Ramadan Promo!All users that send a manual request for premium upgrade on sallah day will be granted for 1 month free.
Soyayyanovels
Zaytoonah Part One Complete Hausa Novel
Zaytoonah Part One Complete Hausa Novel
By Azizat
Login to keep your reading position saved.
Book Page Chapters
Zaytoonah Part One Complete Hausa Novel

Zaytoonah Part One Complete Hausa Novel

Author: Azizat
Chapter 78 of 161
About 8 min read
Chapter progress: 0%
Listen Mode
Listen to this chapter using your device voice.
Ready to listen from this chapter.
Free access is active. You can keep reading and download during this access window.

Book chapters

Choose a chapter and continue reading.

Start chapters
Chapter 1 1,689 words Chapter 2 1,523 words Chapter 3 1,583 words Chapter 4 1,696 words Chapter 5 1,682 words Chapter 6 1,693 words Chapter 7 1,594 words Chapter 8 1,673 words Chapter 9 1,663 words Chapter 10 1,668 words Chapter 11 1,678 words Chapter 12 1,698 words Chapter 13 1,687 words Chapter 14 1,699 words Chapter 15 1,656 words Chapter 16 1,634 words Chapter 17 1,681 words Chapter 18 1,675 words Chapter 19 1,655 words Chapter 20 1,613 words Chapter 21 1,669 words Chapter 22 1,655 words Chapter 23 1,671 words Chapter 24 1,650 words Chapter 25 1,677 words Chapter 26 1,696 words Chapter 27 1,598 words Chapter 28 1,699 words Chapter 29 1,694 words Chapter 30 1,659 words Chapter 31 1,683 words Chapter 32 1,309 words Chapter 33 1,691 words Chapter 34 1,697 words Chapter 35 1,553 words Chapter 36 1,588 words Chapter 37 1,682 words Chapter 38 1,680 words Chapter 39 1,677 words Chapter 40 1,649 words Chapter 41 1,700 words Chapter 42 1,698 words Chapter 43 1,676 words Chapter 44 1,625 words Chapter 45 1,633 words Chapter 46 1,675 words Chapter 47 1,693 words Chapter 48 1,668 words Chapter 49 1,688 words Chapter 50 1,647 words Chapter 51 1,653 words Chapter 52 1,568 words Chapter 53 1,689 words Chapter 54 1,699 words Chapter 55 1,669 words Chapter 56 1,578 words Chapter 57 1,564 words Chapter 58 1,660 words Chapter 59 1,694 words Chapter 60 1,415 words Chapter 61 1,653 words Chapter 62 1,690 words Chapter 63 1,685 words Chapter 64 1,618 words Chapter 65 1,652 words Chapter 66 1,674 words Chapter 67 1,687 words Chapter 68 1,699 words Chapter 69 1,644 words Chapter 70 1,698 words Chapter 71 1,691 words Chapter 72 1,671 words Chapter 73 1,689 words Chapter 74 1,679 words Chapter 75 1,677 words Chapter 76 1,678 words Chapter 77 1,655 words Chapter 78 Reading now Chapter 79 1,696 words Chapter 80 1,700 words Chapter 81 1,694 words Chapter 82 1,697 words Chapter 83 1,692 words Chapter 84 1,668 words Chapter 85 1,554 words Chapter 86 1,666 words Chapter 87 1,677 words Chapter 88 1,694 words Chapter 89 1,667 words Chapter 90 1,700 words Chapter 91 1,670 words Chapter 92 1,670 words Chapter 93 1,655 words Chapter 94 1,640 words Chapter 95 1,607 words Chapter 96 1,668 words Chapter 97 1,659 words Chapter 98 1,689 words Chapter 99 1,675 words Chapter 100 1,614 words Chapter 101 1,610 words Chapter 102 1,700 words Chapter 103 1,683 words Chapter 104 1,657 words Chapter 105 1,698 words Chapter 106 1,700 words Chapter 107 1,695 words Chapter 108 1,656 words Chapter 109 1,683 words Chapter 110 1,699 words Chapter 111 1,699 words Chapter 112 1,641 words Chapter 113 1,696 words Chapter 114 1,626 words Chapter 115 1,695 words Chapter 116 1,691 words Chapter 117 1,698 words Chapter 118 1,645 words Chapter 119 1,673 words Chapter 120 1,691 words Chapter 121 1,635 words Chapter 122 1,694 words Chapter 123 1,689 words Chapter 124 1,688 words Chapter 125 1,673 words Chapter 126 1,692 words Chapter 127 1,686 words Chapter 128 1,697 words Chapter 129 1,660 words Chapter 130 1,691 words Chapter 131 1,674 words Chapter 132 1,670 words Chapter 133 1,693 words Chapter 134 1,691 words Chapter 135 1,687 words Chapter 136 1,672 words Chapter 137 1,691 words Chapter 138 1,657 words Chapter 139 1,687 words Chapter 140 1,650 words Chapter 141 1,695 words Chapter 142 1,607 words Chapter 143 1,699 words Chapter 144 1,676 words Chapter 145 1,698 words Chapter 146 1,684 words Chapter 147 1,664 words Chapter 148 1,696 words Chapter 149 1,674 words Chapter 150 1,680 words Chapter 151 1,697 words Chapter 152 1,628 words Chapter 153 1,618 words Chapter 154 1,688 words Chapter 155 1,664 words Chapter 156 1,692 words Chapter 157 1,584 words Chapter 158 1,644 words Chapter 159 1,646 words Chapter 160 1,618 words Chapter 161 1,797 words

Sati biyu da su ka wuce ta cika shekaru shatakwas a duniya, to abu uwan da su ka faru sun hana ma ta tuna balle ta yi wani abu. Ita ba da Mommy ta kirata ba ranan da kuma text É—in Salman da na Auwal da ta gani da ba abinda zai sa ta tuna da wani birthday É—in ta.

Ofcourse sai da Zuhayr ya Angonce da Amaryar sa dan ya nuna ma ta fa rashin lafiyar sa bai hana engine É—in sa aiki ba domin body É—in ne mai jinya shi engine garau ya ke.

Mamakinta bai ƙare ba sai da dare da ya ce su sake shiryawa saboda akwai birthday party da ya haɗa ma ta. Ita ba ta so ba dan with all that is happening she's in no mood for any party. Sai dai ya za ta yi tunda ya riga ya haɗa komai ba tareda ya shawarceta ba.

Ta É—auka mutane kaÉ—an ne ya gayyata ashe gari guda ne. Ma'aikatan sa na Kamfani dama na gidan su duk sun zo, sai tsirarun abokanan sa, hatta Farha ta zo. Mr Ben ma ba a barshi a baya ba shima ya zo wajen dan duk wani shirye-shirye na party É—in shi yai tunda Zuhayr dai sai dai ya ce yana son kaza shi kuma zai kira ya tabbatar anyi hakan.
A chan bayan resort ɗin ake party ɗin. Inda aka ƙayata shi na musamman saboda wannan party. Yadda wajen ya ke da haske tarau ka ce da rana ake ba da dare ba. 'Yan jarida ma sun zo sakamakon wannan ne fitowar farko da Zuhayr zai yi wajen taro tunda ya fara chemotherapy treatment.
Ya sha tambayoyi kam shi da Zaytoonah musamman saboda recent attack É—in da aka kaiwa Zaytoonah wanda ya faÉ—a kan Dreban ta. Ofcourse an kewaye wajen da securities dan kafin ka shiga wajen sai kana da kati, katin ma sai an duba da na'ura an tabbatar cewa na gaskiya ne ba na bogi ba, hakan ma kuma sai an duba ka da na'ura kafin ka wuce.

Party É—in dai yana tafiya lafiya domin har an yanka cake. Zuhayr ya bawa Zaytoonah a baki itama ta bashi a baki, aka sa tafi.
Yanzu haka ma rawa su ke yi ita da Zuhayr ɗin, ba rawa ne na jijjiga jiki ba dan waƙar irin mai sanyi ɗin nan aka saka.

"Ki shirya anjima idan an tashi dan ban ƙoshi ba" ya raɗa ma ta a kunne

"Sai dai idan Allah ya kaimu gobe ka samu É—umame" ta amsa ma sa tana murmushi.

"Kafin gobe bawan Allah ya jigata ai"

"Ka san yadda É—umame ke da daÉ—i kuwa"

"Bari mu ga dai ko zan iya haƙura" ya faɗa yana juyawa da ita...

Daga kan bishiya da ya ke tun ɗazu yana ƙoƙarin saita Zaytoonah da bindiga, duk da nisan da ke tsakaninsa da inda ake party ɗin hakan bai hanashi hangota ba da kuma saita ta a matsayin target. Ta ɗan ƙaramin lens daya ke leƙawa a jikin bindigar duk inda ya ga red dot a jikin Zaytoonah a nan bullet ɗin zai sauka. Tun ɗazu ya ke son yin halbin amma kuma Mijinta na tarewa, sai ya yi niyyar halbin sai Zuhayr ya tare ta ko da hannunsa ko ma ya rungume ta. Sau biyu wanda ya bashi kwangilar aikin nan yana tura ma sa text akan ya ji shiru har yanzu shi bai san aikin na su yana buƙatar nitsuwa ba. A matsayinsa na Hit man bai taɓa karɓan aiki ya missing target ɗin sa ba sai dai idan fasawa yai. Sau ɗaya ya taɓa fasa kashe target ɗin sa wanda lokacin farko-farkon fara aikin sa ne inda aka bashi kwangilar kashe wata yarinya 'yar wani minister. Yarinyar kwata-kwata shekarunta takwas ne, daga inda ya targetting ɗinta ta fito daga makaranta ita da bodyguard ɗin ta za su je su shiga mota, murmushinta ya taɓa ma sa zuciya ya ji ba zai iya kasheta ba. Daga nan indai aiki ya shafi yaro ɗan ƙasa da shekara shabiyar to ba zai karɓa ba.

A lokacin da ya samu damar da ya ke ganin indai ya halbi Zaytoonah sai dai wata ba ita ba, saboda direct zuciyarta harsashin zai shiga, yai saurin sake harsashin sai dai kafin ta kai ga Zaytoonah sai ta shiga jikin mutumin da ya sa hannu yana goge ma ta icing sugar da ya gani a gefen kunnen ta.

Bindiga ce da take da silencer dan haka babu ƙara sai dai kawai aji shigar harsashi jikin mutum.

"Kin ma fi kyau a.." maganar da bai ƙarasa ba kenan harsashin ya shige shi ta baya. A hankali ya fara yin ƙasa-ƙasa har ya kai ƙasan gaba ɗaya. Ihu da mutane su ke yi da kuma Ben da ya zo da gudu ya rungume Zuhayr yana ƙoƙarin tada shi yana sunbatu shine abu na ƙarshe da ta iya tunawa kafin ta yanki jiki ta faɗi.

Lokacin da helicopter É—in ta sauka a bakin asibitin tuni anriga anzo da gado saboda tun kafin su iso anyi waya an sanar da su.

"Dont leave me my love, dont leave me please" abinda Ben ke maimaitawa kenan lokacin da ake tura gadon zuwa cikin asibitin.
Ƙoƙarin shiga ICU ya ke yi wani nurse ya tareshi hakan ya sa dole ya ja birki a bakin ƙofa zuciyar sa na bugawa da ƙarfi kamar za ta bulloƙo. Abu ɗaya ya sani shine matuƙar Zuhayr ya mutu to sai ya yanka Zaytoonah da hannun sa kafin shima ya kashe kan sa dan babu wani amfani da zai yi a duniya idan ya rasa masoyin sa.

*hold on, mun kusa ganin bayan Ben fa*
2/11/21, 10:04 PM - ****: 37

Bismillahir Rahmanir Rahim

*ASSALAMU ALAIKUM*

*Ina ba da haƙurin jina da kuka yi shiru tsawon kwanaki dayawa, hakan ya faru saboda doguwar tafiya da na yi sannan komawa school da wasu shirye-shirye. Amma yanzu komai ya zama normal za mu cigaba Insha Allah. Wanda su ka yi ta ƙorafi su ka ga ban tanka ba Dan Allah ku yi haƙuri, Wanda su ka samu saɓani dalilin cecekuce da aka yi ina ba su haƙuri. Ba komai ne duniyan ba balle har mu dinga samun matsala a haɗuwan group. Sannan wanda ba su yi haƙuri ba kuma su ke ga ba za su iya haƙuri ba ƙofa a buɗe ta ke su min magana ta pc zan maida mu su kuɗin su Insha Allah.*

*daga yau zuwa sati biyu ma su zuwa ina fatan za mu kammala labarin nan Insha Allah. Ni ma ban so aka samu akasi ba wannan karan na rashin update akai-akai*

*na sani kuna da haƙƙi akai na har sai na kammala rubutun nan. Amma idan har kun min uzuri nan da lokaci kaɗan za mu gama labarin ba tareda wani matsala ba Insha Allah. Wanda su ka bani shawarwari da waɗanda su ka bibiyi lafiyata duk ina godiya kun nuna min cewa abinda ya haɗamu ya fi ƙarfin littafi domin an riga an zama 'yan uwa*

*ina da yaƙinin cewa kowanne a cikin mu yanada matsalolinsa. Sometimes despite duk abinda ya ke damun mutum na rayuwa dole ka nemi abinda zai dinga ɗebe ma ka kewa saboda idan ba hakan ka yi ba sai damuwa ta saka a gaba har ya iya jawo ma ka matsala a jiki, shiyasa wani lokaci mu ke karatu ko mu yi kallo ko ma wani abin duk dan mu kauda zuciyar mu daga matsalolin da su ka sha mana kai. From December last year zuwa jiya ina fama da wata matsala wanda sai yau ɗin nan Allah ya warware min komai, na samu nasara na samu sauƙi. Under this pressure and stress na rubuta litattafai har 4 yanzu ina kan na biyar (Duk kyan namiji, Sakatariyata, Tsohuwar Soyayya, Ribar uwa sannan Chronicles of Zaytoonah). Rubutu na ɗebe min kewa shiyasa ko ina cikin damuwa ina tunani akan labari ko dai wanda na ke kan rubutawa ko kuma wanda na ke son rubutawa a gaba. Kunada haƙƙi akaina kuma Insha Allahu zan sauke hakkin ku da ke kai na. Idan har zan iya rubutu a lokacin da na ke cikin damuwa to yanzu da na samu sauƙi Insha Allah zan ƙara zage damtse ne. Until then plz ku yi haƙuri*

*masu fama da matsaloli na rayuwa daban-daban ina addu'ar Allah ya yaye muku shi Amin. Sannan ina ƙara ƙarfafa mu ku gwiwa da ku ci gaba da Addu'a ku kuma dogara da Allah domin wallahi Allah shine mai yaye damuwa da matsaloli. Samun sauƙin ka zai iya ɗaukan lokaci amma kuma daga ƙarshe indai ka riƙe Allah sai ka ga kaine da nasara. Dukkan mun nan ba mu fi ƙarfin jarabtar Allah ba walau ta ɓangaren iyayen mu ne ko 'yan uwan mu ko auren mu, wajen aikin mu ne, anguwar mu ne ko ma jarabta ta faɗa kan 'ya'yan mu. Allah ya ba mu ikon cin jarrabawan mu Amin. Nagode*

*arrested*

Safa da marwa Ben ya ke yi a bakin ICU É—in yana kissima abubuwa dayawa a ran sa. Shi kaÉ—ai ya san ya yake ji a zuciyar sa gameda halin da masoyinsa ya ke ciki. Shi bai yarda da Allah ba balle ya É—aga hannu yai addu'a.

Asibitin da aka kawo Zuhayr nan aka kawo Zaytoonah, da ke ita da mota aka taho da ita shiyasa ba su yi sauri ba. Faɗuwar da ta yi ya sa jini ya tsinke ma ta. Lokacin da aka shigo da ita ƙoƙarin tsaida jinin aka fara yi kafin a cigaba da ba ta taimakon da ya kamata.

A hankali ta buɗe idonta da ya ma ta nauyi. Sama sama ta ke jin muryan Farha da ke zaune gefenta. Ta ɗau kusan 30 seconds kafin komai ya fara dawo ma ta. Yunƙurin tashi ta yi amma Farha ta yi saurin riƙe ta saboda jini da aka ɗaura ma ta.
"Zuhayr, ina Zuhayr" ta furta da murya mai rauni.

"Yana nan, ki kwantar da hankalinki"

"Ya mutu ko?" Ta faÉ—a hawaye na zubo ma ta

"No Zaytoonah, he's very much alive"

"Ki kai ni wajen shi dan Allah"

End of Chapter 78Continue to the next chapter or choose another story below.

More Hausa novels

Browse all books →
Previous Login to Save Next