Ramadan Promo!All users that send a manual request for premium upgrade on sallah day will be granted for 1 month free.
Soyayyanovels
Zaytoonah Part One Complete Hausa Novel
Zaytoonah Part One Complete Hausa Novel
By Azizat
Login to keep your reading position saved.
Book Page Chapters
Zaytoonah Part One Complete Hausa Novel

Zaytoonah Part One Complete Hausa Novel

Author: Azizat
Chapter 11 of 161
About 8 min read
Chapter progress: 0%
Listen Mode
Listen to this chapter using your device voice.
Ready to listen from this chapter.
Free access is active. You can keep reading and download during this access window.

Book chapters

Choose a chapter and continue reading.

Start chapters
Chapter 1 1,689 words Chapter 2 1,523 words Chapter 3 1,583 words Chapter 4 1,696 words Chapter 5 1,682 words Chapter 6 1,693 words Chapter 7 1,594 words Chapter 8 1,673 words Chapter 9 1,663 words Chapter 10 1,668 words Chapter 11 Reading now Chapter 12 1,698 words Chapter 13 1,687 words Chapter 14 1,699 words Chapter 15 1,656 words Chapter 16 1,634 words Chapter 17 1,681 words Chapter 18 1,675 words Chapter 19 1,655 words Chapter 20 1,613 words Chapter 21 1,669 words Chapter 22 1,655 words Chapter 23 1,671 words Chapter 24 1,650 words Chapter 25 1,677 words Chapter 26 1,696 words Chapter 27 1,598 words Chapter 28 1,699 words Chapter 29 1,694 words Chapter 30 1,659 words Chapter 31 1,683 words Chapter 32 1,309 words Chapter 33 1,691 words Chapter 34 1,697 words Chapter 35 1,553 words Chapter 36 1,588 words Chapter 37 1,682 words Chapter 38 1,680 words Chapter 39 1,677 words Chapter 40 1,649 words Chapter 41 1,700 words Chapter 42 1,698 words Chapter 43 1,676 words Chapter 44 1,625 words Chapter 45 1,633 words Chapter 46 1,675 words Chapter 47 1,693 words Chapter 48 1,668 words Chapter 49 1,688 words Chapter 50 1,647 words Chapter 51 1,653 words Chapter 52 1,568 words Chapter 53 1,689 words Chapter 54 1,699 words Chapter 55 1,669 words Chapter 56 1,578 words Chapter 57 1,564 words Chapter 58 1,660 words Chapter 59 1,694 words Chapter 60 1,415 words Chapter 61 1,653 words Chapter 62 1,690 words Chapter 63 1,685 words Chapter 64 1,618 words Chapter 65 1,652 words Chapter 66 1,674 words Chapter 67 1,687 words Chapter 68 1,699 words Chapter 69 1,644 words Chapter 70 1,698 words Chapter 71 1,691 words Chapter 72 1,671 words Chapter 73 1,689 words Chapter 74 1,679 words Chapter 75 1,677 words Chapter 76 1,678 words Chapter 77 1,655 words Chapter 78 1,683 words Chapter 79 1,696 words Chapter 80 1,700 words Chapter 81 1,694 words Chapter 82 1,697 words Chapter 83 1,692 words Chapter 84 1,668 words Chapter 85 1,554 words Chapter 86 1,666 words Chapter 87 1,677 words Chapter 88 1,694 words Chapter 89 1,667 words Chapter 90 1,700 words Chapter 91 1,670 words Chapter 92 1,670 words Chapter 93 1,655 words Chapter 94 1,640 words Chapter 95 1,607 words Chapter 96 1,668 words Chapter 97 1,659 words Chapter 98 1,689 words Chapter 99 1,675 words Chapter 100 1,614 words Chapter 101 1,610 words Chapter 102 1,700 words Chapter 103 1,683 words Chapter 104 1,657 words Chapter 105 1,698 words Chapter 106 1,700 words Chapter 107 1,695 words Chapter 108 1,656 words Chapter 109 1,683 words Chapter 110 1,699 words Chapter 111 1,699 words Chapter 112 1,641 words Chapter 113 1,696 words Chapter 114 1,626 words Chapter 115 1,695 words Chapter 116 1,691 words Chapter 117 1,698 words Chapter 118 1,645 words Chapter 119 1,673 words Chapter 120 1,691 words Chapter 121 1,635 words Chapter 122 1,694 words Chapter 123 1,689 words Chapter 124 1,688 words Chapter 125 1,673 words Chapter 126 1,692 words Chapter 127 1,686 words Chapter 128 1,697 words Chapter 129 1,660 words Chapter 130 1,691 words Chapter 131 1,674 words Chapter 132 1,670 words Chapter 133 1,693 words Chapter 134 1,691 words Chapter 135 1,687 words Chapter 136 1,672 words Chapter 137 1,691 words Chapter 138 1,657 words Chapter 139 1,687 words Chapter 140 1,650 words Chapter 141 1,695 words Chapter 142 1,607 words Chapter 143 1,699 words Chapter 144 1,676 words Chapter 145 1,698 words Chapter 146 1,684 words Chapter 147 1,664 words Chapter 148 1,696 words Chapter 149 1,674 words Chapter 150 1,680 words Chapter 151 1,697 words Chapter 152 1,628 words Chapter 153 1,618 words Chapter 154 1,688 words Chapter 155 1,664 words Chapter 156 1,692 words Chapter 157 1,584 words Chapter 158 1,644 words Chapter 159 1,646 words Chapter 160 1,618 words Chapter 161 1,797 words

"Tabbas Biri yayi kama da mutum, na gane manufarku Baffah. Hamma shi ne Shalele É—an Boko shiyasa za a bashi ita ko?, to wallahi ba zai yiwu ba. Maryam ni ta ke so kuma ni za ta aura"
Daga haka ya buga ƙafa ya fita.

Baffah ya sauke ajiyar zuciya, wani irin daƙiƙanci ke kan Muntari. Yanzu shi aka ce ya auri Maryam sai ya aura, bayan ga wanda ya kawota. Ko Tijjani bai faɗa ba sun san akwai soyayya a ƙasan ran sa gameda Maryam. Balle ko da ace wani daban ne ya kawo Maryam gidan, sau dubu Tijjani zai zaɓa ma ta saboda shi ne zai iya riƙeta amana ya kuma nutsar da ita bisa tarbiyan musulunci. Shi Muntari da Boko da Arabin duk yayi fatali da su ya shiga gari shi dole yana son yin zaman Birni, yana son yin kuɗi ba ta hanyar noma da kiwo ba.

Baffah ya kawar da zancen zucin da ya ke, ya sawa ransa yarinta ke damun Muntari da sannu zai haƙura da Maryam.

Washe gari da safe sai ga ɗan aika wai Baffa ya je gidan Alhaji Isa yana neman sa. Baffah ya shirya ya wuce gidan ƙanin mahaifin na sa. Daga zuwa sai ga Muntari zaune gaban Alhajin yana ta rarraba idanu.

Baffa ya zauna ya gaida Alhaji amma Muntari yai ƙyam ya ƙi yiwa Baffah magana.

"Shaƙiyancinka ya kai ba za ka gaida Uban ka ba Muntari?"

Muntari ya haÉ—e rai ya gaida Baffah sama-sama.

Alhaji ya ce " Habubakar ga ɗan ka ya kawo ƙara, wai yana son yarinya kai kuma ka ce a Shehu za ka ba wa. Miye gaskiyar magana?"

Takaici ya kama Baffah amma ya daure ya ce " Alhaji yarinyar da ake magana yarinyar da Shehu ya kawo ne kusan shekara ɗaya kenan yanzu, sai jiya Allah ya sa ta amshi musulunci. A nan wajen jiya ka min faɗa akan nauyi da ya ƙaru min na haƙƙin yarinyar da ya hau kai na, saboda ko ba komai Maryam ta zama 'ya ta. Ni ban ce zan ba wa Shehu yarinya ba, na dai ce bai dace daga ta musulunta jiya sai a fara ma ta batun aure ba. Haka nan na jaddada mi shi ba zan ma ta auren dole ba, idan Maryam ba ta son shi dole ya haƙura da ita. Iya abinda mu ka yi da shi jiya kenan"

Alhaji ya kalli Muntari ya ce " kai kuma wuyan ka yayi ƙauri har kana yiwa mahaifinka sharri ko?. Za ka zo gaba na ka yi min ƙarya"

"Alhaji ni ba ƙarya na yi ba. Baffah baya so na yayi maganar nan ne saboda ba Hamma ba ne. Yasin da Hamma ne ya ce zai auri yarinyar nan da a jiya an ɗaura mu su aure"

"Yi min shiru!"

Muntari ya haɗiye sauran maganar yana ƙyafƙyafta ido.

"Magana ta mutu a nan Muntari. Idan lokaci yayi da za ayiwa Maryam aure za'a nemeka"

Muntari ya miƙe fuu ya bar ƙofan gidan. Da Baffah da Alhaji su ka bi bayansa da kallo.

Yana zuwa ya kira Nkiru wai ta zo Alhaji Isa na nemanta. Goggo ba ta san miya ke faruwa ba ta ce lafiya? Ya ce ba ruwanta dan itama haushinta ya ke ji, ya san duk yadda aka yi harda sa hannunta a maganar da Baffah yai jiya, dama dole ta goyi bayan Hamma Tijjani tunda ita ta rene shi, tun yana shekara uku ya koma hannunta.

Nkiru ta É—au mayafin da Goggo ta ba ta jiya ta yafa ta bi bayan Muntari. A hanya sai da ya sake tambayarta ko tana son shi ta ce ta yi dariya ta ce tana son shi.
Tambaya ne da ya ke ma ta a mafiya yawan lokuta wanda ita kuwa ta É—auka duk cikin barkwancinsa ne, musamman saboda yanayin turancin da ya ke amfani da shi wajen tambayar.

Alhaji da Baffa suna tattaunawa sai ga Muntari ya dawo tareda Maryam.

"Kai kuma lafiyan ka?" Baffah ya tambaya tun kafin Alhaji yai magana.

Kafin ya amsa Alhaji ya ce " barshi mu ji wani rashin kunyar zai kuma yi"

Muntari ya nuna Maryam ya ce " na kawota ne ta faÉ—a mu ku da bakinta cewa ni ta ke so. Kunga sai a mana aure tunda ba ita da bakinta ta ce tana sona"

Baffah dai kunya ya kamashi ya sunkuyar da kai kawai yana yiwa Muntari addu'ar shiriya.

"Lallai kam, yanzu dai zamani ya kawo mu É—an kunyan nan da ake ji ta iyaye ba ajinta yanzu. Allah ya huci ranka Muntari, bari mu ji daga bakin yarinya"

Ita dai Maryam na gefe tana É—an cancankan maganganun su amma ba ta gane inda maganar ta dosa ba dan haryanzu ba wai yaren ya zauna a bakinta ba ne har gara ma Hausa a kan Fulatanci.

Alhaji ya ƙwalawa wa su yara da ke wasa a ƙofar gida kira ya ce su shiga gida su kira ma sa Hamza. Hamza ɗan Alhaji Isa ne kuma shima kaman T J yana da son karatu, dan yanzu haka ya ƙare Sakandare School yana son wucewa Jami'a.

Ba a jima ba sai ga Hamzan ya fito. Ya rusuna ya gaida Baffah tareda Muntari.

Alhaji ya ma sa bayani kan abinda ke faruwa a taƙaice ya ce ya tambayi Maryam ko ita ta ce tana son Muntari da aure.

Muntari ya ce " ai ba sai ya fassara mu ku ba nima nan ina jin turancin"

Alhaji ya ce " ban sa ka ba"

Hamza ya iya turanci ba kaman Muntari da ya ke turancin kame-kame ba.
Tunda ya fara bayani Maryam ta fara girgiza kai, sai da ya ma ta tambayar da Alhajin yai ne ta zaro ido ta ce "No" da ɗan ƙarfi

Muntari ya ce " No kuma?. Me i say i love you, you you say you love me. For everyday i can ask you, you say you love me harda dariya wallahi"

Maryam ta dafa ƙirji dan sai yanzu ta fahimci inda maganar ta dosa.

Ta kalli Muntari sannan ta maida duban ta ga Hamza ta ce " i never said i love him. I just said i like him. I like him because his funny"

"Banten Uba. Mary kalle ni nan. Ki ji tsoron Allah, afraid of God Maryam. We for come here i say i love you you say you like me. Miye maraban dambe da faÉ—a?"

Alhaji ya ce "Hamza mi ya ke faruwa ne?"

Hamza ya fara bayani cewa Maryam cewa ta yi Muntari na burgeta amma ba wai tana son sa ba ne shi kuma ya doge wai cewa ta yi tana son sa.

"Muntari ka ji abinda ta ce dan haka tashi ka bamu waje, daga yanzu na kashe maganar" Alhaji yai maganar yana kallon Muntari

"Wallahi ba zai yiwu ba. Da like da love duk É—aya ne, ni na san Goggo ce ta kitsa wannan munafurcin, ita ta hana Maryam ta faÉ—i abinda ke ranta"

Baffah dai ya ka sa magana Alhaji kuma sai ya kama dariya dan buruntsun Muntarin dariya ya bashi.

Muntari har da taɓa kafaɗar Maryam ya ce " i love you, you love me we marry. Dont afraid of Goggo ko wasu 'yan baƙin ciki. We marry for love"

Idon Maryam har cikowa da hawaye yai saboda yadda Muntari ke maganar yana zare ma ta ido.
Ta ce "I'm sorry Muntari but i dont love you, i only like you as a friend"

"Friend ɗin uwarki, na ce auren ki zan yi. Marriage" ya ƙarisa maganar yana kamo hannunta.

Alhaji ya daka ma sa tsawa akan ya sake ma ta hannu. Sannan ya kalli Hamza ya ce ya cewa Maryam ta koma gida.

Har Maryam ta tashi Muntari bai bar masifa ba, har ta fara tafiya Hamza ya sake kiranta. Ta dawo jiki a sanyaye. Ba ta san miyasa Muntari ya misunderstanding maganar ta ba, ko dan baya jin turanci sosai ne?

"Tambaya min ita ko tana son auren Shehu Tijjani?" Alhaji ya faÉ—a fiskar sa É—aure.

"Do you love Tijjani?"

Murmushi ne ya suɓuce ma ta, ta yi saurin sa hannu ta tare bakinta, she cant believe she actually blushed a gaban waɗannan manyan mutane.

"Do you want to Marry him?"

Wannan karan gyalenta ta jawo ta rufa fiskarta da shi tana murmushi zuciyarta na bugawa da ƙarfi ƙarfi.

Wannan kaÉ—ai ya isa ya nuna mu su tana son T J amma sai da Alhaji ya sake cewa Hamza ya sake ma ta tambayar dan su na son gane wani abu ne.
Ya sake maimaita tambayar wannan karan ta cikin gyalenta ta ɗan leƙo ta ce "Yes"

Gaban Muntari ya buga kaman tashin nakiya.

Alhaji ya ce "Ka dai ji Shehu Tijjani ta ke so. Dan haka daga nan, daga yanzu magana ta wuce. Idan ba kai butulu ba ne ba Tijjani ba ne ya kawota garin nan?"

Muryar sa a raunane ya ce " Allah ya isa, dukkan kun nan kun ci amanata. Kuma fin ƙarfi kuka min amma Maryam ni ta ke so ba Hamma ba. Kuma..."

Yadda Alhaji Isa ya haushi da faÉ—a ne ya sa yai shiru sai ga hawaye na zubo ma sa. An cuce shi, an cuce shi abinda ya sani kenan...

Maryam da ta koma gida gaba ɗaya wani shauƙi da kewar T J ta ke yi gashi saura sati ɗaya ya dawo.

Da Baffa ya dawo ne ya sanar da Goggo duk abinda ake ciki ita kuma ta ce yai wa Iya magana dan Muntari yana jin maganar Iyan.
Sanda Baffah ya samu Iya da maganar ita kuwa ta ƙeƙasa ƙasa ta ce sharri ne ƙila ma Maryam ce ta shanye shi amma ba abinda zai sa Muntari ya ce zai auri Maryam.
Abu dai sai gashi gaba É—aya gida an É—auki zancen.
Shi kuwa Muntari daga ƙofar gidan Alhaji Isa sai gidan Sarki. Ba kunya ba tsoron Allah ya faɗi ƙarya da gaskiya akan abinda ya faru yana kuma so a bi ma sa hakkin sa.
Iyalen Modibbo ba bare ba ne a Fada dan haka Sarki ya aika sammaci.

End of Chapter 11Continue to the next chapter or choose another story below.

More Hausa novels

Browse all books →
Previous Login to Save Next