Ramadan Promo!All users that send a manual request for premium upgrade on sallah day will be granted for 1 month free.
Soyayyanovels
Zaytoonah Part One Complete Hausa Novel
Zaytoonah Part One Complete Hausa Novel
By Azizat
Login to keep your reading position saved.
Book Page Chapters
Zaytoonah Part One Complete Hausa Novel

Zaytoonah Part One Complete Hausa Novel

Author: Azizat
Chapter 67 of 161
About 8 min read
Chapter progress: 0%
Listen Mode
Listen to this chapter using your device voice.
Ready to listen from this chapter.
Free access is active. You can keep reading and download during this access window.

Book chapters

Choose a chapter and continue reading.

Start chapters
Chapter 1 1,689 words Chapter 2 1,523 words Chapter 3 1,583 words Chapter 4 1,696 words Chapter 5 1,682 words Chapter 6 1,693 words Chapter 7 1,594 words Chapter 8 1,673 words Chapter 9 1,663 words Chapter 10 1,668 words Chapter 11 1,678 words Chapter 12 1,698 words Chapter 13 1,687 words Chapter 14 1,699 words Chapter 15 1,656 words Chapter 16 1,634 words Chapter 17 1,681 words Chapter 18 1,675 words Chapter 19 1,655 words Chapter 20 1,613 words Chapter 21 1,669 words Chapter 22 1,655 words Chapter 23 1,671 words Chapter 24 1,650 words Chapter 25 1,677 words Chapter 26 1,696 words Chapter 27 1,598 words Chapter 28 1,699 words Chapter 29 1,694 words Chapter 30 1,659 words Chapter 31 1,683 words Chapter 32 1,309 words Chapter 33 1,691 words Chapter 34 1,697 words Chapter 35 1,553 words Chapter 36 1,588 words Chapter 37 1,682 words Chapter 38 1,680 words Chapter 39 1,677 words Chapter 40 1,649 words Chapter 41 1,700 words Chapter 42 1,698 words Chapter 43 1,676 words Chapter 44 1,625 words Chapter 45 1,633 words Chapter 46 1,675 words Chapter 47 1,693 words Chapter 48 1,668 words Chapter 49 1,688 words Chapter 50 1,647 words Chapter 51 1,653 words Chapter 52 1,568 words Chapter 53 1,689 words Chapter 54 1,699 words Chapter 55 1,669 words Chapter 56 1,578 words Chapter 57 1,564 words Chapter 58 1,660 words Chapter 59 1,694 words Chapter 60 1,415 words Chapter 61 1,653 words Chapter 62 1,690 words Chapter 63 1,685 words Chapter 64 1,618 words Chapter 65 1,652 words Chapter 66 1,674 words Chapter 67 Reading now Chapter 68 1,699 words Chapter 69 1,644 words Chapter 70 1,698 words Chapter 71 1,691 words Chapter 72 1,671 words Chapter 73 1,689 words Chapter 74 1,679 words Chapter 75 1,677 words Chapter 76 1,678 words Chapter 77 1,655 words Chapter 78 1,683 words Chapter 79 1,696 words Chapter 80 1,700 words Chapter 81 1,694 words Chapter 82 1,697 words Chapter 83 1,692 words Chapter 84 1,668 words Chapter 85 1,554 words Chapter 86 1,666 words Chapter 87 1,677 words Chapter 88 1,694 words Chapter 89 1,667 words Chapter 90 1,700 words Chapter 91 1,670 words Chapter 92 1,670 words Chapter 93 1,655 words Chapter 94 1,640 words Chapter 95 1,607 words Chapter 96 1,668 words Chapter 97 1,659 words Chapter 98 1,689 words Chapter 99 1,675 words Chapter 100 1,614 words Chapter 101 1,610 words Chapter 102 1,700 words Chapter 103 1,683 words Chapter 104 1,657 words Chapter 105 1,698 words Chapter 106 1,700 words Chapter 107 1,695 words Chapter 108 1,656 words Chapter 109 1,683 words Chapter 110 1,699 words Chapter 111 1,699 words Chapter 112 1,641 words Chapter 113 1,696 words Chapter 114 1,626 words Chapter 115 1,695 words Chapter 116 1,691 words Chapter 117 1,698 words Chapter 118 1,645 words Chapter 119 1,673 words Chapter 120 1,691 words Chapter 121 1,635 words Chapter 122 1,694 words Chapter 123 1,689 words Chapter 124 1,688 words Chapter 125 1,673 words Chapter 126 1,692 words Chapter 127 1,686 words Chapter 128 1,697 words Chapter 129 1,660 words Chapter 130 1,691 words Chapter 131 1,674 words Chapter 132 1,670 words Chapter 133 1,693 words Chapter 134 1,691 words Chapter 135 1,687 words Chapter 136 1,672 words Chapter 137 1,691 words Chapter 138 1,657 words Chapter 139 1,687 words Chapter 140 1,650 words Chapter 141 1,695 words Chapter 142 1,607 words Chapter 143 1,699 words Chapter 144 1,676 words Chapter 145 1,698 words Chapter 146 1,684 words Chapter 147 1,664 words Chapter 148 1,696 words Chapter 149 1,674 words Chapter 150 1,680 words Chapter 151 1,697 words Chapter 152 1,628 words Chapter 153 1,618 words Chapter 154 1,688 words Chapter 155 1,664 words Chapter 156 1,692 words Chapter 157 1,584 words Chapter 158 1,644 words Chapter 159 1,646 words Chapter 160 1,618 words Chapter 161 1,797 words

Haka su ka tafi yana ma ta taÉ—i gameda abinda ya faru a office. Maganar Ben da ya kawo ne ya sa ta ji zuciyar ta yayi dum. Chan ta kalleshi ta ce "ni kam Ben ba shi da budurwa ne? Yaushe zai yi aure?"

Zuhayr yai dariya yace "miyasa ki ka tambaya?"

"Kawai dai na ga kamar ya tsufa ne"

"This is America, kowa da ra'ayin sa. He's probably waiting for the perfect girl"

A zuciyar ta tace "Or the perfect guy ba"

***

Tana wanka a banÉ—aki kawai sai wuta ya É—auke. Innalillahi ta furta a zuciyarta ta fara lalube har ta fito daga banÉ—akin, ta gwada kunna switch É—in banÉ—akin amma bai yi ba shiyasa kawai ta fito.
Ɗakin ma ba wuta dan haka ta fara ƙoƙarin zuwa wajen gado saboda ta lalubo wayarta ta kunna sai kuma wutan ya dawo.

"Af ƙila matsala aka samu" ta furta tareda juyawa za ta koma banɗakin, sai dai kuma tana buɗe ƙofa wutan ya sake ɗaukewa, ta juyo da sauri ƙirjinta na bugawa da ƙarfi-ƙarfi ta fara tafiya a hankali dan ta isa wajen gado ta lalubo wayarta, wannan karan ko da ace an maida wutar dole ta kunna fitilar wayarta. Ta lalubo wayar ta kunna sai kuma aka sake dawo da wutan.
Ta san Zuhayr baya gida amma kuma ai akwai wasu ma'aikata a gidan, idan ma matsala aka samu na wutan gara ta fita ta ji, dan haka ta nemo jallabiyarta baƙa ta saka ta ta buɗe ƙofa ta fita still wayarta a hannu amma ta kashe torchlight ɗin tunda akwai wuta.
Tana fitowa ta kai tsakiyar stairs sai aka kashe wutan.

"Zuhayr, Zuhayr. Ben, Benedict, Chef Green" haka ta dinga kiran sunan su amma shiru. Ta rasa ina za ta je ɗaya, ta koma ɗaki ne ko ta sauka ƙasa ta fita waje. Ta samu ta kunna hasken wayarta amma still saboda duhun daya ƙaraɗe wajen sai ya zamana ba ta gani da kyau.

Tana sa ƙafa za ta taka stairs ɗin ta ji an dafa ƙafaɗarta wanda ya sa tayi mutuwar tsaye a wajen.

"Zu Zuhayr"

"I'll kill you" aka faÉ—a da wata munafukar murya sannan aka hankaÉ—a ta.

Bayan minti goma da faÉ—owarta sai ga Zuhayr ya shigo gidan, ya zo zai haura sama ya kalli Zaytoonah kwance a wajen ta suma hakan ya sa shi yin kanta da sauri...

***

Sati biyu ta yi jinya a asibiti kafin aka sallameta. Wannan karan da ta yiwa Zuhayr bayanin abinda ya faru bai yi wasa da maganar ba nan da nan aka fara investigation amma ba a gano komai ba daga ƙarshe aka saka cctv camera a lungu da saƙo na gidan.
Lokacin da ta ma sa maganar tana zargin Ben da abinda ya faru bai yarda da hakan ba sai ma kwantar ma ta da hankali da yai da cewa tun suna yara ya san Ben kuma shi mutum ne da ba zai taɓa iya aikata mummunan abu irin haka ba.
Ta yi shiru da zancen sai da su ka koma gida ta sake tada maganar tareda faÉ—a ma sa duk abinda Linda ta gaya ma ta dama Voicemail É—in da ta saurara na Alinah.

"Ki kwantar da hankalin ki Zaytoon, har yanzu ba ki da lafiya. Linda kuma zanyi magana da ita da kaina.

Fashe ma sa tayi da kuka saboda yadda bai É—auki maganar Ben serious ba.

"Lokacin da ka aureni ka min alƙawarin kula da ni kamar ƙanwar ka, anyi ƙoƙarin kasheni har sau biyu amma ba abinda ka yi. Ben is gay, sonka ya ke yi kuma..."

"What are you saying" ya faɗa yana kama hannunta. Ta yafce hannun da ƙarfi ta ce " ni dai ka barni, kuma daga gobe tafiyata zan yi tunda ba ka damu da rayuwata ba, kafi damuwa da Ben"

"Zaytoon, Benedict is my brother ki daina zargin sa. He will never hurt you"

"Shikenan idan ya kasheni ba ka da asara tunda ba sona ka ke ba, amma dan Allah kafin ya kasheni ka barni na koma wajen Mommy na. Na fasa zama a nan, na fasa karatun" ta ƙarisa maganar tana kuka.

Kissing ɗin goshinta yai ya ce " ba abinda zai sameki, ba wanda zai kasheki matuƙar ina raye. Indai akan abinda ya faru ne zan ƙara saka matakan tsaro a gidan nan sannan zan kawo ma'aikata da za su dinga kwana da ke"

Yana ganin Zuhayr ya rungume Zaytoonah ya tura mu su ƙofa ya bar wajen. Ya ji komai, kuma ya sani akwai aiki a gabansa matuƙar bai hallaka Zaytoonah once and for all ba daga ita har Linda ɗin...

Yau ta fara zuwa makaranta bayan abinda ya faru. Suna gama class Farha ta matso kusa da ita tana ma ta ya jiki, ta je ta gaisheta a asibiti har sau biyu ma.

"Lover girl ya mijin ki?"

Zaytoonah ta harareta

"Seriously ban san haka mijin ki ya haÉ—u ba, dole koyaushe ki dinga kallon hoton sa a class"

"Ya Allah! Farha ni yaushe na kalli hoton sa?"

"Koyaushe ma kina kallo" ta faÉ—a tana dariya.

Lokacin da su ka fito daga class za su tafi gida saboda ba su da wani class É—in sai Zaytoonah ta fara jin hajijiya.

"Are you Ok?" Farha ta faɗa tana riƙe Zaytoonah.

"Hajijiya na ke ji"

"Ko za ki koma Asibiti?"

Zaytoonah ta girgiza kai. Sai da su ka zauna na wajen kusan minti shabiyar kafin Zaytoonah ta ce su je ta dena ji.

Gidan su Akwai ma'aikata mata biyu da Zuhayr ya kawo ma su kula da gidan da kuma Zaytoonah, aikin su shine ko bacci ba za su yi ba sai Zaytoonah ta yi bacci.
Ita dai kawai ta haƙura ne amma ba ta yarda da gidan ba har yanzu, har Mommy ta kira tana faɗa ma ta abinda ya faru Mommy ta ce ta cigaba da addu'a itama za ta tayata...

***

Tana zaune a library tana karatu ƙarar shigowar text ya shiga wayarta ta ɗauka ta karanta saƙon da aka rubuta. Linda ce ta turo ma ta saƙo akan ta zo gidan ta yanzu-yanzu ta samu wani evidence.

Jiki na rawa ta kwashe kayanta ta fita daga library É—in. Indai evidence akan Ben ne to ba abinda zai sa ta zauna. The last time da Linda ta zo ta gaisheta a.Asibiti ta yadda da ita akan Ben ne ya turota daga stairs.
Ba ta ma kira Mr Dawson ba taxi ta shiga ta wuce gidan Linda É—in tana Allah ya sa su samu abunda beyond doubt zai incriminating Ben. "Ko idon sa ka kalla ka san ba shi da gaskiya, shege Mugu" ta faÉ—a a zuciyarta.

Yana kallo sanda ta fito a taxi É—in ta nufo gidan yai murmushin mugunta a ransa tareda tunanin once and for all Zaytoonah za ta bar rayuwar Zuhayr.

Ta danna ƙararrawa amma shiru ba a buɗe ba dan haka ta murɗa ƙofan gidan sai kuma ta ji ya buɗu ta yi Bismillah ta shiga falon tana kiran sunan Linda.

Tana isa tsakiyar falon aka rufe ma ta hanci da wani handkerchief tana fita hayyacin sa ya jawota har zuwa kitchen inda gawar Linda ke kwance a ƙasa cikin jini.

Sai da ya jira minti biyar ta yi dan ya san minti goma Zaytoonah za ta yi ba tareda ta dawo hayyacinta ba kafin ya kira 911 inda ya sanar da 'yan sanda akan shi maƙocin Linda ne ya ji hayaniya a gidan ta daga baya kuma ya ji ihu azo a duba saboda yana tunanin ƙila ɓarayi ne su ka shiga gidan.

A hankali ta fara buɗe idonta, ta ƙurawa ceiling ido kafin cikin 'yan daƙiƙai hankalinta ya dawo jikinta gaba ɗaya ta tuna abinda ya faru. Miƙewa ta yi zumɓur sai kuma taga mutum a kwance a ƙasa ga jini na malala.

"Innalillahi wa Inna Ilaihi Raji'oun!"
A hankali ta matsa kusa da gawan sai kuma ta ga ashe Linda ce ke kwance cikin jini ga wuƙa nan an daɓa ma ta a ƙirji. Ihun da ta sa yai dai-dai da isowar police gidan...

Sorry for not updating yersterday
2/11/21, 10:04 PM - ****: 32

Bismillahir Rahmanir Rahim

*Home Sweet Home*

"Wannan hoton yarinya da ku ke gani wata yarinyace sheɗaniya 'yar ƙwaya wacce ta kashe wata mata a ƙasar America. An ce ta daɓawa matar wuƙa har sau uku saboda ta ƙi sayar ma ta da ƙwaya. Yanzu haka tana ɗaure a gidan yari an yanke ma ta hukuncin kisa. Al'umman Annabi dan Allah mu dena shaye-shaye saboda mugayen illolin sa. Dan Allah ayi ta sharing har ya isa wajen mutane dayawa"

Dayawa mutane da su ka saurari voicenote É—in suna tsinewa hoton yarinyar da aka turo ne wacce ke tsaye police na sanya ma ta ankwa.

Wasu kuma na ƙoƙarin jawo hankalin mutane wajen sanin sahihancin labarin kafin su fara tsinuwa da zagi kar Allah ya tuhume su da alhakin yarinyar. Matar da ta turo ta dage a wani group ta gani kuma wacce ta turo ɗin ta rantse ta wayi Yarinyar da ke jikin hoton. Haka dai akayita cecekuce kafin daga baya maganar ya lafa lokacin da aka posting ɗin wani labari da su ke tsumayin jira.

Maman Abdul na ganin chats ɗin da ake yi sai dai ba ta tofa albarkacin bakin ta ba dan ita irin waɗannan voicenote ɗin da ake forwarding tareda hoto ba ta ɓata lokacin ta wajen sauraran su sai dai daga baya out of curiosity sai ta clicking hoton da aka turo dan ta ga yarinyar da ake magana akai.
Ta ƙurawa hoton tana tunanin possibility na hasashenta ya zama gaskiya ko kuma akasin sa. Ƙarshe dai zuciyarta ya amince da yarinyar dai Zaytoonah ce, Zaytoonah 'yar gidan Maryam maƙociyarta dan gidajen su duk a layi ɗaya ya ke duk da akwai ɗan tazarar gida kusan shida tsakanin su.

Ta san Zaytoonah na ƙasar America kuma hoton da aka turo hotone da akayi shi a chan ɗin saboda yanayin tsarin wajen da kuma baturen ɗan sanda da ke hoton.

"Innalillahi, Zaytoonah" ta furta lokacin da ta ƙarƙare lissafinta.

Wayar Maryam ta kira kuma ta ci sa'a bugu É—aya ta É—auka.

End of Chapter 67Continue to the next chapter or choose another story below.

More Hausa novels

Browse all books →
Previous Login to Save Next