Ramadan Promo!All users that send a manual request for premium upgrade on sallah day will be granted for 1 month free.
Soyayyanovels
Zaytoonah Part One Complete Hausa Novel
Zaytoonah Part One Complete Hausa Novel
By Azizat
Login to keep your reading position saved.
Book Page Chapters
Zaytoonah Part One Complete Hausa Novel

Zaytoonah Part One Complete Hausa Novel

Author: Azizat
Chapter 37 of 161
About 8 min read
Chapter progress: 0%
Listen Mode
Listen to this chapter using your device voice.
Ready to listen from this chapter.
Free access is active. You can keep reading and download during this access window.

Book chapters

Choose a chapter and continue reading.

Start chapters
Chapter 1 1,689 words Chapter 2 1,523 words Chapter 3 1,583 words Chapter 4 1,696 words Chapter 5 1,682 words Chapter 6 1,693 words Chapter 7 1,594 words Chapter 8 1,673 words Chapter 9 1,663 words Chapter 10 1,668 words Chapter 11 1,678 words Chapter 12 1,698 words Chapter 13 1,687 words Chapter 14 1,699 words Chapter 15 1,656 words Chapter 16 1,634 words Chapter 17 1,681 words Chapter 18 1,675 words Chapter 19 1,655 words Chapter 20 1,613 words Chapter 21 1,669 words Chapter 22 1,655 words Chapter 23 1,671 words Chapter 24 1,650 words Chapter 25 1,677 words Chapter 26 1,696 words Chapter 27 1,598 words Chapter 28 1,699 words Chapter 29 1,694 words Chapter 30 1,659 words Chapter 31 1,683 words Chapter 32 1,309 words Chapter 33 1,691 words Chapter 34 1,697 words Chapter 35 1,553 words Chapter 36 1,588 words Chapter 37 Reading now Chapter 38 1,680 words Chapter 39 1,677 words Chapter 40 1,649 words Chapter 41 1,700 words Chapter 42 1,698 words Chapter 43 1,676 words Chapter 44 1,625 words Chapter 45 1,633 words Chapter 46 1,675 words Chapter 47 1,693 words Chapter 48 1,668 words Chapter 49 1,688 words Chapter 50 1,647 words Chapter 51 1,653 words Chapter 52 1,568 words Chapter 53 1,689 words Chapter 54 1,699 words Chapter 55 1,669 words Chapter 56 1,578 words Chapter 57 1,564 words Chapter 58 1,660 words Chapter 59 1,694 words Chapter 60 1,415 words Chapter 61 1,653 words Chapter 62 1,690 words Chapter 63 1,685 words Chapter 64 1,618 words Chapter 65 1,652 words Chapter 66 1,674 words Chapter 67 1,687 words Chapter 68 1,699 words Chapter 69 1,644 words Chapter 70 1,698 words Chapter 71 1,691 words Chapter 72 1,671 words Chapter 73 1,689 words Chapter 74 1,679 words Chapter 75 1,677 words Chapter 76 1,678 words Chapter 77 1,655 words Chapter 78 1,683 words Chapter 79 1,696 words Chapter 80 1,700 words Chapter 81 1,694 words Chapter 82 1,697 words Chapter 83 1,692 words Chapter 84 1,668 words Chapter 85 1,554 words Chapter 86 1,666 words Chapter 87 1,677 words Chapter 88 1,694 words Chapter 89 1,667 words Chapter 90 1,700 words Chapter 91 1,670 words Chapter 92 1,670 words Chapter 93 1,655 words Chapter 94 1,640 words Chapter 95 1,607 words Chapter 96 1,668 words Chapter 97 1,659 words Chapter 98 1,689 words Chapter 99 1,675 words Chapter 100 1,614 words Chapter 101 1,610 words Chapter 102 1,700 words Chapter 103 1,683 words Chapter 104 1,657 words Chapter 105 1,698 words Chapter 106 1,700 words Chapter 107 1,695 words Chapter 108 1,656 words Chapter 109 1,683 words Chapter 110 1,699 words Chapter 111 1,699 words Chapter 112 1,641 words Chapter 113 1,696 words Chapter 114 1,626 words Chapter 115 1,695 words Chapter 116 1,691 words Chapter 117 1,698 words Chapter 118 1,645 words Chapter 119 1,673 words Chapter 120 1,691 words Chapter 121 1,635 words Chapter 122 1,694 words Chapter 123 1,689 words Chapter 124 1,688 words Chapter 125 1,673 words Chapter 126 1,692 words Chapter 127 1,686 words Chapter 128 1,697 words Chapter 129 1,660 words Chapter 130 1,691 words Chapter 131 1,674 words Chapter 132 1,670 words Chapter 133 1,693 words Chapter 134 1,691 words Chapter 135 1,687 words Chapter 136 1,672 words Chapter 137 1,691 words Chapter 138 1,657 words Chapter 139 1,687 words Chapter 140 1,650 words Chapter 141 1,695 words Chapter 142 1,607 words Chapter 143 1,699 words Chapter 144 1,676 words Chapter 145 1,698 words Chapter 146 1,684 words Chapter 147 1,664 words Chapter 148 1,696 words Chapter 149 1,674 words Chapter 150 1,680 words Chapter 151 1,697 words Chapter 152 1,628 words Chapter 153 1,618 words Chapter 154 1,688 words Chapter 155 1,664 words Chapter 156 1,692 words Chapter 157 1,584 words Chapter 158 1,644 words Chapter 159 1,646 words Chapter 160 1,618 words Chapter 161 1,797 words

Shekaru shabakwai da su ka wuce Muntari ya tafi Lagos. Aiki ya ke tuƙuru shi a ganin sa hakan zai sa ya samu kuɗi. Duk wani aikin wahala indai akwai kuɗi to yana nan. Shekaru biyu yai yaga bai wani tara abin a zo a gani ba, har yana son jona aikin wani abokin shi wato sata sai kuma labari ya chanja lokacin da ya haɗu da Madam Talatu.
Madam Talatu tsohuwar karuwa ce da ta yi tashe a zamaninta. 'Yar Kafanchang ne da ke Jihar Kaduna, auren dole za a ma ta ta gudu wai ta shiga duniya. A garin Lagos ta tsinci kan ta bayan doguwar tafiya da ta yi. Bayan ta samu masauki a gidan karuwai ta shiga karuwanci, ba ta da wani kyaun fiska amma akwai ta da kyaun diri, irin wanda ke ɗauke hankalin duk wanda yai tozali da ita. Cikin loƙaci kaɗan ta zama ɗaya daga cikin manya-manyan karuwai da ake ji da su a Lagos, wanda Turawa ke ɗauka, 'yan siyasa da manya manyan sojoji ke rububi. Daga gidan karuwai ta ɓalle ta samu gidan kanta ta zauna wanda cikin kuɗaɗen da ta tara ne ta siya da shi. Ta yi karuwanci na shekaru talatin kafin ta yi retire ta bazama kasuwanci, dama tana ɗan taɓa kasuwancin amma yanzu da ta dena karuwanci sai ta riƙe kasuwanci zallah.
To abu ne da ta jima tana tatsan kuɗi daga mazan da ba sa iya kama abun su, dan haka ba ƙaramin maƙudan kuɗi gareta ba. Tana da manya-manyan shaguna da kuma hannun jari.
Bayan ta bar karuwanci ta kan dai nemi yara ƙanana wanda za su biya ma ta buƙata lokaci zuwa lokaci ita kuma ta ba su kuɗi.
Lokacin da ta haÉ—u da Muntari tana shekaru Arba'in da takwas a duniya. Ta gan shi ne lokacin da su ka zo sauke ma ta kaya a É—aya daga cikin shagunan ta. Nan da nan É—an farin Bafulatanin ya burgeta. Bayan ta nemi ganin shi ta ce ya zo washegari za ta bashi aiki. Ganin kuÉ—in da za a dinga bashi a wata ya ninka wanda ya ke samu a da ya sa shi amincewa da aikin.
Yana aiki da Madam Talatu ita kuma tana daɗa lura da shi, bayan wata biyu ta fito ma sa da maitar ta fili, ya ce baya so. Ta sanar da shi kuɗin da za ta dinga bashi duk wata idan ya amince amma still bai amince ba. Da ta dameshi sai ya ajiye aikin da ya ke yi ya kama gaban sa. Bayan ya tafi ta kasa haƙuri da shi ta neme shi ya dawo tareda ma sa alkawarin aure ta ke so su yi kuma indai ya amince to za ta ba shi ɗaya daga cikin shagunan ta, da yai lissafi sai ya ga arziƙi ne ya zo ma sa cikin sauƙi. Auren shekara goma su ka yi alƙawarin za su yi da shi kafin nan zai saketa ya kama gaban sa.
Bayan sun yi Aure kuwa ta bashi ɗaya daga cikin shagunan ta ya zama shi ke sarrafa shi. Ta sa mishi ido sosai akan ko zai ci amanarta kaman sauran ƙananun samarin da ta ke yi sai taga shi Muntari ba ruwan sa da mata. Daga baya ta tambayeshi dalilin zuwansa Lagos ya ce ma ta ya zo neman kuɗi ne saboda matar da ya ke so.
A mafiya yawancin lokutan da ya ke saduwa da ita yana ambatun ta da Maryam hakan ya sa ta san ba ƙaramin so ya kewa wannan Maryam ɗin ba.

Shi kuwa Muntari saboda a dole ya ke tarayya da Madam Talatu ya sa ya fara shan giya da sigari saboda ya dinga É—auke ma sa hankali a duk lokacin da ya ke tarayya da ita, hakan ya sa ya ke ganin Maryam a tareda shi a lokacin da ya ke tare da Madam Talatu.

Cikin shekaru tara da su ka yi tare yana aika kaya Kano ana sayar ma sa da shi hakan ya sa kasuwancin sa ya haɓaka sosai ga shi ba shi da matsalar komai, cin sa da shan sa da suturan sa duk Madam Talatu ce.

Bayan shekara tara da auren su MadamTalata ta fara jinya ashe cervical cancer ne. Ana magani ana jigilar asibiti amma abin ya mata mugun kamu saboda ba a gane shi ke damunta ba da wuri. Ganin fa kullum jigilar Asibiti ake ya sa Madam Talatu ta fara tunanin iyayenta da 'yan uwanta da ta baro shekaru ma su yawa da su ka wuce. A da ƙasar waje Muntari zai fita da ita ta ce ta fasa ya kaita Kafanchang za ta nemi iyayenta su gafarta ma ta. Da su ka je ta samu mahaifinta yana nan amma mahaifiyarta ta jima da rasuwa. Yayyenta da ƙannenta da ba ta san su ba kafin ta tafi duk sun girma suna da iyali. Anyi koke-koke kafin daga baya aka karɓeta hannu bibbiyu.
Saura wata biyar shekara goman auren su ta cika Madam Talatu ta ce Muntari ya saketa saboda tana son zama da 'yan uwanta zuwa lokacin da za ta mutu.
Cikin kaso ɗari na dukiyarta kusan kashi talatin ta ba wa Muntari wanda shima a lokacin side business ɗin sa ya haɓaka sosai. Sauran dukiyarta kuwa 'yan uwanta ta rabawa sannan aka gina Makaranta da Asibiti a ƙauyen su da ke Kafanchang. Shekara ɗaya bayan rabuwar su da Muntari ta rasu.

Shi kuwa Muntari tunda su ka rabu da Madam Talatu ya fara ƙoƙarin yadda zai dawo da kasuwancin sa Kano saboda ya kasance kusa da masoyiyar sa. A shekaran ne kuma ya tafi Umara dan ya fito a Alhaji ya bawa kowa mamaki.
Tunda kuÉ—i su ka fara zama ma sa ya fara bibiyan labarin É—an uwansa Tijjani da kuma halin da masoyiyar sa ke ciki. Bai sha wahalar samun information da ya ke so ba. Nan ta ke ya sayi fili a anguwar ya fara gini, ya so ace kusa da gidan Maryam yai ginin amma bai samu fili a wajen ba, duk da haka tunda anguwa É—aya ne ba shi da matsala.

Wannan kenan

***

Assembly ake yi da sassafiyar ranan Litinin. Kowa da ka gani a cikin uniform za ka gan shi tsaf-tsaf da shi.
Kamar kullum a layin na su ita ce ƙarshe saboda ba ta son tsayiwa a gaba ko a tsakiya 'yan ajin na su su dinga tsokalar ta.

"Zaytu Mama kin yi assignment É—in Maths kuwa?" wata yarinya da ke gaban Zaytoonah ta faÉ—a.
Nuratu kenan wacce duk cikin 'yan matan ajin na su ita ce su ke É—an mutunci, itama ayi faÉ—a a shirya ne.
Anguwar su ɗaya ne kuma Islamiyya ɗaya su ke zuwa hakan ya sa su ka ɗan shaƙu.

Sai da ta haɗiyi baƙin cikin da ya taso ma ta sannan ta ce " na yi" ta tsani kalmar Maman nan da su ke alaƙantata da shi. Duk cikin sunannakin da su ke kiranta ba wanda ya fi tsaya ma ta a rai irin Maman aji ko Zaytu Mama da su ke ce ma ta.

"Za ki bani na kwafa dan Allah"

Shiru ta yi ba ta amsa ma ta ba.
Bayan an gama assembly su ka wuce aji. Tana zuwa kuwa Nuratu ta tsareta sai da ta bata notebook É—in ta na Maths.
Nuratu na cikin kwafa sai ga Zaliha ma ta leƙo kai ta fara kwafa. Kan kace me duk waɗanda ba su yi assignment ɗin ba sun yiwa desk ɗin su Zaytoonah rumfa. Zaytoonah na gefe ta cika ta yi fam, ba dama ta yi assignment ita ɗaya musamman ma dai idan Maths ne.
A haka za su kwafi assignment É—in ta amma hakan ba zai hana su dinga tsokanarta ba.

Wasu ba su gama kwafa ba ma Mr Isaac Maths teacher É—in su ya shigo saboda shi su ke da shi darasin farko.
Bayan ya gama darasin ranan ya tattara Assignment É—in ya tafi da shi dan ya yi marking a staff room.

Ko da ya je sai ya ga kusan duk matan class É—in sun cinye Assignment É—in bayan ya san acikin matan Ajin Zaytoonah, Kabirat da Felicia su kaÉ—ai ne su ka iya Maths sosai, su ke kuma fahimtar darussan sa. Bayan ya gama marking É—in ne ya je class ya nemi izinin Malamin English É—in su a kan yana son ganin Tijjani Zaytoonah.

A staff room ta sameshi. Faɗa Mr Isaac ya fara ma ta akan ta ya za ta ba da assignment ɗin ta a kwafa. Ba ta da ta cewa tunda ba iya magana ta ke mu su ba. Daga ƙarshe ya ce duk lokacin da ta yi assignment ya ga irin na ta a wajen wata sai ya ma ta bulala. Bayan ya gama faɗan ne ya ba ta books ɗin ya ce ta je ta raba a class.
Tafiya ta ke yi É—auke da litattafan 'yan ajin su idon ta cike da hawaye.

She wasnt like this before, tana da rigima tanada ƙiriniya amma kuma cikin ƙanƙanin lokaci ta chanja. Ba komai ne ya chanja ta ba face yadda mutane ke ma ta magana akan ƙibanta. There are days da ta ke cewa ba za ta kuma zuwa school ba amma Mommy sai ta korata dole ta je. There are days da ta ke raba dare tana kuka duk dan saboda wata kalma da wani ko wata ya ma ta. A da ba ta ɗaukan abun da zafi amma a hankali-a hankali abun ya fara damunta. Ta kai ko kallonta ka yi sai ta ga kamar kana judging ɗin ƙibanta ne.

Ta sani ƙiba halittanta ne tunda mommyn ta ma na da ƙiba, but kamar yadda Mommy ke yawan faɗa shine ta bari ciye-ciyen ta ya sa ƙiban ya zama unhealthy.

"Shikenan dan inada ƙiba ba zan ci kayan daɗi ba" amsar ta kenan a mafiya yawancin lokutan da Mommyn ta ma ta magana akan ta rage ciye-ciye.

Da karfin hali ta ke zuwa makaranta saboda yadda kowacce rana ke zuwa ma ta da sabbin salo. Suna kam da su na tabo a jikin mutum da duk jikinta ya nuna.

End of Chapter 37Continue to the next chapter or choose another story below.

More Hausa novels

Browse all books →
Previous Login to Save Next