Ramadan Promo!All users that send a manual request for premium upgrade on sallah day will be granted for 1 month free.
Soyayyanovels
Zaytoonah Part One Complete Hausa Novel
Zaytoonah Part One Complete Hausa Novel
By Azizat
Login to keep your reading position saved.
Book Page Chapters
Zaytoonah Part One Complete Hausa Novel

Zaytoonah Part One Complete Hausa Novel

Author: Azizat
Chapter 74 of 161
About 8 min read
Chapter progress: 0%
Listen Mode
Listen to this chapter using your device voice.
Ready to listen from this chapter.
Free access is active. You can keep reading and download during this access window.

Book chapters

Choose a chapter and continue reading.

Start chapters
Chapter 1 1,689 words Chapter 2 1,523 words Chapter 3 1,583 words Chapter 4 1,696 words Chapter 5 1,682 words Chapter 6 1,693 words Chapter 7 1,594 words Chapter 8 1,673 words Chapter 9 1,663 words Chapter 10 1,668 words Chapter 11 1,678 words Chapter 12 1,698 words Chapter 13 1,687 words Chapter 14 1,699 words Chapter 15 1,656 words Chapter 16 1,634 words Chapter 17 1,681 words Chapter 18 1,675 words Chapter 19 1,655 words Chapter 20 1,613 words Chapter 21 1,669 words Chapter 22 1,655 words Chapter 23 1,671 words Chapter 24 1,650 words Chapter 25 1,677 words Chapter 26 1,696 words Chapter 27 1,598 words Chapter 28 1,699 words Chapter 29 1,694 words Chapter 30 1,659 words Chapter 31 1,683 words Chapter 32 1,309 words Chapter 33 1,691 words Chapter 34 1,697 words Chapter 35 1,553 words Chapter 36 1,588 words Chapter 37 1,682 words Chapter 38 1,680 words Chapter 39 1,677 words Chapter 40 1,649 words Chapter 41 1,700 words Chapter 42 1,698 words Chapter 43 1,676 words Chapter 44 1,625 words Chapter 45 1,633 words Chapter 46 1,675 words Chapter 47 1,693 words Chapter 48 1,668 words Chapter 49 1,688 words Chapter 50 1,647 words Chapter 51 1,653 words Chapter 52 1,568 words Chapter 53 1,689 words Chapter 54 1,699 words Chapter 55 1,669 words Chapter 56 1,578 words Chapter 57 1,564 words Chapter 58 1,660 words Chapter 59 1,694 words Chapter 60 1,415 words Chapter 61 1,653 words Chapter 62 1,690 words Chapter 63 1,685 words Chapter 64 1,618 words Chapter 65 1,652 words Chapter 66 1,674 words Chapter 67 1,687 words Chapter 68 1,699 words Chapter 69 1,644 words Chapter 70 1,698 words Chapter 71 1,691 words Chapter 72 1,671 words Chapter 73 1,689 words Chapter 74 Reading now Chapter 75 1,677 words Chapter 76 1,678 words Chapter 77 1,655 words Chapter 78 1,683 words Chapter 79 1,696 words Chapter 80 1,700 words Chapter 81 1,694 words Chapter 82 1,697 words Chapter 83 1,692 words Chapter 84 1,668 words Chapter 85 1,554 words Chapter 86 1,666 words Chapter 87 1,677 words Chapter 88 1,694 words Chapter 89 1,667 words Chapter 90 1,700 words Chapter 91 1,670 words Chapter 92 1,670 words Chapter 93 1,655 words Chapter 94 1,640 words Chapter 95 1,607 words Chapter 96 1,668 words Chapter 97 1,659 words Chapter 98 1,689 words Chapter 99 1,675 words Chapter 100 1,614 words Chapter 101 1,610 words Chapter 102 1,700 words Chapter 103 1,683 words Chapter 104 1,657 words Chapter 105 1,698 words Chapter 106 1,700 words Chapter 107 1,695 words Chapter 108 1,656 words Chapter 109 1,683 words Chapter 110 1,699 words Chapter 111 1,699 words Chapter 112 1,641 words Chapter 113 1,696 words Chapter 114 1,626 words Chapter 115 1,695 words Chapter 116 1,691 words Chapter 117 1,698 words Chapter 118 1,645 words Chapter 119 1,673 words Chapter 120 1,691 words Chapter 121 1,635 words Chapter 122 1,694 words Chapter 123 1,689 words Chapter 124 1,688 words Chapter 125 1,673 words Chapter 126 1,692 words Chapter 127 1,686 words Chapter 128 1,697 words Chapter 129 1,660 words Chapter 130 1,691 words Chapter 131 1,674 words Chapter 132 1,670 words Chapter 133 1,693 words Chapter 134 1,691 words Chapter 135 1,687 words Chapter 136 1,672 words Chapter 137 1,691 words Chapter 138 1,657 words Chapter 139 1,687 words Chapter 140 1,650 words Chapter 141 1,695 words Chapter 142 1,607 words Chapter 143 1,699 words Chapter 144 1,676 words Chapter 145 1,698 words Chapter 146 1,684 words Chapter 147 1,664 words Chapter 148 1,696 words Chapter 149 1,674 words Chapter 150 1,680 words Chapter 151 1,697 words Chapter 152 1,628 words Chapter 153 1,618 words Chapter 154 1,688 words Chapter 155 1,664 words Chapter 156 1,692 words Chapter 157 1,584 words Chapter 158 1,644 words Chapter 159 1,646 words Chapter 160 1,618 words Chapter 161 1,797 words

Tana buɗe ƙofa ta ganshi yana murmushi.
"Dear ga É—an uwa nan na kawo miki" yai maganar yana É—an muskutawa gefe.

Ben ta gani sanye da riga da wando fari irin na mazan pakistan har da hula fara.

Zuhayr ya ce " Masha Allah, after all this years Ben ya karɓi musulunci. I present to you my brother Benedict now Zubayr"

Ya nuna kan sa ya ce "Zuhayr" ya nuna Ben ya ce " Zubayr"

Zaytoonah sai ta yi mutuwar tsaye a wajen ga Ben kuma da ke ma ta wani munafukin murmushi yana ƙanƙanta munafukan idanun na san nan.

Ben ya karɓi musulunci ta yaya? Mutumin da iya zaman da ta yi da su ta san shi ba practicing jew ba ne. Ba ya komai na ibada da jews ke yi, ba za ta kirashi christian ba saboda nan ma baya yin ibada irin ta su. Ben atheist ne wanda ba shi da addini.

Ben musulmi🤔
*Ben fa zai yi komai dan ya samu abinda ya ke so. Team Ben mi kuka shirya mana ne? Mun bar muku gidan ma ashe ba mu tsira ba*
2/11/21, 10:04 PM - ****: 34

Bismillahir Rahmanir Rahim

*leukemia*

Satin su Zaytoonah É—aya da dawowa aka fara shirye-shiryen bikin Muhsina da AbdulHameed, cousin É—inta ne dan Mahaifiyar sa Yayar Mahaifin Muhsina É—in ne Uban su É—aya amma Uwa banban.

Daga wajen 'yanuwan Zuhayr ta samu kulawa a wajen su sosai musamman ma Kakannin Zuhayr mata wato Hajiya Nenne da Hajiya Saudah. Da ke tunda aka fara hidimar bikin gidan cika ya ke yi ita kam agidan su ta ke wuni, ba dan Mommy ba ma da anan za ta dinga kwana. Ba wai ta saba da 'yan gidan su Zuhayr ba ne, har yanzu idan ka cire tsofaffin sai kuma Muhsina da Hajiya Maryam wacce ta ke immediate ƙanwar marigayi Muhammad. Wasu cikin cousins ɗin Zuhayr da su ka haɗu a wajen hidiman bikin sun ɗan yi mutunci wasu kuwa sai dai kallon-kallon da harara kawai saboda girman kai da ya mu su katutu a zuciya...

"D har yanzu ba ka shirya ba ne?" Ta faÉ—a lokacin da ta shigo É—akin na su. Towel ne ajikinsa yana zaune a bakin gado, tissue da ya goge hancinsa da shi yai saurin takewa da room slippers É—in sa dan kar ta gani.

Ta riga ta shirya tuntuni yanzu ma daga É—akin Hajia Saudah ta ke wacce ta kirata ko sun gama shiri ne tunda an fara tafiya wajen da za'ayi dinner É—in. Lokacin da ta fita ta bar Zuhayr a banÉ—aki ne yana wanka.

"D ɗazu fa ka ke ƙorafin ban shirya ba amma gashi har na je na dawo ko kaya ba ka sa ba"

Ya ƙaƙaro murmushin dole ya ce "ina ga ba zan je wajen dinner ɗin ba. Kai na na ciwo"
Ido ta zaro lokacin da ya ke magana ta ga jini na ƙoƙarin fitowa a hancin sa.

"D jjjjjini a hancin ka" ta faÉ—a tana nuna ma sa hancin.
Sauran tissue da ya ɓoye yai saurin cirowa ya fara toshe hancin da shi.

"Mi ya sameka?, ba ka da lafiya ne? Na kira ma ka Kamal ya kai ka Asibiti ne"
Ta jero tambayoyin tana tattaɓa goshin sa.

Ya riƙo hannunta da sauri ya ce "kar ki damu haɓo ne"

"Haɓo?"

Ya gyaÉ—a ma ta kai yana murmushi.

Duk yadda ta ke ɗokin zuwa wajen dinner ɗin sai ta ji ya fita ma ta a ka. Lokacin da ta taimaka ma sa ya kwanta kamar yadda ya buƙata ne ta ga sauran tissue da yai amfani da su wanda suma cike su ke da jini hakan ya sa ta tsorata, ta fara tambayar kan ta anya haɓo ne kamar yadda ya ce ɗin ko kuma akwai wani abun daban.
Duk da ya ce ta tafi wajen dinner ɗin tunda ta shirya amma ba ta kulashi ba. Fita tayi ta je ta gayawa Hajia Saudah cewa sun fasa zuwa saboda Zuhayr ba ya jin daɗi. Da ta dawo kayan jikinta ta cire ta saka kayan bacci ta kwanta gefen mijinta kanta na kan ƙirjin sa.

"Gobe za mu je Asibiti a duba ka. Ƙila whether ɗin Nigeria ne bai karɓeka ba, na lura tunda muka zo zafi ke damunka, sai ka riƙa yin zufa, ko ni da ke da ƙiba ma bana irin zufan da ka ke yi tunda akwai sanyi"

"Na gaya miki ba komai haɓo ne kawai"

"Ni dai ban yarda ba"

Ya É—an rankwafo kan sa ya kissing goshinta ya ce "I love you"

"I love you too"...

Washegari duk yadda ta so ya je Asibiti cewa yai ba zai je ba lafiyar sa ƙalau. Ranan sai ta maƙale ma sa duk wani motsinsa yana idon ta, wajen ɗaurin aure kawai ya je a ranan amma tare su ke a ɗaki tun safe har yamma. Ko gidan su ba ta je ba kiran Mommy ta yi ta ce ma ta Zuhayr ba ya jin daɗi ba za ta zo ba.

Lura da ta yi da shi na wuni É—aya sai ta gane ashe ya rame ma ta.

"My D dan Allah mu je Asibiti a duba ka. Ka kalleka fa"

"Ki kwantar da hankalinki, ba abinda ke damina" ya faÉ—a yana jawota jikinsa.

"Ko dan kin ga kwana biyu ban ban ban..." ya shiga kissing wuyanta.

"Ni dai ban ce ba, kawai..."

Duk da baya jin daɗin jikinsa sai da ya tabbatar ya biya mu su buƙatun su, sai a sannan Zaytoonah ta ɗan kwantar da hankalinta.

Anyi biki an ƙare lafiya, Amarya Muhsina kuma an kaita Abuja inda mijinta ke aiki. Zaytoonah ta so zuwa amma yadda ta lura da yanayin Zuhayr sai ta fasa zuwa.

Tun zuwan su garin yau ne rana na biyu da za su je gidan su Mommy tare. Wannan karan ma Sallama za su yi saboda za su je ziyara Ringim washegari.

Bayan sun gaisa da Mommy sai ta ke tambayar sa ya jiki. Ya ce ma ta da sauƙi.

"Mommy Dan Allah ki ma sa magana ko zai ji, ya ƙi ya je Asibiti kuma har yanzu ba shi da lafiya fa" ta yi maganar cikin shagwaɓa.

"Mommy kar ki kulata lafiyata ƙalau, ta ƙi yarda ne"

Ta harareshi ta ce " Mommy sau uku ina kamashi yana goge jini a hancin sa, ya ce wai haɓo ne. Mommy ina kan haɓo a lokacin zafi ake yi?"

Mommy ta ce "garin ya ma sa zafi tunda kinga ba irin sanyin chan ba ne"

"Still Mommy..."

"Ki bari idan ku ka koma sai ku je Asibiti, zai fi ganewa da likitocin sa na chan"

Da wannan ta yi shiru ta É—au wani zancen a nan ta ke jin wai Hajjo mahaifiyar Humairah ta yi aure wai haihuwa ko yau ko gobe, Zaytoonah ta ce Allah ya sauketa lafiya.

Ba su jima da zuwa ba Zaytoonah ta ce za ta je gidan Maman Abdul ta karɓo Dambu dan sun yi waya akan za ta ma ta.
"Allah ya shiryeki da kwaÉ—ayi Zaytoonah" Salman da ke wajen ya faÉ—a. Mommy ta wurga ma sa wani kallo.

"To Mommy wai wani gida za ta je cin Dambu fa, miye daÉ—i a Dambu idan ba kwaÉ—ayin Adaeze ba"

"Salman tashi ka bar nan" Mommy ta daka ma sa tsawa.
Salman ya miƙe yana ƙunƙuni.

Falon ya saura daga Mommy sai Zuhayr sai kuma Junior da ke karatun dole da Mommy ta sa shi bayan ya fita yawo ba takalmi a ƙafar sa. Da zane shi za ta yi sai ta ga kamar dukan ma ba ya ma sa komai yanzu shiyasa ta tursasashi yin karatu. Daga inda su ke zaune tana jin karatun na sa, idan yai shiru ta sake waiwayan sa ta ce ya cigaba bai isa ba.

"Ina fata dai Zaytoonah ba ta da wata matsala?"

"No" ya furta a taƙaice.

Chan da shirun yai yawa ne sai Mommy ta miƙe dan ta shige ɗaki idan ya so ta turo ma sa Salman. Sai kuma ta ji ya ce

"ba ni da lafiya"

Mommy ta yi saurin zama tana jin ƙirjinta na bugun tara-tara.

"Ba na son hankalin Zaytoon ya tashi ne shiyasa na ke ɓoye ma ta. Inada cancer na jini, Chronic myelogenous leukemia"

"Innalillahi" Mommy ta furta a fili.

"Ciwon da ya kashe mahaifiyata kenan. Ina zuwa Asibiti check-up kuma sun fixing za a min Chemotheraphy da radiation farkon wannan watan amma na ce a É—aga"

"Miyasa?" Mommy ta faÉ—a cike da alhini.

"Na yiwa Zaytoon alƙawarin zan kawota gida kuma za ayi bikin Muhsina. Lokacin biki lokaci ne da 'yan uwa ke haɗuwa, ba na so na missing ganin 'yan uwan Baba na"

"Ya Allah! Zuhayr ai lafiyar ka tafi komai mahimmanci"

Ya gyaɗa kai ya ce "hakane, sai dai na zaɓi zuwa nan ɗin fiye da treatment ɗin. Idan na koma sai a fara ba matsala ba ne. Ina roƙon alfarma ɗaya a wajen ki"

Ya gyara zaman sa sosai ya kalli Mommy ya ce " a lokacin da ba ni da ƙarfin da zan supporting Zaytoonah, Dan Allah ki daure ki dinga kiranta kullum kina ƙarfafa ma ta gwiwa"...

Ba su kwana a Ringim ba kamar yadda su ka tsara da. Kwana biyu za su yi amma Mommy ta cewa Zaytoonah ka da su kwana su je a ranan su dawo a ranan. Da ta tambayi dalili cewa ta yi dan kar su ɗaurawa 'yan gidan hidima. Duk da family ɗin su T J yanzu ya zama ɓangarenci hakan bai hana an tarbesu da kyau ba. Ba ma kamar Goggo wacce da ta ga Zaytoonan sai da ta zubda ƙwalla saboda tunowa da ta yi da Tijjani.
Abinda ya faru tsakanin Maryam da Muntari da kuma abinda Rabi'u ke yi da dukiyar Muntari duk shi ya sa Family ɗin ya rarrabu, kowa da ɓangaren da ya kama. Wasu ma su kwaɗayi sun rufawa Rabi'u baya, wasu ma su kishin Ahalin Modibbo na ɗaura laifin abinda ya faru ga Maryam da kuma gaba da Rabi'u, wasu kuma na ganin tun farko an zalinci Maryam musamman bayan ɓatar T J.

End of Chapter 74Continue to the next chapter or choose another story below.

More Hausa novels

Browse all books →
Previous Login to Save Next