Ramadan Promo!All users that send a manual request for premium upgrade on sallah day will be granted for 1 month free.
Soyayyanovels
Zaytoonah Part One Complete Hausa Novel
Zaytoonah Part One Complete Hausa Novel
By Azizat
Login to keep your reading position saved.
Book Page Chapters
Zaytoonah Part One Complete Hausa Novel

Zaytoonah Part One Complete Hausa Novel

Author: Azizat
Chapter 108 of 161
About 8 min read
Chapter progress: 0%
Listen Mode
Listen to this chapter using your device voice.
Ready to listen from this chapter.
Free access is active. You can keep reading and download during this access window.

Book chapters

Choose a chapter and continue reading.

Start chapters
Chapter 1 1,689 words Chapter 2 1,523 words Chapter 3 1,583 words Chapter 4 1,696 words Chapter 5 1,682 words Chapter 6 1,693 words Chapter 7 1,594 words Chapter 8 1,673 words Chapter 9 1,663 words Chapter 10 1,668 words Chapter 11 1,678 words Chapter 12 1,698 words Chapter 13 1,687 words Chapter 14 1,699 words Chapter 15 1,656 words Chapter 16 1,634 words Chapter 17 1,681 words Chapter 18 1,675 words Chapter 19 1,655 words Chapter 20 1,613 words Chapter 21 1,669 words Chapter 22 1,655 words Chapter 23 1,671 words Chapter 24 1,650 words Chapter 25 1,677 words Chapter 26 1,696 words Chapter 27 1,598 words Chapter 28 1,699 words Chapter 29 1,694 words Chapter 30 1,659 words Chapter 31 1,683 words Chapter 32 1,309 words Chapter 33 1,691 words Chapter 34 1,697 words Chapter 35 1,553 words Chapter 36 1,588 words Chapter 37 1,682 words Chapter 38 1,680 words Chapter 39 1,677 words Chapter 40 1,649 words Chapter 41 1,700 words Chapter 42 1,698 words Chapter 43 1,676 words Chapter 44 1,625 words Chapter 45 1,633 words Chapter 46 1,675 words Chapter 47 1,693 words Chapter 48 1,668 words Chapter 49 1,688 words Chapter 50 1,647 words Chapter 51 1,653 words Chapter 52 1,568 words Chapter 53 1,689 words Chapter 54 1,699 words Chapter 55 1,669 words Chapter 56 1,578 words Chapter 57 1,564 words Chapter 58 1,660 words Chapter 59 1,694 words Chapter 60 1,415 words Chapter 61 1,653 words Chapter 62 1,690 words Chapter 63 1,685 words Chapter 64 1,618 words Chapter 65 1,652 words Chapter 66 1,674 words Chapter 67 1,687 words Chapter 68 1,699 words Chapter 69 1,644 words Chapter 70 1,698 words Chapter 71 1,691 words Chapter 72 1,671 words Chapter 73 1,689 words Chapter 74 1,679 words Chapter 75 1,677 words Chapter 76 1,678 words Chapter 77 1,655 words Chapter 78 1,683 words Chapter 79 1,696 words Chapter 80 1,700 words Chapter 81 1,694 words Chapter 82 1,697 words Chapter 83 1,692 words Chapter 84 1,668 words Chapter 85 1,554 words Chapter 86 1,666 words Chapter 87 1,677 words Chapter 88 1,694 words Chapter 89 1,667 words Chapter 90 1,700 words Chapter 91 1,670 words Chapter 92 1,670 words Chapter 93 1,655 words Chapter 94 1,640 words Chapter 95 1,607 words Chapter 96 1,668 words Chapter 97 1,659 words Chapter 98 1,689 words Chapter 99 1,675 words Chapter 100 1,614 words Chapter 101 1,610 words Chapter 102 1,700 words Chapter 103 1,683 words Chapter 104 1,657 words Chapter 105 1,698 words Chapter 106 1,700 words Chapter 107 1,695 words Chapter 108 Reading now Chapter 109 1,683 words Chapter 110 1,699 words Chapter 111 1,699 words Chapter 112 1,641 words Chapter 113 1,696 words Chapter 114 1,626 words Chapter 115 1,695 words Chapter 116 1,691 words Chapter 117 1,698 words Chapter 118 1,645 words Chapter 119 1,673 words Chapter 120 1,691 words Chapter 121 1,635 words Chapter 122 1,694 words Chapter 123 1,689 words Chapter 124 1,688 words Chapter 125 1,673 words Chapter 126 1,692 words Chapter 127 1,686 words Chapter 128 1,697 words Chapter 129 1,660 words Chapter 130 1,691 words Chapter 131 1,674 words Chapter 132 1,670 words Chapter 133 1,693 words Chapter 134 1,691 words Chapter 135 1,687 words Chapter 136 1,672 words Chapter 137 1,691 words Chapter 138 1,657 words Chapter 139 1,687 words Chapter 140 1,650 words Chapter 141 1,695 words Chapter 142 1,607 words Chapter 143 1,699 words Chapter 144 1,676 words Chapter 145 1,698 words Chapter 146 1,684 words Chapter 147 1,664 words Chapter 148 1,696 words Chapter 149 1,674 words Chapter 150 1,680 words Chapter 151 1,697 words Chapter 152 1,628 words Chapter 153 1,618 words Chapter 154 1,688 words Chapter 155 1,664 words Chapter 156 1,692 words Chapter 157 1,584 words Chapter 158 1,644 words Chapter 159 1,646 words Chapter 160 1,618 words Chapter 161 1,797 words

Kwana biyu kenan Zaytoonah ba ta sake yiwa Justice girki ba, duk abinda za ta yi dai dai cikinta ta ke yi ba ta ma zama a wajen dining É—in.

Rashin ganin ta da bai yi ba kwana biyu ya dame shi hakan ya sa ya nufi É—akin ta yau da Asuba tun ma kafin ya wuce masallaci.
Raka'atanil fajri ya samu tana yi lokacin da ya shigo wanda hakan ya burge shi.

Da ta idar sai da ta yi addu'o'in ta kafin ta juyo ta kalle shi, yana zaune bakin gado jikinsa sanye da farar jallabiya.

"Barka da Asuba" ta faÉ—a bayan ta kauda kan ta gefe.

"Princess na yi laifi ne ki ke gudu na?"

"Ranka shi daÉ—e gudun ka kuma, ai ban isa ba"

"To minene matsalar?"

Ta yi shiru tana kallon zanen masallacin ka'aba da ke jikin darduman ta.

"Ni ne na miki laifi ko kuma 'ya'yan ki?"

Still ba ta bashi amsa ba dan ba ta san mi za ta faÉ—a ba.

Ganin ta yi shiru ya sa shi cewa "ba zan takura mi ki ba amma ina so ki sani zan fi jin daÉ—i idan za ki sake jiki da ni. Mu ci abinci tare as a family, a zauna a yi hira ayi raya. Infact ina so Yaran nan su É—auke ki a matsayin uwa ba Anty ba"

"Daga baya kenan" Zaytoonah ta faÉ—a a ran ta.

"Idan kina zaman ɗaki haka ba za su saba da ke ba. Na yadda yaran suna da sakalci saboda hannun da na riƙe su da shi tun bayan rasuwan mahaifiyar su amma duk da haka idan kin ga sun yi ba daidai ba ki kwaɓe su sannan ki ja su a jiki saboda yanzu sun zama na ki. Ina neman alfarma ɗaya a wajen ki"

Ta É—an kalleshi sannan ta sauke idon ta

"Ko da once in a while ne a dinga sammani girki, saboda matar tawa gwana ce wajen sarrafa abinci Masha Allah"

Ko ya aka yi maganar yai tasiri a ranta har ta yi murmushi oho.

Ya miƙe tsaye ya ce " barin wuce masallaci kar na rasa jam'i"

Daga lokacin kuma Zaytoonah ta koma riƙe gidan ta. Tuni ta dakatar da Atika wajen yiwa Justice girki ta ce za ta dinga yi ma sa ita ta dinga yin na sauran ma su aikin gidan.
Kusan kullum sai Raziya ta yi ƙorafi a kan girkin Zaytoonah. Ba ta wani tanka ma ta dan ɓata lokaci kawai za ta yi. Sauran yaran na ci babu complain amma ita kullum bakin ta ba ya shiru, idan ta yi magana Justice ba zai ma ta faɗa ba sai dai kawai ya ce ta je ta karɓi abinci a wajen Atika. Daga baya ma sai ya koma Raziya abincin Atika ta ke ci dan dole, ta so Justice ya dakatar da Zaytoonah ta dena girki amma bai yi hakan ba.

A sati na biyu da zuwan ta gidan ne Maman Tope ta karɓi aiki. Matar tana da sauƙin kai sosai. Professional Chef ce da ta yi aiki a manyan manyan hotels na Abuja, lokacin da mijin ta ya rasu ya barta da yara biyar komai ya zo ya dagule ma ta. Abubuwa su ka ma ta yawa har ta kai ma ta rasa aikin ta. Aikin da ta zo ta samu daga baya albashin bai ma ta ba ga kuma aikin yana cinye ma ta lokaci.

A lokacin da Justice ya dawo Abuja da aiki yana neman mai abinci saboda cook ɗin da aka bashi daga office namiji ne shi kuma baya son namiji saboda yaran sa, shine Hajiya Ghazala ta nemo ma sa Maman Tope. Da farko ita ta nemo ma sa Atika amma ya complain ɗin gaskiya bai gane da aikin ta ba, ya so ma ya sallameta ne sai Hajia Ghazalan ta ce ma sa ai Atikan na buƙatan aikin saboda kula da 'ya'yan ta. Da tana aiki ne a gidan wani Alhaji to sai ya zo ya rasu aka sallami ma su aikin gidan gaba ɗaya. Jin wannan bayani ya sa ya haƙura ya barta.

Zuwan Maman Tope gidan ne ta koyawa Atika wasu girke- girken zamani da na gargajiya musamman abincin mutanen Kudu. Da ke ita ta koyi girki ne professionally har da certificate kuma aikin abincin hotel da ta yi na kusan shekaru shabakwai ya sa tanada experience É—in girki sosai.

Maman Tope a Gwagwalada ta ke zaune da yaran ta. Idan ta zo ta yi 15 days a gidan Justice sai ta koma chan ta huta na 15days inda ta ke ɗan taɓa ƙananun sana'a dan tana ƙoƙarin buɗe ƙaramin restaurant ɗin ta ne nan da shekara mai zuwa, idan kuɗin sun taru.
Atika kuwa a Mararraba ta ke...

***

"Ahmad idon ka kenan?"
Zaytoonah ta faɗa tana karɓan jakar Justice da ke hannun Ahmad ɗin.

"Anty Zaytoonah ai na zo hidimar biki ba mu haÉ—u ba ne saboda jama'a sun yi yawa"

Hararan sa ta yi tana faÉ—in "Anty kuma?" ta bi bayan Justice da tuni ya haura stairs É—in. Shi kuwa Ahmad sai ya kama dariya.

"Sannu da dawowa" ta faɗa yayinda ta ke ajiye ma sa jakar a saman kujerar da ya ke zama yayi aiki. Ɗakin ba baƙon ta bane dan kullum tana shiga ta gyara ma sa.

"Mun same ku lafiya"
Lafiya ta amsa a taƙaice yayinda ta sunkuyar da kan ta ƙasa ganin yana ɓalle button ɗin shirt ɗin sa.

"Za ku ci abinci yanzu ne ko sai kun yi sallah?"

"Ki tambayi Ahmad ko zai ci yanzu amma ni kam sai na yi sallah"
Ta amsa da toh ta fita daga É—akin.

Komawa wajen Ahmad ta yi ta zauna yana zuba ma ta taɗi yana ba ta labarin wani case mai sarƙaƙiya da Justice ya haɗa shi da shi.

"Anty Zaytoonah wai yaushe za ki dawo office ne?, mun yi kewar ki fa"

"Rufa min asiri Ahmad ko zan yi aiki ba yanzu ba. Ka san tashin hankalin da na shiga a case É—in Chief Udodiri"

"Habawa! Ke da ki ke da Justice a kusa wani tsoro za ki ji"

Dai dai nan su ka ji saukowar Justice ɗin dan haka kowa yai gum da bakin sa. Lokacin da ya sauko ya ce za su wuce masallaci Ahmad ya miƙe yana faɗin sai mun dawo Anty.

Al'adar Justice ne idan ya fita sallar magariba a masallacin ya ke zama yai ta azkar har sai anyi Isha kafin ya dawo gida. Indai ya dawo kafin nan to akwai dalili mai girma.

Bayan sun dawo daga sallar ne aka haɗu a dinning ana cin abinci. Ahmad sai santin girkin ya ke yi. Raziya haushi har wuya, ba abin da ta tsana irin ta buɗe ido ta ga Zaytoonah a gidan su. Ga uwa uba ƙannenta da duk faɗan da ta ke yi mu su akan Zaytoonan sun ƙi sauraranta. Ita dai Falaq ba ta wani shiga harkan Zaytoonah saboda dama haka halittar ta ya ke ba ta cika sake jiki da mutane ba amma Suhailah kam cikin ƙanƙanin lokaci ta sake da Zaytoonah, har ɗakin ta tana shiga ta ce za ta yi kallo ko kuma ta ce Zaytoonan ta ma ta wanka.

"Uncle na ce za ka bar Anty ta dawo office ko?" Ahmad ya faÉ—i maganar hankali kwance.

"Insha Allah" ya faÉ—a tareda cigaba da cin abinci.
Zaytoonah ta kalli Ahmad tana jijjiga kai alamar za ka gamu da ni.

Ahmad bai bar gidan na su ba sai kusan ƙarfe goma saura. Da ake akwai surutu kafin ka ce me lokaci ya ja, sai da Justice ya ce zai je ya kwanta ne ma ya iya yin shiru yana faɗin shima bari ya wuce gida kar dare yai sosai...

Washegari kuma Muhsina ta kira ta akan za ta kawo ma ta ziyara. Zaytoonah ta ji daɗin hakan dan tun a gidan rasuwa rabon ta da Muhsinar. Ƙarfe shabiyu saura na rana su ka iso gidan ita da Azma. Tuni dama Zaytoonah ta mu su girki. Sai da aka ɗan taɓa hira kafin ta kawo mu su abinci, su ka haɗu dukkan su a tsakiyar falo suna ci. Muhsinar ce ta ce ta kawo mu su abincin nan dan yanzu ba ta iya cin abinci a dinning. Zaytoonah ta fara tsokanar ta akan ko dai ciki gareta.

"Za ki sani ai. Kema na ki na nan tafe ƙila naki abinci sai idan Galadima ya ba ki a baki za ki iya ci"
Zaytoonah ta kai ma ta dundu yayinda Azma ke ta dariyan su.

"Yo ƙarya na yi ne? Waya sani ko yanzu ma junior yarima na jina"

"Za ki yi ki bari ai, kin gannin nan ni kaɗai na ke wasu fa?. Ashe dai zuwan Abban su Habib saƙo mai mahimmanci ya zo turawa" Zaytoonah ta yi maganar tana dariya ita da Azma ita kuma Muhsinar na faɗin " oho dai tunda saƙon ya je inda ya kamata"...

Haka dai su ka sha hiran su, a ƙalla sun kai awa uku a gidan kafin su ka fara shirin tafiya, da za su tafi Zaytoonah ta mu su jagora zuwa ɗakin ta. Sun yaba ɗakin na ta saboda komai na zamani ne aka saka a wajen.

"Ya 'yan matan na ki?, fatan ba wata matsala?"
Muhsinah ta faÉ—a lokacin da su ke saukowa.

"Babbar na bani ciwon kai wallahi, ina ga randa ta kai ni maƙura duka zan ma ta"

"Haba Zaytoonah, ai gara ki haɗata da uban ta, idan ki ka fara dukan yaran nan yanzu kowa kallon muguwa zai dinga yi miki. Yaran yanzu ai sai a hankali, na ka ma ya ka ƙare da su balle na wani"

"Abin na ta ne ya fara isa na Allah"

"Ki bita a hankali sai kiga nan gaba kaÉ—an kun zo kun saba"

"Allah ya sa haka"...

***

Yau Asabat yaran na gida sun dawo daga Islamiyyar safe kenan sun baje a falo suna kallo ko uniform ba su cire ba.

End of Chapter 108Continue to the next chapter or choose another story below.

More Hausa novels

Browse all books →
Previous Login to Save Next