Ramadan Promo!All users that send a manual request for premium upgrade on sallah day will be granted for 1 month free.
Soyayyanovels
Zaytoonah Part One Complete Hausa Novel
Zaytoonah Part One Complete Hausa Novel
By Azizat
Login to keep your reading position saved.
Book Page Chapters
Zaytoonah Part One Complete Hausa Novel

Zaytoonah Part One Complete Hausa Novel

Author: Azizat
Chapter 17 of 161
About 8 min read
Chapter progress: 0%
Listen Mode
Listen to this chapter using your device voice.
Ready to listen from this chapter.
Free access is active. You can keep reading and download during this access window.

Book chapters

Choose a chapter and continue reading.

Start chapters
Chapter 1 1,689 words Chapter 2 1,523 words Chapter 3 1,583 words Chapter 4 1,696 words Chapter 5 1,682 words Chapter 6 1,693 words Chapter 7 1,594 words Chapter 8 1,673 words Chapter 9 1,663 words Chapter 10 1,668 words Chapter 11 1,678 words Chapter 12 1,698 words Chapter 13 1,687 words Chapter 14 1,699 words Chapter 15 1,656 words Chapter 16 1,634 words Chapter 17 Reading now Chapter 18 1,675 words Chapter 19 1,655 words Chapter 20 1,613 words Chapter 21 1,669 words Chapter 22 1,655 words Chapter 23 1,671 words Chapter 24 1,650 words Chapter 25 1,677 words Chapter 26 1,696 words Chapter 27 1,598 words Chapter 28 1,699 words Chapter 29 1,694 words Chapter 30 1,659 words Chapter 31 1,683 words Chapter 32 1,309 words Chapter 33 1,691 words Chapter 34 1,697 words Chapter 35 1,553 words Chapter 36 1,588 words Chapter 37 1,682 words Chapter 38 1,680 words Chapter 39 1,677 words Chapter 40 1,649 words Chapter 41 1,700 words Chapter 42 1,698 words Chapter 43 1,676 words Chapter 44 1,625 words Chapter 45 1,633 words Chapter 46 1,675 words Chapter 47 1,693 words Chapter 48 1,668 words Chapter 49 1,688 words Chapter 50 1,647 words Chapter 51 1,653 words Chapter 52 1,568 words Chapter 53 1,689 words Chapter 54 1,699 words Chapter 55 1,669 words Chapter 56 1,578 words Chapter 57 1,564 words Chapter 58 1,660 words Chapter 59 1,694 words Chapter 60 1,415 words Chapter 61 1,653 words Chapter 62 1,690 words Chapter 63 1,685 words Chapter 64 1,618 words Chapter 65 1,652 words Chapter 66 1,674 words Chapter 67 1,687 words Chapter 68 1,699 words Chapter 69 1,644 words Chapter 70 1,698 words Chapter 71 1,691 words Chapter 72 1,671 words Chapter 73 1,689 words Chapter 74 1,679 words Chapter 75 1,677 words Chapter 76 1,678 words Chapter 77 1,655 words Chapter 78 1,683 words Chapter 79 1,696 words Chapter 80 1,700 words Chapter 81 1,694 words Chapter 82 1,697 words Chapter 83 1,692 words Chapter 84 1,668 words Chapter 85 1,554 words Chapter 86 1,666 words Chapter 87 1,677 words Chapter 88 1,694 words Chapter 89 1,667 words Chapter 90 1,700 words Chapter 91 1,670 words Chapter 92 1,670 words Chapter 93 1,655 words Chapter 94 1,640 words Chapter 95 1,607 words Chapter 96 1,668 words Chapter 97 1,659 words Chapter 98 1,689 words Chapter 99 1,675 words Chapter 100 1,614 words Chapter 101 1,610 words Chapter 102 1,700 words Chapter 103 1,683 words Chapter 104 1,657 words Chapter 105 1,698 words Chapter 106 1,700 words Chapter 107 1,695 words Chapter 108 1,656 words Chapter 109 1,683 words Chapter 110 1,699 words Chapter 111 1,699 words Chapter 112 1,641 words Chapter 113 1,696 words Chapter 114 1,626 words Chapter 115 1,695 words Chapter 116 1,691 words Chapter 117 1,698 words Chapter 118 1,645 words Chapter 119 1,673 words Chapter 120 1,691 words Chapter 121 1,635 words Chapter 122 1,694 words Chapter 123 1,689 words Chapter 124 1,688 words Chapter 125 1,673 words Chapter 126 1,692 words Chapter 127 1,686 words Chapter 128 1,697 words Chapter 129 1,660 words Chapter 130 1,691 words Chapter 131 1,674 words Chapter 132 1,670 words Chapter 133 1,693 words Chapter 134 1,691 words Chapter 135 1,687 words Chapter 136 1,672 words Chapter 137 1,691 words Chapter 138 1,657 words Chapter 139 1,687 words Chapter 140 1,650 words Chapter 141 1,695 words Chapter 142 1,607 words Chapter 143 1,699 words Chapter 144 1,676 words Chapter 145 1,698 words Chapter 146 1,684 words Chapter 147 1,664 words Chapter 148 1,696 words Chapter 149 1,674 words Chapter 150 1,680 words Chapter 151 1,697 words Chapter 152 1,628 words Chapter 153 1,618 words Chapter 154 1,688 words Chapter 155 1,664 words Chapter 156 1,692 words Chapter 157 1,584 words Chapter 158 1,644 words Chapter 159 1,646 words Chapter 160 1,618 words Chapter 161 1,797 words

A haka dai lokaci yai ta tafiya har ta kai watan Nkiru goma a garin Ringim. Ba tareda wani ya tursasata ba, ita da kan ta ta ji son wannan addini, tun lokacin Azumi addinin ya fara burgeta. Yadda Goggo ke tashi tana sallar dare a goman ƙarshe abun ya tsaya ma ta a rai, gashi bauta ta ke yi amma ba hayaniya ba tashin hankali. Ta kan tambayi T J ko su Malam Abdullahi akan addinin musulunci kuma a hankali ta fara ganin girman wannan addini. Akwai abubuwa da su ka shige ma ta duhu shiyasa tun da jimawa ba ta gama amincewa da addinin ba amma a hankali komai ya fara warwarewa. Kullum tana addu'an idan addinin T J ne gaskiya Allah ya sa ta ji tana son addinin. Kuma yadda T J ke fassara ma ta wa su ayoyi hakan ya ƙara sa ma ta sha'awar wannan addini.

Wata ranan Jummu'ah ta samu Goggo da ta idar da sallar la'asar ta ce tana so ta koya ma ta sallah. Goggo ba ta gama fahimtar maganarta ba dan haka ta sa aka kira ma ta Pendo dan ta ma ta bayani da kyau.
Da Pendo ta zo ta sake maimaita zancenta. Pendo ta yiwa Goggo bayani Goggo ta É—au Kabbara tana faÉ—in "ki tambayeta tana son musulunta ne? Tana son yin addini kamar na mu?"

Duk tambayar da aka ma ta sai ta ce eh.

Goggo ta sa aka nemo ma ta Baffah inda Nkiru ta sake maimaita sha'awarta na son karɓan musulunci. A yammacin ranan aka kai ta gaban malami inda ta karɓi kalmar shahada.
Zo ka ga murna a wajen 'yan gidan su T J, wanda ke ƙyamatarta a da yanzu su ne su ke ta jan ta a jiki suna ta rungumarta.

Daren ranan kuwa Muntari ya dira a gidan, a bakin Iya ya ke jin wai Boɗɗiyon Tijjani ta musulunta. Ita har da ƙarawa da cewa " ni ban yarda musulunta ta yi ba, yaudara ce kawai irin ta Arna"

Shi kam Muntari jin maganar Iya ya sa wani sanyi ya shigeshi lokaci guda, bai san ma sanda ya tashi ya bar É—akin ba ya nufi É—akin Goggo. Sai dai da Goggon da Nkirun ba sa É—aki ya tambayi Asma'u ta ce ba ta san inda su ka je ba. ÆŠakin Baffah ya wuce dan ya samu abunda ya jima yana muradi, maganar Goggo ta tabbata, yanzu da Nkiru ta musulunta babu mai aibanta auran su.

Yana zuwa kuwa ya ci sa'a Baffan na É—aki " Baffa maganar kwanakin baya ne na zo da ita"

"Wacce magana kenan?"

"Auren Mary"

"Maryam" Baffah ya gyara ma sa

"Yawwa auren Maryam"...

*Don samun daman karanta cigaban labarin za a biya 300 ta account number kamar haka:*
3099546325
Firstbank
Azizat Hamza
*ko kuma katin MTN na 300 zuwa ga wannan numbar 08137311900*
Za'a tura Shaidar biya zuwa ga wannan numbar still 08137311900 ko kuma ma dai domin ƙarin bayani za a iya tuntuɓar numban, preferably chat ko text.
*Allah ya ba da ikon biya amin*
2/11/21, 10:04 PM - ****: *Chronicles of*
*...... ...... .......ZAYTOONAH*

https://m.facebook.com/Inside-Arewa-Writers-107691760958755/?ref

𝕀ℕ𝕊𝕀𝔻𝔼 𝔸ℝ𝔼𝕎𝔸 𝕎ℝ𝕀𝕋𝔼ℝ𝕊©
*(Ƙungiyar Nazarin Harshen Hausa)*

Rubutawa.....Azizat
Wattpad@Azi_zat

*Free page*
*9-good news*

Bismillahir Rahmanir Rahim

Karatu Maryam ta ke babu kama hannun yaro. Yanzu kam tunda aka rufe wannan case ɗin nan ta cire rai da samun soyayyar Iya. Matar ta tsaneta to the core dan haka itama ta kama kan ta, ko sun je Ringim ba ta ko shiga ɗakinta. Sau ɗaya da ta yi ƙoƙarin shiga ta gaisheta daga bakin ƙofa Iya ta wurgeta da mafifici hakan ya sa ta fita da sauri. Tun lokacin ko kallo ƙofar ɗakin Iya ba ta yi.
Ita Iya yanzu ba ta da abokiyar gaba a duniya irin Maryam. Tunda Maryam ta zo gidan su komai ya lalace, Baffah har ya rasu fishi ya ke da ita saboda ta ƙi karɓan Maryam hannu bibbiyu. Ga uwa uba Muntari da har yau ba ta ji ɗuriyar sa ba tunda ya ce zai je Lagos. Ga uwa uba irin zagin da sarakanan ta su ka ma ta duk dan akan Maryam ɗin. Wai ace saboda Maryam Inyamura ɗan ta ya bar gida ya ƙi dawowa ba abinda ya fi wannan ci ma ta tuwo a ƙwarya.

Babban damuwarta shine yanda har yanzu shiru ba ta samu ciki ba. Goggo kan ce ma ta haihuwa lokaci ne idan Allah ya nufa lokacinta yai za ta samu.
Itama ba ta haifi Ruma ba sai da ta yi shekara huÉ—u da marigayi mijinta. Ko 'ya'ya ukun da ta haifa da Baffah haka ta haifesu da ratan shekara hurhuÉ—u ba plannning ba komai.

A ɓangaren T J ma yana son ganin Maryam ta samu ciki ko dan hankalinta ya kwanta to amma Allah ke ba da haihuwa.

Sadiq kam yau lafiya gobe ba lafiya ne, ita kan ta Hajjo rashin lafiyar Sadiq É—in ya sa ta É—an yi hankali kaÉ—an.
T j ya zaunar da ita ya ma ta bayanin ciwon Sadiq tareda gaya ma ta matuƙar su ka cigaba da zama za ta iya haihuwan 'ya'ya ma su irin lalurar sa. Ya ce ma ta zai sawwaƙa ma ta idan ya so sai ya karɓi Sadiq ɗin shi da Maryam za su raine shi, idan yana da tsawon rai to idan kuma ba mai zama ba ne duk ƙaddarar da Allah ya rubuta ma sa za su amsa hannu bibbiyu.
Amma fir Hajjo ta ƙi karɓan wannan shawara. Ita ba abinda ta ke gani irin ƙasƙanci ne T J ya saketa ya cigaba da zama da Maryam ƙabila wai har ma Maryam ce za ta reni ɗan da ta sha wahala ta haifa. Ta ce ko za su haifi irin Sadiq goma ne ba za ta rabu da shi ba.

Tsoron fushin Iya ya sa bai sawwaƙa wa Hajjo ba, yana lallaɓata ne ƙila idan ta amince su rabun Iya ba za ta ji haushi ba sai dai da Hajjon da Iyan duk sammakal. Abinda ake nuna mu su daban, abinda su ke dubawa daban.

Shekaran Sadiq biyu da wata biyar ya rasu. Ba T J da Hajjo kaɗai ba hatta Maryam ta ji mutuwar yaron nan dan tana son sa sosai. Shi ya fara kiranta da sunan Uwa a duniya "Ama" haka ya ke kiranta. A da Hajjo ba ta bari ta taɓa ma ta shi amma tun wani rana da ciwon sa ya tashi T J baya gari ta ga Maryam ne ta tsaya ma ta har aka kaishi asibiti aka yi komai sai ta janye takunkumin da ta sa, ta fara barin Maryam na riƙe yaron a hankali har yaron ma ya fi sabawa da Maryam ɗin.
Maryam yadda ta ke son yaron ita ne yi ma sa wanka, wanke kayan sa. Tsabar samun guri ko yana wajen Hajjo yai kashi indai Maryam na nan haka za ta kawo wa Maryam ta ce ga ɗan ta yayi kashi, Maryam ta karɓeshi ta ma sa tsarki ta gyara shi.

Ranan da ta fara gwada goyonsa kasa tashi ta yi ta zauna a bakin gado tana nan jijjiga shi, tana tsoron ƙila idan ta tashi faɗowa zai yi. A haka T J ya dawo ya sameta yai ta mata dariya daga baya daya ga ta yi fishi sai ya ce ma ta ta tashi ba abinda zai samu Sadiq. Sai da ta miƙe ta sa hannu ta baya incase ta ji zai faɗo ta taro shi shi kuma ya kama hannunta yana murmushi.
"See ba zai faÉ—o ba"

Sai kuma ta fashe da dariya. TJ ya kissing goshinta ya ce "Insha Allahu ke ma naki na zuwa"...

Lokacin rasuwan Sadiq saura ma ta sati ɗaya ta fara jarrabawarta na ƙarshe a makaranta. Ta dai yi jarrabawan ne kawai amma har lokacin mutuwar yaron bai saketa ba musamman da Inna Saratu ta zo mu su ta'aziyar ta dinga habaici tana referring mutuwar Sadiq da cewa "cinyeshi aka yi"
Iya kam ba ta zo ba duk da kuwa Alhaji Isa ya ba su damar su je Zaria su yi ta'aziya. Bayan anyi ukun yaron kowa ya watse amma Inna Saratu sai da ta tsaya ta ƙara kusan sati biyu wai tana kula da Hajjo.

Kasancewarta matar aure yasa ta nemi yin Service na ta a Kaduna kuma ta samu. Da farko cikin Kaduna ta ke PPA É—inta T J ya ce bai yarda ba dole ta kuma neman alfarma aka dawo da ita Zaria.

Zaman na su dai gwanin sha'awa ranakun girkinta tana samun kulawa sosai wajen T J haka itama tana ajiye duk wani kishi ta tarairayi mijinta. Ba ta da matsala da Hajjo daya wuce baƙar ƙazantar ta wanda har yau ta kasa ɗaukan gyara, ita har mamaki ta ke yi yadda za ta ga ta wuni ba ta yi wanka ba sai zani kaɗai da za ta dinga yawo da shi. Idan ta yi wanka da safe to T J na ɗakinta ne nan ma ta tabbata T J ke matsa ma ta takeyi. Amma indai ba ranan girkinta ba ne to sai yamma ta ke wanka wani lokaci ma haka ta ke kwana ba tareda ta yi wankan ba. Ko lokacin zafi da Maryam ke wanka so goma da ashirin a rana ita Hajjo da ƙyar ta ke yin biyu.
Haihuwa É—aya amma ta lalace. Ko Maryam da ta girmeta ba ta yi tsufan da Hajjo ta yi ba kuma a hakan ba ta cika shekara ishirin ba har yanzu, dan tana shekara shabiyar T J ya aureta.

Wasa-wasa sai gashi Maryam ta ƙare bautar ƙasarta.
Watarana da safe Maryam na soya doya da ƙwai a kitchen saboda ita ke da girki sai ga Hajjo ta fito daga ɗaki da gudu ta shige banɗaki tana kela amai. Bayan ta fito ne Maryam ta fara ma ta sannu saboda ta ji yadda ta ke ta ƙaƙarin aman kaman za ta amayar da kayan cikinta.

"Sannu Hajjo, ba ki da lafiya ne dama?"

Hajjo ta fara shafa cikinta tana ɗaɗɗaga hanci ta ce "ƊanBaba baya son ƙarnin ƙwai"

Maryam ba ta gane hausarta ba tace "waye ÆŠanBaba?"

End of Chapter 17Continue to the next chapter or choose another story below.

More Hausa novels

Browse all books →
Previous Login to Save Next