Ramadan Promo!All users that send a manual request for premium upgrade on sallah day will be granted for 1 month free.
Soyayyanovels
Zaytoonah Part One Complete Hausa Novel
Zaytoonah Part One Complete Hausa Novel
By Azizat
Login to keep your reading position saved.
Book Page Chapters
Zaytoonah Part One Complete Hausa Novel

Zaytoonah Part One Complete Hausa Novel

Author: Azizat
Chapter 99 of 161
About 8 min read
Chapter progress: 0%
Listen Mode
Listen to this chapter using your device voice.
Ready to listen from this chapter.
Free access is active. You can keep reading and download during this access window.

Book chapters

Choose a chapter and continue reading.

Start chapters
Chapter 1 1,689 words Chapter 2 1,523 words Chapter 3 1,583 words Chapter 4 1,696 words Chapter 5 1,682 words Chapter 6 1,693 words Chapter 7 1,594 words Chapter 8 1,673 words Chapter 9 1,663 words Chapter 10 1,668 words Chapter 11 1,678 words Chapter 12 1,698 words Chapter 13 1,687 words Chapter 14 1,699 words Chapter 15 1,656 words Chapter 16 1,634 words Chapter 17 1,681 words Chapter 18 1,675 words Chapter 19 1,655 words Chapter 20 1,613 words Chapter 21 1,669 words Chapter 22 1,655 words Chapter 23 1,671 words Chapter 24 1,650 words Chapter 25 1,677 words Chapter 26 1,696 words Chapter 27 1,598 words Chapter 28 1,699 words Chapter 29 1,694 words Chapter 30 1,659 words Chapter 31 1,683 words Chapter 32 1,309 words Chapter 33 1,691 words Chapter 34 1,697 words Chapter 35 1,553 words Chapter 36 1,588 words Chapter 37 1,682 words Chapter 38 1,680 words Chapter 39 1,677 words Chapter 40 1,649 words Chapter 41 1,700 words Chapter 42 1,698 words Chapter 43 1,676 words Chapter 44 1,625 words Chapter 45 1,633 words Chapter 46 1,675 words Chapter 47 1,693 words Chapter 48 1,668 words Chapter 49 1,688 words Chapter 50 1,647 words Chapter 51 1,653 words Chapter 52 1,568 words Chapter 53 1,689 words Chapter 54 1,699 words Chapter 55 1,669 words Chapter 56 1,578 words Chapter 57 1,564 words Chapter 58 1,660 words Chapter 59 1,694 words Chapter 60 1,415 words Chapter 61 1,653 words Chapter 62 1,690 words Chapter 63 1,685 words Chapter 64 1,618 words Chapter 65 1,652 words Chapter 66 1,674 words Chapter 67 1,687 words Chapter 68 1,699 words Chapter 69 1,644 words Chapter 70 1,698 words Chapter 71 1,691 words Chapter 72 1,671 words Chapter 73 1,689 words Chapter 74 1,679 words Chapter 75 1,677 words Chapter 76 1,678 words Chapter 77 1,655 words Chapter 78 1,683 words Chapter 79 1,696 words Chapter 80 1,700 words Chapter 81 1,694 words Chapter 82 1,697 words Chapter 83 1,692 words Chapter 84 1,668 words Chapter 85 1,554 words Chapter 86 1,666 words Chapter 87 1,677 words Chapter 88 1,694 words Chapter 89 1,667 words Chapter 90 1,700 words Chapter 91 1,670 words Chapter 92 1,670 words Chapter 93 1,655 words Chapter 94 1,640 words Chapter 95 1,607 words Chapter 96 1,668 words Chapter 97 1,659 words Chapter 98 1,689 words Chapter 99 Reading now Chapter 100 1,614 words Chapter 101 1,610 words Chapter 102 1,700 words Chapter 103 1,683 words Chapter 104 1,657 words Chapter 105 1,698 words Chapter 106 1,700 words Chapter 107 1,695 words Chapter 108 1,656 words Chapter 109 1,683 words Chapter 110 1,699 words Chapter 111 1,699 words Chapter 112 1,641 words Chapter 113 1,696 words Chapter 114 1,626 words Chapter 115 1,695 words Chapter 116 1,691 words Chapter 117 1,698 words Chapter 118 1,645 words Chapter 119 1,673 words Chapter 120 1,691 words Chapter 121 1,635 words Chapter 122 1,694 words Chapter 123 1,689 words Chapter 124 1,688 words Chapter 125 1,673 words Chapter 126 1,692 words Chapter 127 1,686 words Chapter 128 1,697 words Chapter 129 1,660 words Chapter 130 1,691 words Chapter 131 1,674 words Chapter 132 1,670 words Chapter 133 1,693 words Chapter 134 1,691 words Chapter 135 1,687 words Chapter 136 1,672 words Chapter 137 1,691 words Chapter 138 1,657 words Chapter 139 1,687 words Chapter 140 1,650 words Chapter 141 1,695 words Chapter 142 1,607 words Chapter 143 1,699 words Chapter 144 1,676 words Chapter 145 1,698 words Chapter 146 1,684 words Chapter 147 1,664 words Chapter 148 1,696 words Chapter 149 1,674 words Chapter 150 1,680 words Chapter 151 1,697 words Chapter 152 1,628 words Chapter 153 1,618 words Chapter 154 1,688 words Chapter 155 1,664 words Chapter 156 1,692 words Chapter 157 1,584 words Chapter 158 1,644 words Chapter 159 1,646 words Chapter 160 1,618 words Chapter 161 1,797 words

Ko kwana a Ringim Mommy ba ta yi ba kamar yadda ta tsara. Labarin da ta ji a chan ya ɗaure ma ta kai. Wani irin fin ƙarfi ne wannan? Ta ya za a bayar da auren Zaytoonah ba tareda an tuntuɓeta ba? Ta san ita mace ce amma still bai kamata a yanke ɗanyen hukunci irin wannan ba tareda an sanar da ita ba.

Ko da ya ke ba laifin su ba ne, laifin Justice ne da ya aikata wannan abin, ba ta ɗauka da ilimin sa da darajar sa he'll stoop so low har ya aikata abinda ya aikata ba. Idan yana taƙama da sarauta ne Zaytoonah tana da 'yancin da za ta auri duk wanda ta ke so a tsarin musulunci dama na demokraɗiya.

Ta ina ma za ta fara yiwa Zaytoonah maganar nan. Tana son Zaytoonah ta samu farin ciki, tana so ta gan ta a ɗakin mijin ta ƙarƙashin kulawar mijinta, amma wannan hanya da aka bi bai dace ba.

Mommy ba ta yanke hukunci ba sai da ta kira Hajia Ni'ima dan ta ji daga gareta. A wayan ne Ni'ima ta ma ta bayanin komai akan ita ta sa aka yiwa Mai Martaba maganan Justice da Zaytoonah to da ya yiwa Justice É—in magana sai ya nuna a bar maganan zuwa wani lokaci zai yi tunani akai. Shi kuma Mai Martaba ya san halin É—an sa da zurfin ciki shiyasa kawai ya tura magabata aka je aka tambayi auren Zaytoonah kuma 'yan uwan Mahaifin ta su ka ba da ita har ma an saka lokacin biki nan da wata biyu.

Mommy kam sai jinjina kai take yi da jin wannan batu mai É—aure kai. Ana wata ga wata.

Sai da ta gama yanke shawara da zuciyar ta kafin ta tuntuɓi Zaytoonah da maganar.

Zaytoonah na gyara alayyaho Mommy ta jeho ma ta tambaya.

"Akwai wani abu tsakanin ki da Justice ne?"

Zaytoonah ta É—ago ido ta ce "bangane ba Mommy"

Sai da ja numfashi kafin ta ce " an nemawa Justice auren ki, kuma su Baffan ki sun bashi ke"

Zaytoonah ta ajiye ganyen da ta fara yankawa ta gyara zama dan ta ji tatsuniyar da Mommy ke ba ta da kyau, wannan kam ai tatsuniya ne kawai.
Aure ita da Justice sai ka ce a film ta faÉ—a a ran ta...
2/11/21, 10:04 PM - ****: 48

Bismillahir Rahmanir Rahim

*The Decision*

Bayanta ya dinga shafawa a hankali wanda hakan ya saukar ma ta da nitsuwa.

Auwal na barin ƙofar ɗakin kai tsaye hanyar fita daga Asibitin yai, chan wajen wani dakali ya zauna yana maida numfashi. Ɗumin da ya ji a saman kumatun sa ya sa shi saurin shafa wajen ya tabbatar dai hawaye ne ke zubowa.
Da ya san abinda zai tarar kenan da bai bi bayan Justice ba.

"Daddy" ya furta a fili yana mai burin ina ma yana tareda su a nan yau. Da Daddy na nan da tun farko bai rasa Zaytoonah ba, da yana nan ya sani babu wanda ya isa ya bawa Justice auren Zaytoonah.

Ya jima a wajen yana hawaye kafin daga baya ya koma ciki bayan ya nemi ruwa ya wanke fiskar sa.

Justice bayan ya tabbatar bacci ya É—auki Zaytoonah sannan ya shifiÉ—ata a kan gadon ya fita, kai tsaye wajen Likita ya je bayan ya tambayi nurse ta ma sa kwatancen office É—in.
Ya yiwa Likita bayanin yadda Zaytoonah ta tsorata lokacin da ta tashi, Likita ya ma sa bayanin dalilin wannan tsoro É—in wanda ya ke da nasaba da ciwon ta.

Lokacin da Likita da Justice su ka koma É—akin sun samu Mommy ta idar da sallah. Justice ya ma ta ya jiki a kunyace tunowa da yai da abinda ya wakana tsakanin sa da 'yarta É—azu. Da ya san Mommy ta gansu da shikenan ya gama gaisuwar kenan ba zai kuma dawowa ba. Sai dai rashin sani ya fi dare duhu. Itama Mommy sai ta tsinci kan ta da jin kunyar Justice É—in.

Sun É—an tattauna da Likita kan jikin Salman wanda ya tabbatar mu su da Insha Allahu ba wani matsala sosai bullet É—in bai affecting any of the vital organ É—in sa ba...

Washegari da sassafe Justice ya taho Asibiti gaisuwa, biye da shi kuma mai aikin sa ce wacce ta taho mu su da abin karyawa. Mommy ta ma sa godiya da addu'a.

Kaman zai tambayi Zaytoonah dan bai ganta a É—aki ba amma sai ya fasa ya wuce É—akin da aka kwantar da Salman.

Ganin Salman na bacci ya tambayi Auwal ya mai jiki wanda ya amsa ma sa a daƙile. Komawa ɗakin su Zaytoonah yai dan gaskiya ba zai iya tafiya ba tareda ya sanyata a ido ba.

Sallah takeyi lokacin da ya dawo É—akin, ya É—an tsaya ko za ta idar su gaisa tunda a tunanin sa sallar Asuba takeyi amma Zaytoonah da ta tafi sujjada minti É—aya, biyu, uku, huÉ—u... ba ta É—ago ba.
Sallama yai da Mommy ya wuce office dan yau sunada zaman kotu. Ya sani Zaytoonah ba ta son ganin sa ne ya sa ta ƙi ɗagowa balle har ta sallame sallar tata.
Bayan fitar shi kuwa Zaytoonah ta ɗago ta yi tahiyya sannan ta yi sallama tana sauke ajiyar zuciya. Jiya bayan ta tashi daga bacci ta samu nitsuwa sosai, ƙanshin turaren Justice da ta ji a jikinta ne ya sa ta fara tunanin abubuwan da ya faru.
Salati ta doka lokacin da ta tuno kiss ɗin da su ka yi ta dinga jin haushin kan ta na yadda aka yi ta biyewa zuciyarta a lokacin. Ta ya ma za ayi ta rinƙa ganin Justice a matsayin Zuhayr?.

Kwanan su biyu a Asibiti aka sallami Mommy da Zaytoonah yanzu jinyar Salman kawai su ke yi.
Kullum sai Justice ya zo dubiya duk da ana kawo abinci daga gidan Muhsina hakan bai sa Justice ya dena aiko mu su da abinci ba. Safe rana dare duk sai mai aikin sa ta kawo mu su abinci...

"Adaeze" Mommy ta kira sunan ta tana kafe ta da idanu. Ta lura duk zuwan Justice sai dai ta nemi excuse ta gudu daga É—akin kafin ya zo. Yau ma É—in ya kamata red-handed ne tunda ya zo da wuri ba lokacin da ya saba zuwa ba.

"Ina wuni" ta faÉ—a ba tareda ta É—ago ba. Tun da ya shigo É—akin ta ja bakin ta tayi shiru, har su ka gama gaisawa da Mommy da kuma Salman É—in ba ta ce da shi uffan ba, sai ma game da ta kunna ta farayi a wayar ta.

"Ya jiki?" Ya faÉ—i yana kallon ta.

Ka ji É—an rainin hankali ta faÉ—a a ranta tareda É—agowa ta harare shi.
Maimakon ya ɓata rai sai ta ga yayi murmushi.

Sallama yai wa Mommy sannan ya ce "ki ɗan fito ki karɓi saƙo ko" yai maganar yana kallon Zaytoonah, har ya fita ba ta ce komai ba saima tsaki da ta yi.

"Ba za ki bishi ba?"

"Mommy ni kam..."

"Ba na son walaƙanci Zaytoonah"

"Mommy bai fa kira sunana ba..."

"Za ki wuce ko sai na make ki"

Ta turo baki tana É—aukan mayafin ta da ke kan kujera ta fita daga É—akin da sauri. Tana ji Salman na faÉ—in "daÉ—in abin ma kun fi kusa" ta murguÉ—a baki ta cigaba da tafiya.

Ba lallai ya tsaya a cikin Asibitin ba shiyasa direct farfajiyan Asibitin ta nufa. Dreban sa ta hango tsaye a bakin motar yana É—aga ma ta hannu.

"Shegen mulki ba zai ma iya tsayawa a waje ba" ta furta a fili tareda yin tsaki.

Tana zuwa Dreban ya buɗe ma ta gidan baya haɗeda gaisheta. Sai da ta ɗan tsaya na wasu daƙiƙu kafin ta shiga motar, ta yi niyyar barin ƙofar a buɗe amma kawai sai Dreban ya rufo ƙofar da ƙarfi, daga haka kuma ya bar wajen.

Sau É—aya ta kalle shi ta É—auke kai ta maida duban ta ga window.

Kusan minti biyu ba wanda yai magana. A ranta tana ƙiyasta indai ya kai minti biyar bai yi magana ba fita za ta yi ta kama gabanta.

"Zuwa yanzu ya ci ace kin saba da sallama a bakin ki"

Ta juyo ta kalleshi amma idon sa na kan wayar da ya ke dannawa.

Chan ƙasan ranta ta ce 'ba za a yi sallamar ba'.

"Ina da tabbacin Chief Udodiri yana da hannu wajen attacking na ku da aka yi. Akwai matakan tsaro da na riga na É—auka, ciki harda sama muku bodyguards da za su dinga kula da ku har komai ya lafa, ina fata za ki bani haÉ—in kai wajen ganin komai ya tafi dai-dai"

"Ba ma buƙatar komai daga gareka. Idan bodyguards ne zan iya hiring ɗin su da kaina ba sai ka nuna fin ƙarfi ba kamar yadda ka saba"

Tana gama maganar ta kama ƙofa za ta fita amma ta ji ta a rufe.
Ta juyo ta kalleshi da mamaki.

"Ba mu gama magana ba"

"To ni na gama" ta faɗa da ɗan ƙarfi hakan ya sa ya juyo ya kalleta. Ta yi saurin sunkuyar da kan ta saboda nauyin da idon sa ya ma ta.

" bisa rana da aka saka yau saura kwana ishirin da ɗaya a ɗaura aure. Saboda rashin sanin tabbas na ranan da case ɗin nan zai ƙare, za a ɗaura aure a ranan da aka saka ɗin amma duk wani hidima zai biyo bayan an ƙare case ɗin nan ne"

Ta rintse ido jin maganar da ya ke yi, maimakon ta ga duhu sai kuma ta fara ganin hoton ta da Justice yayinda ya ke kissing É—in ta. Ta yi saurin buÉ—e idon saboda jin tsikar jikinta na tashi daga wannan tunanin.

"Idan akwai abinda ki ke son sani kafin nan ko kuma ki ke buƙata za ki iya sanar da ni"

"I dont want this marriage, Dan Allah ka yi haƙuri ka rabu da ni" hawaye ya biyo bayan maganar da ta yi.

Shiru yai bai ce komai ba, itama kuma ba ta sake cewa komai ba sai ma ƙoƙarin goge hawaye da ta ke yi.

End of Chapter 99Continue to the next chapter or choose another story below.

More Hausa novels

Browse all books →
Previous Login to Save Next