoonah Part One Complete Hausa Novel
By Azizat
Login to keep your reading position saved.
Book Page Chapters
Zaytoonah Part One Complete Hausa Novel

Zaytoonah Part One Complete Hausa Novel

Author: Azizat
Chapter 46 of 161
About 8 min read
Chapter progress: 0%
Listen Mode
Listen to this chapter using your device voice.
Ready to listen from this chapter.
Free access is active. You can keep reading and download during this access window.

Book chapters

Choose a chapter and continue reading.

Start chapters
Chapter 1 1,689 words Chapter 2 1,523 words Chapter 3 1,583 words Chapter 4 1,696 words Chapter 5 1,682 words Chapter 6 1,693 words Chapter 7 1,594 words Chapter 8 1,673 words Chapter 9 1,663 words Chapter 10 1,668 words Chapter 11 1,678 words Chapter 12 1,698 words Chapter 13 1,687 words Chapter 14 1,699 words Chapter 15 1,656 words Chapter 16 1,634 words Chapter 17 1,681 words Chapter 18 1,675 words Chapter 19 1,655 words Chapter 20 1,613 words Chapter 21 1,669 words Chapter 22 1,655 words Chapter 23 1,671 words Chapter 24 1,650 words Chapter 25 1,677 words Chapter 26 1,696 words Chapter 27 1,598 words Chapter 28 1,699 words Chapter 29 1,694 words Chapter 30 1,659 words Chapter 31 1,683 words Chapter 32 1,309 words Chapter 33 1,691 words Chapter 34 1,697 words Chapter 35 1,553 words Chapter 36 1,588 words Chapter 37 1,682 words Chapter 38 1,680 words Chapter 39 1,677 words Chapter 40 1,649 words Chapter 41 1,700 words Chapter 42 1,698 words Chapter 43 1,676 words Chapter 44 1,625 words Chapter 45 1,633 words Chapter 46 Reading now Chapter 47 1,693 words Chapter 48 1,668 words Chapter 49 1,688 words Chapter 50 1,647 words Chapter 51 1,653 words Chapter 52 1,568 words Chapter 53 1,689 words Chapter 54 1,699 words Chapter 55 1,669 words Chapter 56 1,578 words Chapter 57 1,564 words Chapter 58 1,660 words Chapter 59 1,694 words Chapter 60 1,415 words Chapter 61 1,653 words Chapter 62 1,690 words Chapter 63 1,685 words Chapter 64 1,618 words Chapter 65 1,652 words Chapter 66 1,674 words Chapter 67 1,687 words Chapter 68 1,699 words Chapter 69 1,644 words Chapter 70 1,698 words Chapter 71 1,691 words Chapter 72 1,671 words Chapter 73 1,689 words Chapter 74 1,679 words Chapter 75 1,677 words Chapter 76 1,678 words Chapter 77 1,655 words Chapter 78 1,683 words Chapter 79 1,696 words Chapter 80 1,700 words Chapter 81 1,694 words Chapter 82 1,697 words Chapter 83 1,692 words Chapter 84 1,668 words Chapter 85 1,554 words Chapter 86 1,666 words Chapter 87 1,677 words Chapter 88 1,694 words Chapter 89 1,667 words Chapter 90 1,700 words Chapter 91 1,670 words Chapter 92 1,670 words Chapter 93 1,655 words Chapter 94 1,640 words Chapter 95 1,607 words Chapter 96 1,668 words Chapter 97 1,659 words Chapter 98 1,689 words Chapter 99 1,675 words Chapter 100 1,614 words Chapter 101 1,610 words Chapter 102 1,700 words Chapter 103 1,683 words Chapter 104 1,657 words Chapter 105 1,698 words Chapter 106 1,700 words Chapter 107 1,695 words Chapter 108 1,656 words Chapter 109 1,683 words Chapter 110 1,699 words Chapter 111 1,699 words Chapter 112 1,641 words Chapter 113 1,696 words Chapter 114 1,626 words Chapter 115 1,695 words Chapter 116 1,691 words Chapter 117 1,698 words Chapter 118 1,645 words Chapter 119 1,673 words Chapter 120 1,691 words Chapter 121 1,635 words Chapter 122 1,694 words Chapter 123 1,689 words Chapter 124 1,688 words Chapter 125 1,673 words Chapter 126 1,692 words Chapter 127 1,686 words Chapter 128 1,697 words Chapter 129 1,660 words Chapter 130 1,691 words Chapter 131 1,674 words Chapter 132 1,670 words Chapter 133 1,693 words Chapter 134 1,691 words Chapter 135 1,687 words Chapter 136 1,672 words Chapter 137 1,691 words Chapter 138 1,657 words Chapter 139 1,687 words Chapter 140 1,650 words Chapter 141 1,695 words Chapter 142 1,607 words Chapter 143 1,699 words Chapter 144 1,676 words Chapter 145 1,698 words Chapter 146 1,684 words Chapter 147 1,664 words Chapter 148 1,696 words Chapter 149 1,674 words Chapter 150 1,680 words Chapter 151 1,697 words Chapter 152 1,628 words Chapter 153 1,618 words Chapter 154 1,688 words Chapter 155 1,664 words Chapter 156 1,692 words Chapter 157 1,584 words Chapter 158 1,644 words Chapter 159 1,646 words Chapter 160 1,618 words Chapter 161 1,797 words

Ba'a jima ba ta farfaɗo amma ba ta da ƙarfin jiki hakan ya sa su ka ma ta allura aka ɗaura ma ta ruwa nan da nan bacci ya ɗauketa.
Ko ta kan Sadiq da ya zo dubawa bai yi ba sai ya tsaya kula da Maryam. Ya tambayi likita miya ke damunta ya ce jininta ne ya hau amma sauran bayani sai an kawo result É—in gwajin da aka je yi ma ta bayan an É—eba jinin ta.

Bayan awa É—aya aka kirashi wajen Likita inda ya bayyana ma sa Maryam na É—auke da juna biyu kuma ta rage damuwa dan zai iya jawowa ta rasa cikin.
Muntari ya hangame baki yana jin bayanin Likita.

"Ciki fa ka ce? Har yanzu ba ta dena haihuwa ba ne? Kai a dai sake dubawa ko an jirkita result É—in, rabonta da samun ciki shekaru shida no shekaru bakwai kenan"

Likita da ya É—auka Muntari mijin Maryam ne ya ce "ai ba ta wuce shekarun haihuwa ba ma su shekaru hamsin ma suna haihuwa balle ita da na ke tunanin ba ta fi arba'in ba"

"Talatin da tara ne ma" ya gyara ma sa, kar ya ƙarawa Maryam ɗin sa tsufa.

"To ka gani, she's still very active ta samu ciki. Tana buƙatar hutu sosai, za mu riƙeta na kwana biyu kafin mu sallameta, kuma idan ta koma gida ma ta rage yawan ayyuka ta kuma cire damuwa a ranta"

Muntari ya gyaɗa kai kafin ya miƙe ya bar office ɗin bayan sun yi musabaha da Likita.

Yana shiga ɗaki ya ƙurawa Maryam ido wani kishi da haushi na turnuƙe shi. A fili ya furta "shege Tijjani sai da yai yadda ya ƙunsa ma ta ciki kafin ya tafi"

Daga baya ne ya kira Hajjo ya je ya duba Sadiq ya kuma gaya ma ta Maryam ma an ba ta gado saboda ta faÉ—i lokacin suna shigowa.

"Miya sameta?" Hajjo ta tambaya tana mamakin abun

"Likita ya ce damuwa ce ta ma ta yawa"

"Ai dole, ta fi kowa damuwa da rashin Hamma amma kuma ta ke daurewa tana nuna ba komai".

Sa'ilin da Maryam ta tashi ta so a barta ta tashi ta tafi saboda ta ɗan ji ƙarfin jikinta amma Likita ya ƙi Muntari ma na gefe yana ba ta baki.

Tana son yiwa Likitan bayanin jinyar Sadiq sai maganar likitan ya katse ta.

"Hajiya kina buƙatan hutu fa, dan rashin samun nutsuwa ka iya sa ki rasa abinda ke cikin ki"

"Ciki?" Ta furta da mamaki

"Yes, inaga Maigidan bai riga ya faÉ—a miki ba kenan?"

Muntari yai saurin cewa "tana tashi na zo na kira ka" nan kuwa sai da ta yi kusan 15mins da tashi kafin ya je ya gayawa Likitan bayan da ta ce mi shi ya je ya ce a cire ma ta Canula da ke hannunta za ta tafi É—akin Sadiq.

Shafa ƙasan cikinta ta yi sai ga hawaye. Ciki a lokacin da ta cire rai da sake haihuwa, ciki a lokacin da ake tsaka da neman T J. Ba za ta yi abinda zai sa ta rasa cikin nan ba, not after 'yan biyun ta da ta rasa.

Washegari Maryam ta sa aka Sallameta bayan ta bawa Likita tabbacin za ta kiyaye dokokin sa saboda lafiyar ta. Muntari dai haushin cikin ya cika shi amma kuma soyayyar Maryam ya shafe haushin.
Sadiq kam sai da yai kwana tara a Asibitin aka sallameshi su ka dawo gida, yawan jinya da ya ke yi ma ya sa makarantar sa ma lilo ta ke yi, ya kasa wani yin nisa a karatun.

Addu'a da sadaƙa kam ba wanda aka fasa yiwa T J dan a gano inda ya ke. Tun suna sa ran za'a ji labarin sa har kuma su ka fara fidda rai amma ga Maryam kam kowacce rana da ta fito da hope ɗin ganin T J ta ke musamman yanzu da ta gano tana ɗauke da cikin sa.
Sai da cikin ma ya kai wata biyar ma yawancin mutane su ka gane tana ɗauke da cikin, ciki kuwa har da Iya. Hanne ce ba lafiya ta je gaisheta shine ta haɗu da Iya ashe Hannen laulayi ta ke yi, duk da damuwar ɓatar T J da Iyan ke ciki samun cikin Hanne ya sa ta kwantar da hankalin ta.
Ba laifi da Maryam ta gaisheta ta amsa, haka ta bita da kallo lokacin da za ta tafi tana ƙara tabbatarwa kanta cewa ciki ne a jikin Maryam ɗin...

***

"Zaytoonah miye wannan?"
Ta faÉ—i tana nuna takardan da Zaytoonan ta ba ta.

"Mommy report card ma na" ta amsa tana tura baki

"Sai yaushe za ki maida hankali a karatu ne. Second term 21st a cikin ku 35 yanzu third term kuma 28th. I'm not happy, from 3rd position a first term sai ki koma ƙarshe-ƙarshe"

"Mommy first term Daddy yana nan, yanzu kuma bayanan, ni daga yanzu ma ba zan je school ɗin ba" ta ƙarisa maganar tana tashi za ta bar ɗakin.

"Come back here Zaytoonah. Kar ki sake tashi a gabana ba tareda mun gama maganan ba"
Ta zo ta zauna tana zumɓura baki. Maryam na fara ma ta maganan maida hankali a karatu ta fashe da kuka.
"Mommy ba zan yi karatun ba, ba zan yi ba. Just leave me alone"

"Zan mugun saɓa miki kuwa, ke kaɗai ce kika rasa Uba? Su Salman, Sadiq da Humairah su mutu kenan saboda kin fi su son Daddyn ku?. Haba Zaytoonah sai kin kasheni hankalin ki zai kwanta? Ke ce Babba amma kin fi kowa wauta. Da wanne zan ji Dan Allah"

"Mommy dan Allah ki yi haƙuri" Auwal da shigowar sa ɗakin kenan ya faɗa.

"Ita za ka bawa haƙuri kar ta kashe ni. Na gaji da matsalarta a gidan nan"

Zaytoonah ta fice daga É—akin da gudu.
Ya sani ba halin Mommy ba ne ƙorafi amma duba da abubuwan da su ka faru da kuma cikinta da ya girma gaba ɗaya ta chanja. Abu kaɗan yanzu faɗa ta ke yi. Akwai ranan da tana yiwa Zaytoonah magana sai da ta haɗa da mari, ba dan ya shiga tsakani ba ma da ba ƙaramin duka za ta yiwa Zaytoonan ba. Ya sani Mommy na fama da depression ne.

ÆŠakin Zaytoonah ya wuce ya samu ta kifa kai akan gado sai kuka ta ke yi.

Bai ce ma ta komai ba sai ya zauna bakin gado yana sake duba report card ɗin Zaytoonan. Kusan minti biyar da shigowar sa bai ce komai ba hakan ya sa Zaytoonah ta tsaida kukan ta ɗago tana kallon sa, suna haɗa ido ta harareshi ta cigaba da sheshsheƙar kuka.

"Ki cigaba da harara ta, idan idonki ya faÉ—o na Kare za a sa miki"

Ta murguÉ—a ma sa baki ta ce "ina ruwan ka"

"Da ruwa na mana tunda ni za a nuna a gari ace ga Yayan Zaytoonah dog eyes"
Ta É—au pillow ta buga ma sa a ka.

"Ashe dai ba Mommy kawai za ki kashe ba har da ni" ya faÉ—a yana dariya
Zaytoonah ta ja tsaki.

Kusan 5 seconds kafin ya kira sunan ta a hankali "Zaytoonah"
Ba ta amsa ba amma ta zuba ma sa idanun ta.

"Abinda ki ke yi ba shi zai sa a ga Daddy ba. Infact abinda ki ke yi zai sawa Mommy ɓacin rai ne ƙarshe watarana ta samu heart attack ta mutu"

Zaytoonah ta zaro ido

"Ki na so Mommy ta mutu ne?"
Ta yi saurin girgiza kai

"To ki dena sa ma ta ɓacin rai. Na sha gaya miki addu'a za ki dinga yiwa Daddy ba wai kuka ko taurin kai ba. Ki na so Daddy ya dawo ya samu ba kya karatu ran sa ya ɓaci da ke?"

Nan ma ta girgiza ma sa kai.

"To ki dage da karatu, ban da rashin kunya da taurin kai kin ji"

Jikinta ne ya sanyi ta sunkuyar da kai tana zubda ƙwalla. She's trying to accept the fact that Daddy ya ɓata, ɓata kamar yadda ake neman abu a rasa ko kuma kana kiwon dabba sai ka nemeshi ka rasa. Over this few months ba abin da ba ta riyawa ran ta ba gameda ɓatan Daddyn su. Ta yi tunanin ko 'yan yankan kai ne su ka ɗauke shi ko kuma dai accident yai gawarsa ta ƙone aka rasa waye aka bisine shi. Akwai lokutan da ta ke tunanin ko dai ya gaji da su ne ya gudu dan ya gina sabuwar rayuwa ba tareda su ba, sai kuma ta tuna da cewa Daddyn su na son su sosai, ba zai taɓa guduwa ya bar su.

"Come here" Auwal ya faÉ—a yana jawota jikinsa, ya dinga bubbuga bayanta yana cigaba da rarrashinta...

Da yamma lis Zaytoonah ta shiga kitchen.

"Mommy whats cooking?"

"Your eyes" Mommy ta amsa a hasale

Ta je ta rungume Mommyn ta baya tana faÉ—in "Mommy i'm sorry"

"Sorry for yourself"

"Ah Ah Mommy na tuba fa, no more bad result daga yanzu"

"Har da kukan banza?"

"Yes Mommy, babu kukan banza"

"Sakeni na yi aiki to"

Maimakon ta saketa sai ta ƙara ƙanƙameta tana faɗin "i love you Mommy"

"Na ji sakeni"

"Ai ba ki amsa ba"

Maryam ta yi murmushi ta ce "I love you too"

Sai a sannan Zaytoonah ta saketa, ta kama ma ta aiki har su ka haÉ—a girkin.

***

Ƙarfe biyun dare Auwal ya kira Maryam akan ta zo gidan Hajjo Sadiq ba lafiya. Maryam ta zura dogon hijabi na sallah ta ɗau key ta fita. Addu'a ta ke yi a ranta saboda yanayi na sanyi da aka shiga lokacin ne ciwon Sadiq ya fi tashi. Bai fi sati biyu da ya wuce ba aka sallamoshi daga Asibiti. Shekaranjiya da kan sa ya zo gidan ta ya wuni, dan har sai dare da Auwal zai koma gidan Hajjo ya tafi da shi. Ɗan zaman da yayi da ita ba ƙaramin tausayi ya ba ta ba dan da crutches ya ke tafiya saboda ciwon ƙafa, ciwon ya hanashi girma sai ƙaton kai. Makaranta kam kusan watan sa uku ma bai zuwa.

End of Chapter 46Continue to the next chapter or choose another story below.

More Hausa novels

Browse all books →
Previous Login to Save Next