Ramadan Promo!All users that send a manual request for premium upgrade on sallah day will be granted for 1 month free.
Soyayyanovels
Zaytoonah Part One Complete Hausa Novel
Zaytoonah Part One Complete Hausa Novel
By Azizat
Login to keep your reading position saved.
Book Page Chapters
Zaytoonah Part One Complete Hausa Novel

Zaytoonah Part One Complete Hausa Novel

Author: Azizat
Chapter 60 of 161
About 7 min read
Chapter progress: 0%
Listen Mode
Listen to this chapter using your device voice.
Ready to listen from this chapter.
Free access is active. You can keep reading and download during this access window.

Book chapters

Choose a chapter and continue reading.

Start chapters
Chapter 1 1,689 words Chapter 2 1,523 words Chapter 3 1,583 words Chapter 4 1,696 words Chapter 5 1,682 words Chapter 6 1,693 words Chapter 7 1,594 words Chapter 8 1,673 words Chapter 9 1,663 words Chapter 10 1,668 words Chapter 11 1,678 words Chapter 12 1,698 words Chapter 13 1,687 words Chapter 14 1,699 words Chapter 15 1,656 words Chapter 16 1,634 words Chapter 17 1,681 words Chapter 18 1,675 words Chapter 19 1,655 words Chapter 20 1,613 words Chapter 21 1,669 words Chapter 22 1,655 words Chapter 23 1,671 words Chapter 24 1,650 words Chapter 25 1,677 words Chapter 26 1,696 words Chapter 27 1,598 words Chapter 28 1,699 words Chapter 29 1,694 words Chapter 30 1,659 words Chapter 31 1,683 words Chapter 32 1,309 words Chapter 33 1,691 words Chapter 34 1,697 words Chapter 35 1,553 words Chapter 36 1,588 words Chapter 37 1,682 words Chapter 38 1,680 words Chapter 39 1,677 words Chapter 40 1,649 words Chapter 41 1,700 words Chapter 42 1,698 words Chapter 43 1,676 words Chapter 44 1,625 words Chapter 45 1,633 words Chapter 46 1,675 words Chapter 47 1,693 words Chapter 48 1,668 words Chapter 49 1,688 words Chapter 50 1,647 words Chapter 51 1,653 words Chapter 52 1,568 words Chapter 53 1,689 words Chapter 54 1,699 words Chapter 55 1,669 words Chapter 56 1,578 words Chapter 57 1,564 words Chapter 58 1,660 words Chapter 59 1,694 words Chapter 60 Reading now Chapter 61 1,653 words Chapter 62 1,690 words Chapter 63 1,685 words Chapter 64 1,618 words Chapter 65 1,652 words Chapter 66 1,674 words Chapter 67 1,687 words Chapter 68 1,699 words Chapter 69 1,644 words Chapter 70 1,698 words Chapter 71 1,691 words Chapter 72 1,671 words Chapter 73 1,689 words Chapter 74 1,679 words Chapter 75 1,677 words Chapter 76 1,678 words Chapter 77 1,655 words Chapter 78 1,683 words Chapter 79 1,696 words Chapter 80 1,700 words Chapter 81 1,694 words Chapter 82 1,697 words Chapter 83 1,692 words Chapter 84 1,668 words Chapter 85 1,554 words Chapter 86 1,666 words Chapter 87 1,677 words Chapter 88 1,694 words Chapter 89 1,667 words Chapter 90 1,700 words Chapter 91 1,670 words Chapter 92 1,670 words Chapter 93 1,655 words Chapter 94 1,640 words Chapter 95 1,607 words Chapter 96 1,668 words Chapter 97 1,659 words Chapter 98 1,689 words Chapter 99 1,675 words Chapter 100 1,614 words Chapter 101 1,610 words Chapter 102 1,700 words Chapter 103 1,683 words Chapter 104 1,657 words Chapter 105 1,698 words Chapter 106 1,700 words Chapter 107 1,695 words Chapter 108 1,656 words Chapter 109 1,683 words Chapter 110 1,699 words Chapter 111 1,699 words Chapter 112 1,641 words Chapter 113 1,696 words Chapter 114 1,626 words Chapter 115 1,695 words Chapter 116 1,691 words Chapter 117 1,698 words Chapter 118 1,645 words Chapter 119 1,673 words Chapter 120 1,691 words Chapter 121 1,635 words Chapter 122 1,694 words Chapter 123 1,689 words Chapter 124 1,688 words Chapter 125 1,673 words Chapter 126 1,692 words Chapter 127 1,686 words Chapter 128 1,697 words Chapter 129 1,660 words Chapter 130 1,691 words Chapter 131 1,674 words Chapter 132 1,670 words Chapter 133 1,693 words Chapter 134 1,691 words Chapter 135 1,687 words Chapter 136 1,672 words Chapter 137 1,691 words Chapter 138 1,657 words Chapter 139 1,687 words Chapter 140 1,650 words Chapter 141 1,695 words Chapter 142 1,607 words Chapter 143 1,699 words Chapter 144 1,676 words Chapter 145 1,698 words Chapter 146 1,684 words Chapter 147 1,664 words Chapter 148 1,696 words Chapter 149 1,674 words Chapter 150 1,680 words Chapter 151 1,697 words Chapter 152 1,628 words Chapter 153 1,618 words Chapter 154 1,688 words Chapter 155 1,664 words Chapter 156 1,692 words Chapter 157 1,584 words Chapter 158 1,644 words Chapter 159 1,646 words Chapter 160 1,618 words Chapter 161 1,797 words

"Ni ba na tunanin abinci" ta faÉ—a tana tura baki

"Its ok Baby girl, ki ci abinci yadda ki ke so amma banda satan abinci da dare dan kin ga akwai ma su kama mutane, inaga su ne ma su ka zo É—aukan ki jiya"

Ta zaro ido waje " da gaske?"

Yai murmushi ya ce "just kidding"

Ta haÉ—e fuska tana tura baki.

Ya haÉ—a hannayan sa biyu alamar sorry.

Ben ya ce "we'll be late"

Zuhayr ya bi shi su ka fita. Ita kuwa Zaytoonah ta bi bayan sa da harara. Bayan sun fita sai ta tsaya tana kokonton abinda ya faru, ko dai da gaske ne abinda Zuhayr ya faÉ—a mafarki ta yi? Amma abinda ya faru look so real.
Bayan ta shiga ɗaki ne ta yi wanka ta fito ta kalli madubi ta ga tsakiyar goshinta ya ɗan kumbura, ta taɓa wajen tana tunawa ai buguwa da gini da ta yi ne, to ko dai da gaske ne?
Ganin ta fara ja'in'ja da zuciyarta sai ta tattara zancen ta watsar ta barshi a magagin bacci ta yi ta bugu ta faɗi shine ta yi bacci a wajen har ta yi mummunan mafarki. Akwai lokacin tana Zaria tun ma Daddy yana nan, ta yi tashin dare irin haka ta je falo ta buɗe fridge ta ɗauko ragowan shinkafar da aka ci da dare ta ajiye a ƙasa ta fara ci saboda tsabar yunwa, ranan fushi ta ke da Mommy sai ta ƙi cin abincin dare ta kwanta haka to kuwa ita da ba ta iya juran yunwa sai yunwa ya tada ita. Ranan da Asuba Daddy ya tasheta a gefen fridge ta yi bacci da sauran shinkafa a hannu...

Shi kuwa Ben suna cikin gudu ya tambayi Zuhayr dalilin da ya sa ya ke sakewa Zaytoonah haka.

"A Ƙanwata na ɗauketa, kuma tana buƙatar kulawa a wannan lokaci"

Ben yai shiru amma chan ƙasan zuciyar sa ya san akwai matsala domin Alinah ma da irin haka ya fara kafin ya zo ya fara son ta.

***

Tun da su ka yi magana da Zuhayr ya fara sa wa Muntari ido ya ga inda zai je, a ranan ya bi shi zuwa wani gida chan wani anguwa wanda bai cika ba saboda sabuwar anguwa ce. Ya kira wanda Zuhayr ya haÉ—a su ya ma sa bayani shi kuma ya ce za su cigaba da bincike daga wajen.

A ɓangaren Maryam kam har ta fara fita hayyacinta. Duk abincin da ya kawo ma ta babu wanda ta ci, sallah kawai ta ke yi tanayi tana hutawa. Muntari ya ƙara ma ta kwana uku wai bayan nan duk abinda ta yanke shine sakamakon 'ya'yanta. Zuciyarta ya gamsu Muntari ne ya hallaka ma ta T J, mutumin da ba kunya ba tsoron Allah ya ce zai kashe 'ya'yan Yayan sa, ai kenan Uban su mai sauƙi ne, dan Uban su ne ma ya ma sa laifi.
Ta riga ta sa a ranta in kwana ukun nan su ka cika cikin biyu za ta yi É—aya. Ko dai ta amince da auren na sa ko kuma ta kashe kan ta.
A safiyar rana ta uku da ya kawo ta gidan sai gashi ya shigo É—auke da tray kaman yadda ya saba.

"Wannan sallan ba zai fishshe ki da komai ba dan aikin gama ya gama. Ni Muntari na riga na ci galaba akan ki"

Ba ta kulashi ba ta cigaba da addu'an da ta ke yi.

"Ki tashi ki ci abinci, wannan azumin da ki ke yi ulcer zai sa miki kuma ba na so ki zo gida na da ciwo"

Ko kallo bai isheta ba haka ya gama ɓuruntun sa ya fita.

Daga fitar Muntari ya kulle ɗakin da Maryam ta ke ta baya kamar yadda ya saba, yana isowa falo ya ji kaman ana buga gate. Ya ɗan leƙo ta window ya na yiwa Maigadin sa magana.

"Tanimu ko ma waye kar ka buɗe ƙofa bana karɓan baƙi a nan"

Ya zauna a kujera ya fito da wayar sa yana lissafin kuÉ—in da zai kashe wajen hidiman biki, yanzu haka ma wasu mahaukatan kaya ya sa a haÉ—o ma sa daga Dubai na lefen Amarya.
Ya ga tsoro a tattare da Maryam ya san dole haƙura za ta yi, wannan karan ba ta da zaɓi sai na shi.

Baifi minti huɗu ba ya ji ana buga ƙofar falo.

"Tanimu miye ne wai, ka sha ƙwaya ne?"

Muryan Tanimu da aka titsiye da bindiga a shaƙe ya ce "ranka shi daɗe wani yaro ne wai sunan sa Auwal ya ce wai yana son ganin ka Allah ya yiwa Iya rasuwa yanzu. Na ce ya tafi ba ka karɓan baƙi ya ƙi ya tsaya a bakin gate sai kuka ya ke yi"

Jin zancen Iya ta rasu ko tunani bai tsaya ba ya zabura da sauri ya buɗe ƙofa ya fito. Ganin Tanimu da Auwal da wani mutum ya sa shi cewa "Lafiya?"
Bindiga aka sa a ƙeyar sa aka ce "You are under arrest Alhaji Muntari"...

***

Asalin sunan sa Benedict Atkinson. Mahaifin shi Robert Atkinson Bayahude ne (Jew), Haifaffen ƙasar America ne amma iyayen sa 'yan ƙasar Ireland ne. Yana tareda matar sa ɗaya mai suna Laura Vincent.
Tun bayan shekaru goma da auren su da ya rasa aikin sa ya koma wani dabba, shan giya ya ke yi kamar ba gobe hakanan sai yai ta dukan matar sa Laura. Ƙarshe ma saboda dukan ɗan su Ben da ya taɓayi sai ya sa ta kai shi boarding school. Da wuya ta yi yawa sai ta gudu ta koma wani ƙauye inda wata ƙawarta ta sama ma ta aiki a wani gidan gona.

Laura tana aiki a gidan gonar su Mr and Mrs Haddish. A nan ne kuma Ben da Zuhayr su ka zama abokai wani lokaci da Ben É—in ya zo hutu ya kuma haÉ—u da Zuhayr a wajen da ya ke koyon hawan doki.
Shekaru biyu Laura ta yi ba tareda mijinta Robert ya san inda ta ke ba, sai watarana kwatsam sai ga shi ya ɓullo. Ya zo akan dole ta bishi su tafi amma taƙi, garin suna kokawada shi ya bugata da gini sai kan ta ya bugu sosai har ya zo da ƙarar kwana.
Yana shirin guduwa ma aka kama shi. Ƙarshe aka shigar da ƙara aka kama shi da laifin kashe matar sa aka wuce da shi prison.

Kasancewar Ben bai kai shekarun da zai iya rayuwa shi ɗaya ba sai ya zamana an fara ƙoƙarin maida shi gidan marayu kafin a samu wanda zai adopting ɗin sa tunda ba shi da wani family da za a iya maidashi wajen su. Kakar sa ɗaya ta wajen uwa tana gidan tsofaffi saboda ciwon mantuwa da ta ke da shi.

Wannan ya sa Zuhayr yai wa Kakan sa magana akan ya adopting É—in sa saboda Ben abokin sa ne, da ke suna son duk abinda É—an lelen su ke so shiyasa su ka adopting Benedict wanda sunan sa ya koma Benedict Vincent Haddish.

Makarantar da ya ke yi da aka cire shi aka maida shi makarantar da Zuhayr ya ke, daga lokacin kuma komai za ayiwa Zuhayr to za a yiwa Ben. Shaƙuwa mai tsanani ya shiga tsakanin su wanda za ka ɗauka ma 'yan biyu ne.

Boarding school da Ben yai a wajen ya fara sanin maza saboda makarantar duka maza ne, inda wani ɗan ɗakin su ya fara saduwa da shi a shekaran sa goma shauku. Abun ya taɓa shi sosai shiyasa ma duk lokacin da zai koma makaranta ya ke jin tsoro. A hankaki kuma har ya ɗan fara sabawa. Bayan ya koma ɗan gidan su Zuhayr kuwa kyautatawar Zuhayr gareshi ya fara kissima ma sa soyayyar shi saboda oreintation da ya samu daga makarantar su na maza na neman maza.

A hankali tun bai yarda so ba ne har ya zo ya tabbata ma sa soyayyar Zuhayr ne ya ma sa mugun kamu. Yayi ƙoƙarin bayyanawa Zuhayr abinda ke ran sa alokacin da su ka cika shekara ishirin da ɗaya, a lokacin kuma namiji na neman namiji ba komai ba ne a ƙasar tunda har aure ana yi.
Da ya tambayi Zuhayr ko zai iya son namiji É—an uwan sa sai Zuhayr ya ce Allah ya kiyaye, shi bai yarda da irin halin dabbancin nan ba. Daga wannan amsa da ya bashi ya sa Ben ya rufe soyayyar Zuhayr a zuciyar sa sai dai...
2/11/21, 10:04 PM - ****: 27

Bismillahir Rahmanir Rahim

*weight loss vs self love*

End of Chapter 60Continue to the next chapter or choose another story below.

More Hausa novels

Browse all books →
Previous Login to Save Next