Ramadan Promo!All users that send a manual request for premium upgrade on sallah day will be granted for 1 month free.
Soyayyanovels
Zaytoonah Part One Complete Hausa Novel
Zaytoonah Part One Complete Hausa Novel
By Azizat
Login to keep your reading position saved.
Book Page Chapters
Zaytoonah Part One Complete Hausa Novel

Zaytoonah Part One Complete Hausa Novel

Author: Azizat
Chapter 101 of 161
About 8 min read
Chapter progress: 0%
Listen Mode
Listen to this chapter using your device voice.
Ready to listen from this chapter.
Free access is active. You can keep reading and download during this access window.

Book chapters

Choose a chapter and continue reading.

Start chapters
Chapter 1 1,689 words Chapter 2 1,523 words Chapter 3 1,583 words Chapter 4 1,696 words Chapter 5 1,682 words Chapter 6 1,693 words Chapter 7 1,594 words Chapter 8 1,673 words Chapter 9 1,663 words Chapter 10 1,668 words Chapter 11 1,678 words Chapter 12 1,698 words Chapter 13 1,687 words Chapter 14 1,699 words Chapter 15 1,656 words Chapter 16 1,634 words Chapter 17 1,681 words Chapter 18 1,675 words Chapter 19 1,655 words Chapter 20 1,613 words Chapter 21 1,669 words Chapter 22 1,655 words Chapter 23 1,671 words Chapter 24 1,650 words Chapter 25 1,677 words Chapter 26 1,696 words Chapter 27 1,598 words Chapter 28 1,699 words Chapter 29 1,694 words Chapter 30 1,659 words Chapter 31 1,683 words Chapter 32 1,309 words Chapter 33 1,691 words Chapter 34 1,697 words Chapter 35 1,553 words Chapter 36 1,588 words Chapter 37 1,682 words Chapter 38 1,680 words Chapter 39 1,677 words Chapter 40 1,649 words Chapter 41 1,700 words Chapter 42 1,698 words Chapter 43 1,676 words Chapter 44 1,625 words Chapter 45 1,633 words Chapter 46 1,675 words Chapter 47 1,693 words Chapter 48 1,668 words Chapter 49 1,688 words Chapter 50 1,647 words Chapter 51 1,653 words Chapter 52 1,568 words Chapter 53 1,689 words Chapter 54 1,699 words Chapter 55 1,669 words Chapter 56 1,578 words Chapter 57 1,564 words Chapter 58 1,660 words Chapter 59 1,694 words Chapter 60 1,415 words Chapter 61 1,653 words Chapter 62 1,690 words Chapter 63 1,685 words Chapter 64 1,618 words Chapter 65 1,652 words Chapter 66 1,674 words Chapter 67 1,687 words Chapter 68 1,699 words Chapter 69 1,644 words Chapter 70 1,698 words Chapter 71 1,691 words Chapter 72 1,671 words Chapter 73 1,689 words Chapter 74 1,679 words Chapter 75 1,677 words Chapter 76 1,678 words Chapter 77 1,655 words Chapter 78 1,683 words Chapter 79 1,696 words Chapter 80 1,700 words Chapter 81 1,694 words Chapter 82 1,697 words Chapter 83 1,692 words Chapter 84 1,668 words Chapter 85 1,554 words Chapter 86 1,666 words Chapter 87 1,677 words Chapter 88 1,694 words Chapter 89 1,667 words Chapter 90 1,700 words Chapter 91 1,670 words Chapter 92 1,670 words Chapter 93 1,655 words Chapter 94 1,640 words Chapter 95 1,607 words Chapter 96 1,668 words Chapter 97 1,659 words Chapter 98 1,689 words Chapter 99 1,675 words Chapter 100 1,614 words Chapter 101 Reading now Chapter 102 1,700 words Chapter 103 1,683 words Chapter 104 1,657 words Chapter 105 1,698 words Chapter 106 1,700 words Chapter 107 1,695 words Chapter 108 1,656 words Chapter 109 1,683 words Chapter 110 1,699 words Chapter 111 1,699 words Chapter 112 1,641 words Chapter 113 1,696 words Chapter 114 1,626 words Chapter 115 1,695 words Chapter 116 1,691 words Chapter 117 1,698 words Chapter 118 1,645 words Chapter 119 1,673 words Chapter 120 1,691 words Chapter 121 1,635 words Chapter 122 1,694 words Chapter 123 1,689 words Chapter 124 1,688 words Chapter 125 1,673 words Chapter 126 1,692 words Chapter 127 1,686 words Chapter 128 1,697 words Chapter 129 1,660 words Chapter 130 1,691 words Chapter 131 1,674 words Chapter 132 1,670 words Chapter 133 1,693 words Chapter 134 1,691 words Chapter 135 1,687 words Chapter 136 1,672 words Chapter 137 1,691 words Chapter 138 1,657 words Chapter 139 1,687 words Chapter 140 1,650 words Chapter 141 1,695 words Chapter 142 1,607 words Chapter 143 1,699 words Chapter 144 1,676 words Chapter 145 1,698 words Chapter 146 1,684 words Chapter 147 1,664 words Chapter 148 1,696 words Chapter 149 1,674 words Chapter 150 1,680 words Chapter 151 1,697 words Chapter 152 1,628 words Chapter 153 1,618 words Chapter 154 1,688 words Chapter 155 1,664 words Chapter 156 1,692 words Chapter 157 1,584 words Chapter 158 1,644 words Chapter 159 1,646 words Chapter 160 1,618 words Chapter 161 1,797 words

A chan Ringim kuwa abin bai mu su daɗi ba kowa kuma gani ya ke laifin Maryam ce dan ita ce ba ta yiwa Zaytoonah tarbiyya mai kyau ba shiyasa har ta iya buɗe baki ta ce ba za ta auri Galadima ba, Galadiman Zazzau fa. Har da cewa da Tijjani na nan ai ba ta isa ta take maganar sa ba. Sun manta cewa duk wani ɗawainiyyar Zaytoonah babu hannun su a ciki sai yanzu dan sun ji Ɗan Sarki na neman ta shi ne hankalin su ya tashi kowa yana bugun ƙirji yana faɗin shima Baffan Zaytoonah ne.

Zaytoonah na kwance a ɗaki sai rawan sanyi ta ke yi, tun maganar su da Mommy ta fara zazzaɓi, Mommy ba ta san ma tana yi ba dan ko kulata ba ta sake yi ba. Sau ɗaya ta je asibiti wajen Salman amma ganin yadda Mommy ta ke ta shashshareta ya sa ta dawo gida ta kwanta ta fara kuka daga ƙarshe kuma sai zazzaɓi.

Wayar ta ne ya shiga ringing da ƙarfi, ta sa hannu ta jawo wayar ta sa a kunne ba tareda ta lura da wa ke kiran ba. Ta yi sallama a hankali.

"Gimbiya Hajiya Zainabu ke kan layi"

"Ok" Zaytoonah ta faɗa tana ƙoƙarin tashi zaune dan tunda ta ji ance Gimbiya ta san 'yar uwan Justice ne.

"Na bugo ne na ja miki kunne, kin yi kaÉ—an ki rena mana wayo. Sai da aka gama shirya komai za ki zo ki ce kin fasa saboda baki san darajan Mai Martaba ba.

" ko kaɗan ba na son auren nan saboda ba ki dace da babban gida ba. Amma yanzu da ki ka nuna ke 'yar iska ce to ni zan nuna miki duk iskancin ki ba ki isa ki walaƙanta babban gida ba. Aure ne kamar anyi an gama ki sawa ran ki wannan"

Daga haka aka katse kiran.

Jiya Hajia Abu ta dawo daga Dubai inda ta je ta haɗowa Galadima kayan aure sai kawai ta ke jin wai an fasa auren dan yarinyar ta ce ba ta so. Da farko ta share maganan tunda dama ba son Zaytoonah ta ke ba har ta ke cewa su ne 'ya'yan matsiyata ai kuma Justice zai auri 'ya'yan babban gida wanda su ka dace da shi. Amma daga baya sai girman kan su ka motsa, ta ga ai idan ba ayi auren nan ba kamar cin mutunci aka yiwa gidan su musamman Galadima. A ce mutum mai daraja irin sa wata banza ta ce ba za ta aure shi ba. Yadda yaken nan duk macen da ya nuna ba ta isa ta ƙi shi ba saboda martabar sa.

Zaytoonah ta yi murmushi tana faÉ—in lallai ma matar nan.

Muhsina ce ta turo ƙofar ɗakin ta shigo.

"Hajjaju lafiya ki ke ƙunshe a ɗaki tun da safe?"

Ta sa hannu ta taɓa goshinta ta ji zafi
"Zazzaɓi ki ke ji?"

"Na sha magani"

"Ban yarda ba, yaushe ma kika ci abinci da za ki ce kin sha magani. Ki shirya mu je asibiti a duba ki kawai"

"Da gaske na sha magani"

"Wani magani ki ka sha?"

"Paracetamol"

"Lallai kam, tashi ki shirya mu je Asibiti"

"Muhsina dan Allah ki yi haƙuri ba zan iya zuwa ba"

"Kun yi faÉ—a da Mommy ko?"

"Ban san ya zan yi ba, Mommy fishi ta ke yi dani akan maganar Justice. I dont know what to do, ba zan iya auren Justice ba" ta yi maganar tana kuka.

"Miyasa?" Muhsina ta yi maganar tana kallon ta

Zaytoonah ta yi shiru tana kallon ta cike da rashin fahimta.

"Miyasa ba za ki iya auren sa ba?"

"Haka kawai"

"Ba za ki iya auren sa ba saboda ya miki tsufa?"

Zaytoonah ta girgiza kai

"Saboda yana da 'ya'ya har uku?"

Nan ma ta girgiza kai.

"Saboda ba kya son shi akwai wanda kike so?"

Nan ma ta girgiza kai.

Muhsina ta gyara zamanta sosai kusa da Zaytoonah ta ce " na san yadda maganar auren Justice ya zo miki ba a bi tsarin da ya dace ba amma still ko da ya bi ta hanyar da ya dace ne the same response za ki bashi, kin san saboda me?.

"Saboda ba kya son aure Zaytoonah, ba kya son sake wani auren. Bari ki ji abu biyu za ki yi ki muzgunawa kan ki da 'ya'yan ki. Na farko ki ƙi aure ki ƙare rayuwar ki a haka, ya zamana kin denying 'ya'yan ki samun Uba kenan. Na biyu ki yi aure ki auri mutumin da ba zai riƙe 'ya'yan ki da amana ba.

"See, ko Zuhayr da ke ƙabari ba zai so ace kina zaune haka ke kaɗai ba, he'll want you to be happy, to be with someone that makes you happy. Zaytoonah you need a companion, your children needs a father ba zai yiwu ki cigaba da zama a haka ba. And idan har ba wai ɗaya daga cikin dalilin da na irgo ba ne to ni banga aibu a auren Galadima ba, he's a good man, kuma na tabbata idan kika aure shi 'yan biyu ba za suyi kukan rashin Uba ba"...

"Uncle Salman tush tush tush" Hadid ya faÉ—a yana harba bindigar roba wa Salman É—in da ke kishingiÉ—e yana shan tea.

Mommy na riƙe da Hashir tana saka ma sa takalmi, daga zuwa ya cire su ya watsar bayan ga sanyin tiles.

Sallamar Justice su ka ji wanda har yau bai fasa zuwa duba Salman ba.

"Hadid miƙowa Daddyn ku kujera ya zauna" ta yi maganar ne zuciyar ta ɗaya saboda ɗaya kujeran zaman na gefen Hadid ɗin. Ba ta ankara ba ta ji ya ce "GrandMa wannan ne Daddyn mu?"

Sai lokacin Hashir ya kalli fiskar Justice ya ce "Lah! GrandMa dama idan aka je Aljannah ana samun gemu ne?"

Sai kuma dukkan su biyu su ka zo gaban Justice suna kallon sa. Sun fi minti É—aya suna kallon sa suna nemo kamannin mutumin da ke tsaye da kuma kamannin mutumin da ke jikin hotunan da Mom ta ke nuna mu su.

Salman ne ya katse shirun da cewa " Daddyn ku yana Aljannah, wannan Daddy Babba ne"

Hadid ya riƙo hannun Justice yana faɗin "i like you Daddy Babba"

Hashir kuma ya ce "ina kai ba ka bulala kaman É—aya Daddy Babban na Zaria?"

Justice ya shafa kumatunsa yana faÉ—in " ba na bulala amma ba na shiri da wanda ba sa jin magana".

Da kan sa ya jawo kujeran ya zauna ya É—aura su kan cinyarsa yana sauraron surutun su. Duk da bai san yaran waye ba ne amma yaran sun burgeshi, wani zuciya na bashi cewa yaran Zaytoonah ne amma bai tabbatar ba tunda da Mommy da Salman babu wanda ya ma sa bayani.

Cikin ƙanƙanin lokaci wani bond mai ƙarfi ya shiga tsakanin sa da yaran. Dama yaran akwai saurin sabo musamman idan za ka biyewa surutun su. Saboda yaran ya jima a wajen dan ya fi minti talatin bai yi niyyar tafiya ba ma sai da Mommy ta ce su Hadid su bar shi hakanan zai tafi gobe idan ya zo sai su ƙarisa bashi labarin.

Duk yadda ta ke jin rashin ƙarfin jiki tunda Muhsina ta ce ma ta 'ya'yan ta sun zo suna Asibiti ta ji ta warke kawai, ta tashi ta shirya ta fito za ta je Asibitin, Muhsina ta ce ta jira su tafi tare dan itama ta kwana biyu ba ta leƙa Salman ɗin ba.
A motar Muhsina su ka tafi bayan Azma ta miƙo mu su abincin da za su kai.

Suna fitowa daga mota ta hango Justice riƙe da hannun 'yan biyu sun nufi wajen motar sa tareda Junior. Suna tafiya suna hira.

"Hadid, Hashir" ta ƙwala mu su kira dan a tunanin ta bin Justice za su yi.

Dukkan su suka juyo suna kallon ta. Sake hannun Justice su ka yi su ka nufi wajen Zaytoonah da gudu.

Yaran ta ne abinda zuciyar sa ta ambata kenan.

"Mom zo ku gaisa da Daddy Babba, yana da kirki"

Yadda su ke jan hannun ta ya sa dole ta ƙarisa wajen Justice ɗin. Kallon ta ya ke with full admiration.

"Daddy ga Mom É—in mu nan" Hashir ya faÉ—a yana nuna Zaytoonah.

"Ina wuni Sir" ta faÉ—a cike da kunyar sa, sau É—aya ta kalle shi ta kauda kai gefe tana kallon Junior da ke wasa da wayan da ta ke tunanin na Justice É—in ne.

"Daddy ina dai ba ka manta ba gobe za ka kaimu shan ice cream?"

Zaytoonah ta zarewa Hadid ido.

"Insha Allah za mu je" ya faÉ—a yana murmushi.

Tana tsaye a wajen yai wa yaran na ta musabaha tareda kissing goshin su sannan ya karɓi wayar sa a wajen Junior ya shige mota.

Tunda su ka shigo kuwa 'yan biyu kaman haÉ—in baki sai su ka kama taÉ—in Justice, Daddy Babban ma sun dena kira sai dai Daddy kawai.
Kallo É—aya Mommy ta ma ta ta kau da kai, irin kallon 'gashi dai kin gani da idon ki'.

Ba su bar Asibitin ba sai bayan sallar Isha.
Yaran na bacci ta zuba mu su ido tana kallon su, har su ka yi bacci ba su dena taÉ—in Justice ba 'Daddy yayi kaza, Daddy ya ce kaza, gemun Daddy kaman na kaza, maganan Daddy kaza...'

Ko ba dan ita ba, za ta nemawa yaranta farinciki. Idan har aurenta da Justice yana haÉ—e da farin cikin yaran ta to za ta aure shi.

Wayar ta ta ɗauko ta rubuta saƙo sannan ta tura, tana ganin ya tafi ta kashe wayan ta kwanta tana jin zuciyarta na bugawa da sauri-sauri...
2/11/21, 10:04 PM - ****: 50

Bismillahir Rahmanir Rahim

*Married again*

End of Chapter 101Continue to the next chapter or choose another story below.

More Hausa novels

Browse all books →
Previous Login to Save Next