Ramadan Promo!All users that send a manual request for premium upgrade on sallah day will be granted for 1 month free.
Soyayyanovels
Zaytoonah Part One Complete Hausa Novel
Zaytoonah Part One Complete Hausa Novel
By Azizat
Login to keep your reading position saved.
Book Page Chapters
Zaytoonah Part One Complete Hausa Novel

Zaytoonah Part One Complete Hausa Novel

Author: Azizat
Chapter 129 of 161
About 8 min read
Chapter progress: 0%
Listen Mode
Listen to this chapter using your device voice.
Ready to listen from this chapter.
Free access is active. You can keep reading and download during this access window.

Book chapters

Choose a chapter and continue reading.

Start chapters
Chapter 1 1,689 words Chapter 2 1,523 words Chapter 3 1,583 words Chapter 4 1,696 words Chapter 5 1,682 words Chapter 6 1,693 words Chapter 7 1,594 words Chapter 8 1,673 words Chapter 9 1,663 words Chapter 10 1,668 words Chapter 11 1,678 words Chapter 12 1,698 words Chapter 13 1,687 words Chapter 14 1,699 words Chapter 15 1,656 words Chapter 16 1,634 words Chapter 17 1,681 words Chapter 18 1,675 words Chapter 19 1,655 words Chapter 20 1,613 words Chapter 21 1,669 words Chapter 22 1,655 words Chapter 23 1,671 words Chapter 24 1,650 words Chapter 25 1,677 words Chapter 26 1,696 words Chapter 27 1,598 words Chapter 28 1,699 words Chapter 29 1,694 words Chapter 30 1,659 words Chapter 31 1,683 words Chapter 32 1,309 words Chapter 33 1,691 words Chapter 34 1,697 words Chapter 35 1,553 words Chapter 36 1,588 words Chapter 37 1,682 words Chapter 38 1,680 words Chapter 39 1,677 words Chapter 40 1,649 words Chapter 41 1,700 words Chapter 42 1,698 words Chapter 43 1,676 words Chapter 44 1,625 words Chapter 45 1,633 words Chapter 46 1,675 words Chapter 47 1,693 words Chapter 48 1,668 words Chapter 49 1,688 words Chapter 50 1,647 words Chapter 51 1,653 words Chapter 52 1,568 words Chapter 53 1,689 words Chapter 54 1,699 words Chapter 55 1,669 words Chapter 56 1,578 words Chapter 57 1,564 words Chapter 58 1,660 words Chapter 59 1,694 words Chapter 60 1,415 words Chapter 61 1,653 words Chapter 62 1,690 words Chapter 63 1,685 words Chapter 64 1,618 words Chapter 65 1,652 words Chapter 66 1,674 words Chapter 67 1,687 words Chapter 68 1,699 words Chapter 69 1,644 words Chapter 70 1,698 words Chapter 71 1,691 words Chapter 72 1,671 words Chapter 73 1,689 words Chapter 74 1,679 words Chapter 75 1,677 words Chapter 76 1,678 words Chapter 77 1,655 words Chapter 78 1,683 words Chapter 79 1,696 words Chapter 80 1,700 words Chapter 81 1,694 words Chapter 82 1,697 words Chapter 83 1,692 words Chapter 84 1,668 words Chapter 85 1,554 words Chapter 86 1,666 words Chapter 87 1,677 words Chapter 88 1,694 words Chapter 89 1,667 words Chapter 90 1,700 words Chapter 91 1,670 words Chapter 92 1,670 words Chapter 93 1,655 words Chapter 94 1,640 words Chapter 95 1,607 words Chapter 96 1,668 words Chapter 97 1,659 words Chapter 98 1,689 words Chapter 99 1,675 words Chapter 100 1,614 words Chapter 101 1,610 words Chapter 102 1,700 words Chapter 103 1,683 words Chapter 104 1,657 words Chapter 105 1,698 words Chapter 106 1,700 words Chapter 107 1,695 words Chapter 108 1,656 words Chapter 109 1,683 words Chapter 110 1,699 words Chapter 111 1,699 words Chapter 112 1,641 words Chapter 113 1,696 words Chapter 114 1,626 words Chapter 115 1,695 words Chapter 116 1,691 words Chapter 117 1,698 words Chapter 118 1,645 words Chapter 119 1,673 words Chapter 120 1,691 words Chapter 121 1,635 words Chapter 122 1,694 words Chapter 123 1,689 words Chapter 124 1,688 words Chapter 125 1,673 words Chapter 126 1,692 words Chapter 127 1,686 words Chapter 128 1,697 words Chapter 129 Reading now Chapter 130 1,691 words Chapter 131 1,674 words Chapter 132 1,670 words Chapter 133 1,693 words Chapter 134 1,691 words Chapter 135 1,687 words Chapter 136 1,672 words Chapter 137 1,691 words Chapter 138 1,657 words Chapter 139 1,687 words Chapter 140 1,650 words Chapter 141 1,695 words Chapter 142 1,607 words Chapter 143 1,699 words Chapter 144 1,676 words Chapter 145 1,698 words Chapter 146 1,684 words Chapter 147 1,664 words Chapter 148 1,696 words Chapter 149 1,674 words Chapter 150 1,680 words Chapter 151 1,697 words Chapter 152 1,628 words Chapter 153 1,618 words Chapter 154 1,688 words Chapter 155 1,664 words Chapter 156 1,692 words Chapter 157 1,584 words Chapter 158 1,644 words Chapter 159 1,646 words Chapter 160 1,618 words Chapter 161 1,797 words

Ko da Zaytoonah ta tashi ba ta manta abinda ta gani ba amma kasancewa Justice bai yarda ba ya sa ta yi shiru ta fara tunanin kodai da gasken ne mafarki ta yi. Wunin ranan dai ta yi shi a tsorace ne dan sau ɗaya kawai ta sauƙa ƙasa.

Kwana biyu ba abinda ya kuma faruwa dan haka ta share abin kamar bai faru ba.

Yau kwana huÉ—u da faruwan wancan abin. Tana kitchen tana aikin abinci. Ita kaÉ—ai ne a gidan sai Atika wacce ba ta san ma inda ta shiga ba, duk da dai tun sanda Justice ya ma ta faÉ—a ta ke kaffa-kaffa da Zaytoonah amma ita Zaytoonan ba ta sake jiki da ita ba, aiki idan ba ya zama dole ba ba ta sakata.

Bayan ta gama komai ta ɗauka tray da ta jera kayan abinci ta wuce da shi sama, bayan ta gama shirya mu su abincin ne ta wuce ɗakinta dan ta yi wanka. Any moment from now Galadima zai iya dawowa. Bayan ta shiga banɗaki mamaki ya kamata ganin ba ta ga komai ba. 'Har yanzu' ta furta a ƙasan ranta. Bai cika ma ta latti ba, sai dai wannan kwana huɗu kenan tana zuba ido amma ba ta ga alamar sa ba.
Ta gama wanka ta fito sanye da bathrobe dogo kalar Madara.
A stool da ke gaban dressing mirror ɗin ta ta zauna tana ƙoƙarin shafa mai. Kallon kanta ta yi jikin madubi ta yi murmushi gaskiyar Mommy ne da ta ce ma ta tana glowing kwana biyun nan.

Ƙirjinta ne ya buga yayinda numfashin ta ya fara fita da sauri-sauri jikinta na rawa ta fara juyawa a hankali dan ta tabbatar da abinda ta ke gani a jikin madubi ko dai da gaske ɗin yana bayanta ne. Ihu ta saka ganin Ben tsaye a ta bayanta.

"Zuhayr, Zuhayr help, help..." ta ke ta faɗa bayan ta takure jikin bango, jikinta sai ƙyarma ya ke.

Da gudu Justice ya hauro sama dai dai ya iso ƙofar ɗakin ya ga Atika ma ta fito daga ɗakin Ghazala.

"Yallaɓai"
Bai kulata ba ya shige É—akin.
Har lokacin Zaytoonah sai sunbatu kawai ta ke yi a waje É—aya.
Yana zuwa rungumeta yai ya na kiran sunan ta.
Jin muryan sa ya sa ta ƙara ƙanƙameshi tana kiran "Zuhayr i know you'll come. Na san ba za ka taɓa bari Ben ya kashe ni ba"

Ajiyar zuciya Galadima ya sauke yana tunanin akwai babbar matsala...

Maganar dai irin ta ranan ce wai Ben ta gani a cikin É—akinta, Abinda ta gaya ma sa kenan bayan ta samu nitsuwa. Shi dai ya shigo bai ga komai ba amma ita ta dage Ben ya shigo É—akinta har da nuna ma sa inda ya tsaya.
Ƙoƙarin kwantar ma ta da hankali yai amma ina ta ƙi sauraren sa ita wai dole sai ya yadda da abinda ta gani.

Abin har ya so ba shi haushi amma da ya tuna cewa ita ɗin ba cikakkiyar lafiya gareta ba sai ya cigaba da lallashinta har ta haƙura akan ba ta ga Ben ba...

Washegari da safe ya É—auketa su ka je ganin wani Psychiatrist Doctor. Galadima ne ya ma sa bayanin gameda ciwon na ta da kuma yadda ya ke tashi idan ta tsinci kan ta a cikin duhu amma yanzu kwana biyun nan ba a duhu ma ya ke tashi ba.
Wasu tambayoyi yai wa Zaytoonah tareda cewa yana so ya ga result na test da diagnosis da aka ma ta a chan Madina da kuma America lokacin da ciwon ya fara. Da ke ba su taho da shi ba Galadima ne ya koma gida bayan Zaytoonah ta gaya ma sa inda ta ajiye su.

A É—an tambayoyin da Likitan yai wa Zaytoonah ya fahimci tabbas idan da duhu ke tada ciwon to yanzu akwai abinda ta ke gani da ke tunzura ta har ciwon ya tashi.
Bayan Galadima ya kawo takardun Likitan ya kai kusan minti talatin yana dubawa kafin daga baya yai wa Galadima bayani bayan ya ce Zaytoonah ta basu waje.

"Ranka shi daɗe gaskiya matar ka na buƙatar kulawa sosai. Dole a gano mi ta ke gani ya ke sa ta tunanin ta ga shi wancan Ben ɗin, ko dai tana ganin hoton sa ko kuma wani abu mai kama da shi ko kuma wani abu dai da ya ke da nasaba da shi. Idan aka kawar da wannan zai kawo ma ta sauƙi amma idan ta cigaba da haka ina tsoron za a koma gidan jiya"

Galadima ya kalleshi cikin rashin fahimta.

"Report É—in da na karanta ya nuna cewa Zaytoonah ta yi hauka a baya"

"Hauka!"

"Ka kwantar da hankalin ka Yallaɓai ba irin hauka ta yawo a titi ana tsince-tsince ba, ina nufin hauka saboda damuwa, a yadda su ka rubuta alokacin ba ta iya tuna cewa ta haihu balle ma ta kula da 'ya'yanta. Tana kallon duk wani bature saurayi marar gashin baki ko gemu a matsayin Ben. Ta taɓa attacking wani nurse namiji a Asibiti akan saita kashe shi saboda kallon Ben ta ke ma sa. Ko da ya ke ta samu lafiya daga baya amma har yanzu da saura. Idan ta cigaba da tsorata haka ina tsoron za a koma gidan jiya, za ta dinga kallon kowa a matsayin Ben"

"Innalillahi wa Inna Ilaihi Raji'oun" Galadima ya furta yana sauke ajiyar zuciya.

"Insha Allah za ta samu lafiya" Likitan ya faÉ—a...

***

"Zaytoonah ki saurareni Dan Allah..."

"Farha ba wanda ya yarda da ni a nan kema ba za ki yarda ba. Ben na gani, Ben. He wanted to kill me, kin manta sau nawa yai yunƙurin kashe ni. Believe me Farha"

Idon Farha ya ciko da hawaye saboda tausayin ƙawarta.

"Zaytoonah Ben is dead. An halbeshi ya mutu, babu ghost a musulunci you of all people should know that"

"Kina cewa na haukace kenan, haka Ghazala ma ta faÉ—a wai na fara hauka"

"Zan zo Nigeria, zan zo na duba ki, Zaytoonah kin ji"

Ba tare da ta katse kiran ba ta rufe Laptop É—in da su ke video call É—in da shi.

Ba wanda ya yarda da ita, har Mommy ma ba ta yarda ba. 'Nan gaba idan na ganshi kashe shi zan yi kafin ya kashe ni' ta furta a fili...

Mommy da Galadima sun tsaida magana akan za a sake kai Zaytoonah wajen Likitan ta. Tun rana na uku da Zaytoonah ta sake firgita saboda Ben da ta gani Galadima ya kama hanya ya tafi Zaria inda ya sanar ma Mommy duk abinda ke faruwa. Bayan ya dawo, Mommy da kanta ta zo Abujan ta yi kwana biyu inda ta yi ta ƙoƙarin fahimtar da Zaytoonah cewa Ben ya mutu, ba shi ta ke gani ba, sai dai har ta tafi ba wai Zaytoonan ta yarda ba ne.

Wannan ya sa Mommy ta yiwa Galadima magana akan tana so ta kai Zaytoonah wajen Likitan da ya duba ta da farko, shima kuma ya amince da hakan...

**
Ghazala ce ta shigo ɗakin Zaytoonah ta ajiye mutum-mutumin Ben a tsakiyar ɗakin, za ta fita kenan ta ji kamar za a buɗe ƙofa, da sauri ta yi hanyar banɗaki saboda ba ta yi tunanin Zaytoonan za ta shigo yanzu ba.

Zaytoonah na buɗe ɗakin ta kalli Ben a tsakiyar ɗakinta, irin shigar da ta ke ganin sa da shi kullum ne ta gani yanzu. Ta ɗan tsorata kam amma da ke bayansa ta gani ba fiskarsa ba sai ba ta firgita sosai ba. Kulle ƙofar ta yi ta fita da gudu dan ta kira su Maman Tope da su Raziya da ke ƙasa, wannan karan so ta ke kowa ya ga Ben ɗin da ta ke gani a ɗakinta kullum. Sai dai ba ta ankara ba ta ture Falaq da ke bakin stairs.
Tsayawa ta yi chak ganin Falaq tana gangarawa ƙasa.

Raziya da Suhailah su ka yi wajen da gudu jin ihun Falaq É—in.

Zaytoonah ta tsaya chak ta kasa motsawa tana hango su Raziya na kuka suna jijjiga Falaq.

Maman Tope ta fito daga kitchen jin kukan Yaran. Ta kama salati ganin Falaq a sume. Har Ghazala ta zo ta wuceta ba ta iya motsawa ba tana kallon yadda su ke ta kuka...

Suna zuwa Asibiti aka admitting Falaq wacce har lokacin ba ta farfaÉ—o ba. Tuni Ghazala ta kira Galadima ta faÉ—a mishi ai Zaytoonah ta turo Falaq daga stairs gatanan kwance a Asibiti rai a hannun Allah. A rikice Justice ya baro office ya taho Asibitin inda ya samesu sun yi jugum suna jiran Likita ya fito. A nan ne kuma Ghazala ta sake tabbatar ma sa da cewa Zaytoonah ne ta turota. Ganin Raziya ba ta ce a'a ba ya sa jikinsa yai sanyi dan tunanin sa abinda Likita ya faÉ—a ne ya ke shirin faruwa.

Bayan Likita ya fito ne ya gaya mu su halin da Falaq ke ciki ta samu karaya a hannu sannan kanta ya bugu sosai kuma suna tunanin kunnen ta ɗaya ya taɓu dan haka ba lallai ta dinga ji sosai ba, amma sai ta farfaɗo kafin su tabbatar. Allah ma ya taimaka ba bu wani bleeding ta cikin kan ta.
Kusan ƙarfe bakwai na dare ya maida Raziya gida tareda son duba halin da Zaytoonah ke ciki. Abin mamaki da su ka je a falon ƙasa su ka tadda Zaytoonah tana jiran Galadima yana zuwa ta fara ma sa maganar ai yau kam za ta tabbatar ma sa da gaskiyarta dan Ben na ɗakin ta. Bai musa ba ya bita har ɗakin sai dai tana buɗe ƙofa sai wayam ba komai.

"Ina Ben É—in ya ke?"

"Na gan shi fa, ina ga guduwa yai. Believe me"

"Falaq na Asibiti, Raziya sun ce ke kika turota, miyasa?"

"Ina son gaya mu su cewa Ben na É—akina ne, ni ban san tana wajen ba. Ka yarda da ni"
Girgiza kai kawai yai ya wuce É—akin sa dan ya san ba laifinta ba ne, dole ya ma ta uzuri...

End of Chapter 129Continue to the next chapter or choose another story below.

More Hausa novels

Browse all books →
Previous Login to Save Next