Ramadan Promo!All users that send a manual request for premium upgrade on sallah day will be granted for 1 month free.
Soyayyanovels
Zaytoonah Part One Complete Hausa Novel
Zaytoonah Part One Complete Hausa Novel
By Azizat
Login to keep your reading position saved.
Book Page Chapters
Zaytoonah Part One Complete Hausa Novel

Zaytoonah Part One Complete Hausa Novel

Author: Azizat
Chapter 137 of 161
About 8 min read
Chapter progress: 0%
Listen Mode
Listen to this chapter using your device voice.
Ready to listen from this chapter.
Free access is active. You can keep reading and download during this access window.

Book chapters

Choose a chapter and continue reading.

Start chapters
Chapter 1 1,689 words Chapter 2 1,523 words Chapter 3 1,583 words Chapter 4 1,696 words Chapter 5 1,682 words Chapter 6 1,693 words Chapter 7 1,594 words Chapter 8 1,673 words Chapter 9 1,663 words Chapter 10 1,668 words Chapter 11 1,678 words Chapter 12 1,698 words Chapter 13 1,687 words Chapter 14 1,699 words Chapter 15 1,656 words Chapter 16 1,634 words Chapter 17 1,681 words Chapter 18 1,675 words Chapter 19 1,655 words Chapter 20 1,613 words Chapter 21 1,669 words Chapter 22 1,655 words Chapter 23 1,671 words Chapter 24 1,650 words Chapter 25 1,677 words Chapter 26 1,696 words Chapter 27 1,598 words Chapter 28 1,699 words Chapter 29 1,694 words Chapter 30 1,659 words Chapter 31 1,683 words Chapter 32 1,309 words Chapter 33 1,691 words Chapter 34 1,697 words Chapter 35 1,553 words Chapter 36 1,588 words Chapter 37 1,682 words Chapter 38 1,680 words Chapter 39 1,677 words Chapter 40 1,649 words Chapter 41 1,700 words Chapter 42 1,698 words Chapter 43 1,676 words Chapter 44 1,625 words Chapter 45 1,633 words Chapter 46 1,675 words Chapter 47 1,693 words Chapter 48 1,668 words Chapter 49 1,688 words Chapter 50 1,647 words Chapter 51 1,653 words Chapter 52 1,568 words Chapter 53 1,689 words Chapter 54 1,699 words Chapter 55 1,669 words Chapter 56 1,578 words Chapter 57 1,564 words Chapter 58 1,660 words Chapter 59 1,694 words Chapter 60 1,415 words Chapter 61 1,653 words Chapter 62 1,690 words Chapter 63 1,685 words Chapter 64 1,618 words Chapter 65 1,652 words Chapter 66 1,674 words Chapter 67 1,687 words Chapter 68 1,699 words Chapter 69 1,644 words Chapter 70 1,698 words Chapter 71 1,691 words Chapter 72 1,671 words Chapter 73 1,689 words Chapter 74 1,679 words Chapter 75 1,677 words Chapter 76 1,678 words Chapter 77 1,655 words Chapter 78 1,683 words Chapter 79 1,696 words Chapter 80 1,700 words Chapter 81 1,694 words Chapter 82 1,697 words Chapter 83 1,692 words Chapter 84 1,668 words Chapter 85 1,554 words Chapter 86 1,666 words Chapter 87 1,677 words Chapter 88 1,694 words Chapter 89 1,667 words Chapter 90 1,700 words Chapter 91 1,670 words Chapter 92 1,670 words Chapter 93 1,655 words Chapter 94 1,640 words Chapter 95 1,607 words Chapter 96 1,668 words Chapter 97 1,659 words Chapter 98 1,689 words Chapter 99 1,675 words Chapter 100 1,614 words Chapter 101 1,610 words Chapter 102 1,700 words Chapter 103 1,683 words Chapter 104 1,657 words Chapter 105 1,698 words Chapter 106 1,700 words Chapter 107 1,695 words Chapter 108 1,656 words Chapter 109 1,683 words Chapter 110 1,699 words Chapter 111 1,699 words Chapter 112 1,641 words Chapter 113 1,696 words Chapter 114 1,626 words Chapter 115 1,695 words Chapter 116 1,691 words Chapter 117 1,698 words Chapter 118 1,645 words Chapter 119 1,673 words Chapter 120 1,691 words Chapter 121 1,635 words Chapter 122 1,694 words Chapter 123 1,689 words Chapter 124 1,688 words Chapter 125 1,673 words Chapter 126 1,692 words Chapter 127 1,686 words Chapter 128 1,697 words Chapter 129 1,660 words Chapter 130 1,691 words Chapter 131 1,674 words Chapter 132 1,670 words Chapter 133 1,693 words Chapter 134 1,691 words Chapter 135 1,687 words Chapter 136 1,672 words Chapter 137 Reading now Chapter 138 1,657 words Chapter 139 1,687 words Chapter 140 1,650 words Chapter 141 1,695 words Chapter 142 1,607 words Chapter 143 1,699 words Chapter 144 1,676 words Chapter 145 1,698 words Chapter 146 1,684 words Chapter 147 1,664 words Chapter 148 1,696 words Chapter 149 1,674 words Chapter 150 1,680 words Chapter 151 1,697 words Chapter 152 1,628 words Chapter 153 1,618 words Chapter 154 1,688 words Chapter 155 1,664 words Chapter 156 1,692 words Chapter 157 1,584 words Chapter 158 1,644 words Chapter 159 1,646 words Chapter 160 1,618 words Chapter 161 1,797 words

"Dole na yi kuka Zaytoonah, waɗannan watanni are the tough times of my life idan aka cire lokacin tafiyar mahaifin ku. Na tsorata da halin da ki ka shiga Adaeze, ranan da aka ce kin yanki Raziya da wuƙa i couldnt sleep. Tunani na ya tafi cewa ko dai da gasken ne kin fara hauka, but i couldnt accept it shiyasa na yiwa Galadima magana indai ana treating PTSD zan je ko ina ne a duba ki. Zaytoonah lokacin da mu ka fara zuwa nan na ƙara tsorata sosai. Kina ɗauke da ciki and hankalin ki ya kasu kashi biyu idan ki na maganar Zuhayr kaman yana raye ki ke yi, idan kika koma wajen Galadima kuma kaman kuna tare da shi kike gani. Zan je wajen D, zan tanadi Tsoho. Ben zai kasheni its all over now"

Ta ƙarisa maganar tana fashewa da kuka itama Zaytoonan sai ta saka kuka tareda rungume Mommy...
2/11/21, 10:04 PM - ****: 68

Bismillahir Rahmanir Rahim

*Husband and wife*

"Ban gane za ku tafi America gobe ba". Ghazala ta faÉ—a cike da Zullumi

Galadima bai kulata ba sai ma ƙoƙarin zuge jakar sa da ya ke.

"Ranka shi daÉ—e ka sani a duhu"

Sai da ya ajiye jakar gefen gado kafin ya juyo ya kalleta tana tsaye ta riƙe ƙugu da hannayenta duka biyu.

Jiya da dare ta dawo daga Lagos ta je clearing kayanta da su ka iso. Isowar da za ta yi ta ga 'yan biyun Zaytoonah da Junior a gidan suna kallo tareda sauran yaran a Falo. Ba ta tambayi dalilin zuwan su ba dan Galadima ya sha zuwa ya É—auko su suzo su wuni a gidan amma ba sa kwana. Yau da safe kuwa bayan sun karya Galadima ya sanar da ita gobe jirgin su zai tashi shi da duka yaran za su tafi ganin Zaytoonah da Baby.

" wannan ba adalci ba ne, idan har 'yar ka kake son gani ka ce ta kawo ma ka ita mana, kai da yara yanzu idan duka kuka tafi sai ta É—auka ma ko kana son mayar da ita É—akinta ne ni kuma wannan ba zan amince da shi ba..."

"Ba na tunanin zuwa duba lafiyar matata da 'ya ta zai zama rashin adalci a gareki. Ki kama girman ki Dan Allah"

"Ban gane matar ka ba, yaushe ka mayar da ita?" Ghazala ta faÉ—a cikin tashin hankali.

Kallon rashin hankali ya ma ta na 'yan daƙiƙu. Har ba zai yi magana ba amma sai ya ga gara kawai ya fayyace ma ta koma minene ta ke ɗauka ba dai-dai ba.

"Kamar yadda kike matata haka Zaytoonah ta ke matata. Idan kina da wani labari saɓanin haka to ban san wannan ba"

Ashe dai gani da ji na iya gushewa mutum a wasu lokuta domin kuwa maganar Galadima na ƙarshe ya saka Ghazala ta rasa jinta da ganinta na wani ɗan ƙaramin lokaci.

Fitan Galadima daga É—akin ne ya ba ta daman zama a bakin gado tareda dafe kan ta dake wani mugun sarawa.

Galadima bai saki Zaytoonah ba. Mi hakan ke nufi? ...

***

"Hamma dan Allah ka karya kafin ka fita" Humairah ta faÉ—a tana marairaice murya.

"Muna da zaman kotu yau kuma na makara"

"Hamma Dan Allah ko shayi ne ka sha"

"Auwal ka tsaya ka ci abinci, komai ai sai da lafiyar jiki ake yi" Muntari ne yai wannan magana wanda shima ke zaune kan keken sa yana karyawa.

Ba yadda ya iya dole ya ja kujeran dinning ɗin ya zauna ya ɗauki mug ɗin da Humairah ta ajiye a gaban sa ya kurɓa. Cikin minti uku ya kammala cin slize ɗin bread huɗu wanda ke haɗe da ƙwai ya kora da shayi ya miƙe ya fita.

Yana ƙoƙarin tada machine ɗin sa Humairah ta fito da gudu riƙe da wayarsa ashe inda ya zauna a wajen dinning ɗin ya manta.

"Hamma gashi" ya amsa tareda yi ma ta godiya.

Har ya buÉ—e gate ya fita ba ta bar bin sa da murmushi ba. Duk shawaran da Zaytoonah ta ba ta tana amfani da shi amma still har yanzu ba ta ga wani chanji tattare da shi ba.

Bayan ta koma cikin gida ne Muntari ke tambayarta yaushe su Zaytoonah za su dawo. Humairah ta ce sun yi magana da Zaytoonah akan sai Alinah ta cika kwana sittin kafin nan ta ɗan yi ƙwari. Muntari ya mu su fatan Allah ya kawo su lafiya Humairah ta amsa da Amin.

Humairah da Zaytoonah sun riga sun sake jiki da Muntari hakama Auwal amma Salman har yanzu ya kasa sake jiki da shi, wannan ya sa ma ko gidan ba ya zuwa, idan ta kama dole kuwa a ƙofar gidan zai tsaya ya kira Auwal ya fito su yi maganar da za su yi.

Wannan abu na damun Muntari sosai sai dai kamar yadda Iya ta faɗa a hankali zai haƙura ya yafe ma sa...

***

Duk da ba wannan ne karon farko da yaran ke zuwa ƙasar America ba amma wannan karan ziyarar ta daban ne. Dukkan su shida kowa na ɗokin ganin baby Alinah.
Shi kan sa uban gayyar da ka ganshi ka san he's excited. Duk wani hayaniyar Ghazala da ta yi safiyar da za su fito daga airport ya ajiye shi suna hawa jirgi kuwa ya maida hankalinsa kacokam wajen Qurratul ayn.

Da tsakar dare su ka isa California kuma babu jirgi da zai tafi Las Vegas sai washegari ƙarfe tara na safe, dan haka dole suka kwana a hotel. Yara Matan ya kama mu su ɗaki ɗaya shima da yara mazan su ka kwana a ɗaki ɗaya.

Tun kafin su fita ya riga ya kira ya booking jirgi dan haka suna zuwa bai jima ba suka samu ticket. Akwai gajiya a tattare da yaran amma ɗokin da su ke bai sa sun yi ƙorafi ba.

Ƙarfe uku na rana su ka isa Las Vegas abin mamaki sai ga motoci biyu suna jiran su wanda Mommy ta aiko. Zuwan bazata ya mu su amma Salman da su ka yi tsarin da shi ashe bai iya riƙe sirri ba.
Suna cikin motar Galadima ya kira Salman.
Yana ɗaukan wayan kuwa ya fara ba da haƙuri.

"Ranka shi daÉ—e wallahi Mommy ce ta kira tana son magana da Junior shine na ce baya kusa, da ta sake kira da dare still na ce ba ya kusa shine ta sa dole na gaya ma ta inda ya ke. Sai kawai na faÉ—a ma ta komai"

"Nan gaba ba ni ba jan labule da kai"

"Tuba na ke ranka shi daÉ—e" Salman ya faÉ—a yana dariya...

Wani ƙaton gida motocin su ka shiga yayinda 'yan biyu ke ta ihun murna harda rige-rigen fita lokacin da motar ta tsaya. Da ke gidan ba baƙon su ba ne tuni su ka shige cikin gidan da gudu suna faɗin su za su fara ganin Baby.

"GrandMa" su ka faÉ—a ganin Mommy tsaye tana waya.

Rungumeta su ka yi suna tambayar ina ƙanwar su.

Mommy ta ce su je sama tana wajen Zaytoonah.

Itama É—in duk da ta san da zuwan su amma ba ta gayawa Zaytoonah duka gaskiyan ba, ce ma ta tayi 'yan biyu da Junior za su zo ba ta ce harda Galadima da 'ya'yan sa ba.

Zaytoonah na zaune bakin gado tana bawa Alinah nono 'yan biyu su ka shigo da gudu.

"Yehhhh mu muka fara kallon Baby"

"Ba na hanaku shigowa É—aki ba sallama ba"

"Sorry Mom" su ka faɗa suna riƙe kunne.

Hannu su ka sa suna shashshafa kan Alinah da goshin ta. Zaytoonah ta ce su bari ta ƙarisa su ganta da kyau.

"Mom, ina Baby Alinah da ni ta ke kama?" Hadid ya faÉ—a yana nuna kan sa.

"Dalla chan da ni ta ke kama, ko Mom?" Hashir ya faÉ—a yana yiwa Hadid gwalo.

"Kun zo fa kenan yaran nan, ba na son hayaniya Dan Allah"

"Mom su Daddy da su Suhailah ma sun zo"

"Ba na son ƙarya Hashir"

"Allah Mom"

Ba su ida maganar ba Junior da Suhailah su ka shigo É—akin followed ba Raziya da Falaq.

Yadda su ka yanyameta ya sa dole ta miƙa mu su 'yar ba tareda yarinyar ta ƙoshi ba.

Miƙewa ta yi ta fita daga ɗakin, so ta ke ta tabbatar da cewa da gaske dai tareda Galadima su ke.
Ta sama ta leƙa ta hango shi zaune suna magana da Mommy. Bai wani chanja ma ta ba sai dai furfura da za ta ce ya ƙara wanda kuma baiwa ce ya ke da shi, dan akwai dayawa da su ke da shekarun sa amma ba su da furfuran ko kuma na su bai kai haka ba.

Ta jima tana kallon shi, wani sabon sauƙin shi na zuwan ma ta. A ɓangare ɗaya tana jin kamar ta sauka da gudu ta je ta faɗa jikin sa, yayinda wani ɓangare ke ƙoƙarin tuna ma ta fa har yanzu tana fishi da shi. Ta jima tana kallon shi kafin ta koma ɗaki wajen yaran. Ba ta fi minti biyar da shigowa ba Mommy ta zo ta ce Raziya ta kaiwa Daddyn su Alinah a ƙasa.
Raziya ta riƙe yarinyar da kyau ta fita yayinda sauran su ka bi bayanta da sauri.

Zaytoonah da ta kwanta kamar mai bacci Mommy ta kalla ta ce "ki shirya ki je ku gaisa sannan ki duba guest room a ƙasa ko akwai abinda zai buƙata a kawo ma sa"

Yi ta yi kamar ba ta ji ba dan har Mommyn ta fita ba ta motsa ba.
Sai da ta ƙara minti huɗu akan gadon kafin ta miƙe da sauri.
Gaban mirror ta je ta duba kan ta sannan ta É—an fesa turare kafin ta fita daga É—akin.
Lokacin da ta sauko yana riƙe da yarinyar Raziya na mu su hoto.
Zama ta yi a kujera tana kallon su, sau ɗaya su ka haɗa ido da shi ya kauda kai kamar bai gan ta ba hakan ya sake tunzurata. Miƙewa ta yi ta wuce ɗakin baƙin da ke ƙasa ta duba duk wani abinda zai buƙata akwai a ɗakin. Bayan ta fito ne ta ce "Daddyn Raziya ko za ka shigo ka ɗan watsa ruwa"

End of Chapter 137Continue to the next chapter or choose another story below.

More Hausa novels

Browse all books →
Previous Login to Save Next