Ramadan Promo!All users that send a manual request for premium upgrade on sallah day will be granted for 1 month free.
Soyayyanovels
Zaytoonah Part One Complete Hausa Novel
Zaytoonah Part One Complete Hausa Novel
By Azizat
Login to keep your reading position saved.
Book Page Chapters
Zaytoonah Part One Complete Hausa Novel

Zaytoonah Part One Complete Hausa Novel

Author: Azizat
Chapter 39 of 161
About 8 min read
Chapter progress: 0%
Listen Mode
Listen to this chapter using your device voice.
Ready to listen from this chapter.
Free access is active. You can keep reading and download during this access window.

Book chapters

Choose a chapter and continue reading.

Start chapters
Chapter 1 1,689 words Chapter 2 1,523 words Chapter 3 1,583 words Chapter 4 1,696 words Chapter 5 1,682 words Chapter 6 1,693 words Chapter 7 1,594 words Chapter 8 1,673 words Chapter 9 1,663 words Chapter 10 1,668 words Chapter 11 1,678 words Chapter 12 1,698 words Chapter 13 1,687 words Chapter 14 1,699 words Chapter 15 1,656 words Chapter 16 1,634 words Chapter 17 1,681 words Chapter 18 1,675 words Chapter 19 1,655 words Chapter 20 1,613 words Chapter 21 1,669 words Chapter 22 1,655 words Chapter 23 1,671 words Chapter 24 1,650 words Chapter 25 1,677 words Chapter 26 1,696 words Chapter 27 1,598 words Chapter 28 1,699 words Chapter 29 1,694 words Chapter 30 1,659 words Chapter 31 1,683 words Chapter 32 1,309 words Chapter 33 1,691 words Chapter 34 1,697 words Chapter 35 1,553 words Chapter 36 1,588 words Chapter 37 1,682 words Chapter 38 1,680 words Chapter 39 Reading now Chapter 40 1,649 words Chapter 41 1,700 words Chapter 42 1,698 words Chapter 43 1,676 words Chapter 44 1,625 words Chapter 45 1,633 words Chapter 46 1,675 words Chapter 47 1,693 words Chapter 48 1,668 words Chapter 49 1,688 words Chapter 50 1,647 words Chapter 51 1,653 words Chapter 52 1,568 words Chapter 53 1,689 words Chapter 54 1,699 words Chapter 55 1,669 words Chapter 56 1,578 words Chapter 57 1,564 words Chapter 58 1,660 words Chapter 59 1,694 words Chapter 60 1,415 words Chapter 61 1,653 words Chapter 62 1,690 words Chapter 63 1,685 words Chapter 64 1,618 words Chapter 65 1,652 words Chapter 66 1,674 words Chapter 67 1,687 words Chapter 68 1,699 words Chapter 69 1,644 words Chapter 70 1,698 words Chapter 71 1,691 words Chapter 72 1,671 words Chapter 73 1,689 words Chapter 74 1,679 words Chapter 75 1,677 words Chapter 76 1,678 words Chapter 77 1,655 words Chapter 78 1,683 words Chapter 79 1,696 words Chapter 80 1,700 words Chapter 81 1,694 words Chapter 82 1,697 words Chapter 83 1,692 words Chapter 84 1,668 words Chapter 85 1,554 words Chapter 86 1,666 words Chapter 87 1,677 words Chapter 88 1,694 words Chapter 89 1,667 words Chapter 90 1,700 words Chapter 91 1,670 words Chapter 92 1,670 words Chapter 93 1,655 words Chapter 94 1,640 words Chapter 95 1,607 words Chapter 96 1,668 words Chapter 97 1,659 words Chapter 98 1,689 words Chapter 99 1,675 words Chapter 100 1,614 words Chapter 101 1,610 words Chapter 102 1,700 words Chapter 103 1,683 words Chapter 104 1,657 words Chapter 105 1,698 words Chapter 106 1,700 words Chapter 107 1,695 words Chapter 108 1,656 words Chapter 109 1,683 words Chapter 110 1,699 words Chapter 111 1,699 words Chapter 112 1,641 words Chapter 113 1,696 words Chapter 114 1,626 words Chapter 115 1,695 words Chapter 116 1,691 words Chapter 117 1,698 words Chapter 118 1,645 words Chapter 119 1,673 words Chapter 120 1,691 words Chapter 121 1,635 words Chapter 122 1,694 words Chapter 123 1,689 words Chapter 124 1,688 words Chapter 125 1,673 words Chapter 126 1,692 words Chapter 127 1,686 words Chapter 128 1,697 words Chapter 129 1,660 words Chapter 130 1,691 words Chapter 131 1,674 words Chapter 132 1,670 words Chapter 133 1,693 words Chapter 134 1,691 words Chapter 135 1,687 words Chapter 136 1,672 words Chapter 137 1,691 words Chapter 138 1,657 words Chapter 139 1,687 words Chapter 140 1,650 words Chapter 141 1,695 words Chapter 142 1,607 words Chapter 143 1,699 words Chapter 144 1,676 words Chapter 145 1,698 words Chapter 146 1,684 words Chapter 147 1,664 words Chapter 148 1,696 words Chapter 149 1,674 words Chapter 150 1,680 words Chapter 151 1,697 words Chapter 152 1,628 words Chapter 153 1,618 words Chapter 154 1,688 words Chapter 155 1,664 words Chapter 156 1,692 words Chapter 157 1,584 words Chapter 158 1,644 words Chapter 159 1,646 words Chapter 160 1,618 words Chapter 161 1,797 words

Kusan minti talatin kafin likitan ya fito ya mu su bayanin ta farfaÉ—o amma sun ma ta allurar bacci. Cewa yai ta sha wani abu ne da ya birkita ma ta ciki sannan akwai yunwa a tattare da ita.
Maryam kallon sa ta ke yi tana ajiyar zuciya. Idan ka cire ƙananun ciwuka da Zaytoonah ta yi lokacin tana jaririya zuwa kafin a yayeta ba ta taɓa wani rashin lafiya da har zai sa a kawota asibiti ba.
Bayan sun gama jin bayanin Doctor su ka shiga É—akin da aka kwantar da Zaytoonan. Tana kwance an É—aura ma ta drip. Sai yanzu ma Mommy ta lura idon Zaytoonan ya faÉ—a, laifi ta É—aurawa kan ta na rashin damuwa da bin diddigin miyasa Zaytoonah ta dena cin breakfast da lunch tareda su.

A asibitin ta kwana tareda Zaytoonah da Salman, duk yadda ta so Salman ya je gida ya kwana ƙi yai, shi da Muntari su ka koma gida Salman ya shiga gida ya ɗauko mu su abubuwan buƙata wanda Mommy ce ta gaya ma sa abubuwan da zai ɗauko. Da su ka koma asibitin ya ƙeƙasa ƙasa akan shima a nan zai kwana dan haka Maryam ta bar shi. Muntari ma bai so tafiya ba amma ya zai yi dole ya tafi.

Zuwa Asuba Zaytoonah ta farka. Mommy ta É—an saka kan ta a bakin gado tana barci dan kwanan zaune ta yi, towards Asuba ne ma baccin ya É—auketa.

"Mommy, Mommy" Zaytoonah ta faÉ—a da dashashshiyar murya.

Maryam ta yi girgigit ta tashi.

"Adaeze, Adaobi nmo are you ok" ta faÉ—a tana kissing É—in hannunta.

"I'm thirsty"

"Ki tsaya barin tambayi likita ko za ki iya shan ruwa" ta kissing É—in kumatunta da goshin ta sannan ta fita da sauri...

Kwana uku Zaytoonah ta yi aka sallamota. Ba ta ɓoye mu su komai ba ta sanar da su duk yadda ta ke ƙin cin abinci da kuma maganin da ta siya ta sha. Maryam da Tijjani kam sai ido dan gaba ɗaya kan su ya ɗaure amma Maryam ta san result ne na bullying ɗin ta da ake yi a makaranta. Ba wanda ya ma ta masifa illa jaddada ma ta da su ka yi akan suna tsananin son ta a yadda ta ke.

Da safiya Maryam ta kira T J ta sanar da shi dan haka maimakon zuwa yamma da ya ce zai dawo a safiyar ya kamo hanya zuwa ƙarfe ɗaya ya iso asibitin. Kafin nan Muntari ne ya ke zaune tareda su shi ya biya kuɗin komai. Ko da T J ya zo ya tambayeshi kuɗin yana so ya maida ma sa cewa yai Zaytoonah 'yar sa ce babu bashi tsakanin su.
Har aka sallameta kullum sai ya je ya gaisheta kuma ganin Maryam ta sake jiki da shi ya sa shi farinciki ya kuma ba shi ƙarfin gwiwar zuwan. Da aka sallame su ma shi ya dawo da su gida a motar sa. Ya shiga gidan aka wuni da shi har ya ci abinci. Shi kan sa T J ya yi mamakin yadda Maryam ta sake da Muntari.

Hajjo dai ta je ta duba Zaytoonah a asibiti sau É—aya amma Iya ba ta je ba. Humairah kuwa T J da kan sa ya je ya É—aukota ta gaisheda yayarta sai huhhura hanci ta ke ita a dole ba ta so. Dan ta jima tana zargin Daddy ya fi son Zaytoonah a kan ta...

Yau ne kwana na takwas da aka sallami Zaytoonah a Asibiti kuma Alhamdulillah tana cin abinci sosai musamman ma yadda T J da Maryam su ka maida hankali akan movement É—in ta.
A É—an madaidaicin gadon na ta su ka zauna su uku su ka sa ta a tsakiya.

Maryam tana shafa kan ta ta ce "Zaytoonah kin san muna son ki sosai ko?"
Ta gyaÉ—a kai
T J ya ce " kuma kin san ke Princess ce"
Sai ta yi dariya

"I know how you feel Adaeze. Nima an bullying ɗina lokacin ina makaranta. Ina son rawan Balle, tun ina yarinya na ke son zama Ballerina. Ina shekara biyar na fara koya kuma ina da ƙoƙari sosai, ina shekara bakwai aka fara tsokana na idan muna practice wanda sai daga baya na gane ba wai dan ƙiba na bane ya sa su ke tsokana na ƙwazo na ya sa su ke tsokanana saboda su ɓata min rai. Then watarana ina shekara tara za mu representing school ɗin mu a gasar rawar Balle, muna practice sai na miƙar da ƙafa na sama kawai sai hantsar wando na ya yage kasancewa rigan ya ɗan matseni. Aka fara min dariya nan da nan na fara hawaye na gudu na bar wajen and that's the end. Wannan dariya ya kashe min dream ɗina, har rana ita yau sai dai na kunna video na kalli rawan in yi sha'awar sa amma ban sake ko gwadawa ba just because an min dariya a stage practice.
Ba na so ki kashe dream ɗin ki just because ana miki dariya ko ana kiran ki da wasu suna. You are beautiful just the way you are, you dont need to be slim to look pretty. And always remember ko kin fi haka ƙiba ni da Dad ɗin ki will always love you and you'll always be our Princess"

Ta É—auko Cadbury chocolate guda biyu ta ba ta Zaytoonah ta waro ido.

"Indai saboda ina hanaki ciye-ciye ne kika sa damuwa a ran ki daga yau ba zan hana ki ba. Ki ci duk abinda ki ke so kin ji"

Zaytoonah ta amsa tana murmushi. T J ya ce "ni kuma da na ke ɗan firit ba za a bani kayan daɗi na ci na yi ƙiban ba"

Maryam ta ja kunnen sa da ɗan ƙarfi Zaytoonah ta sa dariya tana yi tana cin chocolate ɗin ta...

An chanjawa Zaytoonah makaranta inda ta fara zuwa SS1, da ke sabuwar zuwa ne 'yan ajin na É—an ma ta gani-gani amma ba wanda ya ma ta wani nasty comment so far.
Tana samun kulawa daga iyayenta da ƙaninta da Auwal wanda tun rashin lafiyarta shima ya ƙara ninka kulawar da ya ke ba ta. Ɗan tsokalarta da ya ke yi da saboda ƙiban ta ya dena.

Ba wai ta dena jin haushin ƙiban ta ba ne but gradually she's learning to accept herself and love herself more. Ta ga yadda Iyayenta su ka damu lokacin da ta ke Asibiti ba ta fatan ta sake sa su cikin damuwa because she loves them very much...

***

Muntari tun rashin lafiyar Zaytoonah da ya ga Maryam ta sauko daga fushin da ta ke yi da shi ya ƙara matsuwa da raba auren ta da Tijjani. Ya tabbata dai Bokan da ya ma sa aiki wancan karan kuɗin sa kawai ya ci amma duk da haka bai daddara ba wajen neman inda zai dace buƙatar sa ta biya.

Bayan wata uku da rashin lafiyan Zaytoonah Maryam ta samu kyautar Mota. Akwai wani client ɗin ta ne da ta jagorance shi wajen wata shari'a mai sarƙaƙiya har su ka je Supreme court Abuja kuma yai winning shari'ar, ita ta ma manta da shi dan an kwana biyu da yin case ɗin. Kawai sai gashi har gida ya kawo ma ta key ɗin mota, lokacin ma suna tareda TJ. Duk yadda ta so ƙin karɓan motan nan sai da ya dage tareda roƙan T J ya sa baki tunda tsakani da Allah ya ba ta. Gadon su ne wani Yayan Baban su ke son cinyewa shine Maryam ta shige mu su gaba har su ka winning case ɗin. Ita kuma ta karɓi case ɗin ne saboda yadda case ɗin su na son danne hakkin marayu yai kama da yadda itama ƙanin Babanta ya kashe iyayenta ya cinye dukiyar su.

Bayan ta ƙarɓi motan a T J ta bawa amma ya ce fir ba zai karɓa ba saboda kyautar ta ce. Shima yana taru nan ba da jimawa ba zai sayi ta shi. Ba'a jima ba ta koyi mota ta fara fita da ita tana saka L tag da ke nuna ita ɗin mai koyo ce.

Daga jin Maryam ta yi mota Hajjo ta fara ƙananun maganganu, ta je wajen Iya ta ma ta gulman wai a wajen aiki aka bata kuma idan ba karuwanci ba ba wanda zai ba da kyautar mota haka kawai siddan.

Iya ta kira T J ta ce ba ta yarda da aikin da Maryam ta ke yi ba ya hanata zuwa. Yana fara ba ta baki ta ce idan ya ƙara barin Maryam ta yi aiki za ta tsine ma sa. Ya shiga ruɗu ya cigaba da ba ta haƙuri amma ta ƙi fir. Ya yiwa Muntari magana akan ya taya shi ba wa Iya haƙuri shi kuwa ganin ya samu hanyar da zai raba kan Maryam da T J ya sa ya je ya zauna ya zuga Iya ya ce kar ta yarda, ta matsa ma sa sai ya hana Maryam aiki. A tunanin sa Maryam na son aikin ta sosai idan kuma aka hanata aiki zai jawo matsala tsakanin ta da T J.

Ganin yayi-yayi ta ƙi yarda ne ya sa shi yiwa Maryam magana akan ta ajiye aiki for now daga baya ko teaching job ne ta nema. Ko kuma ta koma ta yi masters ɗin ta ƙila ta samu koyarwa a Jami'a ko kwaleji.

Maryam ta san haka siddan ba zai yi maganar nan ba sai dai idan iya ce ta sa shi. Tashin farko tace ma sa aiki kam yanzu ta fara. Yayi-yayi da ita ta ce ba ta yarda ba idan za su rabu sai dai su rabu amma ba za ta ajiye aikin ta ba. Daga ƙarshe ya furta ma ta abinda Iya ta ce da shi. Ta yi mamaki kam amma ta dake ta ce"your choice Barkindo. Sai ka zaɓi abinda ka ga ya dace"

Yai shiru yana kallon ta yana sauke ajiyar zuciya.

"Maryam ki min alfarman nan dan Allah. Ina so na rabu da Iya lafiya"
Maganar da ya faÉ—a kenan lokacin da ya ga ta tashi daga kan gadon.

End of Chapter 39Continue to the next chapter or choose another story below.

More Hausa novels

Browse all books →
Previous Login to Save Next