Ramadan Promo!All users that send a manual request for premium upgrade on sallah day will be granted for 1 month free.
Soyayyanovels
Zaytoonah Part One Complete Hausa Novel
Zaytoonah Part One Complete Hausa Novel
By Azizat
Login to keep your reading position saved.
Book Page Chapters
Zaytoonah Part One Complete Hausa Novel

Zaytoonah Part One Complete Hausa Novel

Author: Azizat
Chapter 89 of 161
About 8 min read
Chapter progress: 0%
Listen Mode
Listen to this chapter using your device voice.
Ready to listen from this chapter.
Free access is active. You can keep reading and download during this access window.

Book chapters

Choose a chapter and continue reading.

Start chapters
Chapter 1 1,689 words Chapter 2 1,523 words Chapter 3 1,583 words Chapter 4 1,696 words Chapter 5 1,682 words Chapter 6 1,693 words Chapter 7 1,594 words Chapter 8 1,673 words Chapter 9 1,663 words Chapter 10 1,668 words Chapter 11 1,678 words Chapter 12 1,698 words Chapter 13 1,687 words Chapter 14 1,699 words Chapter 15 1,656 words Chapter 16 1,634 words Chapter 17 1,681 words Chapter 18 1,675 words Chapter 19 1,655 words Chapter 20 1,613 words Chapter 21 1,669 words Chapter 22 1,655 words Chapter 23 1,671 words Chapter 24 1,650 words Chapter 25 1,677 words Chapter 26 1,696 words Chapter 27 1,598 words Chapter 28 1,699 words Chapter 29 1,694 words Chapter 30 1,659 words Chapter 31 1,683 words Chapter 32 1,309 words Chapter 33 1,691 words Chapter 34 1,697 words Chapter 35 1,553 words Chapter 36 1,588 words Chapter 37 1,682 words Chapter 38 1,680 words Chapter 39 1,677 words Chapter 40 1,649 words Chapter 41 1,700 words Chapter 42 1,698 words Chapter 43 1,676 words Chapter 44 1,625 words Chapter 45 1,633 words Chapter 46 1,675 words Chapter 47 1,693 words Chapter 48 1,668 words Chapter 49 1,688 words Chapter 50 1,647 words Chapter 51 1,653 words Chapter 52 1,568 words Chapter 53 1,689 words Chapter 54 1,699 words Chapter 55 1,669 words Chapter 56 1,578 words Chapter 57 1,564 words Chapter 58 1,660 words Chapter 59 1,694 words Chapter 60 1,415 words Chapter 61 1,653 words Chapter 62 1,690 words Chapter 63 1,685 words Chapter 64 1,618 words Chapter 65 1,652 words Chapter 66 1,674 words Chapter 67 1,687 words Chapter 68 1,699 words Chapter 69 1,644 words Chapter 70 1,698 words Chapter 71 1,691 words Chapter 72 1,671 words Chapter 73 1,689 words Chapter 74 1,679 words Chapter 75 1,677 words Chapter 76 1,678 words Chapter 77 1,655 words Chapter 78 1,683 words Chapter 79 1,696 words Chapter 80 1,700 words Chapter 81 1,694 words Chapter 82 1,697 words Chapter 83 1,692 words Chapter 84 1,668 words Chapter 85 1,554 words Chapter 86 1,666 words Chapter 87 1,677 words Chapter 88 1,694 words Chapter 89 Reading now Chapter 90 1,700 words Chapter 91 1,670 words Chapter 92 1,670 words Chapter 93 1,655 words Chapter 94 1,640 words Chapter 95 1,607 words Chapter 96 1,668 words Chapter 97 1,659 words Chapter 98 1,689 words Chapter 99 1,675 words Chapter 100 1,614 words Chapter 101 1,610 words Chapter 102 1,700 words Chapter 103 1,683 words Chapter 104 1,657 words Chapter 105 1,698 words Chapter 106 1,700 words Chapter 107 1,695 words Chapter 108 1,656 words Chapter 109 1,683 words Chapter 110 1,699 words Chapter 111 1,699 words Chapter 112 1,641 words Chapter 113 1,696 words Chapter 114 1,626 words Chapter 115 1,695 words Chapter 116 1,691 words Chapter 117 1,698 words Chapter 118 1,645 words Chapter 119 1,673 words Chapter 120 1,691 words Chapter 121 1,635 words Chapter 122 1,694 words Chapter 123 1,689 words Chapter 124 1,688 words Chapter 125 1,673 words Chapter 126 1,692 words Chapter 127 1,686 words Chapter 128 1,697 words Chapter 129 1,660 words Chapter 130 1,691 words Chapter 131 1,674 words Chapter 132 1,670 words Chapter 133 1,693 words Chapter 134 1,691 words Chapter 135 1,687 words Chapter 136 1,672 words Chapter 137 1,691 words Chapter 138 1,657 words Chapter 139 1,687 words Chapter 140 1,650 words Chapter 141 1,695 words Chapter 142 1,607 words Chapter 143 1,699 words Chapter 144 1,676 words Chapter 145 1,698 words Chapter 146 1,684 words Chapter 147 1,664 words Chapter 148 1,696 words Chapter 149 1,674 words Chapter 150 1,680 words Chapter 151 1,697 words Chapter 152 1,628 words Chapter 153 1,618 words Chapter 154 1,688 words Chapter 155 1,664 words Chapter 156 1,692 words Chapter 157 1,584 words Chapter 158 1,644 words Chapter 159 1,646 words Chapter 160 1,618 words Chapter 161 1,797 words

Ita ta fara zuwa wajen ko dan ta ƙagu su haɗun ne oho. Sai da ta yi kusan Minti shatakwas kafin ya iso.

"Yi haƙuri Dan Allah, sanda kika kira ina wanke Machine ɗina ne da na gama na fito kuma na haɗu da friend ɗina a bakin layi..."

"Ya wuce ai, da ban san hali ba ne sai na yi ƙorafi"

"Da gaske na chanja" yai maganar yana murmushi.

Sai da ya nitsu sosai kafin ta sanar da shi maganar da su ka yi da Mommy.

"CabÉ—i!" Abinda ya furta kenan bayan ya gama sauraron ta.

"CabÉ—i kuma?"

"To mi zan ce, abin ne na ji banbaraƙwai. Yanzu Mommy ta ina ma take so ki fara?"

"Wallahi ban sani ba Ya Auwal. Ita gani take abu ne mai sauƙi kuma case ɗin nan babban sauƙi ne"

"Gaskiya kam. Duk ban san dalilin ta na cewa ki jagoranci case ɗin nan ba amma gaskiyar magana shine indai ki ka ɗau case ɗin nan ba inda za aje za a kori ƙarar nan"

Zaytoonan ta haÉ—e rai ta ce "irin ka rena ni É—in nan"

"Sorry Dear, kin san ke É—in JJC ce"

Zaytoonah ta murguÉ—a ma sa baki...

Duk da Auwal ya sa baki Mommy ba ta chanja magana ba, abu ɗaya ta jaddada mu su. Ko dai Zaytoonah ta jagoranci case ɗin ko kuma ta haƙura da case ɗin har abada. Wannan ya sa jikin Zaytoonah yai sanyi, ta kuma ɗaura aniyar bin umurnin Mommy duk da tana hango mu su rashin nasara a case ɗin.

"Mommy na amince" ta faÉ—i maganar lokacin da Mommyn ke shirin kwanciya. Jin ba ta tanka ma ta ba ne ya sa ta sake maimaita maganar "Mommy na amince zan jagoranci case É—in nan"

Wannan karan Mommy ta kalleta briefly kafin ta É—auke ido ta ce "Allah ya shige mana gaba"
Zaytoonah ta amsa da Amin.

Washegari Mommy ta sanar da ita details É—in yadda take son komai ya tafi. It wasnt easy kamar yadda tayi hasashe É—in.

"Mommy gani da ke a gida amma sai kin tura ni wajen wani yayi coaching ɗina" ta yi maganar tana flipping ƙwan da ke cikin Pan yayinda Mommy ke juye ruwan tea cikin flask.

"Yaushe rabon na yi zaman kotu, ni yanzu ai Malama ce"

Zaytoonah ta sa dariya " Malama Mommy kenan"

"Ki faÉ—a da kyau dan hakan ta ke"

"GrandMa! Hashir is not brushing his teeth very well" muryan Hadid ya katse mu su hiran.

Mommy ta ce "to kinga É—alibai na nan"

Zaytoonah ta sa dariya...

***

Ta kai minti biyar tana tuƙa da warwara kan yadda za ta tura text message. Ba za ta iya kiran sa ba gaskiya dan tsoron harka da manyan mutane ta ke yi musamman ma shi da aka ce ma ta mai sarauta ne. Daga ƙarshe kawai ta tura ma sa *fatan an wuni lafiya, Bar. Zaytoonah ce wacce za ta zo wajen ka ranan Monday* ko yayi ko bai yi ba ita dai ta riga ta tura. Kamar yadda ba ta tsammanci reply ba hakanan har rana ta faɗi ba ta ga reply ɗinsa ba duk da kuwa tanada yaƙinin cewa ya ga message ɗin.

Haka dai ta shirya ta wuce Abuja yammacin ranan Lahdi kuma har lokacin ba ta ji daga gareshi ba. A gidan Muhsina ta sauka duk da kuwa akwai wasu 'yan uwan Zuhayr a Abujan amma gidan Muhsina ya fi mata saboda tafi sakewa a gidan. Mijin ta yanzu baya ƙasar ya je yin Phd ɗin sa a South Africa. Gidan daga ita sai 'ya'yan ta guda biyu Nabil da Aysha sai kuma Azma ƙanwar mijinta da ke tayata kwana.

Ba ta san ya aka yi baccin ta yai nauyi har haka ba, dan ko bugawar alarm ba ta ji ba. Sanda ta tashi har ƙarfe bakwai na safe ta shige da 'yan mintuna.

"Shine ba ki tasheni ba" ta faÉ—awa Muhsina da ke shirin kai yara Makaranta.

"Au ni fa har na manta yau za ki fara fita"

"Wannan yawan mantuwa na ki anya????"

"Rufa min asiri yaushe Abban Nabil ya zo gida"

"Na sani ko lokacin da ki ka je ma sa ziyara kin taho da tsaraba" Zaytoonah ta yi maganar tana dariya.

"Ki dai ƙaraci gulman ki ni banida komai".

Tare su ka karya da Azma dan itama sai lokacin ta ke tashi. Ba ta zuwa ko'ina dan tun lokacin da ta yi jarrabawan WAEC ta dawo Abuja da zama, ko jarrabawar JAMB da ta yi ma a nan É—in ta yi.
Lokacin da Zaytoonah ta isa Chamber ɗin ƙarfe goma har da rabi. Ita kanta ta san ba ta kyauta ba balle kuma wanda za ta je wajen na sa. Gaskiya wajen ya tsaru iya tsaruwa sai dai taste ɗin su wajen furnitures bai ma ta ba.
A wajen Sakatare ta zauna tana jiran tsammanin man Rabbuka bayan ya shaida ma ta ta jira Honorable yana aiki. Tun tana duba agogo har ta haƙura kawai ta cigaba da buga game a wayarta.
Minti talatin da biyu cur ta yi a wajen kafin Sakataren ya ce ta shiga office É—in.
Office ne mai girma da ya wadatu da shelves wanda ke cike da manyan litattafai. Ta kai duban ta ga mamallakin office ɗin wanda ke zaune akan kujera yana nazarin wasu litattafai guda uku da ke gaban sa. Mutumin da aka kira da Justice Yunus Muhammad Abbas fari ne sosai, yanayin farin sa yana zubi da Larabawa, furfura daya wadaci sajen sa da gemun sa shi zai sa ka ma sa tunanin shekaru irin sittin ɗin nan amma a zahiri shekarun sa Arba'in da shida ne. Allah dai ya bashi baiwar furfuran ne, hatta gashin kan sa kusan rabi da furfuran. Sanye ya ke da baƙin suit, da ke a buɗe ta ke kana ganin farin shirt ɗin da ke ciki. Ko bai sa tie ba ne ko dai ya cire dan ba ta ga tie a wuyan sa ba.

"Good morning Sir" ta bashi 'yan sakanni amma ta ga shiru bai amsa ba, ta ɗan ƙara ɗaga murya ta ce "Barrister Zaytoonah Tijjani Abubakar Sir"
Still shiru bai yi magana ba bai kuma É—ago ya kalleta ba.
Tsaki ta yi a ranta tana faÉ—in Girman kai rawanin tsiya.
Ba za ta manta walaƙanci da ya mu su ba ranan da su ka haɗu a gidan sa, bai yaba aikin su ba, bai ma nuna ya ji daɗin aikin ba. Yana gama dubawa da ya sauko ƙasa lokacin suna hira da Hajiya Ni'ima ya ce "Hajiya Ni'ima a tambaye su nawa ne kuɗin su" daga haka ya fice a falon, tana ma shirin gaishe shi ne amma jin abinda ya faɗa ya sa ta ja bakin ta tayi shiru. Tsabar haushi ma ranan ƙin ba da account number ɗin ta tayi sai kawai ta bada business account na kamfanin Alhaji Ibrahim. Kuɗin ma yafewa ta yi, dan da su ka yi magana da Alhaji Ibrahim ce ma sa tayi payment ɗin kaya ne dana sauran ma'aikatan da su ka tayata aiki ita ta cire na ta.

"Sarauta my foot" ta faÉ—i a zuciyarta haÉ—eda yin tsaki.

Tun tana sa ran zai yi magana har ta gaji, ta yi yunƙurin magana for the last time dan ta yi Alƙawarin daga wannan kam tafiyarta za ta yi ta fasa koyon aiki a wajen sa. Ita kam yadda Mommy ta yi ta yabon wannan mutumin exactly opposite ɗin sa ta gani. A hakan wai Mommy ta yi aiki ƙarƙashin sa lokacin yana Judge of High court Kaduna.

"Sir ni ce wacce Barrister Maryam Nkiru ta maka magana akan za..."

"Idan kin koyi zuwa da wuri sai mu É—aura daga nan" abinda ya faÉ—a kenan still idon sa na kan littafi. Yadda yai maganar kamar ma ba da ita ya ke ba...

"Mommy Allah yana da girman kai, ko fa amsa gaisuwata bai yi ba"

Daga ɓangaren Mommy ta ce " ke ma laifin ki ne ai da ki ka je a makare. Barin gaya miki shi mutum ne mai tsari bai yadda da wasa da lokaci ba"

"Duk tsarin sa ai ba zai hana ya amsa common gaisuwa ba. Mommy ko kallona fa bai yi ba"

Mommy ta yi dariya ta ce "to Zaytoonah ya kalleki na me kenan?"

"Allah ni kam ki chanja min wani ba abinda zan koya a wajen sa sai girman kai"

"Idan ki ka nitsu ki ka fahimce shi Wallahi shi mutum ne mai sauƙin sha'ani"

"Ina ga dai shekarun baya kenan da kika yi aiki da shi, yanzu kam ya chanja"

"Galadima ba shi da girman kai Zaytoonah, wannan kam zan ma sa shaida akai"

Duk da Mommy ta faÉ—a ma ta haka itakam ba ta yarda ba tunda ta ga zahiri ba sau É—aya ba har sau biyu...

***

Bai koma gida da wuri ba sai bayan sallar Maghriba. Da sallama ya shigo falon yayinda fiskar sa ke É—auke da Murmushi. Falaq da Suhailah su ka yo wajen sa da gudu su ka rungume shi.

Sai da ya kissing goshin su kafin ya kama hannun su duka biyu su ka ƙariso wajen da Hajia Ghazala da Raziya ke zaune.

"Ranka shi daÉ—e, barka da dawowa"

"Sannu da ƙoƙari" yai maganar yana tambayar Raziya ya jiki ta ce ma sa da sauƙi. Daren jiya bai samu yayi bacci ba saboda ciwon cikin da Raziya ta tashi da shi tsakar dare. Da su ka je Asibiti ne ake faɗa ma sa ai ciwon cikin period ne. Ashe 'yar ta sa an zama budurwa.

Tunda safe kuwa da Hajia Ghazala ta ji labari ta zo ta tare a gidan. Tuntuni take son tafiya amma kuma ba ta saka Galadima a ido ba ba abinda zai sa ta tafi dan haka ta cigaba da zama da yaran.

Wanka yai ya chanja kaya zuwa baƙar Jallabiya sannan ya fito dan ya wuce masallaci sai a lokacin ne Hajia Ghazala ke shirin tafiya. Bayan Allah ya kiyaye hanya da ya ma ta bai kuma cewa komai ba.

End of Chapter 89Continue to the next chapter or choose another story below.

More Hausa novels

Browse all books →
Previous Login to Save Next