Ramadan Promo!All users that send a manual request for premium upgrade on sallah day will be granted for 1 month free.
Soyayyanovels
Zaytoonah Part One Complete Hausa Novel
Zaytoonah Part One Complete Hausa Novel
By Azizat
Login to keep your reading position saved.
Book Page Chapters
Zaytoonah Part One Complete Hausa Novel

Zaytoonah Part One Complete Hausa Novel

Author: Azizat
Chapter 7 of 161
About 8 min read
Chapter progress: 0%
Listen Mode
Listen to this chapter using your device voice.
Ready to listen from this chapter.
Free access is active. You can keep reading and download during this access window.

Book chapters

Choose a chapter and continue reading.

Start chapters
Chapter 1 1,689 words Chapter 2 1,523 words Chapter 3 1,583 words Chapter 4 1,696 words Chapter 5 1,682 words Chapter 6 1,693 words Chapter 7 Reading now Chapter 8 1,673 words Chapter 9 1,663 words Chapter 10 1,668 words Chapter 11 1,678 words Chapter 12 1,698 words Chapter 13 1,687 words Chapter 14 1,699 words Chapter 15 1,656 words Chapter 16 1,634 words Chapter 17 1,681 words Chapter 18 1,675 words Chapter 19 1,655 words Chapter 20 1,613 words Chapter 21 1,669 words Chapter 22 1,655 words Chapter 23 1,671 words Chapter 24 1,650 words Chapter 25 1,677 words Chapter 26 1,696 words Chapter 27 1,598 words Chapter 28 1,699 words Chapter 29 1,694 words Chapter 30 1,659 words Chapter 31 1,683 words Chapter 32 1,309 words Chapter 33 1,691 words Chapter 34 1,697 words Chapter 35 1,553 words Chapter 36 1,588 words Chapter 37 1,682 words Chapter 38 1,680 words Chapter 39 1,677 words Chapter 40 1,649 words Chapter 41 1,700 words Chapter 42 1,698 words Chapter 43 1,676 words Chapter 44 1,625 words Chapter 45 1,633 words Chapter 46 1,675 words Chapter 47 1,693 words Chapter 48 1,668 words Chapter 49 1,688 words Chapter 50 1,647 words Chapter 51 1,653 words Chapter 52 1,568 words Chapter 53 1,689 words Chapter 54 1,699 words Chapter 55 1,669 words Chapter 56 1,578 words Chapter 57 1,564 words Chapter 58 1,660 words Chapter 59 1,694 words Chapter 60 1,415 words Chapter 61 1,653 words Chapter 62 1,690 words Chapter 63 1,685 words Chapter 64 1,618 words Chapter 65 1,652 words Chapter 66 1,674 words Chapter 67 1,687 words Chapter 68 1,699 words Chapter 69 1,644 words Chapter 70 1,698 words Chapter 71 1,691 words Chapter 72 1,671 words Chapter 73 1,689 words Chapter 74 1,679 words Chapter 75 1,677 words Chapter 76 1,678 words Chapter 77 1,655 words Chapter 78 1,683 words Chapter 79 1,696 words Chapter 80 1,700 words Chapter 81 1,694 words Chapter 82 1,697 words Chapter 83 1,692 words Chapter 84 1,668 words Chapter 85 1,554 words Chapter 86 1,666 words Chapter 87 1,677 words Chapter 88 1,694 words Chapter 89 1,667 words Chapter 90 1,700 words Chapter 91 1,670 words Chapter 92 1,670 words Chapter 93 1,655 words Chapter 94 1,640 words Chapter 95 1,607 words Chapter 96 1,668 words Chapter 97 1,659 words Chapter 98 1,689 words Chapter 99 1,675 words Chapter 100 1,614 words Chapter 101 1,610 words Chapter 102 1,700 words Chapter 103 1,683 words Chapter 104 1,657 words Chapter 105 1,698 words Chapter 106 1,700 words Chapter 107 1,695 words Chapter 108 1,656 words Chapter 109 1,683 words Chapter 110 1,699 words Chapter 111 1,699 words Chapter 112 1,641 words Chapter 113 1,696 words Chapter 114 1,626 words Chapter 115 1,695 words Chapter 116 1,691 words Chapter 117 1,698 words Chapter 118 1,645 words Chapter 119 1,673 words Chapter 120 1,691 words Chapter 121 1,635 words Chapter 122 1,694 words Chapter 123 1,689 words Chapter 124 1,688 words Chapter 125 1,673 words Chapter 126 1,692 words Chapter 127 1,686 words Chapter 128 1,697 words Chapter 129 1,660 words Chapter 130 1,691 words Chapter 131 1,674 words Chapter 132 1,670 words Chapter 133 1,693 words Chapter 134 1,691 words Chapter 135 1,687 words Chapter 136 1,672 words Chapter 137 1,691 words Chapter 138 1,657 words Chapter 139 1,687 words Chapter 140 1,650 words Chapter 141 1,695 words Chapter 142 1,607 words Chapter 143 1,699 words Chapter 144 1,676 words Chapter 145 1,698 words Chapter 146 1,684 words Chapter 147 1,664 words Chapter 148 1,696 words Chapter 149 1,674 words Chapter 150 1,680 words Chapter 151 1,697 words Chapter 152 1,628 words Chapter 153 1,618 words Chapter 154 1,688 words Chapter 155 1,664 words Chapter 156 1,692 words Chapter 157 1,584 words Chapter 158 1,644 words Chapter 159 1,646 words Chapter 160 1,618 words Chapter 161 1,797 words

"ÆŠan Fillo mota za ta tashi ka matso kusa"
Ya amsa da to. Ya kalli Nkiru ya ce mata zai tafi, nan da nan idon ta su ka ciko da hawaye. Ya fito da kuɗi a aljihunsa ya miƙa ma ta ya ce ta je tasha ta nemi motan Calabar kuma ta sayi takalmi.

"Take me with you" ta faÉ—a ba tareda ta san dalilin da ya sa ta faÉ—i hakan ba.

A hankali ya fara ma ta bayanin cewa shi ba É—an nan ba ne kuma garin su akwai nisa.

"ÆŠan Fillo" aka sake kira

Ya miƙe tsaye yana jin zuciyar sa na ma sa nauyi.

"Nice meeting you Inkiru-Mary, and goodluck" ya faÉ—a a hankali sannan ya juya ga Malam Idi ya ce "Malam Idi zan wuce, idan ba damuwa ka yiwa yarinyar nan kwatancen inda za ta samu motar Kalaba"
Malam Idi ya ce to tareda ma sa addu'ar Allah ya tsare.

A hankali ya ke tafiya saboda tsananin tausayin Nkiru da ya ke ji ya kashe ma sa jiki, fatan sa Allah ya sa ta samu kakannin ta idan ta je Calabar. Wani zuciya na raya ma sa ya fasa tafiya ya raka Nkiru zuwa Calabar, to amma idan bai tafi yau ba sai wani sati domin ba koyaushe ake samun motar Kano ba. sannan idan bai tafin ba zai rasa bikin ƙannen sa da za ayi ranan Jummu'a ya kama saura kwana huɗu kenan. Da Eze bai riga ya tafi na su ƙauyen ba a chan Nsukka da ya haɗata da Eze ya rakata. Haka dai yaita tunani har ya kai wajen trailer ɗin, har dreban ma ya tada motar. Ya buɗe gidan gaba zai shiga sai ya juya ya hango Nkiru tana tahowa wajen da sauri. Murmushi yai ya ɗaga ma ta hannu ɗaya, yana ganin sanda hawaye ya zuba a idonta ta sa hannu ta fara sharewa. Yai saurin shigewa cikin motar dan kada shima ya fara hawayen.

Yana shiga mota ta tashi, Dreba da yaron motan sa guda É—aya su ka fara tsokanan T J. Su uku ne a gaba yayinda bayan aka cikata da jarakunan manja ciki harda jarka guda biyu na T J wanda ya rubuta sunan sa saboda shaidah. Jakar Ghana-must-go guda biyu ya É—auka wanda É—aya kayan sa ne aciki da littattafai sai É—aya Jakar ta tsaraba ce.

Ko kalma ɗaya bai faɗi ba, idanun sa na kan side mirror yana hango Nkiru tsaye tana kuka, bayan sun ma ta nisa ya dena hangota ya sunkuyar da kansa yana lissafin abubuwa a ransa. Ƙarshe dai answer ɗaya ya samowa kansa ita ce kawai mafita, ita ce kawai zai yi ya ji hankalin sa ya kwanta. Duk da wannan mafitar za ta zo da ƙalubale amma a hakan gara ya san ya taimakawa wannan yarinya da ya barta ba tareda ya san halin da za ta shiga ba.

"Dreba ki tsaya" ya faÉ—a lokacin da ya É—ago kan sa. Har yau dai a mafiya yawancin lokuta idan zai yi Hausa yana maida mace namiji ya maida namiji mace. Shi idan ba karatun da yai a Zaria ba da ba zai ji Hausa har haka ba. A gidan su jefi-jefi ake Hausa amma Fulatanci kawai su ka sani, shi kuma ya bi harshen su.

"Zamu tafi da wancan yarinyar" ya faÉ—a lokacin da ya ga Dreban bai da niyyar tsayawa.

Da Dreban da Yaronsa suka sa T J a gaba da faɗa suna gaya ma sa illar abinda yake da niyyar yi. T J ya nuna koya nene zai tafi da Nkiru idan ya so idan ya dawo dan ya ƙarisa watanni huɗu da ya rage ma sa a garin sai ya raka Nkiru zuwa Calabar ya sa da ta da 'yan uwan Mahaifiyarta.
Da Dreba da Yaronsa dukkan su Hausawa ne sai su ke ganin wautar T J ɗan Fulani. Ƙarshe da su ka ga ya dage sai su ka barshi amma da sharaɗin T J zai biya ma ta kuɗin mota duk da kuwa shi T J ɗin alfarma aka ɗauke shi. T J ya ce ya amince.
Yana saukowa daga trela ɗin gudu ya fara yana fata ba ta bar tashar ba. A wajen da ya barta tsaye lokacin da zai shiga motar a nan ya ganta tsaye tana hawaye yayinda wata mata ke tsaye kusa da ita tana ma ta magana. Tunda ya ganta kuwa yai Hamdala a ransa ya ƙara gudu. Ɗago idon da za ta yi ta hangoshi yana gudu nan ta kama murmushi. Har T J ya iso ba ta dena murmushi ba, matar ganin tana murmushi ita ɗaya ya sa ta ja tsaki ta wuce dan acewarta Nkiru mahaukaciya ce.
Yana haki yana tambayarta ko za ta bishi garin su idan ya so sai su dawo tare ya rakata har Calabar. Ta gyaÉ—a kai.

Ya duƙa ya fara cire takalmin sa tareda socks ɗin. Da ya gama cirewa ya ce ta sa, ta kalli cikin idon sa cike da mamaki, ya gyaɗa ma ta kai yana murmushi. Jiki na rawa ta fara saka socks ɗin wanda sai alokacin ta ga yadda ƙafarta ya ɓaci, ta gama ta sa takalmin wanda ba dan socks da kuma ɗaurewa da ta yi tamtam ba da haka ƙafar za ta yi ta lilo a ciki, T J dogo ne sosai gashi siriri ita kuma duk da ta ɗan fishi faɗin ƙafa amma ba ta kai shi tsayin ƙafa ba.
Jacket É—in sa ya ba ta ta sa sannan ya ce su tafi. Da gudu-gudu sauri-sauri su ka kai wajen da motar ta ke, ya taimaka ma ta ta hau sannan shima ya shiga.

Dreba da yaronsa Ibrahim ba fahimtar turancin ta su ke ba lokacin da ta ke gaishesu. Su pidgin su ke ji ita kuma turanci kamar Sarauniyar Ingila. Ban da gaisuwa kuma ba abinda su ke ji a yaren Igbo.

Haka su ka kama doguwar tafiya. Tun ba a kai awa ɗaya da kama hanya ba Nkiru ta sa kan ta a kafaɗar T J ta fara bacci. Dreba ya ce T J ya ma ta magana ta koma kan doguwar kujera da ke bayan su wanda su ka maidata gado. Nkiru ta koma baya ta miƙe jiki sai bacci.
Lokaci zuwa lokaci T J yana leƙata ko ta tashi amma ba ta tashi ba. A ƙalla ta kai awa biyar tana bacci kafin ta farka. Haka dai tafiyar ta kasance jefi-jefi T J yana ma ta tambayoyi wanda ta ke amsa ma sa bisa gaskiyarta...

Tafiyar ta su ta ƙara daɗewa saboda ɓaci da motar ta yi a hanya, sai da su ka yi kusan awa huɗu su na jira kafin aka gama gyarata. Ba su suka iso Kano ba sai
Ƙarfe takwas na safiyan washegari.
Kafin T J ya samu ya haɗa kan kayan sa ma sai da su ka kai wajen ƙarfe shaɗaya. Daga nan ya nema mu su Bus da za ta kai su garin su wato Ringim wacce lokacin ke haɗe da Kano saboda ba a raba Jigawa da Kano ba...

Abu uku ya gaya ma ta wanda ya ce ta riƙe su da kyau, idan ta yi haka har su dawo ba za ta samu damuwa ba.

"Gidan mu musulmai ne kuma Fulani ke kuma Christian ce 'yar ƙabilar Igbo. Ba kowa ne mai sauƙin kai kamar ni ba dan haka duk abinda za a miki na nuna ƙyama ko wariya ka da ki bari ya ɗaga miki hankali. Na biyu kuma iyayena da mafiya yawanci 'yan uwana ba su yi Boko ba dan haka ba sa jin turanci, kusan maganar kurame za a dinga yi idan ba na kusa da zan fassara miki ko kuma wanda su ke ji ɗin ba sa kusa. Na uku kuma za ki yi haƙuri da yanayin gidan mu, gidan mu gidan yawa ne kuma ba gida ne irin wanda ki ka taso ba, ina fata yadda kika lallaɓa da zaman ƙauyen mahaifin ki za ki lallaɓa da zaman gidan mu"

"Thank you. You are truly a good man" abinda ta faÉ—a ma sa kenan lokacin da ya gama ma ta bayani...

***

Bayan Isha su ka isa daidai ƙofar gidan su T J, mai mota ya fitar mu su da kaya sannan ya ƙara gaba. Tun da yaran da ke ƙofar gida su ka ƙyalla ido su ka gan shi su ka fara ihu suna kiran "Hamma Tijjani wartoyi, Hamma wartoyi" su ka yo kan shi da gudu, ya ɗauki ƙaramin cikin su yana cillashi yaron na ta dariya.
Cikin gidan su ka shiga nan ma dai ihun murna ake yi, tunda ya tafi bautar ƙasa wannan ne karon farko da ya zo gida.
Nkiru dai bin bayan sa kawai ta ke yi tana mamakin yaran, ita tun a hanya ta ke mamakin ƙasar Hausa.

Magana yai da wata mace da Fulatanci sannan ya juyo ya kalli Nkiru ya ce ta bi ƙamwarsa za ta kai ta ɗaki.
Yarinyar da ba za ta wuce shekara bakwai zuwa takwas ba ta jagoranceta har wani É—aki, ganin yarinyar ta cire takalmi ya sa Nkiru ma ta cire takalmin T J ta shigo É—akin wanda ke wadace da hasken lantarki saboda akwai wuta a lokacin. Tun kafin ta shigo yarinyar ta soma yiwa tsohuwar da ke zaune akan sallaya bayanin abinda T J ya ce ma ta.

"Maraba da zuwa" tsohuwar ta faÉ—a tana kallon Nkiru.

"Goggo ba ta jin Hausa fa"

Goggo ta ce "tooo"

Ta yiwa Nkiru nuni da ta zauna a kan kujeran da ke É—akin. Nkiru ta zauna tana sauke ajiyar zuciya akai akai...

End of Chapter 7Continue to the next chapter or choose another story below.

More Hausa novels

Browse all books →
Previous Login to Save Next