Ramadan Promo!All users that send a manual request for premium upgrade on sallah day will be granted for 1 month free.
Soyayyanovels
Zaytoonah Part One Complete Hausa Novel
Zaytoonah Part One Complete Hausa Novel
By Azizat
Login to keep your reading position saved.
Book Page Chapters
Zaytoonah Part One Complete Hausa Novel

Zaytoonah Part One Complete Hausa Novel

Author: Azizat
Chapter 94 of 161
About 8 min read
Chapter progress: 0%
Listen Mode
Listen to this chapter using your device voice.
Ready to listen from this chapter.
Free access is active. You can keep reading and download during this access window.

Book chapters

Choose a chapter and continue reading.

Start chapters
Chapter 1 1,689 words Chapter 2 1,523 words Chapter 3 1,583 words Chapter 4 1,696 words Chapter 5 1,682 words Chapter 6 1,693 words Chapter 7 1,594 words Chapter 8 1,673 words Chapter 9 1,663 words Chapter 10 1,668 words Chapter 11 1,678 words Chapter 12 1,698 words Chapter 13 1,687 words Chapter 14 1,699 words Chapter 15 1,656 words Chapter 16 1,634 words Chapter 17 1,681 words Chapter 18 1,675 words Chapter 19 1,655 words Chapter 20 1,613 words Chapter 21 1,669 words Chapter 22 1,655 words Chapter 23 1,671 words Chapter 24 1,650 words Chapter 25 1,677 words Chapter 26 1,696 words Chapter 27 1,598 words Chapter 28 1,699 words Chapter 29 1,694 words Chapter 30 1,659 words Chapter 31 1,683 words Chapter 32 1,309 words Chapter 33 1,691 words Chapter 34 1,697 words Chapter 35 1,553 words Chapter 36 1,588 words Chapter 37 1,682 words Chapter 38 1,680 words Chapter 39 1,677 words Chapter 40 1,649 words Chapter 41 1,700 words Chapter 42 1,698 words Chapter 43 1,676 words Chapter 44 1,625 words Chapter 45 1,633 words Chapter 46 1,675 words Chapter 47 1,693 words Chapter 48 1,668 words Chapter 49 1,688 words Chapter 50 1,647 words Chapter 51 1,653 words Chapter 52 1,568 words Chapter 53 1,689 words Chapter 54 1,699 words Chapter 55 1,669 words Chapter 56 1,578 words Chapter 57 1,564 words Chapter 58 1,660 words Chapter 59 1,694 words Chapter 60 1,415 words Chapter 61 1,653 words Chapter 62 1,690 words Chapter 63 1,685 words Chapter 64 1,618 words Chapter 65 1,652 words Chapter 66 1,674 words Chapter 67 1,687 words Chapter 68 1,699 words Chapter 69 1,644 words Chapter 70 1,698 words Chapter 71 1,691 words Chapter 72 1,671 words Chapter 73 1,689 words Chapter 74 1,679 words Chapter 75 1,677 words Chapter 76 1,678 words Chapter 77 1,655 words Chapter 78 1,683 words Chapter 79 1,696 words Chapter 80 1,700 words Chapter 81 1,694 words Chapter 82 1,697 words Chapter 83 1,692 words Chapter 84 1,668 words Chapter 85 1,554 words Chapter 86 1,666 words Chapter 87 1,677 words Chapter 88 1,694 words Chapter 89 1,667 words Chapter 90 1,700 words Chapter 91 1,670 words Chapter 92 1,670 words Chapter 93 1,655 words Chapter 94 Reading now Chapter 95 1,607 words Chapter 96 1,668 words Chapter 97 1,659 words Chapter 98 1,689 words Chapter 99 1,675 words Chapter 100 1,614 words Chapter 101 1,610 words Chapter 102 1,700 words Chapter 103 1,683 words Chapter 104 1,657 words Chapter 105 1,698 words Chapter 106 1,700 words Chapter 107 1,695 words Chapter 108 1,656 words Chapter 109 1,683 words Chapter 110 1,699 words Chapter 111 1,699 words Chapter 112 1,641 words Chapter 113 1,696 words Chapter 114 1,626 words Chapter 115 1,695 words Chapter 116 1,691 words Chapter 117 1,698 words Chapter 118 1,645 words Chapter 119 1,673 words Chapter 120 1,691 words Chapter 121 1,635 words Chapter 122 1,694 words Chapter 123 1,689 words Chapter 124 1,688 words Chapter 125 1,673 words Chapter 126 1,692 words Chapter 127 1,686 words Chapter 128 1,697 words Chapter 129 1,660 words Chapter 130 1,691 words Chapter 131 1,674 words Chapter 132 1,670 words Chapter 133 1,693 words Chapter 134 1,691 words Chapter 135 1,687 words Chapter 136 1,672 words Chapter 137 1,691 words Chapter 138 1,657 words Chapter 139 1,687 words Chapter 140 1,650 words Chapter 141 1,695 words Chapter 142 1,607 words Chapter 143 1,699 words Chapter 144 1,676 words Chapter 145 1,698 words Chapter 146 1,684 words Chapter 147 1,664 words Chapter 148 1,696 words Chapter 149 1,674 words Chapter 150 1,680 words Chapter 151 1,697 words Chapter 152 1,628 words Chapter 153 1,618 words Chapter 154 1,688 words Chapter 155 1,664 words Chapter 156 1,692 words Chapter 157 1,584 words Chapter 158 1,644 words Chapter 159 1,646 words Chapter 160 1,618 words Chapter 161 1,797 words

Bayan ya gama bayani Zaytoonah ta ma sa tambayoyi kafin nan shima Barrister mai wakiltan Chief Udodiri yai na sa tambayoyin. Bayan ya gama ne aka bayyana sabon evidence wato audio record na muryan Anty Uloma tana bayanin yadda abin ya faru. Da ke da pidgin english ta yi maganan kusan kowa ya gane abinda aka faÉ—a.

"Objetion My Lord. Wannan muryan ba mu yarda da shi ba, zai iya zama wata ne kawai ta zauna ta naɗi muryanta tana shirya bayanai dan a ɓatawa client ɗina suna"

"Objection overruled, Barrister Zaytoon proceed"

Yana maganar idon sa cikin na ta. Da farko sai da ta É—an rasa nitsuwarta na 'yan sakanni saboda tasirin kallon da Justice ya ma ta. Ta yi saurin jan numfashi tareda cigaba da bayani.

"Kamar yadda mu ka saurara Mrs Uloma ta bayyana gaskiyar abin da ya faru kuma wannan bayani ne da aka naɗe shi kwana uku kafin mutuwar Uloma Uzodinma kuma ƙanwa ta ke uwa ɗaya uba ɗaya da Chief Udodiri. Ina so kotu ta bani dama na yiwa Chief Udodiri wa su tambayoyi"

Justice Bulus ya ce an ba ta dama.

Chief Udodiri ya fito yana wani huhhura hanci. Sanye ya ke da igbo attire da wata sanda na alfarma da yawancin ma su kuɗin ƙasashen igbo ke amfani da shi.

Zaytoonah ta matsa kusa da witness box ta ce "Mr Augustus Udodiri ko za ka iya gaya mana yaushe ne Patrick da matar sa su ka mutu?"

With full confidence ya ce " 22nd December 1985"

"Ko za ka iya sanar da mu abinda ya kashe su?"

Wani yawu ya haÉ—iye jin tambayar dan dole ya faÉ—i abinda aka riga aka faÉ—a a baya dan chanja magana ka iya jawo matsala kamar yadda lawyan sa ya bashi shawara.

"Patrick da Caroline sun mutu suna bacci, ba mu san dalili ba amma kasancewar akwai wanda su ka riƙe aladun gargajiya sosai a lokacin. Wasu sun yi iƙirarin cewa an cinye kuruwar su ne"

Zaytoonah ta É—aure fiska ta ce " ko za ka iya gaya mana wa ake zargin ya cinye kuruwar su?"

" 'yar su Mary"

"My Lords, Chief Udodiri ya bayyana ma na a rubuce kuma yayi rantsuwa cewa shi mabiyin addinin kiristanci ne tun sama da shekaru arba'in da su ka wuce. Haka nan a lokacin da Patrick da matar sa su ka mutu Chief Udodiri yana da kwalin degree in order words yana da ilimin boko, amma duk da wannan qualification ɗin Augustus Udodiri ya yarda da iƙirarin da ya ce anyi na cewa Mary-Nkiru mayya ce kuma ita ta kashe iyayen ta. Maimakon a kai case ɗin police station ayi bincike na gaskiya sai ya sa aka ɗaure Mary-Nkiru aka rufeta a wani ɗaki ba abinci ba ruwa. Ko a nan aka tsaya Udodiri ya violating human right kuma ya abusing Mary-Nkiru"

"Objection My Lord, Barrister Zaytoonah ta fara kauce hanyar ƙara"

"Objection Overruled" wannan karan Justice Shafa'atu ce ta yi maganar.

Zaytoonah ta yi godiya kafin ta cigaba.
"Ina so kotu ta sani Udodiri ba shi da hurumin da zai yanke hukunci da kan sa, ina so kotu ta tuna cewa zancen soki buruntsu Udodiri ya ke yi saboda kotu ba ta yarda da maita ba. Kenan maganan Marigayiya Uloma ya tabbata da ta ce guba aka zuba a abinci su ka ci suka mutu.

"Bayan da Mary-Nkiru ta kuɓuta daga kaidin Udodiri wanda ke son a ƙona ta da ran ta bisa umurnin Dibia na ƙauyen su. Udodiri ya juya duk wani kadarori na Patrick da matar sa zuwa sunan sa. Muna da copies na wasu daga cikin takardun da aka yi na kamfani wanda ke ɗauke da sunan Caroline Asibong Uzodinma da kuma Mary-Nkiru Uzodinma a matsayin next of kin ɗin Marigayi Patrick.

"Ina so kotu ta sake duba wannan shaida da Uloma ta bayar a matsayin gaskiyar abinda ya faru"

Bayan ta zauna ne Barrister Toby Rowling wanda tuni ya sha jinin jikin sa saboda zafafan bayanai da Zaytoonah ta gabatar ya miƙe ya fara bayani wanda duk ɓaɓatu ya ke yi da kame-kame. Wancan karan sun samu daman bribing judge ɗin da ya saurari ƙara a High court na Imo state, amma wannan karan duka Justice ɗin da aka saka babu wanda ke da record ɗin ƙarɓan cin hanci a ciki. Infact Justice Bulus da su ka fara tuntuɓa da maganar kuɗi balbalesu yai tareda iƙirarin su ka ƙara kawo ma sa wannan tayin sai ya sa an kama su.
Gaba ɗaya sun riga sun budgeting Justice Sabo da kuma Justice Ifalana za a saka a chair of Justice ɗin amma ƙwatsam aka saka Justice Yunus da sauran Justice ɗin ma su irin ra'ayin sa.

Bayan ya gama na shi kame-kamen ne aka tambayi Zaytoonah ko tana da abun faÉ—a.
Zaytoonah ta miƙe tsaye ta ce "ina neman alfarma daga wannan kotu aba da dama a exhuming jiki ko ƙasusuwan Patrick da Caroline domin a gwada ko poison ne ya kashe su ko wani abun ne daban"

Tana magana kotun aka fara murmuring ƙasa-ƙasa. Shi kan sa Chief Udodiri temporary shock ne ya same shi kasancewar bai tsammanci hakan ba.

Maganar da su ka yi da Galadima kenan kafin su ɓata, inda ya ba ta shawara akan idan tafiya ta yi tafiya ta nemi a tono gawan su Patrick da Caroline ya sani kafin a kai ga yin hakan dole gaskiya za ta fito.

"Kin san cewa wannan aiki ba ƙaramin aiki ba ne tunda experts za a kawo daga ƙasar waje" Justice Bulus yai maganar.

"Idan kotu ta bani dama ko nawa ne Client É—ina za ta biya kuÉ—in da za a biya expert É—in da za su zo su yi aiki" ...

***

Ƙaran shigowar text ya sa ta duba wayan ta lokacin suna magana da Mommy a bayan mota. Tana ganin numbar Justice ne ta ja siririn tsaki.
*Masha Allah! I'm proud of you* abinda aka rubuta kenan.

Ta wani haɗe rai kaman a gaban Justice ɗin ta ke. "Lafiya?" Mommy ta tambaya tana suspecting duk yadda za ayi Justice ne ya turo saƙo, dan tana lura da yanayin 'yartata tunda ta ma ta zancen an bayar da ita wa Justice gaba ɗaya ta tsani jin ko sunan sa ne balle maganar sa...

Udodiri kaman zai yi hauka lokacin da ya ke yiwa Barrister Toby masifa, musamman da ya ke nuna ma sa akwai possibility na za a iya detecting poison a jikin gawa ko da ya zama skeleton ne.

Duk wani bayanan kare kai da ya ke son yi bai saurare shi ba shi dai kawai yai duk yadda za ayi su winning case É—in nan.

Wata ɗaya kotu ta bayar a shigo da experts da za su yi aikin binciken gawan su Patrick. Saboda haka ne ma aka saka matakan tsaro a wajen kabarin na su a chan ƙauyen Okwuohia saboda gudun kar wani ya je ya tone kabarin.

KuÉ—i ne ba kaÉ—an ba da za ayi aikin da shi, dan da Mommy ta ji kuÉ—in sai da ta tsorata har ma ta nuna kawai a ajiye maganar tono gawan nan.

"Adaeze ba sai kin taɓa dukiyar marayu ba. We can still manage"

"Mommy kenan, tun da aka raba gado dai-dai da tsinke ban É—auka a dukiyar Hadid da Hashir ba. I'm using my money"

Mommy ta jinjina kai kawai dan ko shakka babu dukiyar da Zaytoonah ta samu bayan rasuwan Zuhayr ba kaɗan ba ne, and as the years progress duk wasu business da ta ke controlling sai haɓaka su ke yi. Allah ya haɗata da ma su kula ma ta da business ɗin ta wanda su ke da amana da gaskiya duk da fiye da rabin su ba musulmai ba ne...

Yau za su wuce Zaria dan tunda su ka zo Abuja ba su koma ba. 'Yan biyu sun yi kukan har sun gaji, ƙarshema fushi su ka yi da Mom ɗin na su ko an ba su waya sai su ƙi magana.

Tafiya su ke yi suna hira, Dreba ne ke tuƙa su yayinda Salman ke gaba, Mommy da Zaytoonah kuma na baya.

Sun wuce wani ƙauye bai jima ba sai su ka ga wasu soldiers akan hanya, Dreban na ƙoƙarin tsaida mota kawai aka shiga buɗe mu su wuta da bindiga dukkan su suka yi ƙasa a rikice yayinda Dreban ya bawa motar ta su wuta suka wuce arm robbers ɗin wanda su ka yi ɓadda kama da kayan sojoji.

Gudu su ke yi har sai da su ka yi nisa kafin Dreban ya samu ya tsaya wanda da hannu ɗaya ya ke tuƙi saboda ɗaya hannun bullet ya shiga...

"Are they all dead?" Abinda Udodiri ya faÉ—a kenan a wayar ta sa kuma amsar da aka bashi ya sa shi cillar da wayar hannun sa yana ihun Nooooo.

Salman ya samu bullet É—aya a gefen cikin sa kuma shine wanda ya ke critical condition a yanzu. Dreban su a kafaÉ—a aka harbeshi sai Mommy da bullet É—in ya wuce ta gefen shoulder É—in ta. Zaytoonah kam ba abinda ya sameta sai dai shock É—in da ta shiga na abinda ya faru ya tada ma ta ciwon ta. Yanzu haka tunanin ta Ben ne zai kashe su shiyasa ta ke ta ihun Zuhayr ya ceceta. Sau biyu ana ma ta alluran bacci saboda ta bircike mu su a Asibitin.

Justice bai samu labarin da wuri ba sai chan yamma ai kuwa hankalin sa ya tashi sosai, cike da tashin hankali ya nufi Asibitin da aka kwantar da su. Salman ya fara dubawa wanda an samu an cire ma sa bullet ɗin, jinin da aka ɗaura ma sa ma ya kusa ƙarewa. Ya sameshi yana bacci yayinda Auwal ke tareda shi a ɗakin. Da ya fito ya nufi ɗakin Zaytoonah tunda a nan Auwal ɗin ya ce Mommy ta ke dan ɗaki ɗaya aka basu.

End of Chapter 94Continue to the next chapter or choose another story below.

More Hausa novels

Browse all books →
Previous Login to Save Next