Ramadan Promo!All users that send a manual request for premium upgrade on sallah day will be granted for 1 month free.
Soyayyanovels
Zaytoonah Part One Complete Hausa Novel
Zaytoonah Part One Complete Hausa Novel
By Azizat
Login to keep your reading position saved.
Book Page Chapters
Zaytoonah Part One Complete Hausa Novel

Zaytoonah Part One Complete Hausa Novel

Author: Azizat
Chapter 135 of 161
About 8 min read
Chapter progress: 0%
Listen Mode
Listen to this chapter using your device voice.
Ready to listen from this chapter.
Free access is active. You can keep reading and download during this access window.

Book chapters

Choose a chapter and continue reading.

Start chapters
Chapter 1 1,689 words Chapter 2 1,523 words Chapter 3 1,583 words Chapter 4 1,696 words Chapter 5 1,682 words Chapter 6 1,693 words Chapter 7 1,594 words Chapter 8 1,673 words Chapter 9 1,663 words Chapter 10 1,668 words Chapter 11 1,678 words Chapter 12 1,698 words Chapter 13 1,687 words Chapter 14 1,699 words Chapter 15 1,656 words Chapter 16 1,634 words Chapter 17 1,681 words Chapter 18 1,675 words Chapter 19 1,655 words Chapter 20 1,613 words Chapter 21 1,669 words Chapter 22 1,655 words Chapter 23 1,671 words Chapter 24 1,650 words Chapter 25 1,677 words Chapter 26 1,696 words Chapter 27 1,598 words Chapter 28 1,699 words Chapter 29 1,694 words Chapter 30 1,659 words Chapter 31 1,683 words Chapter 32 1,309 words Chapter 33 1,691 words Chapter 34 1,697 words Chapter 35 1,553 words Chapter 36 1,588 words Chapter 37 1,682 words Chapter 38 1,680 words Chapter 39 1,677 words Chapter 40 1,649 words Chapter 41 1,700 words Chapter 42 1,698 words Chapter 43 1,676 words Chapter 44 1,625 words Chapter 45 1,633 words Chapter 46 1,675 words Chapter 47 1,693 words Chapter 48 1,668 words Chapter 49 1,688 words Chapter 50 1,647 words Chapter 51 1,653 words Chapter 52 1,568 words Chapter 53 1,689 words Chapter 54 1,699 words Chapter 55 1,669 words Chapter 56 1,578 words Chapter 57 1,564 words Chapter 58 1,660 words Chapter 59 1,694 words Chapter 60 1,415 words Chapter 61 1,653 words Chapter 62 1,690 words Chapter 63 1,685 words Chapter 64 1,618 words Chapter 65 1,652 words Chapter 66 1,674 words Chapter 67 1,687 words Chapter 68 1,699 words Chapter 69 1,644 words Chapter 70 1,698 words Chapter 71 1,691 words Chapter 72 1,671 words Chapter 73 1,689 words Chapter 74 1,679 words Chapter 75 1,677 words Chapter 76 1,678 words Chapter 77 1,655 words Chapter 78 1,683 words Chapter 79 1,696 words Chapter 80 1,700 words Chapter 81 1,694 words Chapter 82 1,697 words Chapter 83 1,692 words Chapter 84 1,668 words Chapter 85 1,554 words Chapter 86 1,666 words Chapter 87 1,677 words Chapter 88 1,694 words Chapter 89 1,667 words Chapter 90 1,700 words Chapter 91 1,670 words Chapter 92 1,670 words Chapter 93 1,655 words Chapter 94 1,640 words Chapter 95 1,607 words Chapter 96 1,668 words Chapter 97 1,659 words Chapter 98 1,689 words Chapter 99 1,675 words Chapter 100 1,614 words Chapter 101 1,610 words Chapter 102 1,700 words Chapter 103 1,683 words Chapter 104 1,657 words Chapter 105 1,698 words Chapter 106 1,700 words Chapter 107 1,695 words Chapter 108 1,656 words Chapter 109 1,683 words Chapter 110 1,699 words Chapter 111 1,699 words Chapter 112 1,641 words Chapter 113 1,696 words Chapter 114 1,626 words Chapter 115 1,695 words Chapter 116 1,691 words Chapter 117 1,698 words Chapter 118 1,645 words Chapter 119 1,673 words Chapter 120 1,691 words Chapter 121 1,635 words Chapter 122 1,694 words Chapter 123 1,689 words Chapter 124 1,688 words Chapter 125 1,673 words Chapter 126 1,692 words Chapter 127 1,686 words Chapter 128 1,697 words Chapter 129 1,660 words Chapter 130 1,691 words Chapter 131 1,674 words Chapter 132 1,670 words Chapter 133 1,693 words Chapter 134 1,691 words Chapter 135 Reading now Chapter 136 1,672 words Chapter 137 1,691 words Chapter 138 1,657 words Chapter 139 1,687 words Chapter 140 1,650 words Chapter 141 1,695 words Chapter 142 1,607 words Chapter 143 1,699 words Chapter 144 1,676 words Chapter 145 1,698 words Chapter 146 1,684 words Chapter 147 1,664 words Chapter 148 1,696 words Chapter 149 1,674 words Chapter 150 1,680 words Chapter 151 1,697 words Chapter 152 1,628 words Chapter 153 1,618 words Chapter 154 1,688 words Chapter 155 1,664 words Chapter 156 1,692 words Chapter 157 1,584 words Chapter 158 1,644 words Chapter 159 1,646 words Chapter 160 1,618 words Chapter 161 1,797 words

Sosai shawaran da aka bawa Mommy ya taimaka wajen samun lafiyar Zaytoonah.
"Addu'a shine maganin ko wanne irin matsala. Ban ce taimakon da ake ba ta ba zai yi amfani ba amma kuma idan aka haɗa da addu'a sai ka ga sauƙi ya samu da wuri. Zan rubuta miki wasu addu'o'i da za ki dinga yi da wanda ita kan ta za tana yi. Insha Allah za ta samu lafiya"

Bayanin wani babban Malami kenan wanda ta tuntuɓa gameda maganar sihirin da aka yiwa T J ya ke kuma taimaka ma ta da addu'o'i.

Fushi sosai Zaytoonah ke yi da Galadima, tun tana kewar sa har ta koma jin haushin sa gani ta ke dai shareta yai saboda ya yarda da gaske ta yi hauka. Wato a matsayin sa na Mutum mai daraja ba zai iya zama da Mata mai matsalar ƙwaƙwalwa ba.
Sau É—aya an kawo ma ta 'yan biyu hutu duk da sun sanar ma ta yadda Galadima ke yawan zuwa duba su amma hakan bai sa ta sassauta ma sa ba.
Ta kai hannu ta shafa cikinta wanda ke É—an motsawa a hankali.

"Baby ga shi Daddy ya manta da mu, its just me and you now"

"Adaeze" Mommy ta kira sunan ta daga cikin É—aki.

"Yes Mom" ta miƙe a hankali ta wuce ɗakin.

lokacin da ta shigo É—akin Mommy na zaune a bakin gado tana danna waya.
Gefen mommyn ta zauna tana tambayarta mi ya faru.

"Yanzu aka kirani" ta riƙe hannun Zaytoonah ɗaya sannan ta ce "Mrs Haddish is gone"

"Ta sha jinya sosai, she's a good woman" ta faÉ—a a hankali.

Bayan kwana biyu da Mutuwar Mrs Haddish aka yi Funeral ɗin ta inda aka bisine ta kusa da Mr Haddish kamar yadda ta buƙata, Zaytoonah na cikin wanda su ke karɓan gaisuwan mutuwa saboda koba komai an riga an zama ɗaya. Washegarin da aka yi burial ɗin ne su ka dawo Las Vegas kuma a ranan Zaytoonah ta fara naƙuda chan da yamma. Mommy ta wuce da Ita Asibiti duk da kuwa a yadda su ka rubuta haihuwar saura kwana huɗu. Zuwa ƙarfe shaɗaya na dare Zaytoonah ta haihu...

***

"Ikon Allah kamar su É—aya da wannan yarinyar miye ma sunan ta?"

"Falaq" Zaytoonah ta ba da amsa

Mommy ta sake kallon jinjirar dake hannunta tana murmushi.

Tun a daren ta kira gida ta gaya mu su. Ta so kiran Galadima ta sanar da shi amma ta bari sai da safe tunda ta san dare yayi a Nigeria.
Daga baya kuma sai ta tura ma sa text.

A chan Nigeria kuwa Galadima bai duba wayan sa ba sai bayan ya dawo daga sallar Asuba. Da ke babbar wayar ya fara dubawa saboda yana son duba email na shi sai kawai ya ga message daga wajen Hajia Ni'ima da Salman. Tuni ya buɗe message ɗin Hajia Ni'imar inda ya ci karo da hoton jaririya tareda saƙon taya murna a ƙasa.
Saƙon Salman ɗin ma hotunan ne amma maimakon na jaririyan kaɗai harda na Zaytoonah tana kwance a gadon Asibiti.

*Alhamdulillah Princess Alinah Yunus Muhammad Abbas has grace our world*

Abinda Salman ya rubuta kenan aƙasan hoton yarinyar da ko makaho ya san ta shi ce, wannan jinjirar har ta fi Falaq kama da shi.

Tambayar kan sa yai dama da ciki Zaytoonah ta tafi?
2/11/21, 10:04 PM - ****: 67

Bismillahir Rahmanir Rahim

*Recovered*

Cike da É—oki ya dannawa Salman kira ya ci sa'a kuwa ringing É—aya aka É—auka da alama ma wayar dama na hannun Salman.

"Ranka shi daɗe na san ni na fara yin albishir dan haka ina buƙatan goron albishir"

"Kar ka damu wannan ba matsala ba ce. Na gode da wannan karramawa"

Sai da ya ja numfashi kafin ya ce " ina fata suna lafiya?"

"Lafiya Sir, an ma sallamesu, É—azu mu ka yi magana da Adaeze da su ka isa gida"

Murmushi Galadima yai sannan ya ƙara ma sa godiya bayan Salman ɗin ya bashi bayanin da ya ke so.

Bayan ya ga text É—in da Mommy ta ma sa a É—aya wayar sannan ya kira numbar ta ba a É—auka ba hakan ya sa ya sake kira a karo na biyu amma still ba a É—auka ba.

Yana shirin sake kira ne wayar Hajia Abu ya shigo wayar sa.

"Yanzu Ni'ima ke sanar da ni Zaytoonah ta sauka, da gaske mace ta haifa itama?"

Ya ɗan ji ba daɗi a ran sa dan ya san ma'anar abinda Hajiyar ta faɗa sai dai bai taɓa sawa a ransa zai so ɗa namiji fiye da ta mace ba. Dukkan su 'ya'ya ne kuma fatan sa shine Allah ya raya ma sa su da imani, su yi rayuwa mai albarka wanda ya ke fata ranan gobe Manzon Allah yai alfahari da su.

"Alhamdulillah na samu labarin da uwa da 'ya suna nan lafiya" ya faÉ—a a hankali.

"Allah ya raya" Hajia Abu ta faÉ—a ciki-ciki

Amin ya amsa ma ta

"Za su zo ayi suna a nan ne ko kuwa?"

"Ba lallai su zo ba gaskiya"

Daga haka Hajia Abu ta kashe wayar.

Bayan ya gama waya da Hajia Abu ya sake gwada numbar Mommy wannan karan kam an É—auka.

Bayan sun gaisa ya tambayeta ya me jiki ta ce ma sa Alhamdulillah da sauƙi, Zaytoonah da Baby duk suna bacci.
Godiya ya ma ta sannan ya tambayi ko akwai musulmin da ke kusa da zai wa Baby huÉ—uba tunda baya nan. Mommy ta ce tun a Asibitin Sheikh Hassan ya yiwa Baby huÉ—uba.
Yana son tambayarta yaushe za su dawo amma bai samu daman hakan ba saboda Kashe wayar da Mommyn ta yi bayan ta ce ma sa sai anjima.

Duk wannan badaƙalar da ake yi Ghazala ba ta sani ba. Da ke ta fara janye jiki da 'yan uwan Galadima sai ya zamana babu wanda ya kirata ya sanar da ita. Itama tunda ta tashi ba ta bi ta kan wayarta ba kitchen kawai ta wuce.

Fiskar sa ɗauke da annuri ya sauko ƙasan, wani nishaɗi ya ke ji a ran sa kamar wani sabon Ango. Shi kaɗai ake jira a wajen dinning ɗin tun ɗazu su ke jira ya fito amma bai shigo ba hakan ya sa Ghazala ta haura sama ta ma sa magana a hakan ma sai da ya ƙara kusan minti bakwai kafin ya fito.

"Kafin a fara cin abinci ina da good news da zan sanar mu ku"

"Daddy za mu je Yola ko?" Suhailah ta faÉ—a da sauri.

"Wrong"

"Anty Zaytoonah za ta dawo" Falaq ta faÉ—a

"No, Raziya fa, mi ki ke tunani?"

Raziya ta kalli Ghazala sannan ta maida kallon ta ga Daddyn na su ta ce "Anty Zaytoonah ta warke"

Cikin ran Ghazala ta ce 'lallai ma yarinyar nan'

"Tunda ba ku canki dai-dai ba barin faÉ—a"

Sai da ya kalli fuskokin su É—aya bayan É—aya wanda ke É—auke da curiosity na son sanin minene good news É—in kafin ya ce.

"Kun samu baby Sister, Antyn ku ta haihu jiya da dare"

"Yeeeeeeeeh" suka haÉ—a baki wajen faÉ—a yayinda Ghazala ta ji saukar guduma a tsakiyar kan ta.

Sama-sama ta ke jin sanda yaran su ka yanyame Galadima suna ce ma sa ya nuna mu su hoton Baby.
Ta É—ago jajayen idanun ta ta kalli Galadima da ke ta murmushi saboda yadda yaran ke ta praising jinjirar.

"Zaytoonah na da ciki, Zaytoonah ta haihu" abinda ke yawo a ƙwaƙwalwarta kenan. Daga baya kuma da ta tuno abu biyu sai ta yi murmushi wanda yai nasaran kawar da ɓacin ran da ta ke ji yanzu.

Zaytoonah ba Matar Galadima ba ce yanzu sannan 'ya mace ta haifa ba namiji ba.

Sai da yaran su ka nitsu su ka koma wajen zaman su aka fara cin abinci kafin ta ce "Abu Razz Allah ya raya mana ita da imani, ashe da ciki ta tafi jinya. Alhamdulillahi ma da ta sauka lafiya ba ta illata 'yar ba"

Sai da ya kalleta kafin ya kauda kai ya ce "Amin"...

***

"Daddyn Raziya na son magana da ke, nan da minti biyu zai sake kira" Mommy ta faÉ—a tareda ajiye ma ta wayar a gefenta.

"Mommy da kin barshi ma zamuyi magana gobe"

"Idan ya kira kika É—auka sai ki gaya ma sa ya bari gobe ku yi magana"
Daga haka ta fice daga É—akin.

Zaytoonah ta cigaba da kurɓan tea a hankali tanayi tana tura baki kaman a gaban Galadiman ta ke.

Minti huÉ—u sai ga kiran sa ya shigo. Ta bi wayar da kallo ba tareda ta yi niyyar É—auka ba sai da ta kusa yankewa ta É—auka ta sa a kunne ta yi shiru.

Sallama yai cikin muryan sa mai ratsa zuciya.
Ta ciki ta amsa ba tareda bakinta ya motsa ba.

"Qurratul ayn kina jina?"

Kai namiji! wato ta nan kuma ya ɓullo. Ba wai dan ta so ba amma kuma sunan da ya kirata da shi ɗin ya yi tasiri a ranta.

" 'yan mata na ki min magana mana na ji zazzaƙar muryan ki"

Sai da ta juya ido kafin ta ce "minti biyun da ka ce za ka kira kenan"

"Tuba na ke Qurratul ayn, kiran Mai Martaba ne ya shigo wayata"

Ba ta yi magana ba sai ma kumbura baki da ta ke yi.

"Kina jina Princess, ki hau whatsapp na gan ki Dan Allah, na yi kewar ki dan Allah"

"Ba wani, all this while mi ya hana ka zo ka ganni, almost 6months fa. Ni dai na san ba ni da wani matsayi a wajen ka. Dama mi za ka yi da wacce ke son kashe ma ka 'ya'ya. You dont love me, you dont want me..."

"Zaytoon" ya kira sunan ta da sigar da ta san jan hankali ne.

"Ki bani dama na ganki Dan Allah" ya faÉ—a a sanyaye.

Samun kan ta ta yi da kasa yin musu. Ita kan ta tana son ganin sa dan ta yi missing É—in sa sosai, the last time da ta ga hoton sa shine wani zuwan da yai Zaria ya je gidan su suka É—au hoto da 'yan biyu Salman ya saka a status É—in sa. Shine ta gani a wayan Mommy.

End of Chapter 135Continue to the next chapter or choose another story below.

More Hausa novels

Browse all books →
Previous Login to Save Next