Ramadan Promo!All users that send a manual request for premium upgrade on sallah day will be granted for 1 month free.
Soyayyanovels
Zaytoonah Part One Complete Hausa Novel
Zaytoonah Part One Complete Hausa Novel
By Azizat
Login to keep your reading position saved.
Book Page Chapters
Zaytoonah Part One Complete Hausa Novel

Zaytoonah Part One Complete Hausa Novel

Author: Azizat
Chapter 10 of 161
About 8 min read
Chapter progress: 0%
Listen Mode
Listen to this chapter using your device voice.
Ready to listen from this chapter.
Free access is active. You can keep reading and download during this access window.

Book chapters

Choose a chapter and continue reading.

Start chapters
Chapter 1 1,689 words Chapter 2 1,523 words Chapter 3 1,583 words Chapter 4 1,696 words Chapter 5 1,682 words Chapter 6 1,693 words Chapter 7 1,594 words Chapter 8 1,673 words Chapter 9 1,663 words Chapter 10 Reading now Chapter 11 1,678 words Chapter 12 1,698 words Chapter 13 1,687 words Chapter 14 1,699 words Chapter 15 1,656 words Chapter 16 1,634 words Chapter 17 1,681 words Chapter 18 1,675 words Chapter 19 1,655 words Chapter 20 1,613 words Chapter 21 1,669 words Chapter 22 1,655 words Chapter 23 1,671 words Chapter 24 1,650 words Chapter 25 1,677 words Chapter 26 1,696 words Chapter 27 1,598 words Chapter 28 1,699 words Chapter 29 1,694 words Chapter 30 1,659 words Chapter 31 1,683 words Chapter 32 1,309 words Chapter 33 1,691 words Chapter 34 1,697 words Chapter 35 1,553 words Chapter 36 1,588 words Chapter 37 1,682 words Chapter 38 1,680 words Chapter 39 1,677 words Chapter 40 1,649 words Chapter 41 1,700 words Chapter 42 1,698 words Chapter 43 1,676 words Chapter 44 1,625 words Chapter 45 1,633 words Chapter 46 1,675 words Chapter 47 1,693 words Chapter 48 1,668 words Chapter 49 1,688 words Chapter 50 1,647 words Chapter 51 1,653 words Chapter 52 1,568 words Chapter 53 1,689 words Chapter 54 1,699 words Chapter 55 1,669 words Chapter 56 1,578 words Chapter 57 1,564 words Chapter 58 1,660 words Chapter 59 1,694 words Chapter 60 1,415 words Chapter 61 1,653 words Chapter 62 1,690 words Chapter 63 1,685 words Chapter 64 1,618 words Chapter 65 1,652 words Chapter 66 1,674 words Chapter 67 1,687 words Chapter 68 1,699 words Chapter 69 1,644 words Chapter 70 1,698 words Chapter 71 1,691 words Chapter 72 1,671 words Chapter 73 1,689 words Chapter 74 1,679 words Chapter 75 1,677 words Chapter 76 1,678 words Chapter 77 1,655 words Chapter 78 1,683 words Chapter 79 1,696 words Chapter 80 1,700 words Chapter 81 1,694 words Chapter 82 1,697 words Chapter 83 1,692 words Chapter 84 1,668 words Chapter 85 1,554 words Chapter 86 1,666 words Chapter 87 1,677 words Chapter 88 1,694 words Chapter 89 1,667 words Chapter 90 1,700 words Chapter 91 1,670 words Chapter 92 1,670 words Chapter 93 1,655 words Chapter 94 1,640 words Chapter 95 1,607 words Chapter 96 1,668 words Chapter 97 1,659 words Chapter 98 1,689 words Chapter 99 1,675 words Chapter 100 1,614 words Chapter 101 1,610 words Chapter 102 1,700 words Chapter 103 1,683 words Chapter 104 1,657 words Chapter 105 1,698 words Chapter 106 1,700 words Chapter 107 1,695 words Chapter 108 1,656 words Chapter 109 1,683 words Chapter 110 1,699 words Chapter 111 1,699 words Chapter 112 1,641 words Chapter 113 1,696 words Chapter 114 1,626 words Chapter 115 1,695 words Chapter 116 1,691 words Chapter 117 1,698 words Chapter 118 1,645 words Chapter 119 1,673 words Chapter 120 1,691 words Chapter 121 1,635 words Chapter 122 1,694 words Chapter 123 1,689 words Chapter 124 1,688 words Chapter 125 1,673 words Chapter 126 1,692 words Chapter 127 1,686 words Chapter 128 1,697 words Chapter 129 1,660 words Chapter 130 1,691 words Chapter 131 1,674 words Chapter 132 1,670 words Chapter 133 1,693 words Chapter 134 1,691 words Chapter 135 1,687 words Chapter 136 1,672 words Chapter 137 1,691 words Chapter 138 1,657 words Chapter 139 1,687 words Chapter 140 1,650 words Chapter 141 1,695 words Chapter 142 1,607 words Chapter 143 1,699 words Chapter 144 1,676 words Chapter 145 1,698 words Chapter 146 1,684 words Chapter 147 1,664 words Chapter 148 1,696 words Chapter 149 1,674 words Chapter 150 1,680 words Chapter 151 1,697 words Chapter 152 1,628 words Chapter 153 1,618 words Chapter 154 1,688 words Chapter 155 1,664 words Chapter 156 1,692 words Chapter 157 1,584 words Chapter 158 1,644 words Chapter 159 1,646 words Chapter 160 1,618 words Chapter 161 1,797 words

Sauran na ludayin ya kai bakinsa ya shanye, ya sake ɗebo wani wannan karan sai da ya sha ya rage sannan ya miƙa ma ta ta sha. A haka a haka har su ka shanye furan ba tareda wani ya yi magana ba. Ta ji daɗin furan duk da ma sugar ɗin ciki ya yi yawa.

Gefen bakinta akwai sauran furan dan haka ya sa babbar yatsar sa ya share ma ta. Shi kan sa bai san ya aka yi ya yi hakan ba. Its like tunda ya haɗu da yarinyar nan akwai wasu notinan kansa da su ka kunce. Ranan da ya fara ganin ta tana rawa a daren ranan sai da yai mafarkin ta, abun ya bashi mamaki sosai. Tunda ya ke bai taɓa sa wata mace a rai har ya yi mafarkinta ba. Lokacin yana undergraduate akwai wata Helen 'yar Auchi, haka ta nace ma sa wai tana son shi, bai taɓa jin wani abu gameda ita makamancin wanda ya ke ji yanzu ba, ya zo ajin ƙarshe ma ya taimakawa wata yarinya Hamdiyya 'yar Bauchi itama ta zo ta fara liƙe ma sa wai su yi soyayya. Shi tun da ma da yanzu mata ba sa gaban sa amma Nkiru is different. Ya rasa ko tausayinta da ya ke ne ya jawo ya ke jin abinda ya ke ji gameda ita oho.

Itakam tunda ta ji yatsar sa a daidai bakinta ta sandare a wajen. Tunaninta kissing É—in ta zai yi, there's something in his eyes that's so inviting.

"Saura kwana goma na koma Obowo, fatan kin shirya" ya katse shirun na su

"Mmm" kawai ta ce

"Ko kin fasa tafiya ne? za ki koma wajen Okafor, probably ki raising family da shi?"

"No" ta faɗa da ƙarfi tana zaro ido

"Then why Inkiru? Miyasa ki ke zuwa gun sa kullum ki daÉ—e, kin san yadda na ke ji kuwa idan na zo na samu kin fita?"

Ta girgiza kai

"Ina tsoro kar wani abu ya sameki Inkiru, ba zan taɓa yafewa kai na ba. Ban ce kar ki je gidan su Okafor ba ko kar ki je wajen Pastor amma..." ganin hawaye a idonta ya sa shi kasa ƙarisa maganar.

Sai yanzu ta gane miyasa ya ke fushi da ita ashe saboda fitan da ta ke yi ne.
"I'm sorry" ta faÉ—a in between tears.

"Ba na son kuka kin ji" ta gyaÉ—a kai tana share hawayen...

Daga ranan su ka shirya kamar da, sai dai kuma daga ranan Nkiru ta shiga wani hali na fargaba. Ba komai ba ne face tafiyar su da ta ke matsowa kusa, daga ta tafi shikenan ba za ta sake ganin T J ba. Maimakon fitan da su ke da Okafor yanzu da shi su ke fita yai ta nuna ma ta wajaje musamman gonakin su. Har gidan gonan Alhaji Isa sai da ya kaita a nan ta ga yadda ake matsar madaran shanu itama ta gwada matsawa. Ranan sunday kuwa shi ya raka ta har bakin church bayan awa uku ya dawo daidai an fara fitowa kenan, suna fitowa kuwa ta hangoshi, ko sauraron Okafor ba ta yi ba ta je ta sameshi su ka wuce gida.
Da yamma sai ga Muntari ya dira a gidan abun mamaki ko É—akin Iya bai shiga ba ya wuce É—akin Goggo. Yana zuwa kuwa jiki har rawa ya ke sanda ya ke kunce jakar sa. Tsarabar Gurasa, kilishi da dabino yai wa Nkiru wacce tun randa ya bar garin ta ke ran sa.

Goggo ta ce "ikon Allah" ganin yadda Muntarin ke ta rawan jiki a gaban Nkiru.
Ba ta ida mamaki ba sai da ta ga ya yagi kilishi yana ƙoƙarin turawa Nkiru a baki yana cewa ta ci ita kuwa tana girgiza kai.

"Muntari ba na tunanin ka yi sallar la'asar, ka wuce masallaci ko raka'a É—aya ka samu"

Ya miƙe yana cewa "kar wanda ya taɓa kayan nan na Mary ne, ita kaɗai na yiwa tsaraba"

Goggo ta ce ta ji.

Bayan fitar sa Goggo ta sauke ajiyar zuciya tana fatan abinda ta ke tunani ba gaskiya ba ne...

Daga masallaci kuwa ya dawo zai shiga ɗakin Goggo, Iya ta ƙwala ma sa kira. Bai sake samun sarari ba sai chan dare. Yana shigowa ya ga T J a ɗakin, ya yi narai narai da fiska yana tambayar Nkiru ko ta ci abinda ya kawo ma ta ta ce ta ci. Ba ta ma ci ba sai da T J ya zo ta nuna ma sa ya ɗau kusan fiye da rabi ya ba wa Goggo ya ce a rabawa 'yan gida. Nkiru kam dabino kaɗai ta ci ba ta ci kilishi da gurasan ba. Shi kuwa T J haka ya haɗa gurasa da kilishi yai ta ci yana addu'ar Allah ya saka wa Muntari, wannan karan yayi abun kai.

"Hamma ina son magana da ita"

T J ya juya ya kalli kan gado Asma'u ta riga ta yi bacci Goggo kuwa ta wuce turakar miji saboda ita ke da girki.

"Ban gane ba"

"Ina son magana da Mary"

Abun ya bashi dariya amma ya dake ya ce "ga ta nan faÉ—i maganar ka"

"Hamma waje za ka bamu, maganar ta mu biyu ne"

T J ya ce " lallai kana da aiki"

Ya cigaba da koyawa Nkiru gaisuwar Fulatanci.
Ganin an maidashi wani shashasha ya sa shi barin ɗakin kamar zai fashe. T J bai kawo komai a ransa ba dan ya ɗauka irin shiriritan ƙanin na sa ne da ya saba. Sai kusan goma ya bar ɗakin...

Washe gari aka yiwa su T J rasuwa dan haka ranan kam gaba É—aya Nkiru ba ta gan shi ba. Duk da ba a na su sashen ba ne amma kusan kaf 'yan gidan sun fita gaisuwa aka bar Nkiru a gida. Ba abinda ke zuciyarta irin tunanin yadda za ta yi ta cigaba da zama a nan ko da dai ba wai kowa ke son ta ba amma T J yana son ta haka Goggo ma na son ta. Idan ta tafi Calabar ta kasa samun kakannin ta fa?. Ko kuma ta je sun mutu ya za ta yi kenan? Wannan tunanin shi ya É—auke ma ta hankali wunin ranan...

***

Jaka ce madaidaiciya ya kawo ma ta ya ce ta shirya kayanta ciki saboda tafiyar su ta jibi. "Ki tabbatar kin shirya komai saboda mantuwa"

"I'm not leaving" ta faÉ—a a hankali. Da sauri ya juyo saboda dama fita zai yi
"What?"

"I'm not leaving" ta sake maimaitawa wannan karan da ɗan ƙarfi. Dawowa yai gabanta ya tsugunna. Zaune ta ke a shimfiɗar ta da ta ke kwana.

Ta girgiza kai ta kasa magana.

"Na san kin fara sabawa da nan amma dole ne mu tafi, na yi alkawarin zan maida ke na kai ki har Calabar..."

"Idan ba mu same su ba fa? Ina zan je? Chief James Asibong ba shi É—aya ba ne a Calabar, tukunna which part of Calabar za mu fara zuwa?"

Tanada gaskiya amma kuma...

"Tunda mu ka haɗu ka ke mun ɗawainiya, kuma ko da mun koma ɗawainiya za ka yi ta yi da ni. Ba na son ka shiga ƙunci saboda ni, ka bari na zauna a nan na nemi aiki idan na tara kuɗi sai na tafi ka ga ko da ban same su ba zan fara sana'a ko kasuwanci da abin da na tara"

"Inkiru..."

"Shekara É—aya, biyu, uku, i dont care, indai za ka amince zan zauna a nan. Zan yi kowani irin aiki ne, kowani iri"

Shiru yai ya rasa mi zai ce.
Ta sa hannunta É—aya a kan hannun sa da ke kan cinyarsa ta ce "please Barkindo"

Ya kalleta cike da mamaki. Ta gyaÉ—a ma sa kai ta ce Pendo ce ta gaya ma ta Kakansa ne ya ke kiran sa da Barkindo shiyasa wani lokaci ta ke ji Goggo na kiran sa da sunan.

Shiru ne ya ratsa ɗakin, ba kuma dan ya rasa abin faɗa ba ne sai dan wani lissafi ya ke yi a ƙwaƙwalwarsa. Mi zai faru idan Nkiru ta cigaba da zama da su?

*ba a fara komai a chronicles of Zaytoonah ba*

*Don samun daman karanta cigaban labarin za a biya 300 ta account number kamar haka:*
3099546325
Firstbank
Azizat Hamza
*ko kuma katin MTN na 300 zuwa ga wannan numbar 08137311900*
Za'a tura Shaidar biya zuwa ga wannan numbar still 08137311900 ko kuma ma dai domin ƙarin bayani za a iya tuntuɓar numban, preferably chat ko text.
*Allah ya ba da ikon biya amin*
2/11/21, 10:04 PM - ****: *Chronicles of*
*...... ...... .......ZAYTOONAH*

https://m.facebook.com/Inside-Arewa-Writers-107691760958755/?ref

𝕀ℕ𝕊𝕀𝔻𝔼 𝔸ℝ𝔼𝕎𝔸 𝕎ℝ𝕀𝕋𝔼ℝ𝕊©
*(Ƙungiyar Nazarin Harshen Hausa)*

Rubutawa.....Azizat
Wattpad@Azi_zat

*Free page*
*6-A love marriage*

Bismillahir Rahmanir Rahim

"Yanzu dan Allah Muntari daga ta musulunta yau sai a fara ma ta zancen aure?. Ni ban goyi bayan haka ba, sannan duk yadda ka ke son auren yarinyar nan ba fa auren dole za a ma ta ba. Idan ta amince za ta aureka fani'ima amma idan ta nuna ɗan uwanka ko wani daban ta ke so to ka ga dole ka haƙura"

Kaman an buga ma sa guduma a tsakiyar ka haka ya ji kalaman Baffah na ƙarshe a ƙwaƙwalwarsa.

"Baffa ban gane É—an uwana ba. Ba dai Hamma Tijjani ka ke nufi ba?"

Baffa yai shiru dan tambayar ta yi kama da renin hankali.

"Baffa idan za a min adalci, tun kan yarinyar nan ta musulunta na ce ina son aurenta ku ka hanani, yanzu da ta musulunta sai ku ce wai idan ta zaɓi Hamma Tijjani sai dai na yi haƙuri. Wannan son kai ne Baffah. Kuma ba zan taɓa yarda da ba. Ina son auren Maryam kuma Wallahi babu wanda ya isa ya hanani aurenta."

"Muntari ni ka ke faɗawa haka? Wannan yarinya tun kafin ta musulunta na ɗauketa amana a gareni, yanzu da ta shigo musulunci kuwa nauyi ya ƙara ƙaruwa mani, marainiya ce kuma na ɗauki amanar kula da ita kamar 'ya'yan da na haifa. Babu wanda zai ma ta auren dole. Tashi ka bani waje"

End of Chapter 10Continue to the next chapter or choose another story below.

More Hausa novels

Browse all books →
Previous Login to Save Next