Ramadan Promo!All users that send a manual request for premium upgrade on sallah day will be granted for 1 month free.
Soyayyanovels
Zaytoonah Part One Complete Hausa Novel
Zaytoonah Part One Complete Hausa Novel
By Azizat
Login to keep your reading position saved.
Book Page Chapters
Zaytoonah Part One Complete Hausa Novel

Zaytoonah Part One Complete Hausa Novel

Author: Azizat
Chapter 31 of 161
About 8 min read
Chapter progress: 0%
Listen Mode
Listen to this chapter using your device voice.
Ready to listen from this chapter.
Free access is active. You can keep reading and download during this access window.

Book chapters

Choose a chapter and continue reading.

Start chapters
Chapter 1 1,689 words Chapter 2 1,523 words Chapter 3 1,583 words Chapter 4 1,696 words Chapter 5 1,682 words Chapter 6 1,693 words Chapter 7 1,594 words Chapter 8 1,673 words Chapter 9 1,663 words Chapter 10 1,668 words Chapter 11 1,678 words Chapter 12 1,698 words Chapter 13 1,687 words Chapter 14 1,699 words Chapter 15 1,656 words Chapter 16 1,634 words Chapter 17 1,681 words Chapter 18 1,675 words Chapter 19 1,655 words Chapter 20 1,613 words Chapter 21 1,669 words Chapter 22 1,655 words Chapter 23 1,671 words Chapter 24 1,650 words Chapter 25 1,677 words Chapter 26 1,696 words Chapter 27 1,598 words Chapter 28 1,699 words Chapter 29 1,694 words Chapter 30 1,659 words Chapter 31 Reading now Chapter 32 1,309 words Chapter 33 1,691 words Chapter 34 1,697 words Chapter 35 1,553 words Chapter 36 1,588 words Chapter 37 1,682 words Chapter 38 1,680 words Chapter 39 1,677 words Chapter 40 1,649 words Chapter 41 1,700 words Chapter 42 1,698 words Chapter 43 1,676 words Chapter 44 1,625 words Chapter 45 1,633 words Chapter 46 1,675 words Chapter 47 1,693 words Chapter 48 1,668 words Chapter 49 1,688 words Chapter 50 1,647 words Chapter 51 1,653 words Chapter 52 1,568 words Chapter 53 1,689 words Chapter 54 1,699 words Chapter 55 1,669 words Chapter 56 1,578 words Chapter 57 1,564 words Chapter 58 1,660 words Chapter 59 1,694 words Chapter 60 1,415 words Chapter 61 1,653 words Chapter 62 1,690 words Chapter 63 1,685 words Chapter 64 1,618 words Chapter 65 1,652 words Chapter 66 1,674 words Chapter 67 1,687 words Chapter 68 1,699 words Chapter 69 1,644 words Chapter 70 1,698 words Chapter 71 1,691 words Chapter 72 1,671 words Chapter 73 1,689 words Chapter 74 1,679 words Chapter 75 1,677 words Chapter 76 1,678 words Chapter 77 1,655 words Chapter 78 1,683 words Chapter 79 1,696 words Chapter 80 1,700 words Chapter 81 1,694 words Chapter 82 1,697 words Chapter 83 1,692 words Chapter 84 1,668 words Chapter 85 1,554 words Chapter 86 1,666 words Chapter 87 1,677 words Chapter 88 1,694 words Chapter 89 1,667 words Chapter 90 1,700 words Chapter 91 1,670 words Chapter 92 1,670 words Chapter 93 1,655 words Chapter 94 1,640 words Chapter 95 1,607 words Chapter 96 1,668 words Chapter 97 1,659 words Chapter 98 1,689 words Chapter 99 1,675 words Chapter 100 1,614 words Chapter 101 1,610 words Chapter 102 1,700 words Chapter 103 1,683 words Chapter 104 1,657 words Chapter 105 1,698 words Chapter 106 1,700 words Chapter 107 1,695 words Chapter 108 1,656 words Chapter 109 1,683 words Chapter 110 1,699 words Chapter 111 1,699 words Chapter 112 1,641 words Chapter 113 1,696 words Chapter 114 1,626 words Chapter 115 1,695 words Chapter 116 1,691 words Chapter 117 1,698 words Chapter 118 1,645 words Chapter 119 1,673 words Chapter 120 1,691 words Chapter 121 1,635 words Chapter 122 1,694 words Chapter 123 1,689 words Chapter 124 1,688 words Chapter 125 1,673 words Chapter 126 1,692 words Chapter 127 1,686 words Chapter 128 1,697 words Chapter 129 1,660 words Chapter 130 1,691 words Chapter 131 1,674 words Chapter 132 1,670 words Chapter 133 1,693 words Chapter 134 1,691 words Chapter 135 1,687 words Chapter 136 1,672 words Chapter 137 1,691 words Chapter 138 1,657 words Chapter 139 1,687 words Chapter 140 1,650 words Chapter 141 1,695 words Chapter 142 1,607 words Chapter 143 1,699 words Chapter 144 1,676 words Chapter 145 1,698 words Chapter 146 1,684 words Chapter 147 1,664 words Chapter 148 1,696 words Chapter 149 1,674 words Chapter 150 1,680 words Chapter 151 1,697 words Chapter 152 1,628 words Chapter 153 1,618 words Chapter 154 1,688 words Chapter 155 1,664 words Chapter 156 1,692 words Chapter 157 1,584 words Chapter 158 1,644 words Chapter 159 1,646 words Chapter 160 1,618 words Chapter 161 1,797 words

"Maryam ba abinda ki ke tunani ba ne wallahi, zaman ki a Kaduna ba zai yiwu ba, kuma ki dinga to-and-fro tsakanin Kaduna zuwa Zaria expenses É—in zai yi yawa. But wallahi duk ba wannan ba ne babban damuwana, damuwar shine Zaytoonah, ba za ki ji daÉ—in aiki da reno ba"

"Ya wuce" ta faÉ—a tana kwantawa kan gado ta ja bargo har ka.

"Maryam, Maryam, Maryam" ta ƙi ta kulashi hakan ya sa ya hau gadon shima.

"My love na miki alkawarin zan nema miki aiki a nan Zaria amma kiyi haƙuri da maganar Kadunan nan. I know saboda Iya ki ke son tafiya ba dan komai ba. But Maryam ki dinga tausaya min dan Allah, duk lokacin da bakya nan gidan ina wahala. Maryam ke ce hasken gidan nan ke ce farinciki na, ina buƙatar ki kusa da ni. And Maryam what about Zaytoonah? Taya zan dinga ba ta kulawa idan ba ta kusa da ni a koda yaushe?"

"Maryam..." ya kai hannu zai taɓa ta ta buge hannun

"Leave me alone" ta furta da ƙarfi wanda hakan ya sa Zaytoonah da ke kwance tsakiyar su ta kama kuka. Ya ɗau Zaytoonah ya fara lallashin ta.
Ita kuwa rufe kunnuwanta ta yi dan ma kar kukan Zaytoonah ya dameta ga uwa uba haushin T J da ta ke ji. Har zai ce idan ba ta gidan baya samun farinciki bayan daga ta É—an kwana biyu ba ta gidan shikenan boom sai ka ga Hajjo da ciki.
Why on earth did she love this man so much?
Yadda ta ke jinta yanzu kamar ta tattara kayanta ta bar ma sa gida ta yi nisa da shi har abada, ta rabu da tsiyar uwar sa da matar sa but ba za ta iya ba despite everything son T J na maƙale a zuciyarta , so ne da ya bi jininta ya ratsa dukkan sassan jikinta.

Tana jin sa ya shimfiÉ—a Zaytoonah wacce ta koma da bacci ya kwanta yana sauke ajiyar zuciya.

"Ki yafe min Maryam. Na san ban miki adalci ba, na san na nuna miki son kai. Kiyi haƙuri na sama miki aiki a nan dan Allah. Wallahi ko na kwana ɗaya ne ba ma tare ba na jin daɗi, i mean it Maryam, kuma idan za ki yi adalci kema kin san a wajen ki kaɗai na ke samun soyayya, kulawa, tattali, nitsuwa, farinciki da kwanciyar hankali"

Shiru ne ya biyo bayan maganganun sa daga baya ta ji ya ce "I love you Maryam"...

*Don samun daman karanta cigaban labarin za a biya 300 ta account number kamar haka:*
3099546325
Firstbank
Azizat Hamza
*ko kuma katin MTN na 300 zuwa ga wannan numbar 08137311900*
Za'a tura Shaidar biya zuwa ga wannan numbar still 08137311900 ko kuma ma dai domin ƙarin bayani za a iya tuntuɓar numban, preferably chat ko text.
*Allah ya ba da ikon biya amin*
2/11/21, 10:04 PM - ****: *Chronicles of*
*...... ...... .......ZAYTOONAH*

https://m.facebook.com/Inside-Arewa-Writers-107691760958755/?ref

𝕀ℕ𝕊𝕀𝔻𝔼 𝔸ℝ𝔼𝕎𝔸 𝕎ℝ𝕀𝕋𝔼ℝ𝕊©
*(Ƙungiyar Nazarin Harshen Hausa)*

Rubutawa.....Azizat
Wattpad@Azi_zat

*Free page*
*15-Anorexia*

Bismillahir Rahmanir Rahim

Name calling shine abu na farko da ke ɗagawa ma su ƙiba hankali. Wasu kan kau da kai su nuna sunan da ake kiran su da shi baya damun su alhali kuma deep down abin na ƙona mu su rai.
Wasu kuma tun suna damuwa har sun mai da abun jiki sun dena damuwa da hakan, sun rungumi halittar su kuma suna son kan su a yadda su ke duk da kuwa kullum ana cigaba da judging na su.
Akwai wanda kuma yadda ake kiran su da sunaye mabanbanta wanda ke nuna izgili da cin mutunci yana karya mu su confidence da courage É—in su. Sai ka ga maimakon ka gan su suna kazar-kazar kamar kowa sai ya zama ba su da wannan kuzarin. Su na jin zafin maganganun mutane, idan sun shiga wajen da mutane sirara su ke sai su dinga ganin kan su kamar ba su cika ba kamar sauran, kaman su É—in daban ne da waÉ—ancan mutane, kaman su É—in abun aibu ne a cikin Jama'a.
Zaytoonah ta faɗa cikin irin waɗannan mutane. Despite the fact Daddynta na yawan nuna ma ta ƙibanta ba shi da yawa sannan tanada kyau a yadda ta ke hakan bai boosting self esteem ɗin ta ba.

Ga Humairah ma da ke ji da tashen balagar ta kullum su ka haɗu sai ta tsokaleta 'yar ɓukuta,'yar kitiɓirɓir, Tindirƙa, Sukumbiya. Ko a ina ta ke samun ugly sunayen nan oho.
Tun Zaytoonah na iya maida ma ta Martani har ta dena.

Humairah wani jiji da kai ta ke yi a shekarunta shabiyu. Ga shi ta fara period ita kuwa Zaytoonah da ke shauku ba ta fara ba. Falli da tashen balaga haɗe da kwaɗayi ya sa ta ke ƙin zaman gidan su. Sai ta je ta wuni a gidan Uncle Muntari, ta ci cima mai daɗi. Daga baya ma cewa ta yi wa Iya su koma gidan Uncle Muntari gaba ɗaya. Iya ma dai na son komawa kawai tana ganin Tijjani ba zai ji daɗi ba ne idan ta bar gidan sa ta koma gidan Muntari zai ɗauka saboda gidan Muntari ya fi na sa kyau ne shiyasa ta bar gidan.
Amma da Humairah ta takura sai gashi Iya ta yiwa T J maganar, shi kuwa yace Allah ya zaunar da su lafiya. Bai ji daÉ—i ba kam tunda ya riga ya saba da zamanta a gidan sa.

Ɗakunan ƙasa aka ba su, ɗakin Iya daban ɗakin Humairah daban, Humairah sai murna ta ke ɗakinta na yanzu ya fi na da girma da kyau.
Ba su da matsala da Anty Hanne dan ba ta shiga harkan su. Tana da mai aiki da ke mu su girki da duk wani hidiman gidan. Ita sai dai ta ci ta sha ta kwanta. Ta ma nemi gurbin karatu a ABU amma ba ta samu ba saboda result É—in ta na secondary bai yi kyau ba hakan ya sa ta ce za ta sake zanawa.
Zaman su a gidan da É—an kwana biyu ne Iya ta fara sa ma ta ido akan shiru da ta ji har yanzu. Ranan da ta isheta da tambaya wai ko ta yi planning ne.

"Iya ki tambayeshi sau nawa ya ke nemana a wata. Idan ya baki amsa sai ki dawo na gaya mi ki dalilin jin shiru da ki ka yi"
Jin amsar da ta ba ta ya sa ta ja bakin ta ta yi shiru, da Hajjo da Hannen duk da ta É—auka 'ya'yan uwanta ne babu wanda ya É—auketa da wani daraja amma a hakan ba ta iya yi mu su komai sai ma tsoron su da ta ke ji. Sai Maryam Inyamura ne aka renawa hankali.

Da ta samu gogan da maganar haihuwa kuwa cewa yai shi baya son sa'ido. Idan lokacin haihuwan Hanne ya yi za ta haihu.
Dama shi ɗa nagari, ɗan ƙwarai wanda ya san hakkin iyaye shi ake tanƙwarawa amma ɗa marar tarbiyya kamar Muntari sai dai a bishi da ido da addu'a. Duk wani mulki da ta ke zubawa a gidan Tijjani babu shi a gidan Muntari, tana magana zai ce "Iya ba na son sa'ido"

Zaman Hanne da Muntari kuwa gashi nan gashi nan ne. Ran da ya bushi isha zai nemeta amma idan bai nemeta ba ko ta zo da kanta koranta ya ke yi ya ce shi baya son jaraba. Yana dai bata kuÉ—i dan duk wata tana jin alert. Zaman shiru da ta ke yi ne ma ya sa ta yi tunanin komawa karatu.
Mummunan halin sa ta shan giya kuwa tun watannin farko na auren su ta gane. Ita kam tana zargin bayan giya ma yana haÉ—awa da wani abun. Randa ya fara sunbatun Maryam kuwa har tsorata ta ke yi. Ita dai ta rasa wace Maryam ce Muntari ke mutuwar so haka.

***

Inter school competion za su yi daidai ƙarshen zango na shekarar wanda ya kama su Zaytoonah na gab da zana jarrabawan su na JCE.
Rehersals za a fara yau, wanda aka zaɓa za su fito su yi rehersal a gaban ɗalibai.
Wannan ne karo na farko da Zaytoonah za ta yi debate tunda ta shiga JSS. Ta kan representing ɗin makarantar su a Maths competion amma indai debate ne ba ta yarda ta yi. A nursery da primary school she used to be excited duk lokacin da aka zaɓe ta cikin ma su yin debate amma yanzu komai ya chanja ma ta, ba ta da wannan confidence ɗin.
Wannan karan ma Mr Adebayo ne ya dage sai ta shiga ciki.

Ita ce first speaker dan haka sunan ta aka fara kira Tijjani Zaytoonah Abubakar.

Cikinta ya ba da ƙululu, jiya a gaban Auwal ta presenting points ɗin ta ba tareda wata matsala ba amma yanzu da aka kira sunan ta har ta fara jin gudawa.

A hankali ta taso ta fito tsakiyar filin, gaba ɗaya an ƙura ma ta ido wasu na dariya ƙasa-ƙasa.

Bayan ta yi gaisuwa sannan ta gabatar da topic É—in sannan ta introduncing kan ta. Tana cewa "standing before you is Zaytoonah Tijjani Abubakar, I'm..."

'aka Mama Zaytoonah' muryan Sadiya wata 'yar class ɗin su ya doki kunnen ta. Sadiya ta so a saka sunan ta a cikin ma su competition ɗin amma ba a zaɓeta ba, shiyasa ta ke jin haushin Zaytoonah.

Shiru ta yi saboda yadda sunan ya taɓata

"Yes continue" MC É—in ya faÉ—a ma ta

Murya na rawa ta cigaba dan ta ruÉ—e "firstly, I'm.."

"Amoeba" ta sake jin an ambata da ƙarfi. Wannan karan hawaye ne ya zubo daga idon ta wanda ya sa wasu ɗaliban su ka fara dariya. Aka shiga yiwa yara ihu akan su yi shiru amma inaa sai ma ƙarawa da su ka yi saboda yadda su ka ga Zaytoonah ta bar hall ɗin da gudu...

***

"Ni ba na son kame-kame, gaskiya na ke so, za ka iya yi min aiki ko ba za ka iya ba?"

"Indai ba ka yarda da mu ba babu yadda za ayi aikin da za mu maka yai tasiri" mutumin da ke zaune kan wata tsohuwar tabarmar kaba ya faÉ—a.

End of Chapter 31Continue to the next chapter or choose another story below.

More Hausa novels

Browse all books →
Previous Login to Save Next