Ramadan Promo!All users that send a manual request for premium upgrade on sallah day will be granted for 1 month free.
Soyayyanovels
Zaytoonah Part One Complete Hausa Novel
Zaytoonah Part One Complete Hausa Novel
By Azizat
Login to keep your reading position saved.
Book Page Chapters
Zaytoonah Part One Complete Hausa Novel

Zaytoonah Part One Complete Hausa Novel

Author: Azizat
Chapter 27 of 161
About 8 min read
Chapter progress: 0%
Listen Mode
Listen to this chapter using your device voice.
Ready to listen from this chapter.
Free access is active. You can keep reading and download during this access window.

Book chapters

Choose a chapter and continue reading.

Start chapters
Chapter 1 1,689 words Chapter 2 1,523 words Chapter 3 1,583 words Chapter 4 1,696 words Chapter 5 1,682 words Chapter 6 1,693 words Chapter 7 1,594 words Chapter 8 1,673 words Chapter 9 1,663 words Chapter 10 1,668 words Chapter 11 1,678 words Chapter 12 1,698 words Chapter 13 1,687 words Chapter 14 1,699 words Chapter 15 1,656 words Chapter 16 1,634 words Chapter 17 1,681 words Chapter 18 1,675 words Chapter 19 1,655 words Chapter 20 1,613 words Chapter 21 1,669 words Chapter 22 1,655 words Chapter 23 1,671 words Chapter 24 1,650 words Chapter 25 1,677 words Chapter 26 1,696 words Chapter 27 Reading now Chapter 28 1,699 words Chapter 29 1,694 words Chapter 30 1,659 words Chapter 31 1,683 words Chapter 32 1,309 words Chapter 33 1,691 words Chapter 34 1,697 words Chapter 35 1,553 words Chapter 36 1,588 words Chapter 37 1,682 words Chapter 38 1,680 words Chapter 39 1,677 words Chapter 40 1,649 words Chapter 41 1,700 words Chapter 42 1,698 words Chapter 43 1,676 words Chapter 44 1,625 words Chapter 45 1,633 words Chapter 46 1,675 words Chapter 47 1,693 words Chapter 48 1,668 words Chapter 49 1,688 words Chapter 50 1,647 words Chapter 51 1,653 words Chapter 52 1,568 words Chapter 53 1,689 words Chapter 54 1,699 words Chapter 55 1,669 words Chapter 56 1,578 words Chapter 57 1,564 words Chapter 58 1,660 words Chapter 59 1,694 words Chapter 60 1,415 words Chapter 61 1,653 words Chapter 62 1,690 words Chapter 63 1,685 words Chapter 64 1,618 words Chapter 65 1,652 words Chapter 66 1,674 words Chapter 67 1,687 words Chapter 68 1,699 words Chapter 69 1,644 words Chapter 70 1,698 words Chapter 71 1,691 words Chapter 72 1,671 words Chapter 73 1,689 words Chapter 74 1,679 words Chapter 75 1,677 words Chapter 76 1,678 words Chapter 77 1,655 words Chapter 78 1,683 words Chapter 79 1,696 words Chapter 80 1,700 words Chapter 81 1,694 words Chapter 82 1,697 words Chapter 83 1,692 words Chapter 84 1,668 words Chapter 85 1,554 words Chapter 86 1,666 words Chapter 87 1,677 words Chapter 88 1,694 words Chapter 89 1,667 words Chapter 90 1,700 words Chapter 91 1,670 words Chapter 92 1,670 words Chapter 93 1,655 words Chapter 94 1,640 words Chapter 95 1,607 words Chapter 96 1,668 words Chapter 97 1,659 words Chapter 98 1,689 words Chapter 99 1,675 words Chapter 100 1,614 words Chapter 101 1,610 words Chapter 102 1,700 words Chapter 103 1,683 words Chapter 104 1,657 words Chapter 105 1,698 words Chapter 106 1,700 words Chapter 107 1,695 words Chapter 108 1,656 words Chapter 109 1,683 words Chapter 110 1,699 words Chapter 111 1,699 words Chapter 112 1,641 words Chapter 113 1,696 words Chapter 114 1,626 words Chapter 115 1,695 words Chapter 116 1,691 words Chapter 117 1,698 words Chapter 118 1,645 words Chapter 119 1,673 words Chapter 120 1,691 words Chapter 121 1,635 words Chapter 122 1,694 words Chapter 123 1,689 words Chapter 124 1,688 words Chapter 125 1,673 words Chapter 126 1,692 words Chapter 127 1,686 words Chapter 128 1,697 words Chapter 129 1,660 words Chapter 130 1,691 words Chapter 131 1,674 words Chapter 132 1,670 words Chapter 133 1,693 words Chapter 134 1,691 words Chapter 135 1,687 words Chapter 136 1,672 words Chapter 137 1,691 words Chapter 138 1,657 words Chapter 139 1,687 words Chapter 140 1,650 words Chapter 141 1,695 words Chapter 142 1,607 words Chapter 143 1,699 words Chapter 144 1,676 words Chapter 145 1,698 words Chapter 146 1,684 words Chapter 147 1,664 words Chapter 148 1,696 words Chapter 149 1,674 words Chapter 150 1,680 words Chapter 151 1,697 words Chapter 152 1,628 words Chapter 153 1,618 words Chapter 154 1,688 words Chapter 155 1,664 words Chapter 156 1,692 words Chapter 157 1,584 words Chapter 158 1,644 words Chapter 159 1,646 words Chapter 160 1,618 words Chapter 161 1,797 words

Wannan karan za ta cinye É—aya ne idan Mommy ta tambaya ta ce guda biyar ne ba shida ba.
Tana cikin ci ta ji an ja kunnenta ana murÉ—awa. Tsabar daÉ—in cake ba ta san yaushe Mommyn ta shigo kitchen É—in ba.

"Ba kya jin magana Zaytoonah, sau nawa ina hanaki É—aukan abu ba tareda kin tambaya ba"

Zaytoonah ta ɓare baki sai kuka shi kuma Salman sai dariya ya ke ma ta.

"Na hanaki kwaÉ—ayi Zaytoonah ba kya ji. Do you want me to beat you?" Tana maganar tana cigaba da murÉ—a ma ta kunne

"Kin fara ko, kin fara ko" ta tsinkayi muryan shi a kitchen É—in.

"Kai ka ke ɓata yarinyar nan, jiba yadda ta dawo fa, kalleta fa"

Ya kamo hannun Zaytoonah yana tambayar miya faru. Salman ya shiga ba da bahasin abinda Zaytoonan ta yi.
T J ya je ya buɗe fridge ɗin ya ɗauko cupcake guda biyu ya miƙa ma ta ya ce "dena kuka kinji, zo mu je ki ci wannan idan bai isheki ba zan ƙara miki"
Aikuwa ta dena kukan da ta ke ta karɓi cupcake ɗin ta fara ci. T J ya ja hannunta su ka bar wajen.

Maryam ta girgiza kai kawai ta koma wajen fridge ɗin dan taga ta'adin da Zaytoonah ta yi. Ta ci sa'a ma ba ta taɓa cake ɗin birthday ɗin ba...

Da dare tana decorating cake kusan ƙarfe takwas na dare sai ga T J ya shigo yi mu su sallama dan ba a gidan ta zai kwana ba.
"Sannu da aiki Uwargida ran gida"

"Sannu da lallashi" ta faÉ—a tana murmushi

Ya lakato buttercream icing É—in a hannun sa ya lashe.

"Dear kai dai da shan zaƙi"

"Ya zanyi, abinda ya fito damu daga ƙauye kenan"

Dariya ta fara shima ya tayata yi.

"Zan missing É—in ku sosai Maryam" ya faÉ—a bayan ya dena dariyan

"Muma haka"

Shiru ne ya biyo bayan abinda ta ce. Sai chan T J ya ja dogon numfashi ya ce

"Maryam ba dan hali na ba, ba kuma dan halin Iya ko Hajjo ba Dan Allah zan bar miki amanar Humairah da Sadiq musamman ma Sadiq, ki yi haƙuri ta kula min da su"

Shekara ɗaya bayan Maryam ta haifi Salman Hajjo ta sake haihuwa itama ta samu Abubakar Sadiq kuma still shi ɗin ma Sickler ne, sai dai shi har yanzu yana raye. Shekara biyun farko sun ɗauka ba zai yi rai ba dan yadda ciwon sa ke tashi a kai-a kai amma yanzu da ya cika shekara uku abin ya zo ma sa da sauƙi dan yanzu ma ana son sashi a makaranta idan an shiga sabon term.
Bayan haihuwan Sadiq T J ya kai Hajjo aka ma ta planning saboda yadda Hajjo ke saurin É—aukan ciki ba zai juri samun 'ya'ya SS ba, yaro ya wahala suma su wahala.

Murmushi ta yi ta ce " kar ka damu, Allah zai kula maka da mu gabaÉ—aya har ka je ka dawo"...

***

Bayan tafiyar T J gidan ya ma ta faɗi. A da kullum sai ta gan shi, ko da ba ita ke da girki ba zai zo ya duba ta da yaran da safe da kuma dare wani lokaci har da rana amma yanzu shikenan ba za ta sake ganin sa ba har sai ya shekara. Ya ce zai yi ƙoƙarin zuwa mu su bayan wata shida amma ta sani da wahala hakan ya yiwu.
Yaran ma kewar sa da su ke yasa kwana biyu sun nitsu ba sa damunta da rigima. Zaytoonah kuwa ta zama babbar banza dan kukan rashin Daddynta da ta ke yi ƙaninta Salman bai yi ba.
Kullum sai ta tambayi saura kwana nawa Daddy ya dawo Maryam ta ce ya kusa dawowa.

Bisa amanar 'ya'yan sa da ya bar ma ta koyaushe tana zuwa gidan Hajjo ta duba su. Iya dai har yau ba ta amsa gaisuwan Maryam itama Maryam É—in tana yi ne kawai dan ta fita hakkin ta.

Humairah kufulancin Iya ta É—auko shiyasa ba ta son Zaytoonah da Mommy kaman yadda ake kiran Maryam. Shi kam Sadiq da ya ganta zai fara murna.

Makaranta É—aya Humairah su ke zuwa da Zaytoonah amma ajin su ba É—aya ba, duk da haka ba sa jituwa.
Wani lokaci idan Maryam ta yi abin marmari tana aika mu su ta ce a bawa yara.
Iya a ba ta son Maryam ɗin still idan Hajjo ta yi kaso ba ta raba da ita ba za ta ce ina nata. Hajjo kuwa sai ta ma ta tsiya kafin ta ba ta, dan ba ta da zuciya haka za ta ci. Ana kawo abinci daga gidan Maryam za ka ji falon ya buɗe da ƙanshi mai daɗi.

Ita kuwa Maryam kullum ta zo sai ta yi mamakin yadda su ka fara ɓata gidan T J. Falon gaba ɗaya ba kyan gani, ga wani wari-wari da ake ji ta rasa na minene, banɗaki da ba sa wankewa akai akai ne ko na rashin shara da moping da ba sa yi. Daga ka ga rigan yara a kan kujera sai ka ga an bar kwanukan da aka ci abinci ba a tattare ba. Wani lokacin ruwa ko kunu zai zube ba za a goge ba.
Tunda su ka raba gida indai T J zai yi baƙo ko gidan Maryam zai saukeshi ko da ba ranan girkinta ba ne idan ba hakan yai ba ba ƙaramin kunyata shi Hajjo za ta yi ba...

Tafiya ta ke da sauri sauri kaman za ta kife, so ta ke ta yi sauri ta kai abincin ta koma su ci na su abincin. Tsoronta kar kafin ta dawo sun kusa cinyewa.

Tana riƙe da kwandon abinci ta yi sallama sannan ta tura ƙofar falon gidan.

Iya ce a falon da Humairah su na kallo Iya na yiwa Humairah tsifa.

Ta tsani Iya, ba ta son ganinta ita ba dan Mommy ba ba abinda zai sa ta dinga zuwa gidan.

Ta ƙariso wajen glass centre table ɗin da ke falon ta ajiye kwandon abincin. Ta juya za ta tafi Iya ta ce " zo nan"

Zaytoonah ta juyo ta ƙura ma ta ido.
"Shegiya haka uwar ki ta koya miki rashin kunya ki shigo ba za ki gaida ni ba"

Ta turo baki ta ce "ni ba shegiya ba ce"
Iya ta tashi za ta make ta sai Zaytoonah ta sa gudu za ta fita sai gashi ta buge kwandon da ta ajiye a center table dama a baki-baki ta É—okana shi.
Miyan dai sai gashi ya zube

"Iya ki ga ta zubar mana da abinci" Humairah ta faÉ—a kaman za ta yi kuka

Iya ta ƙarisa ta damƙo Zaytoonah ta wanketa da mari. "Ba ki da hankali ko?"

Zaytoonah ta fashe da kuka

Hajjo da ke ɗaki ta leƙo tana Hamma. Gandar girki ta ke yi shiyasa ta zauna a ɗaki tana tsammanin girkin Maryam dan ta san yau Jummu'a jazaman ne za ta aiko mu su da abinci.
Tunda Sadiq ya ce ta dinga kawo mu su abinci kullum saboda abincinta ya fi daÉ—i yanzu kusan kullum sai ta kawo mu su. Idan ba a kawo na rana ba za a kawo na dare wani lokaci da na rana dana dare duk tana aikowa.

Ganin abinda ya faru ne ya sa Hajjo ta ja tsaki ta ce " yanzu gaba É—aya miyan ne ya malale?"

Humairah ta ce "akwai saura kaÉ—an"

"To wallahi ku É—ebe dan ba zan sake wani miya ba"

Iya ta zunguri ƙeyar Zaytoonah ta ce ta wuce ta ba su waje. Zaytoonah ta fita tana kuka.

Sai da ta kusa isowa gida ta ƙara volume ɗin kukanta, daga bakin ƙofa Auwal ya jawota jikin sa yana tambayan miya faru.
Ganin Mommy ta tsura ma ta ido ya sa ta ce "Iya ce ta mare ni"

Maryam ta san ba za ta yi ƙarya ba dan ba tarbiyyan da ta mata ba kenan. Amma kuma ba abinda za ta ce tunda ta san anyi hakan ne dan ta yi magana.

Maryam ta ce"Je ki wanke hannu ki zo mu ci abinci"

"Mommy" ta faÉ—a tana fashewa da wani sabon kukan

Maryam ta ce Auwal ya saketa ya zo su ci abinci. Tarbiyyan da ta É—aura mu su shine dukkan su suke haÉ—uwa su ci abinci a tray É—aya, ko T J na nan ma duk ranan girkinta indai yana nan dukkan su ke haÉ—uwa su ci abinci tare. Indai ta ware mu su abinci to Zaytoonah ne ta dameta da kukan yunwa sai ta zuba ma ta nata. Wani lokaci bayan taci idan sun zo za su ci na su itama za ta sa hannu a ci da ita.

Tana tsaye tana kukan sakalci ta ga Mommy ta serving abincin sun fara ci.
Ta dinga bin bakin su da kallo yadda su ke cin abinci hankali kwance, ganin Salman ya ɗau ƙatuwar hanta yana ci hakan ya sa ta ka sa haƙuri ta zo da gudu ta zauna. Za ta sa hannu Maryam ta daka ma ta tsawa dan haka ta yi hanyar kitchen a ɗari. Da ta dawo kuwa ta fi kowa ƙaton loma tanaci da sauri-sauri kaman abincin zai ƙare.
Tuwon shinkafa da miyan egusi daya ji naman kayan ciki da pomo ne sai ƙanshi miyan ke yi.

"Zaytoonah ki ci a hankali mana"

Auwal ya faÉ—a yana kallon yadda ta ke zare ido saboda ta cika bakinta da abinci kuma tuwon da zafi.

"Bar ta, idan ta ƙware za ta yi hankali"
Maryam ta faɗa tana kau da kai shi kuwa ya miƙo ma ta ruwa a kofi ta karɓa ta kora...

End of Chapter 27Continue to the next chapter or choose another story below.

More Hausa novels

Browse all books →
Previous Login to Save Next