Ramadan Promo!All users that send a manual request for premium upgrade on sallah day will be granted for 1 month free.
Soyayyanovels
Zaytoonah Part One Complete Hausa Novel
Zaytoonah Part One Complete Hausa Novel
By Azizat
Login to keep your reading position saved.
Book Page Chapters
Zaytoonah Part One Complete Hausa Novel

Zaytoonah Part One Complete Hausa Novel

Author: Azizat
Chapter 88 of 161
About 8 min read
Chapter progress: 0%
Listen Mode
Listen to this chapter using your device voice.
Ready to listen from this chapter.
Free access is active. You can keep reading and download during this access window.

Book chapters

Choose a chapter and continue reading.

Start chapters
Chapter 1 1,689 words Chapter 2 1,523 words Chapter 3 1,583 words Chapter 4 1,696 words Chapter 5 1,682 words Chapter 6 1,693 words Chapter 7 1,594 words Chapter 8 1,673 words Chapter 9 1,663 words Chapter 10 1,668 words Chapter 11 1,678 words Chapter 12 1,698 words Chapter 13 1,687 words Chapter 14 1,699 words Chapter 15 1,656 words Chapter 16 1,634 words Chapter 17 1,681 words Chapter 18 1,675 words Chapter 19 1,655 words Chapter 20 1,613 words Chapter 21 1,669 words Chapter 22 1,655 words Chapter 23 1,671 words Chapter 24 1,650 words Chapter 25 1,677 words Chapter 26 1,696 words Chapter 27 1,598 words Chapter 28 1,699 words Chapter 29 1,694 words Chapter 30 1,659 words Chapter 31 1,683 words Chapter 32 1,309 words Chapter 33 1,691 words Chapter 34 1,697 words Chapter 35 1,553 words Chapter 36 1,588 words Chapter 37 1,682 words Chapter 38 1,680 words Chapter 39 1,677 words Chapter 40 1,649 words Chapter 41 1,700 words Chapter 42 1,698 words Chapter 43 1,676 words Chapter 44 1,625 words Chapter 45 1,633 words Chapter 46 1,675 words Chapter 47 1,693 words Chapter 48 1,668 words Chapter 49 1,688 words Chapter 50 1,647 words Chapter 51 1,653 words Chapter 52 1,568 words Chapter 53 1,689 words Chapter 54 1,699 words Chapter 55 1,669 words Chapter 56 1,578 words Chapter 57 1,564 words Chapter 58 1,660 words Chapter 59 1,694 words Chapter 60 1,415 words Chapter 61 1,653 words Chapter 62 1,690 words Chapter 63 1,685 words Chapter 64 1,618 words Chapter 65 1,652 words Chapter 66 1,674 words Chapter 67 1,687 words Chapter 68 1,699 words Chapter 69 1,644 words Chapter 70 1,698 words Chapter 71 1,691 words Chapter 72 1,671 words Chapter 73 1,689 words Chapter 74 1,679 words Chapter 75 1,677 words Chapter 76 1,678 words Chapter 77 1,655 words Chapter 78 1,683 words Chapter 79 1,696 words Chapter 80 1,700 words Chapter 81 1,694 words Chapter 82 1,697 words Chapter 83 1,692 words Chapter 84 1,668 words Chapter 85 1,554 words Chapter 86 1,666 words Chapter 87 1,677 words Chapter 88 Reading now Chapter 89 1,667 words Chapter 90 1,700 words Chapter 91 1,670 words Chapter 92 1,670 words Chapter 93 1,655 words Chapter 94 1,640 words Chapter 95 1,607 words Chapter 96 1,668 words Chapter 97 1,659 words Chapter 98 1,689 words Chapter 99 1,675 words Chapter 100 1,614 words Chapter 101 1,610 words Chapter 102 1,700 words Chapter 103 1,683 words Chapter 104 1,657 words Chapter 105 1,698 words Chapter 106 1,700 words Chapter 107 1,695 words Chapter 108 1,656 words Chapter 109 1,683 words Chapter 110 1,699 words Chapter 111 1,699 words Chapter 112 1,641 words Chapter 113 1,696 words Chapter 114 1,626 words Chapter 115 1,695 words Chapter 116 1,691 words Chapter 117 1,698 words Chapter 118 1,645 words Chapter 119 1,673 words Chapter 120 1,691 words Chapter 121 1,635 words Chapter 122 1,694 words Chapter 123 1,689 words Chapter 124 1,688 words Chapter 125 1,673 words Chapter 126 1,692 words Chapter 127 1,686 words Chapter 128 1,697 words Chapter 129 1,660 words Chapter 130 1,691 words Chapter 131 1,674 words Chapter 132 1,670 words Chapter 133 1,693 words Chapter 134 1,691 words Chapter 135 1,687 words Chapter 136 1,672 words Chapter 137 1,691 words Chapter 138 1,657 words Chapter 139 1,687 words Chapter 140 1,650 words Chapter 141 1,695 words Chapter 142 1,607 words Chapter 143 1,699 words Chapter 144 1,676 words Chapter 145 1,698 words Chapter 146 1,684 words Chapter 147 1,664 words Chapter 148 1,696 words Chapter 149 1,674 words Chapter 150 1,680 words Chapter 151 1,697 words Chapter 152 1,628 words Chapter 153 1,618 words Chapter 154 1,688 words Chapter 155 1,664 words Chapter 156 1,692 words Chapter 157 1,584 words Chapter 158 1,644 words Chapter 159 1,646 words Chapter 160 1,618 words Chapter 161 1,797 words

Bayan Ahmad ya zo gidan ne ta bashi flash akan ya je ya turawa Justice report É—in ta dan tafiya gida za ta yi an mu su rasuwa ba ta tunanin za ta dawo da wuri.

Bayan ya ma ta ta'aziya ne ya ce " da dai kin kai ma sa da kan ki dan Justice yanada wuyan sha'ani zai iya cewa ba za karɓa ba"

Da farko Zaytoonah ba ta yarda ba amma daga baya sai ta amince amma da sharaɗin Ahmad ɗin ne zai kai ta gidan ya kuma dawo da ita gida dan ba ta tuƙi da dare.

Mai aiki ce ta buɗe mu su ƙofa ta kuma sanar da su Justice bai dawo daga masallaci ba. Zama su ka yi a falo suna jiran sa, bai jima ba sai gashi ya dawo sanye da farar jallabiya wacce ta zauna ma sa dai dai jikin sa.
Suna ganin sa su ka miƙe suna gaishe shi. Sau ɗaya ya kalli Zaytoonah ya kuma kauda kai ya maida duban sa ga Ahmad wanda ke ma sa bayanin dalilin zuwan su. Yadda ya ga idon Zaytoonah a kumbure ya isa ya tabbatar ma sa wanda ya rasun na kusa da Zaytoonan ne sosai.

Bayan ya gama jin sa ne ya yiwa Zaytoonah ta'aziya tareda haurawa sama dan ya É—auko laptop É—in sa.

Yaran sa ba sa nan sun wuce Zaria tareda Hajiya Ghazala É—azu da rana bayan sun dawo daga school. Shima zai je amma sai gobe dan zai tsaya ya attending auren 'yar abokin sa tukunna.

Suna zaune sai Ahmad ya miƙe akan zai yi fitsari. Ɗakin baƙi da ke ƙasa ya shiga, da ya fito ya ga Zaytoonah na zaune tayi tagume. Tsokalar ta yai niyyan yi dan haka ya ƙarisa wajen switch na wutan falon ya kashe.

Zaytoonah na zaune ta yi nisa cikin tunani sai kawai ta ga duhu. Nan da nan hankalin ta ya tashi numfashin ta ya fara fita da sauri-sauri.

*ZAYTOONAH* aka kira sunan ta a hankali. Ta wajen da ta ji kiran ta juya ta ga kamar alamar mutum ta wajen labule. Fuskar Ben kawai ta ke gani na ma ta yawo a idonta. Ta ƙwalla ƙara wanda sai da dukkan gidan ya amsa.

Tashi ta yi tana tafiya da baya-baya.

"Zuhayr save me, he's going to kill me Zuhayr. Save me, save me"

Jin kalaman ta ya sa Ahmad yai saurin kunna wutan. A takure jikin bango ya hango Zaytoonah tana maƙyarƙyata tana sunbatu.

Da gudu Justice ya fito daga É—aki jin ihun Zaytoonah. Ahmad da mai aikin sa
ne a gefen Zaytoonah suna tsaye suna ma ta magana amma sai baya takeyi jikin ta na kakkarwa kamar tsoron su ta ke yi.

"Uncle kamar ba ta da lafiya" Ahmad ya faÉ—a lokacin da ya ga Justice.

Kiran sunan ta yai a hankali kuma a dai-dai lokacin wutan gidan ya É—auke gaba É—aya. Hakan ya sa Zaytoonah ta sake birkicewa tana kuka tana kiran Zuhayr ya taimake ta.
Riƙota Justice yai yana faɗin "relax ni ne"

Muryan Zuhayr ta ji a kunnen ta dan haka ta shige jikin Justice da sauri tana faÉ—in " D Ben is here, zai kashe ni"

"Ba wanda zai kashe ki kin ji" ya faÉ—a da tausashashshiyar murya.

Tunanin Aljanu ke damunta dan haka ya kai bakin sa saitin kunnen ta yai Bismillah ya fara karanta ma ta suratul Fatiha cikin daddaɗar muryan sa. Yana gamawa ya ɗaura da Ayatul kursiyyu kafin ya ƙarisa aka maido da wutan gidan, still bai dena karatun ba ya cigaba da karanto ayoyin ruqya.
Kusan minti goma ya ɗauka yana karatun zuwa lokacin jikin Zaytoonah ya dena kakkarwa kuma nitsuwa ya shigeta. Tana son barin jikin Justice amma kunya ya hanata, ba ta san ya aka yi har ta tsinci kan ta a jikin sa ba, ƙila dai ciwon ta ne ya tashi.

Shirun da yai da karatun ne ya sa ta janye jikin ta daga nashi amma ba ta iya É—aga ido ta kalle shi ba.

"I'm sorry Zaytoonah, ba zan sake irin wannan wasan ba" Ahmad ya faɗa a raunane dan Allah na gani ya ruɗe da halin da ya ga Zaytoonah ta shiga cikin ƙanƙanin lokaci daga kashe wuta. Dama ya yi niyyar tsoratata ne amma abinda ya faru is beyond tunanin shi. Maganganun ta sun tabbatar ma sa da Zaytoonah ba ƙalau ta ke ba, dan ba abinda zai sa ta dinga cewa za a kashe ta.

Sau biyu tana kurɓan ruwan da aka ajiye ma ta kafin ta ce "zan tafi gida" ta yi maganar ne tana kallon Ahmad dan Justice kan ta kasa haɗa ido da shi. Tana ji Ahmad na ma sa bayanin abinda ya faru amma ba ta tanka mu su ba. To mi za ta ce mu su? Ta ina za ta fara mu su bayanin duk lokacin da ta tsinci kan ta a wajen duhu hankalin ta na tashi har ta faɗa yanayi na damuwa wanda ke kama da gushewar hankali.

A maimakon Ahmad da ya kawota wannan karan harda Justice aka maida ta gida, Dreban Justice da Ahmad na gaba ita kuma da Justice a baya. Ta san yayi hakan ne saboda ba ya so a barta ita É—aya.
Bai ce ma ta komai ba har su ka isa gidan, itama shiru ta yi kawai tana wasa da yatsun ta har su ka iso. Sai da za ta fita ya ce ma ta "Allah ya ƙara sauƙi" ta amsa da Amin sannan ta fita. Tana fita ya ce Ahmad ya rakata har bakin ƙofa...

A daren Justice ya kira Ni'ima yana tambayarta ko tana da labarin ko Zaytoonah na fama da wata matsala ko irin matsalan Aljanu haka ko kuma dai rashin lafiyar ƙwaƙwalwa. Ni'ima ta ce ba ta sani ba gaskiya amma za ta tambayi Mommy. Justice ya ce ta bari ba yanzu ba tunda tana cikin alhini an mu su rasuwa yau.

Saƙawa da warwara Justice ke yi yana ƙoƙarin gano matsalar Zaytoonah. Daga ƙarshe abinda ya riya a ran sa shine ba shafar Aljanu gareta ba kamar yadda yai hasashe sai dai ko wani abin daban. Daga baya ya ɗau waya ya fara browsing yana neman ƙarin haske gameda abinda ya faru ko zai samo amsar da kan sa.

***

Sati guda Zaytoonah da Mommy su ka yi a Ringim kafin su ka koma Zaria. Mutuwar Goggo ya taɓa su sosai ba kaɗan ba musamman Mommy wacce ta ke ganin Goggo a matsayin Uwa.

Iya ma ta kaɗu matuƙa da rasuwan kishiyar ta ta. Ba abinda ta ke tunawa face irin nasihohin Goggo a lokuta mabanbanta wacce ta ke nuna ma ta cewa rayuwar fa ƙayyadaddiya ce, duk min daren daɗewa mutuwa za ta zo ta riske ka. A lokacin ne kuma za ka gane cewa rayuwar duniya ba komai ba ne musamman idan ka yi ta bisa son zuciya.

A kwana na biyu da rasuwan ne Justice ya kira Mommy ya ma ta ta'aziya kuma ta ji daÉ—in hakan, dama ta daÉ—e da sanin cewa Justice ba shi da girman kai. Duk da yana so ya tambayeta gameda Zaytoonah amma sai ya ga hakan bai dace ba a lokacin.

Abinci ya ke ci da 'ya'yan sa Yammacin ranan Talata sai ga kiran Mommy ya shigo wayar sa. Ya É—auki wayar tareda yin sallama. Bayan sun gaisa ne Mommy ta ce ma sa a office ne yau Hajia Ni'ima ke tambayarta ko Zaytoonah na fama da matsalar Aljanu da ta tambayeta dalilin tambayar ne shine ta gano cewa daga wajen Justice ne.

"Zaytoonah ta samu panic attack lokacin kana wajen ko?" Ta yi tambayar cike da damuwa.

"Da alama ba ta son zama a cikin duhu" amsar da ya ba ta kenan.

"Ranka shi daÉ—e ba Aljanu gareta ba. PTSD ne ta ke fama da shi tun rasuwan mijin ta..."
A hankali ta warware ma sa matsalar Zaytoonah gaba ɗaya, dalilin abubuwan da Ben yai ta ma ta ne ya ke rikita ma ta ƙwaƙwalwa duk lokacin da ta tsinci kan ta a duhu.

Justice yai shiru yana sauraron ta cike da tausayin Zaytoonah, ashe sunan Zuhayr da ta ke ta kira mijin ta ne.

"Ina fata wannan ba zai jawo matsala ba idan Zaytoonah ta fara case É—in nan?"

"Insha Allahu ba abinda zai faru" ya amsa ma ta yana mai tattare da yaƙinin hakan...

Tsaye ya ke jikin madubi yana shiryawa. Damuwar da ke zuciyar sa ce ta watsu duk ilahirin jikin sa har ta kai ya ke jin kan sa kamar marar lafiya. Maganganun Mommy na jiya sun bala'in taɓa shi. Wani abu da ya ke ji na taso ma sa gameda Zaytoonan shiyasa tun farko ya ke kauda kan sa a kan ta yana kuma Allah-Allah zaman da Zaytoonah za ta yi ƙarƙashin sa ya ƙare tayi tafiyar ta. Sai dai bayanan Mommy sun dasa ma sa tausayin Zaytoonah wanda a yanzu ya sawa kan sa ko bayan an gama case ɗin nan zai yi ƙoƙarin taimaka ma ta har ta samu lafiya gaba ɗaya. Ko da hakan na nufin zai ɗauki wani mataki mai nauyi wanda ka iya chanja yanayin rayuwar sa da ta Zaytoonan gaba ɗaya...
2/11/21, 10:04 PM - ****: 42

Bismillahir Rahmanir Rahim

*groomed to seek justice*

Bayan hiran su da Mommy Zaytoonah ko baccin kirki ba ta iya yi ba. Duk ta inda ta auna sai ta ga ba abu ne mai yiwuwa ba, ta ina ma za ta iya representing Mommy a wannan case ɗin. Ƙwararren Lawyer ma sai yayi da gaske kafin ya iya cin case ɗin nan duba da yadda shekaru su ka ja da kuma rashin evidence a ƙasa. Ba za ta iya ba, abin da ta concluding kenan ta kuma sa a ranta za ta nemo one of the best Lawyer da ake da shi a ƙasar, ko nawa zai buƙata za ta biyashi domin ya taimakawa Mommy.

Washegari kamar ba abinda ya faru jiya haka Mommy ke walwalar ta, ita kuwa Zaytoonah ta kasa sakewa. Ƙarshe ma kiran Auwal ta yi akan tana son su haɗu da ke Sunday ne yana gida. Cewa yai su haɗu a wani gidan cin abinci nan da awa ɗaya.

End of Chapter 88Continue to the next chapter or choose another story below.

More Hausa novels

Browse all books →
Previous Login to Save Next